Showing 264001 words to 267000 words out of 288773 words

Chapter 89 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1046

da suka cika idon shi.
Shima Suraj ta b'angaren shi yana gama wayar ya had'a kanshi da babban glass windown da yake tsaye kusa dashi.
Khaleefa daya k'araso gurin yaja tunga ya tsaya yana kallon shi cike da tausayawa, magana yazo suyi amma ganin a yanayin da yake saiya fasa ya juya kawai ya bar gurin.

****Ta b'angaren Raihana bayan sun idar da sallah sunci abinci ammie take tambayarta, "sai kika ga mutumin da kike kaiwa abinci matsayin mahaifin ku ko?, Bayan nace miki d'an uwan shine bashi ba".
Murmushi raihana tayi tace, "na fahimce ki ammie kin tsara komai ne daki daki bada sanin kowa ba".
Ammie tace, "hakane! Saboda a lokacin bana son shida khaleefa wani yaga wani, don ba zaiyi abinda ya kaishi ba, amma yanzu Masha Allah Alhamdulillah tunda komai yana tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali bada gaggawa ba".
"Hakane kam sai hamdala sun karb'i mahaifin su ba tare da wata matsala ba".
Sun d'an ci gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da ta futa suka zamana daga ita sai suhaana, sai a lokacin raihana ta karkata akalarta rankatakaf gare ta tana tambayarta labarin soyayyarta, "kada ki damu zaki ji labarin komai sai dai ba yanzu ba please".
Raihana da take kallonta tace, "ayyah kada ki damu sannan kiyi hak'uri na dame ki da son jin abinda baki shirya futar dashi ba yanzu ko".
"Ba haka bane, abune da bana son tuna shi sam shiyasa amma insha Allah bada jimawa ba zan baki labarin komai".
"Kada ki damu Allah yasa mu dace dear".
"Ameen ya Allah! Sai dai nima akwai abinda nake son tambayarki idan ba zaki damu ba".
"Ko kad'an fad'i tambayar ki direct".
"Auren ki da mijin ki..... Ina nufin taya kuka had'u soyayyah ta fara tsakanin ku har ta kai ku ga aure...?".
Shiru raihana tayi don ta tuna mata abubuwa da yawan gaske hadda wanda hankalinta suke kaucewa daga kansu.
"Ya dai? Na dawo miki da zuciyarki d'anya ko?"
Raihana ta girgiza kai, "a'a kawai na tafi tunanin wani shud'ad'd'en al'amari ne, auren mu ba kamar kowanne aure yazo ba, a tak'aice had'uwar mu da kwana biyar aka d'aura mana aure".
Suhaana aka ta d'ora hannunta tace, "wayyoh taya soyayyah ta shige ku cikin kwana biyar kacal da had'uwa".
A wannan karon murmushi raihana tayi tace, "kuma da yake soyayyah ta shallake duk zato da tunanin mai tunani...... Abinda yafi haka ma yana faruwa, baki jiba akace inda so da yak'i....".
Sai duk sukayi dariya, daga nan suka ci gaba da tattaunawa har zuwa inda dare yayi suka kwanta bacci, suhaana nata mata tsiyar ta kwanta bata ji daga mijinta ba anya ta yiwa kanta adalci kuwa?.

****Kamar yadda Ayman ya bada shawara haka akayi, Suraj ya shirya tafiya a private jet d'inshi, shida khaleefa da raihana zasu tafi, sai doctor andal da momma data tubure sai anyi tafiyar da ita zasu biyo bayansu kwana d'aya bayan zuwan su.
A ranar da zasu tafi duka mutanen suka zama ready banda raihana da batasan ma ana yiba saida ammie take tambayar ya ta ganta bata shirya ba.
"Futa kuma zamuyi ammie?". Ta tambaya, sai a lokacin ammie ta gane ba suyi magana da khaleefa ba gaba d'aya gashi har sun shirya ita kawai suke jira. Sai bata fad'a mata abinda yake faruwa ba a yadda ta ganta shirye tsab tace taje mijinta na jiranta.
Ta yafa mayafinta wadatacce ta d'auki wayarta a hannu ta futa, a babban parlon gidan ta same su suna k'arasa sallama da mutanen gidan. Sai ta tsaya kawai tana mamakin inda zasu tafi kuma ga khaleefa da Abban shi rik'e da jakar kaya. Abune da yake matuk'ar yiwa raihana wahala har yanzu sabawa da mutanen gidan, duk lokacin da zata gansu sun had'u a guri irin haka saita diririce, su kuwa ba ruwan su sai haba haba suke da ita.
A tak'aice suka gama sallama da kowa suka futa, raihana ce ta karb'i jakar hannun Abban su khaleefa suka futa su biyun tana bin bayan su.
Ko a cikin jet d'in ma khaleefa na kusa da ita, ya kwantar da kanshi jikin kujerar da yake zaune, duk da idonshi a lumshe suke amma ita yake kallo ta k'asan ido, komai na yarinyar nan daban ne, yana son nutsuwarta da sassanyan kwalliyarta, komai tana yinshi bada zafi ba.
A hankali yasa hannun shi ya rik'o nata tattausan hannun, sai a lokacin ta juyo ta kalle shi, shima ya wara idonshi a kanta ya sakar mata murmushi mai kyau, had'e ranta tayi kad'an tayi k'asa da kanta tana kiciniyar kwace hannunta, sake fad'ad'a murmushin shi yayi ya tashi zaune da kyau yana ci gaba da kallonta, "Ashe zaki iya....". A dai dai lokacin Allah ya bata ikon kwace hannunta duka, sai tayi murmushi k'asa k'asa da muryarta kamar yadda yayi magana tace, "gashi kuwa ka gani". Wani murmushin ya sake yi har hak'oran shi saida suka bayyana.
Daga nan basu sake ce da juna komai ba har suka k'arasa, sai dai a d'an zaman da sukayi ya samu cikakkiyar nutsuwar daya rasa cikin kwanakin da suka gabata.
Sun sauka lafiya inda suka yada zango a guest house d'inshi da yake a......quarters, gida ne plat part biyu sai k'aton parking lot mai d'auke da motoci na alfarma biyu, duk yadda raihana taso d'auke kanta ga barin kallon tsaruwar gidan amma ta kasa, haka ta wara idanunta tana bin komai da kallo, har khaleefa ya shigo ya same ta, daga bayanta ya tsaya yace, "ya dai madame me kike kallo haka?".
"Gidan yayi kyau sosai Masha Allah".
Murmushi yayi shima yana yaba yadda aka tsara komai yace, "Masha Allah kam yayi kyau".
Sai a lokacin ta juya ta kalle shi, ya sakar mata murmushi had'e da kashe ido d'aya, ta juyar da kanta da sauri tana waige waigen neman Abba gudun kada ace yana parlon. Bata ganshi a gurin ba, saita k'arasa shiga khaleefa na take mata baya har cikin tsakiyar parlon, a lokacin ta fahimci k'urar da muhallin yayi, hakan yasa tabar gurin tana neman inda zata ga mopper ko guntun towel haka.... Khaleefa kam jingina yayi da bango bayan ya shafo k'urar parlon da d'an yatsar shi ya gani. A harabar gidan ta samo dangin su broom, burget, mopper da kyallen da zatayi amfani dasu wajen tsabtace d'akin. Yana nan tsaye ta dawo ta nad'e gyalenta a jikinta ta fara share gurin, ganin tana aikin sai ya k'araso yana kallon yadda take yin komai. Saida ta gama sharewa zatayi mopping ya hana ta, murmushi kawai tayi a lokacin da taga yadda ya zage yana goge k'asan gurin da duka k'arfin shi. Dakatawa yayi yana tambayarta, "meye abun dariyar kuma?". Raihana tana gumtse bakinta tace, "ba komai sannu da aiki". Ya sake had'e girar sama data k'asa yace, "yauwa"
Daga nan suka ci gaba da aikin su. Ko zuwa lokacin da Suraj ya futo sun kusan gama gyare arean da saitin kujerun parlon suke, da hanzari ya k'arasa futowa yana fad'in, "a'a kubar aikin nan haka raihanatu, na nemi layin mai kula da gidan ne ban samu ba da tuni ya k'araso da masu aiki sun gyare ko'ina".
Raihana kanta a k'asa tace, "Abba bari mu k'arasa kawai tunda mun riga mun fara".
Zaiyi magana khaleefa ya rigashi da cewa, "please Abba ka bari mu samu ladan nan". Murmushi yayi cikin matuk'ar sake jin yaran a cikin zuciyarshi yace, "toh shikenan amma ku fara gyara inda zaku gabatar da sallah tukun, ga spare rooms nan zaku iya zab'ar wanda zaku zauna ciki.
Duba lokaci khaleefa yayi, sai ya ajiye burget d'in hannun shi don dama ya gama goge gurin.
D'aya daga bedrooms d'in parlon ya samu ya shiga sai dai shima komai yayi k'ura, alwala kawai ya d'auro yabi bayan mahaifin shi zuwa masjid, hakan yasa raihana shiga d'akin ta gyara shi tsab, bayan ta gama ta feshe ko'ina da room freshener.
Wani abun mamaki sai gashi kafun su dawo ta had'e ko'ina na gidan, sai dai fa kayanta sunyi bud'u bud'u da k'ura, tana son yin wanka amma ba sponge kuma ba kayan da zata sauya, gashi gaba d'aya a jagwale take da ammie ta fad'a mata tafiya zasuyi ba zata yarda ta biyo khaleefa ba shiri ba.
Gefen bed ta samu ta zauna tana danne danne a wayarta har Allah ya dawo dasu gidan, tunda suka shigo Abba yake shi mata albarka da yaba mata, a parlour suka zauna ya kunna wutar gidan, khaleefa zai zauna yayi saurin dakatar dashi, duba plate a kitchen ka kai mata abincin mana".
Baiyi musu ba wajan juyawa ya d'auko plate d'in da cokula, a lokacin raihana tana kwance rigingine idonta k'ur akan rufin d'akin tana tunanin yadda zatayi da kanta, gashi ta hargitse duk cikin d'akin babu komai don baya daga d'akin da yake gudanar da rayuwar shi inya zo garin bare taga wani abu mai kama da suttura. Abun duk ya taru ya yi mata yawa, tana jin turo k'ofar shi ta tashi da sauri tana kallon shi.
A kusa da ita ya k'arasa ya zauna ya fara kiciniyar juye abincin daya musu order har ya gama ya ajiye plate d'in tsakiyarsu yasa cokali ya fara ci bakin shi da basmala. Ganin ta tsaya kallon shi sai ya kalleta, "kici fa tun kafun ma na cinye shi duka?".
Kauda kanta tayi gefe don ita a yanzu bata abincin take ba, shima ajiye cokalin hannun shi yayi duk da irin yunwar da yake ji kuwa yace, "what the problem?".
K'asa ta sake yi da kanta tana wasa da fingers d'inta yayinda hawaye ya cika idanunta fal, dawowa yayi gabanta ya durk'usa ya kamo duka hannunta ya rik'e yana kallonta, kamar ya zugata aikuwa ta fara mishi kuka sosai, baice mata komai ba sai hankie da yasa ya fara share mata hawayen, "nifa ba kuka nace kiyi ba, ki fad'a mun matsalarki simple and fine".
Bata ce dashi komai ba sai dai ta saurara da kukan.
"Raihana". Ya kira sunanta da tattausan sauti, ta d'ago ta kalle shi, ya sake narke kwayar idon shi a nata, "baki da lafiya ne?". Ta girgiza mishi kai. "Nine nayi miki wani abu da bakya so ko?". Nan ma ta girgiza mishi kai, "toh menene matsalar?".
A shagwob'e tace, "ba kune kaida ammie baku fad'a mun tafiya zamuyi ba, kuka sa na shirya na taho ba kayan da zan sauya, ba soson wanka da sabulu, ba brush da.....". Sai tayi shiru lokaci d'aya kuma ta saci kallon shi, karaf suka had'a idanu taga irin shu'umin kallon da yake jifanta dashi.
"Dame kuma? Ai baki gama lissafe lissafen ba".
Tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta cikin jin nauyin shi, shi kam murmushi yayi kurum ya mik'e zaune yana kallonta ya koma mazaunin shi, "kinsan me? ki rubuta mun duk abinda kike buk'ata tunda dai kunyata kike ji sai naje nazo miki dasu gaba d'aya, amma fa in mun cinye abincin nan don ba zai yiwu kiyi ta zama da yunwa ba". Cikin jin dad'in yadda ya fahimce ta cikin sauk'i ta gyara zamanta sai dai tana shirin d'aukar 🥄 ya riga ta, ya d'ebo abincin ya nufi bakinta dashi, galala ta tsaya tana kallon shi, "oya take mana". Ya fad'a cikin bada umarni, mak'ale mishi kafad'a tayi "uhm uhm ni dai ka bani zanci da kaina".
Sai ya ajiye cokalin ya matsar da abincin yace ta taso taci inta rage zaici shi daga baya, arammiya kam sai gata ta mik'e zata huce shi, unexpected ta jita cikin jikin shi tayi zaman dirshan kan cinyar shi. Bai bata damar da zata iya mik'ewa ba kamar yadda taso don ya mata rik'o bana wasa ba, tun tana kiciniyar kwace kanta har dai a k'arshe ta hak'ura, "kin mik'a wuya kenan". Ya fad'i hakan cikin kunnenta da wani irin sauti na daban, ita kuwa cikin sabuwar shagwob'ar dani mariyatu bansan yaushe ta fara taba tace, "Kai ka sani in na staining kayan ka". Juyo da fuskarta yayi dai dai da tashi ya shafo cute lips d'inta da yatsar shi babba yace, "what! Yarinyar nan na fahimci so kike ki raina ni ko?".
Fari tayi da idanunta ta murgud'a mishi baki, yayi murmushi yana sake tsurawa fuskarta idanu, itama tsakiyar idanun shi take kallo tana amsar sak'on da yake aika mata ta cikin kwayar idanun ba tare data shirya ba. Sun shagala a kallon juna kafun yunwar cikin su ta dawo dasu hayyacin su, ta juyar da kanta khaleefa kuma ya d'auko plate d'in abincin ya sake nufar bakinta, wannan karon bata musa mishi ba ta fara karb'an abincin tana ci, yana ci yana bata har suka cinye tas. Sam ba susan adadin da suka ciba saida suka ga plate a gaban su suka farga. Raihana ta yink'ura ta tashi idonta akan inda ta zauna, khaleefa duk yana ankare da ita, zuwa yanzun ya gama fahimtar abinda take yiwa, da so yake sai yayi wanka ya futa amma fahimtar damuwarta yasa ya hak'ura.
A waya ta rubuta mishi duk wani abu da take buk'ata ya karb'a ya tafi ya kawo mata few minute bayan futar shi, don akwai k'aramin supermarket kusa dasu, taji dad'i sosai aikuwa ta shiga wanka ta gyara jikinta, inda aka samu matsala bata da kayan da zata sauya gashi ta cire kayanta gaba d'aya ta wanke su ta shanya har mayafin don ya b'ace da k'ura, sai wata tantal bateten riga daya had'o mata ita cikin kaya, rigar dukanta iya gwiwar k'afarta ce, gashi ta kama jikinta, gaba d'aya data kalli kanta a mirror sai taji kunyar futowa ya ganta a haka, haka ta yita tsayuwa cikin bathroom har saida ta tabbatar ta daina jin motsin shi gaba d'aya sannan ta futo. Da gudu gudu sauri sauri ta shige cikin bargo ta rufe har kanta ba don akwai sanyi a garin ba, a'a sai don b'oye shigar jikinta gare shi.
Ya jima a parlour tare da mahaifin shi suna hira kafun suyi sallama kowa yayi makwancin shi. Bayan ya gudanar da duk abinda yake yi kafun kwanciya bacci, ya tofe duk kusurwowin d'akin da addu'a ya kwanta ya tsurawa bayanta ido saboda ta juya mishi baya, kafun ya matsa ya rungume ta jikin shi tsam tsam yana kallon fuskarta hannun shi saman kanta yana shafa cikakkiyar sumar kanta data rubke a k'eyarta.
A haka wani irin bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi.

******* Washe garin ranar tunda wuri raihana da tayi wanka ta maida doguwar rigar data zo da ita gidan jikinta ta nemi kitchen, so tayi ta had'a musu abinda zasu ci sai dai babu komai na amfanin girki cikin gidan. Ta jima tsaye a kitchen d'in kafun ta juya da nufin futa, sai dai taku biyu yayi burki tana kallon shi da mamaki, mutumin data baro yana bacci. Sai tayi saurin ja baya ta russuna tana gaishe shi, ya amsa yana d'orawa da tambayarta me dame ake buk'ata na girki don yana son girkinta a duniya, ta mishi list ya tafi ya kawo ta fara had'a sauk'ak'k'en girki yana zaune yana kallonta, kunnuwan shi rufe da pod yana sauraren karatun al-qurani. A nan cikin kitchen tayi saving d'inshi don taga yunwa yake ji sosai, aikuwa ya fara da aika sandwich cikin bakin shi, ya lumshe ido ya bud'e yana sake gutsiran na biyu ya kai, a wannan karon kasa hak'uri yayi saida ya magantu, "dear abincin nan yayi dad'i sosai". Tayi murmushi kurum tana k'arasa had'awa Abba tray d'inshi. Tana karyawa a kitchen d'in khaleefa ya kaiwa Abba nashi break d'in har d'akin da yake.


***** Su uku na gani tsaye a gaban gidan, duka su ukun kowa addu'ar da tazo bakin shi yake karantawa, cike da tsoro da d'ari d'ari suka tura k'ofar gidan da suka tarar a bud'e suka shiga, khaleefa ya tambayi wani cikin masu aikin ko Auntie tana gida? Yaron ya fad'a mishi ta d'an futa sai dai kamar ba nesa ta tafi ba don tace ba zata huce minti goma ba.
Gyad'a kai khaleefa yayi ya musu jagora har cikin parlonta na sama inda suka samu mama haleema tana k'arasa aikinta. Ta tsaya da matuk'ar mamaki tana kallon su, raihana ce ta fara russunawa tana gaishe ta, ta amsa duka hankalinta naga mutumin da khaleefa ya shigo dashi, bayan duk sun zauna suka gaisa ta fara gabatar musu drink's da kayan snacks da basa rabo dasu a gidan, don yanzun haka aikin sukeyi auntien ta futa ta dawo. Khaleefa da kanshi ya zubawa mahaifin shi ruwa ya mik'a mishi, ya karb'a ya ajiye a gefe yana tambayar mama haleeman, "surayyah bata nan ne?". Mama haleema tace, "eh ta tafi kawo ketchup ne yanzun nan zata dawo?".
Shiru duk sukayi mama haleema ta futa raihana tabi bayanta da sauri, don yana mata kunya zama gata ga wannan bawan Allah, baya ga haka ma suna buk'atar sirri don batasan ya za'a kwashe da auntie ba in tazo taga mutumin da khaleefa ya kinkimo mata gida.

Suna tare da mama haleema a kitchen tana tambayarta ko mukullin part d'inta yana gurinta, mama haleema tace, "yana gurin doctor surayyah sai dai in ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login