Showing 129001 words to 132000 words out of 288773 words
Chapter 44 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
baka jin komai sai hayaniyar mutane, a hankali khaleefa yaga mutane sun fara rabe mishi gida bibiyu zuwa uku uku, sai ya taka a nutse cikin takunshi na nutsuwa da nuna cikakkiyar kamala ya dafa kafad'ar Ahmad saboda wata hajijiya da yaji anayi dashi, a take kanshi ya fara juya mishi, sai Ahmad ya janye shi gefe yana tambayar shi abinda yake faruwa. Bai iya furta mishi komai ba idanun shi sukayi luuuuh!.....
A lokacin malam yana can yana gaisawa da jama'ah, akazo aka sanar dashi ga ango can ya yanke jiki ya fad'i k'asa baya numfashi.......
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...." Malam ya furta yana dafe kanshi da hannuwan shi bibbiyu. A ranshi yace, "Allah yasa ba abinda ya gani a mafarkin shi bane yau yake shirin tabbata a zahiri......"
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page thirty six3️⃣6️⃣
Duk hankalin mutane ya fara kaiwa inda khaleefa yake rungume jikin Ahmad ba numfashi, yayinda Ahmad d'in yake ta faman kiran sunan shi da tunanin abinda ya faru dashi bayan lafiyar Allah suka futo daga gida har zuwa yanzu da aka d'aura auren nan yanayin shi sam bai nuna bashi da lafiya ba.
Malam ma yazo gurin yana tambayar su meya faru dashi? Hankali tashe, ba wanda ya iya amsa mishi sai wata murya daga ta bayansu da tace, "meya faru da d'an uwana?..... ".
Wannan murya ita ta ankarar dasu malam waye rik'e a hannun Ahmad, sai duk sukayi sak, Ahmad ya fara kallon kayan jikin shi da sam ba irin sune a jikin Khaleefa a lokacin da zasu futo ba, a nutse ya k'araso cikin matuk'ar tashin hankali ya janye d'an uwan nashi yana faman ambaton sunan shi da k'arfi, "Ayman! Ayman!! Ka tashi kada ka tafi ka barni Ayman,,,, bani da kowa bani da komai a wannan duniyar sai kai......". Ya k'arasa fad'a had'e da rintse idanun shi, yana jin yadda abu mai zafi da k'una yake d'iga cikin zuciyarshi.
Da kyar su Ahmad suka saka Ayman a mota akayi asibiti dashi. Don khaleefa ya rik'e shi tsam ya hana a tab'a shima.
***** A gidan su amarya raihana kuwa, innah tana shirin bud'e akwatunan lefe wata y'ar dattijuwa ta shigo gidan tana tsanyara gud'a kafun muryarta ta cika gidan gaba d'aya, "alhamdulillah! Yau dai alk'awarin Allah ya cika, Raihanatu ta zama matar aure, matar Abdallah khaleefa kan sadaki naira dubu d'ari biyu da mukullin mota sabuwa dal! Lakadan gasu a hannuna...".
Wannan magana ta katse hanzari da kuzarin su innah daga abinda suke shirin yi, umma salaha kuwa cikin wani irin mugun tashin hankali da d'imuwa ta futo tsakar gida tana maganar da batasan ma tanayi ba, tsabagen yadda zancen yayi mata dirar mikiya. "wallahi k'arya ne! K'arya akeyi wallahi!! Mu za'a rainawa hankali ace wai an d'aura mata aure da wani Abdallah, waye shi Abdallahn ma..... Wallahi k'arya ake alk'awarina bazai tab'a tashi a banza ba,,,, kamar yadda na fad'a raihana bata da miji indai ina numfashi a wannan duniyar.....".
Gaba d'aya mutanen gidan zuba mata ido sukayi suna kallonta cike da al'ajabi, shin wannan matar haukacewa tayi ne ko kuwa?
Ganin irin kallon da ummie da y'an uwanta suke binta dashi sai ta zura takalmanta bako waiwaye ta fuce daga gidan, zuciyarta taf da bak'in ciki da tashin hankalin yadda akayi raihana ta samu irin wannan mijin ta aura, bayan duk abinda ta dinga yi.
Y'arta ma jakarta ta d'auka da gyale ta saka takalmi cike da kunyar abinda uwarta ta aikata tabi bayanta.
Innah ce ta fara nad'e tabarmar kunya da hauka, gudun kada aga y'ar gaban goshinta tayi kuskure, duk da itama a ranta saida taji wani iri, amma sai bata nuna ba ko a fuska, "toh meye kuma gayyar na ayyeh aka zuba mana ido ana kallon mu,,,,, Ni bana son tsegumi da tsugudidin banza, kinga ziyada bani jakata ma kiga nabar musu gidan su, don in mukaci gaba da zama muma bamu san me za'ayi mana ba".
Ba wanda ya kula ta cikin mutanen da suke gurin, saima ci gaba da harkokin su da sukayi suna juya zantukan umma salahar a cikin ransu, yau har y'an tawagar tata masu zugata babu wanda yace mata ci kanki, don yau jikinsu ba k'aramin sanyi yayi ba, don ba don tayi da gaske ba, sai dai ta tafi ta barsu anan babu wanda zai biyota cikin su. Ziyada kam cewa tayi indai ta futa to fa ba dai gidan umma salaha ba sai dai nata gidan, don ita ba zata bi bayanta ba ace duk tare suka dinga k'ulle k'ullen yadda aka hana yarinya aure.
Haka dai Inna ta ciccirgud'a ta fuce daga gidan, su kuma suka mara mata baya.
Ummie tasa aka bisu da kayan abincin su cooler guda can. Sai dai ba Inna kad'ai ba kowa a gidan bakinshi d'auke yake da alamun tambaya, so suke suji dama tasan da maganar sauyin ango da aka samu, ko kuwa abun ya wanzu a iya yau ne. Duk da ummie kanta ta fahimci yadda kansu yake a kulle amma batayi yink'urin yi musu bayanin komai ba saboda mutane, tafi son sai komai ya lafa, amarya ta tafi tukun ta warware musu zare da abawa.
A sitting room raihana tana zaune taji shelar da matar nan tayi, duk jikinta ya sake yin sanyi ba abinda yake tsattsafo mata sai gumi tako wacce kafar gashi dake jikinta, yanzu fa shikenan ta zama matar khaleefa..... Matar yarjejeniya da zata tafi nan da adadin wasu shekaru ta dawo gida da sunan aurenta ya mutu... Anya kuwa ta yiwa kanta adalci data aikata haka ga iyayenta da y'an uwanta da suke murnar ta samu miji zata tafi ta rayu kamar kowacce mace?, toh amma yata iya ya zamo mata dole ne ba yadda zatayi, auren khaleefa shine kad'ai hanyar tsiranta.....
Khausar ce ta shigo d'akin kamar an wurgo ta, ta zauna kusa da raihana tana tambayarta, "kinsan kuwa da wanda aka d'aura miki aure auntie raihana?".
Ameena da zee har suna had'a baki wajen fad'in, "Ni kaina abinda nake son tambayarta kenan".
Sai ta d'ago kanta wasu zafafan hawaye suka soma silmiyowa kan kuncinta suna sauka k'asa, ta kalle su d'aya bayan d'aya da raunatacciyar muryarta tace, "na sani". Basu sake ce mata komai ba, sai tausayinta da sukaji ya tsirga musu, har khausar data tsura mata ido tana kallonta kuwa.
A haka Salma ta shigo itama donta sanar da ita abinda ya faru wajen d'aurin aure, amma yanayin data gani kad'ai a tare da raihanan ya tabbatar mata da tasan komai. Sai ta nemi guri d'aya itama ta zauna ta zabga uban tagumi, a ranta tana jin haushin yadda su ummie zasu yiwa yayar tasu auren dole irin wannan, don kawai anga tana samun matsala ta wajen aurenta, ana saka rana ana warwarewa, sai a aura mata kowanne irin miji ma, haba shiyasa tunda tazo taga yanayin raihanan a hargitse, kuma daga ita har ummie suka k'i fad'a mata gaskiya, da anyi magana suce bata jin dad'i ne. (Su duk a zaton su salma auren dole aka yiwa raihana).
Babbar Yar su ummie auntie Aysha da kanta ta kawo musu abinci da lemuka, ta kama hannun raihana ta futo da ita daga cikin su saboda sai kuka take. Su kuma duk sun zuba mata ido ba mai iya ko rarrashin ta, madadin haka ma sai wasu cikin su suka soma tayata kukan.
A d'akin ummie aka ajiyeta, auntie hajara ta had'a mata tea mai zafi me kauri don an fad'a mata ko karya kumallo batayi ba, da kyar ta shanye shayin, bata kyale taba saida taci abinci rabin k'aramin plate. Jin jikinta da zafi, saita bata paracetamol tasha ta d'an kwanta ta huta.
Aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, baccin daya d'auke ta har kusan five hours kafun ta farka, ya hanata sanin abinda ake ciki a gidan dama anguwar gaba d'aya. Lokacin data farka fuskarta ta wanke ta rama sallolin da suka huceta a ranar.
Tana idar da sallar auntie hajara na shigowa, "yauwa dama zuwa nayi naga ko kin tashi, ummie sai fad'a take wai a tashe ki kiyi sallah wanne irin bacci ne haka". Murmushi tayi ta nad'e sallayar da take kai ta ajiyeta a gefe. Ruwa ta had'a mata na zafi a bathroom d'in ummie ta shiga wanka, koda ta futo wata atamfa mai kyau da tsada ta bata ta sauya, d'inkin doguwar riga dai dai jikinta daya zauna mata dass! Da mayafi wadatacce da takalmi da jaka duk y'an gida d'aya. Tayi kyau matuk'a gaya duk daba tarin kwalliya tayi a fuskarta ba.
Lokacin data futo tsakar gidan cike da y'an biki, ta durk'usa tana gaisawa dasu rukuni rukuni, kowanne a cikin su sai Allah ya sanya alkhairy yake mata da addu'ar fatan alkhairy.
Su xee suna zaune inda ta barsu d'azu, duk sunyi kwalliya cikin ankon atamfa sai shafta ake sha, musamman da suka had'u da raheela.
"Woww! Masha Allah! Amma fa kinyi kyau raihana, kin futo a amaryarki zam". Fatima ce me yin wannan maganar.
D'an harararta raihana tayi tace, "nifa bana son sharri". Aikuwa suka kyakyale mata da dariya kusan su duka, raheela har tana kwaikwayon salon yadda tayi maganar, sake had'e fuska tayi ita ala dole tayi fushi. Suka k'ara samun nayi, har raheela na fad'a mata wai ba sune angon ba irin wannan shagwob'a haka....
Ganin suna neman tuburata sai tayi banza dasu, sai da suka gama zolayarta son ran su sannan suka fara d'aukan pic da ita. Daga nan sukaci gaba da hirar su har zuwa lokacin da Abba ya buk'aci ganinta.
Yana zaune kan kujera, ta durk'usa kusa da k'afar shi kanta a k'asa tace, "Abba sannu da hutawa". Da kulawa yace, "yauwa sannu raihanatu, ya hidima ya taro, koda yake ance mun ma d'azu bakya jin dad'i....".
"Eh amma yanzu jikin da sauk'i".
Yace "Toh Allah ya k'ara sauk'i". Tace, "ameen".
Abba yayi shiru kafun yaci gaba da maganar shi, "toh raihana kinga dai yadda rayuwar y'a mace take, gaki yau kema zaki tafi gidan auren ki, nan da k'ank'anin lokaci ki zama matar gida ki haifi y'ay'an ki da zaki tarbiyyantar, babban abinda zan miki misali dashi shine rayuwar mahaifiyarki, halayenta, dama yadda take take mu'amulantar mutane, ko halayenta kad'ai nace kiyi koyi dasu a gidan aurenki zaki zauna lafiya da uwar mijin ki da mijin ki,,, da muke yiwa kyakkyawan zaton basu da wata matsala, abu na gaba hak'uri, don hak'uri shine babban makamin da zaki rik'a ki yak'i kowa masoyi da mik'iyi, misali na biyu hallau dai da mahaifiyar ki zan k'ara yi miki, nasan kina sane da yadda zamantakewarta ta kasance da mahaifiyata da wasu cikin y'an uwana, basa sonta basa k'aunarta har matar yayana abubakar, amma hakan bai tab'a hanata kyautata musu ba iya iyawarta, tasa k'afa ta shure duk wani sharri ko k'ulli da zasuyi mata, a wasu lokutan har sai inji haushin su ita bata jiba, kuma ko nace bazan yi musu abu ba in suka k'ure ni sai tasan yadda tayi ta sani nayi musu ko bana so, ba tare data duba komai da sukeyi mata ba na rashin kyautatawa. Alhamdulillah da Allah yaso saka mata saita rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin da babu wanda ya samu irin shi cikin su sai ziyada, itama saboda tana rayuwarta lafiyar Allah ne". Ajiyar zuciya ya sauke me tsayi kafun yaci gaba da maganar shi, "kamar yadda na fad'a rayuwa da kika ganta gaba d'ayan ta y'ar hak'uri ce, yi nayi, bari na bari, kiyi k'ok'arin rik'o da addinin ki da irin tarbiyyar da muka baki, a k'arshe Ina yi miki fatan zama lafiya a gidan auren ki, Allah yasa ki shiga a sa'a, yasa mutuwace zata raba ku.... Tashi kije Allah yayi miki albarka ya bada zuri'a dayyiba".
Tunda ya fara yi mata magana jikinta yayi lakwas, banda kuka ba abinda takeyi har ya dire, duk daya sallameta amma saita kasa tashi saboda sanyi da duk gabban jikinta sukayi. Shi kanshi Abba a yau ji yake kamar yayi mata kuka saboda matuk'ar tausayinta da yake ji a cikin ranshi. Shiyasa bai iya ce mata komai ba har ummie ta turo k'ofar d'akin ta shigo, da sauri ta tafi ta rungume ummien tana kuka, ita kanta ummie idonta hawaye ya tara fal, sannu a hankali hawayen ya soma gangarowa bisa kuncinta, sai tasa tafin hannunta ta share hawayen da sauri ta janye ta jikinta a sanyaye, Abba da yake kallonsu ta kalla tace, "sunzo d'aukar amarya, ance kuma surayyahn har yanzu tana asibiti kan marar lafiyar nan, in dasun hak'ura ai da sun bari a kaita daga baya....".
Da sauri Abba yace, "kull! Kar ki k'ara ma irin wannan maganar, abokin angon ya tabbatar mun ta dawo gida, angon da malam suna tare dasu, saboda haka insha Allah raihana yau a gidanta zata kwana....".
Ummie bata sake cewa komai ba ta kamo hannun raihana har zuwa ga ummaanta da wadda tazo tafiya da amarya, (wata aminiyar auntie doctor seera sai iya).
"Allah ya kare ki daga dukkan sharri raihana.... Ya baki zaman lafiya a gidan auren ki... Fatan alkhairy".
Iya abinda ummie ta fad'a mata kenan sukayi gaba da ita, tana kuka tana komai amma ba'a kyaleta ba har zuwa cikin motar da za'a d'auki amarya.
_Wasu awanni da suka gabata can baya_👈🏻
Auntie tana zaune gidan iya suna tattauna yadda zasuyi taron su gaba d'aya ita da mutanen data gayyata da wanda iya ma ta gayyata a nan gidan iyan, tayi kwalliyarta yauma cikin shadda milk da aka shiryawa lafiyayyen aiki mai kyau da tsari, hallau doguwar riga akayi mata amma ta tsaya cak a jikinta, sauk'ak'k'en d'auri tayi wanda ya bayyana lallausan gashinta ta k'asan dankwalinta, gaba d'aya hankalinta yana kan iya da take bata labarin zuwan Ayman gidan, da yadda ya kwana ya yini baya iya cin abinci sai ruwan tea ko kunu inta takura, gaba d'aya yanayin shi ya nuna bashi da lafiya kuma yana jin jiki, shiru auntie tayi cike da tunanin abinda yake damun shi haka, tunanin daba tun yau ta fara shiba, ita a tak'aice ma jiya bata ankara da bai kwana a gidan ba, duk da da safe tayi mamaki da taga har rana baizo gaisheta ba kamar yadda ya saba. Koda zasu futo dasu doctor seera a motar seeran tare da akwatunan lefe dasu malam zasu kai ta d'auka yana tare da tawagar angwaye. Ashe shi ya baro musu gidan ma tuni.
Tana cikin wad'annan y'an tunane tunanen mama haleema ta shigo, itama sanye da kaya masu kyau, kusa da iya ta durk'usa ta sanar dasu ga wani can ya yanke jiki ya fad'i wajen d'aurin aure ana zaton ma ko khaleefa ne.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel, Allahumma ajirni fil musibati waklifni khairan minha.....". Ta fad'a bayan ta dafe goshinta da hannunta. Sai kuma ta yink'ura ta mik'e kamar wadda aka zabura, ta yafa gyalenta a gefen kafad'ar ta da jakarta tace wa iya "ya kamata naje....". Yadda iya taga duk ta rud'e har jikinta yana rawa, sai ta fara yi mata naseeha kan ta nutsu insha Allah ba wani abun tashin hankali bane. Gyad'awa iya kai kurum tayi ta tambayi mama haleema, "yaushe kika ji labarin".
Mama haleema tace, "Ni yanzu dana futa ne naji wasu maza suna tattaunawa, amma ance tun d'azu nema abun ya faru bayan an d'aura auree, malam da wasu cikin abokan shima duk suna can asibitin da aka kaishi....".
Bata ce komai ba sai hucewa da tayi gurin su doctor seera, ta karb'i mukullin motarta ta kira malam don taji wane asibitin ne, sai dai harta katse bai d'aga ba, hakan ya sake tashin hankalinta matuk'a har idanunta suka fara sauya launi, ta k'ara kiran layin nashi nan ma shiru, ganin ba zata samu malam ba saita nemo no Ahmad, shima har yayi ring ya gama bai d'aga ba. Sai tunaninta ya fara bata ko ya mutu nema suke b'oye mata, hakan tasa ta kira layin shi khaleefan.
A lokacin yana jingine jikin bango ya had'a kanshi da bangon Emergencyn hankalin shi a matuk'ar tashe saboda tunda suka shiga dashi ciki ba wani cikakken bayani, Saida kiran ya kusa katsewa ya d'aga, "a wane asibitin kuke?" Shine tambayar data yi mishi kai tsaye, ya fad'a mata sunan asibitin da b'arin da suke.
Ba tare da b'ata lokaci ba ta shiga motar doctor seera ta nufi asibitin a 360.
Ko bayan futar ta fad'a sosai iya ta yiwa mama haleema kan maganar da tazo ta fad'a mata, yanzu gashi bata nutsuwarta amma a haka