Showing 219001 words to 222000 words out of 288773 words
Chapter 74 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
kan switch duhu ya mamaye ko'ina, da mugun sauri tabar jikin shi ta shige cikin bargon gaba d'ayan ta.
Murmushi yayi kurum ya juya ya futa da manyan taku.
Ko bayan ya koma d'akin shi kasa nutsuwa yayi,,,,, gaba d'aya tariyar mintunan da yayi a d'akinta yake yi tsigar jikin shi na tashi, duk ta inda ya juya sai yaji ta da motsinta ata jikin shi......
Itama yana futa bacci b'arawo bai bata damar yin kowanne tunani ba yayi gaba da ita.
*****Tun daga wannan ranar khaleefa ya kasa d'auke kanshi akanta, har Allah Allah yake ya tashi office yazo yayita kallon kwalliyarta da gilmawarta cikin gidan, duk wani abu daya kasance ba dabi'ar shiba ya maida shi dole cikin kwanakin, kamar yawan kallo shiga cikin harkokinta da son jin k'amshin jikinta ko muryarta, kawai yana zaune sai ya hau sata aiki kusa dashi mara dalili don kawai tazo kusa ya shak'i daddad'an k'amshin turaren ta. Duk yadda yaci burin ta bar mishi d'akin shi yayi yadda yake so yanzu kuma sai abun ya gundure shi, kullum dare ya kwanta sai yaji kewarta abun har ya zame mishi jiki.......
@@@@@ tsaye yake gabanta hannun shi duka hard'e a bayan shi yana fuskantar ta, "tsawon shekaru goma da d'oriya Ina zuwa gurin ki saboda neman y'ar k'aramar hujjar dazan rik'e ta kaini ga isa gare ta, sai dai a kullum amsarki d'aya ce ba'a ganta ba, baki ji labarin taje Sudan ba, duk da haka baki tab'a kirana da karan kanki ba sai wannan karon...... Andal tunda na shigo Germany nake jin matuk'ar kusanci da surayyah ata jinin jikina da zuciyata, tun a airport nake jin k'amshin ta har yanzu da nake tsaye gaban ki ban daina jiba..... Andal ki gaggauta fad'a mun tana Ina don nayi imanin tana tare dake a nan Germany?......".
Happie juma'at Mubarak toh all Muslim Ummah🕋
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page sixty two 6️⃣2️⃣
Mik'ewa tsaye tayi ta nuna mishi kujera da hannunta, "please sit Mr sooraj".
"I don't come here just to sit and listen to kowanne dogon labari.... Doctor andal Ina take? Ina surayyah Adam take?".
Zufa andal ta share da hankie, tana son mishi cikakken bayani kan abinda ta gani yadda zai fahimta sai dai babu alamun zai iya bada goyon baya, duk da itama bata da tabbaci hasashe ne kawai....
"Andal ki fad'a mun gaskiya nasan wannan kiran naki yana nufin abinda na dad'e ina mafarkin gani tsawon shekaru.....andal a shirye nake dana gyara kuskurena ta hanyar neman yafiyar surayyah da shirya kyakkyawar rayuwa ninkin wadda na shirya a baya Allah bai nufa ta tabbata ba..... Wallahi zan auri surayyah auren da zan iya k'arar da komai dana mallaka.....". Da sauri likita andal ta d'aga mishi hannu.
"Ban kira ka don na had'a ka da surayyah ko muyi ta tattaunawa akan labarin tsohuwar soyayyar kuba! Ni na kira kane saboda na damu da lafiyarka..... Kama daina mafarkin k'ara ganin fuskar da kaine silar b'acewarta ga kowa da kowa, ka shiga rayuwarta da sunan soyayyah ka lalata mata duk wani jin dad'i da walwalarta ka raba ta da familyn ta, ta yadda ta gwammaci ta kasance matacciya a idon su kan ta tunkare su..... sooraj indai baso kake ka k'ure k'arshen hak'urina da kawaicin da nake maka tsawon shekaru ba, to mubar wannan maganar, mu fuskanci abinda yake gaban mu. Na saka date na ranar da za'a yi maka surgeryn hannun ka da kace yana damun ka da ciwo, amma kafun nan kasan dole za'ayi hoton hannun don a gano inda matsalar take ko, to na nemo kane saboda naga baka da niyyar zuwa ga lokacin yana gab da k'urewa.... Wannan shine".
Yadda ta fara zancen cikin fad'a yasa sooraj yin shiru yana sauraronta, ko kad'an baya jin haushin duk wanda zaiga laifin shi kan b'acewar surayyah, da gasken gaske laifin shine sai dai ya aikata komai ne cikin fushi da k'iyayyar da baisan lokacin data shiga zuciyarshi har tayi gini mai tsayi a lokacin ba, duk daya shafe shekaru yana ganin doctor andal as his personal doctor bai tab'a jin kwarin gwiwa da kuma kusanci ga abinda yake nema a tare da ita ba kamar wannan lokacin,,, Soo zaiyi hak'uri da komai da zata mishi matuk'ar zai kai ga isa ga muradin shi.
Sai yaja sit ya zauna ya tallabe fuskarshi cikin tafin hannun shi. Doctor andal tayi banza dashi sai aikinta da take cikin system tamkar ba shine shahararren d'an kasuwa sooraj ba, kamar bata san da wanzuwar shima a gurin ba, dauriya kawai take amma zahirin gaskiya maganar surayyah ta taso mata da duk wani rauninta,,,,, akan soyayyar surayyah da sooraj ta k'aryata duk wata soyayyah a duniya, ta gane kowa zai iya shiga rigar soyayyah ya cimma mugun nufin shi ko k'udurin shi kan kowa,,,, ture computer tayi gefe ganin ta fara daina gane komai. Sam ba zata ba sooraj damar ganin hawayenta ba, hakan yasa ta shiga toilet da yake cikin office d'in. Ta jima a ciki kafun ta futo su k'arasa tattaunawa kan abinda ya kamata.
A yau andal ta sake tabbatar da duk wani zarginta sai dai zata tafi da komai a hankali ko Allah zaisa taga y'ar uwarta d'aya tamkar da million data b'ace musu tsawon shekaru.
*****Cikin satin gaba d'aya raihana bata samu zama ba, data dawo school zata tafi gidan yasmine, wani lokacin ma daga makarantar take hucewa saboda laulayi mai d'an karen wahala daya same ta, gashi gaba d'aya ta sake jikinta abinda ya k'ara futo da ciwon nata ma kenan.
Iya k'ok'ari raihana take wajen taimakawa yasmine d'in, wannan yasa ta k'ara matso da lokacin tashin ta a bacci kusa saboda ta gama aikace aikacenta kan lokaci tayi na yasmine d'in ma.
Tun ranar data rungume khaleefa a d'akinta har yanzu bata sake yadda sun had'u ba, da taji alamun futowarshi take guduwa d'akinta ta murza key,,, mafi yawan lokuta ma sai in ta k'ure take kaisu ga hakan amma a k'a'ida kafun ya futo ta shirya mishi karin kumallo ta matsa daga gurin. Ko rashin lafiyar yasmine daga bakin Ahmad ta nemi izinin shi ya lamunce mata ba wai ita da kanta ta tambaye shiba.
Yau data kama weekend raihana tana idar da sallar subh ta fara aikin had'a gidan azhkar ma a kitchen tayi, so take tunda bata da karatu ta had'a abinci irin wanda ta jima ba tayi ba a gidan.
Tana aikin girkinta tana hira da khausar k'anwarta da itama cikinta yayi girma haihuwa kusa, hira suke akan abinda ya shafi matsalolin matar kawunta da kakarta, kusan yanzu sun samawa maman su lafiya sai dai fa ta had'o su da Mom ziyada. Don yanzu ba b'oye b'oye take nuna bata tare dasu k'iri k'iri, rigima tayi tsamarin da har Abba saida ya shiga amma abu yak'i sasantuwa, hakan yasa daga Abba har Abba abubakar yin fushin zuciya su futa harkar umma salaha da ziyadan, hajiya innah kuwa dama ba tace komai ba saboda ta fara zargin salaha kan had'a makirci da yawa cikin al'amuran rayuwarsu, musamman tsakanin rukayyah da fashe fashen auren y'arta da aka dinga yi. Dama tun ranar da aka kawo lefe tayi wannan sub'utar bakin ta fara dasa mata alamar tambaya, tayi shiru ne kad'ai gudun kada ta kwaye mata baya gaban rukayya da danginta ta bad'a mata k'ura bayan kullum cikin goyon bayanta take akan komai da zata aiwatar.
Abu da yawa raihana takan ce Allah ya kyauta, ko Allah ya kiyaye har aka gama bata labarin ta d'ora da musu addu'ar sake samun shiriya da tsayawa gaskiya sai barin hassada, don duk ba komai ya had'a wannan wutar gabar tsakanin ummie da umma salaha ba sai hassada da kyashin yadda Abba yafi mijinta rufin asiri.
Sai gab da zata k'arasa kammala aikin sukayi sallama kowa ta katse kiran ta k'arasa tattare komai ta gyara gurin.
Tana shiga d'akinta tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga wrapper ta material data zauna a jikinta das, ta d'aura d'ankwalin material d'in ta turare jikinta da mayun turarukan da auntie ta had'a mata, tasa na d'akinta da parlour kamar kullum.
System d'inta ta d'auka ta fara operating d'inta a hankali don ba wani iya aiki tayi da ita sosai ba, tunda bata tab'a zama aji na musamman wai don ta koyi sarrafata ba.
Tana cikin danne dannen ta tuna da littafin nan, rabon data d'auko shi tun ranar da khaleefa ya shigo d'akinta, ta yink'ura da nufin mik'ewa aka fara buga k'ofarta, la shakka tasan khaleefa ne, hakan yasa ta yafa madaidaicin gyale ta bud'e k'ofar.
Yana tsaye bakin k'ofar sanye da dogon wando sky blue da farar t shirt, yayi kyau sosai duk da fuskarshi kadaran kadahan ya barta.
Tunda ta bud'e k'ofar ya zuba mata ido yana kallonta tamkar wata sabuwar halittar da tasha banban da jinsin mutane da bai tab'a gani ba, baisan adadin yadda yayi kewar kallon fuskarta, shak'ar k'amshin turaren ta da giftawarta ta gaban shi a lokacin da yake zaune a parlour yana aiki sai yau, hee miss much about her.
Ganin bashi da ta cewa sai kallon maseefa yasa ta russuna tana gaishe shi.
Saida yaja doguwar ajiyar zuciya sannan ya amsa yana sake ci gaba da kallonta yace, "ya wasan b'uya kuma?" Bata ce dashi komai ba, sai ya sake cewa, "d'akina nake son ki gyara mun idan ba zaki damu ba...". Ya k'arasa fad'a a ranshi yana fatan tasa mishi irin turaren d'akinta ko shima yaji k'amshi mai dad'i da sanyaya zuciya.
Lokaci ta kalla sannan tace, "toh ba damuwa! Sai dai ina son mik'awa yasmine abincin dana dafa ko zata iya ci....".
"Alright! Yana ina in kai mata?".
Da kanta ta d'auko ta bashi ya amsa tare da futa a gidan.
Daga k'ofar gidan shi ya kira wayar Ahmad, saida yaga futowar shi ya k'arasa suka gaisa yaji jikin yasmine sannan ya bashi k'aramin plask da raihana tasa a kawo mata.
Ahmad ya karb'a Yana godiya da tambayar khaleefa, "yau ba zata samu damar zuwa ba? Tun safe yasmine take son ganinta".
Harararshi khaleefa yayi yace, "tunda kana gida yau ai saika kula da matarka ko?".
Dariya Ahmad yayi yace, "man maida wuk'ar nasan indai kaine ba hana ta zuwa zakayi ba, tunda kota zauna a gidan ba wani abu zatayi maka ba....".
Cikin rashin fahimta khaleefa ya had'e rai yace, "me kake nufi".
Ahmad ya sake yin dariya had'e da rage sautin muryarshi, "Ina nufin bata da amfani da zatayi maka irin na kowanne miji ga matarshi.....".
"Ahmad!". Ya kira sunan shi a zafafe.
Dafa kafad'ar shi yayi fuskarshi har lokacin da fara'a yace, "sorry man! Na fad'i haka ne saboda nasan kai ba d'aya kake da sauran mutane ba....".
"Ohh! Na futo da sanyin safiya don na faranta ranku shine ka k'are da cimun mutumci".
"I'm sorry bhaiyya.... Mun gode Allah ya saka da alkhairy sai madame d'in tazo ko?".
Zuwa yanzu khaleefa ya gama fahimtar Ahmad magana yake fad'a mishi a kaikaice, har yanzu ya kasa fahimtar meyasa mutane suke saurin gane irin zaman da sukeyi shida raihana, koda yake Ahmad dole zai fahimci komai, amma wannan yana daga dalilin da yasa yak'i yadda Muhammad ya kawo matarshi ko su suje gudun kada ma wani zumunci ya k'ullu su dinga mishi zarya kullum......
Juyawa yayi baice dashi komai ba ya koma gidan.
Ahmad ya bishi da kallo yana murmushi mai kama da dariya.
Raihana kuwa koda ta shiga d'akin nashi saida ta gama bin ko'ina da kallo sannan ta fara gyarawa kamar yadda ya buk'ata. D'akin ma ba wani datti kawai neman magana ne irin nashi. Lokacin daya shigo ta gama aikin harta turare d'akin kamar yadda yayi fata.
Tana shirin komawa d'akinta yasa ta kawo mishi breakfast har d'akin, ba musu tayi duk yadda yake buk'ata, tana sane da yadda yake bin duk wani motsinta da kallo.
Har ta mishi sallama zata tafi ya k'ara tsayar da ita ta hanyar tambayarta, "akwai abinda zaki yine a gidan Ahmad?".
Girgiza mishi kai tayi,
"Then saurin me kike".
"Ba komai".
"Ko zaki jirani minti biyar in gama abinda nake?".
Ba tayi mishi musu ba wajen samun gefe d'aya ta zauna.
Yana cin abincin yana tunanin maganganun Ahmad..... A zahirin gaskiya zuciyarshi tana sake aminta da raihana, sai dai yana yak'i da wannan kusanci nasu a kullum dare da ranar Allah, yana son cika alk'awarin daya d'auka a zuciyarshi tun ranar daya fahimci gaskiya akan soyayyarta........ Duk da yasan inba ita ba babu wata mace da zata tsallake maganar data mishi da wadda Saleema ta mishi...... Ya riga ya zama marar buri game da aure da matar auren.... Inta kama sai ya rayu shi kad'ai har abadan abada, da dai ya auri ballagazar mace da tayi irin rayuwar Saleema.
Abincin ma baici na kirki ba ya ajiye shi gefe, ya kalli sashen da take zaune yaga ta tallafe hab'arta da hannunta, matuk'ar tausayinsu ya kama shi, har yaji ya fasa futar daya shirya da ita don ya d'ebe mata kewar zaman gidan, saboda ya fahimci hakan zai k'ara musu kusanci sosai da juna, kusancin da zai hana shi cika alk'awarin shi.
Jingina kanshi yayi da fuskar gadon da yake zaune yace, "zaki iya tafiya".
A nutse ta mik'e ta futa daga d'akin, khaleefa ya bita da kallo har ta b'ace sannan ya maida kanshi ya kwantar tare da sauke ajiyar zuciya.
****Tana shiga d'akinta a gefen gado ta zauna tayi shiru tana nazarin abubuwa da yawa game da rayuwar khaleefa da Auntie take magana a kai, shin da gaske zata iya kawo gyara wa rayuwar shi kamar yadda mahaifiyarshi take fata,,,,,, littafin nan ne ya sake fad'o mata a rai, ta rasa meyasa take mantawa dashi ko don kwana biyu bata samu zama ba, saita mik'e da sauri ta d'auko shi ta bud'e shafin farko tana duba abinda yake rubuce kamar haka👇
"Sooraj Abdallah,,,, da surayyah Adam". Zagaye cikin hoton zuciya.
Page na gaba ta bud'e mai d'auke da rubutu kamar haka, "Kamar yadda kika sanni... Sunana surayyah Adam haifafiyar k'asar Sudan garin Khartoum, mahaifiyata da mahaifina duka haifaffun k'asar ne, mu biyu suka haifa a duniya.... Yayana sauban daya bani kusan shekara goma sha shida a duniya, sannan aka haifeni naci sunan mamana,,,, mahaifina ba mai kud'i bane amma yana da matuk'ar rufin asirin da yasa muke rayuwa cikin gata kafun rasuwar iyayena ata sanadiyyar had'arin jirgin ruwa, hakan yasa gaba d'aya akalar rayuwata ya koma gurin yayar mamana, a lokacin sauban ya samu gurbin karatu a jami'ar Abuja dake Nigeria, ban nemi komai na rasa a sabon gidan da nake rayuwaba duk da mijinta yana da k'aramin k'arfi sosai ba kamar mahaifina ba.
Nayi karatuna tun daga primary har zuwa matakin junior secondary tare da y'ay'an gidan da nake da k'awayena, musamman k'awata guda d'aya da bazan iya mantawa da ita ba, irin k'awa ta k'uruciya. Kafun sauban ya samu aiki a garin Abuja ya dawo nan garin mu Khartoum yayi aure....
Sarah y'ar kawuna ce kuma yayanta abokin sauban ne tun na k'uruciya da sukayi fad'i tashin neman ilimi tare. Da farko daya nuna yana son na koma gurin shi da zama hanawa y'an uwan mamana sukayi saboda suna ganin kamar ya raina kulawar da suke bani ne, amma daga baya daya zauna ya fahimtar dasu dalilan shi sai suka amince zamana ya koma k'ark'ashin ikon shi da matarshi, a lokacin bazan huce shekaru goma sha hud'u ba.
Naci gaba da zama tare da sauban da matarshi cikin farin ciki da soyayyah, a lokacin kusan rabin abinda sauban yake samu ni yake kashewa saboda Allah bai basu haihuwa da wuri ba, nan da nan na sake wani irin sihirtaccen kyau mai d'aukar hankali... Aikuwa samari suka yimun caa, wanda sauban ya dinga taka musu burki, sai ya zamana ba mai iya tunkurata da shirmen maganar soyayyah saboda tsoron shi dana matakin da zai d'auka in yaga mutum ko yaji labari, hakan yasa har na kammala secondary na shiga jami'a bani da wani tsayayyen saurayi,,,, kafun k'addarar sooraj ta shigo cikin rayuwata......
An raba gadon mu tuni sauban ya fara business yana juya nawa da nashi yana adana mun ribar da ake samu cikin account d'ina".
*Waye sooraj Abdallah tofa?*
Asalin mahaifin sooraj Abdallah haifaffen wani k'auye ne a Kano da ake kira tofa, yayi karatun shi na primary a k'aramar primary da take k'auyen su, tun a lokacin da ilimin boko ba kowa ba sai