Showing 30001 words to 33000 words out of 288773 words

Chapter 11 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1037

kuma ya mik'e tsam ya wanko hannun shi yazo ya zauna yace, "Bismillah".
Tare suka ci abincin suna ci suna hirar su irinta ma'abota soyayyah. Saleema ji take tamkar su dawwama haka, tana son khaleefa k'arshe shiyasa take tunanin komai nashi yana da banbanci da sauran maza, a yanzun da suke cin abinci tare sai take k'ara gasgata gaskiyar hasashenta, komai nashi gwanin burgewa, ranar tare suka wuni suna hirar su ta soyayyah, ko sallah tare sukayi ita dashi bai bar apartment d'inta ba sai dare bayan ya tabbatar tasha maganinta ta kwanta bacci.
Sai bayan ya dawo gida ya kira Auntie suka gaisa, itama tayi complain akan rashin samun shi kwana biyu, ya bata hak'uri ya gabatar mata da uzurin shi. Sun dad'e suna hira da ita har tayi mishi albishir na zuwanta nan da 3 months watak'ila tare da Ayman idan ya samu hutun k'arshen shekara a gurin aikin su, sosai khaleefa yayi murna yayi ta addu'ar Allah yasa taren ma zasu taho.
Sai da suka gama waya da ita sannan ya kira Ayman, anci sa'a yau ba'a samu wata matsala ba sukayi hirar su lami lafiya, shi abinda yafi damun shi kawai yake mishi k'orafi, yayi k'ok'ari ya samu mata daya dawo suyi auren su shi ya gaji, so yake ya mallaki muhallin shi shima, har suka k'arashe maganar su sukayi sallama da juna khaleefa dariya yake yi mishi. Ko bayan sun ajiye wayar murmushi khaleefa yayi yace, "Ayman kenan, Wai yana buk'atar ya mallaki iyalai, wato ni d'in ma kunya ta yake ji".


@@@@@@@@


Toh b'angaren raihana kuwa anyi suna lafiya tare da ita, ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Mubarak da Allah yayi wa rasuwa, sai sukayi mata alkunya da samha, Raihana ce ta zab'i sunan ma.
Tun da safe da me make-up tazo ta yima Salma aka gyarawa raihana fuska da powder da wetlips, ta shirya cikin riga da zani na wani tsadadden lace, irin wanda akayi musu na kayan sallah da bata saka bane, kowa sai yaba kyaun da tayi yake, sunsha hotuna da me jego da dangin auntien ta sai aunty ziyada da tazo tare da yaranta y'an mata, isowar uwar zuga wato kakarta Inna ce ta korata zuwa saman yuseep da sauri har tana tuntub'e, tayi kwanciyarta a can tana kallo, da yake hayaniya bata dame taba, tana iya yini ita kad'ai ma sai bata wani damu da zaman shirun ba.
Hajiya Inna kuwa dama zuwan neman magana ne, tana zama raihana ta fara tambaya, cikin mutanen da suke gurin babu wanda yace mata kanzil har ziyada kuwa, haka ta k'ari bambaminta na banza da wofi da fad'an ita bata ga amfanin wannan karatun da take na boko ba ace, yarinya ko mutuwa akayi a dangi sai dai in tazo hutu tazo dama bikin aure tuni ta soke zuwa bare wani suna.
Ganin mutane sun fara taruwa gudun kada aje ayi ta yayata mahaifiyar tasu a duniya sai ziyada ta tausheta, tace ta bari idan aka gama suna taje har gida tayi fad'an ta a can.
Da farko hayayyak'owa ziyadan tayi, saida su Salma suka fara bata hak'uri da sauran y'an uwan ummie sannan ta sauko ta hak'ura tayi shiru.
Har yamma tana gidan wai kada taje ta tafi a cuci danginta da zasu zo shiyasa ta kasa ta tsare, haka ta dinga zubawa mutane abinci a leda suna tafiya dashi bayan wanda suka ci, lemo kuwa duk kusan mutanen tane suka shanye da wanda yuseep ya ajiye da wanda abban su raihana ya kawo duk ta tattare ta rabar, sai data gama neman rigimarta tsab da sun kewaya matar Abba abubakar na zugata ba'a kulata ba da daddare ta tafi.
Salma da raihana suna zaune a parlon sama inda raihana ta wuni, suna tattauna matsalar hajiya Inna, sai suke ganin abun nata kamar ma k'ara gaba yake, ita dai jin dad'in Salma d'aya da Allah yasa kaf fad'in taron ba y'an gidansu yuseep sunyi taron su a can gidan kakannin shi sai yamma suka zo mata kuma basu jima ba suka tafi.
A ranar raihana da khausar sai y'ar yayar ummie basu kwanta ba sai bayan sun tsabtace gidan tass! Sun gyare ko'ina.
Da sassafe kuwa Ayman ya kirata, bayan sun gaisa yake tambayar ta, "yea zaki tafi yau d'in ko sai gobe".
Shiru raihana tayi tana tunanin yadda zata kauce mishi, "Ina ganin sai gobe da safe saboda yau akwai aiki da yawa". "toh Allah ya kaimu a gaishe da Salma a shafa mun kan baby samha"
"Zataji" raihana ta fad'a jiki a sanyaye tana ajiye wayar, tunanin yadda zasu kwashe dashi kawai take a duk lokacin da ya samu labarin tayi tafiyarta bata jira shiba.....
"Abincin da kika d'ora zai kone Auntie raihana". Cewar Amina y'ar yayar ummie. Da gudu tayi kitchen d'in tana faman zabga salati, tana zuwa ta murde gas ta sauke tukunyar k'asa tana sauke ajiyar zuciya.

Ranar bata tafi ba sai yamma bayan an d'iba mata naman suna da yajin daddawa da yawa da zata kaiwa k'awayenta.
A gurguje ta gama had'a yanata yanata saboda ta samu damar yin sallama da ummie ta tafi akan kari, tana futowa daga gidan Salma wayarta na fara ringing, silencing d'inta tayi taci gaba da tafiyarta, saida taje gida ta huta sannan wani kiran ya sake shigowa ta d'aga "na rok'e ki kona mintuna biyu ne ki yadda na lek'o mu gaisa naga muhallin ki please raihana".
Wannan mutumi nacin shi yayi yawa, raihana ta fad'a a ranta, sai kuma tayi wani tunani, tana ganin ta bakin Ayman ta bashi damar ta gani. Sai tayi b'oyayyiyar ajiyar zuciya.
"Zan turo maka address ko na d'ara minti biyu bazan huce sha biyar ba saboda Ina da abubuwa da yawa da zanyi yau".
"Ba matsala turon da address d'in".
Raihana address ta mishi sending ta text message.
Ai kamar yana k'ofar gidan su saiji jin kira tayi bayan few minute, ko data yi picking sanar da ita yake gashi a k'ofar gidan su
"Wane gida kenan?". Raihana ta tambaye shi tana tunanin ko bai gane address d'in bane, "anguwa...... Gida mai no..... Shine inda nake tsaye yanzu haka".
"Toh fa" raihana ta fad'a tana mik'ewa tsaye "d'an bani minti 5 Ina zuwa".

Tana ajiye waya gurin ummie taje da take aikin had'a abincin dare, ta zauna a gefenta tana tunanin ta yadda zata fara sanar da ita, "am ummie.... Ummie dama... Dama dai wani ne muka had'u ranar da naje gidan Salma, toh..... Toh ya dameni tun a lokacin wai sai yazo ya gabatar da kanshi... Toh shine yanzu wai yazo..... Kuma"
D'aga mata hannu ummie tayi babu yabo babu fallasa tace, "ki daina wannan kame kamen raihana, kije amma dai kina sane da yau zaki koma makaranta ko?".
"Eh ummie" ta fad'a a sanyi, "toh ki kula".
Hijab dogo ta zunbulo kan kayan jikinta ta zura takalmi ta nufi hanyar futa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Yana tsaye jikin gidan su k'afar shi d'aya tokare da ginin, sanye yake da shadda milk, fari ne ba dai sol d'in nan ba, ba laifi kyakkyawa dashi, kallo d'aya zaka fahimci ilimi da kud'i sun jika shi.
Yana ganinta ya k'araso gabanta ya tsaya, a nutse yake k'are mata kallo ta cikin sun glasses da yake idon shi, "barka dai y'an mata".
D'auke kanta gefe tayi tace, "barkan ka dae".
"Yakike ya mutanen gidan?"
"Kowa lafiya qalou".
"Masha Allah". Shiru sukayi 4 a while kafun ya sake cewa, "lastly yau na sake ido hud'u dake bayan dogon jan aji da yanga da akayi mun".
"Hum jan aji ne ma?". Cire glass d'in idon shi yayi yana k'ara wara idanun shi a kanta sosai, "Jan aji mana irin na mata masu aji".
Shiru ita dai raihana tayi, "toh gashi kince mun baki da wadataccen lokaci, ni kaina daga kasuwa na gudo kada na jima alhajin mu ya fara nemana, Soo am bani dama na gabatar da kaina?".
"Me zai hana" ta fad'a fuskarta na kallon wani guri, "toh kamar yadda na fad'a miki nidai sunana Abubakar Muhammad Imran, haifaffen garin Kano anguwar...... Na girma a Kano nayi karatu gwargwadon iko yanzu haka ina kasuwanci tare da mahaifiyana a kasuwar hajj camp, nine na hud'u a gidan mu ina da k'anne uku da suke bina, raihanatu maganar gaskiya na jima Ina neman mace irin ki, kece dai dai da ra'ayina, shiyasa tun a waccen ranar ban yi wasa da damata wajen karb'ar no kiba, duk da daga baya na sare naji tsoron bazaki bani damar da zamu had'u ba haka alak'ar zata kare a waya yadda ta fara. Toh Amma yanzu nagode Allah gani a k'ofar gidan ku raihana, Ina fatan Zan samu amsuwa hannu bibbiyu".
Numfashi ta ja mai tsayi kafun tace, "Ni kuma sunana raihana salees abdallah, an haife ni a Kano na girma a Kano tare da mahaifina da mahaifiyata, muna zaune tare lpy nida y'an uwana, yanzu haka Ina karatu a nursing school dake garin bichi".
Imran idon shi a kanta yace, "wacce shekara kenan kika fara zuwa makarantar? Don in bakiyi nisa ba sai mu hak'ura da karatun a nemar miki admission a nan cikin gari ko?".
Wani kallo raihana ta mishi a ranta tace, "wato guy nan ganin na saki jiki Ina magana dashi yana d'aukar kamar na amince zan aure shine".
"Eh mana kinyi shiru kina kallona".
K'asa tayi da kanta ta sarke yatsun ta guri guda tace, "wata biyu ya rage mu kammala, yanzu haka muna under teaching practice ne".
"Masha Allah har naji dad'i a raina raihana, kinga shikenan kina yin graduation da wata uku sai ayi hidimar auren mu".
"Auren mu?". Ta tambaye shi tana zare ido, "eh mana na fad'a miki Ina sonki kuma auren ki zanyi, yanzu kina ganin da wane lokaci zan samu shi abban namu?".
Shiru raihana tayi, "kinyi shiru dear".
"Ina ganin lokacin dana baka ya huce tun d'azu ma k'arasa saurar maganar a waya".
"Okay shikenan nagode babie sai munyi waya".
"Okay ka sauka lafiya".
Ya d'aga mata hannu ya huce, ita kuma ta koma gida.
Sallah kawai tayi ta d'auko kayan tafiyarta, "Nina tafi ummie sai Allah ya k'ara had'a fuskokin mu kuma, nasan dan yanzu ba zamu samu hutu ba sai ko mun kammala exams din mu gaba d'aya".
Nasiha ummie ta k'ara yi mata sannan sukayi sallama ta futa.


@@@@@@


Raihana ta samu su raheela lafiya, ta basu kayan suna cikin wanda ta taho dasu, ta had'a suda Salma sukayi mata godiya
Toh washe garin ranar data dawo sukayi waya da Imran yake tambayar ta ko zai yiwu yau yazo ya gana da mahaifinta. Ita kam raihana har yanzu ta kasa daina mamaki, duk cikin samarin da tayi bata tab'a samun wanda ana fasa aurenta ya shigo da k'arfin shiba irin wannan, sai dai ita har yanzu bata wani jin shi a zuciyarta hasalima binshi take yi kawai saboda ita yanzu bata da wani zab'i ko buri akan mijin aure, shiyasa ta barwa Allah dukkan zab'i, ta fad'a mishi ita ta koma makaranta amma zai iya samun abban ta a gida bayan sallar isha'i, kowanne lokaci idan ya shirya.
Yayi mata godiya suka ajiye wayar. A cewar Imran da zafi zafi ake dukan k'arfe, a ranar da daddare ya shirya cikin manyan kaya yaje ya gabatar da kanshi gurin alhaji salees mahaifin raihana, akan yana so a bashi dama ya turo magabatan shi idan har raihana ta amince dashi ayi maganar auren su. Abun ya d'aurewa alhaji salees kai, dama suna tare ne tasan da zaman shi ko kuwa fara mik'o kanshi yayi. Abba ya sallame shi akan idan sukayi magana da raihana zai neme shi da kanshi tunda mahaifin shi ba b'oyayyen mutum bane.
Ko bayan ya shiga gida Saida ya tuntub'i ruqayya mahaifiyar raihana da zancen, ta fad'a mishi iya abinda ta sani, tabbas tasan wani yazo sun gaisa jiya da rana amma bata San ko shi bane ko wani ne daban. Sai suka ajiye magana akan zai tambaye ta da kanshi abinda tace su dama basu da wani zab'i sai nata iya kaci dai su taya ta da addu'a.
Kamar da wasa saiga tafiya tana Shirin mik'awa. Mahaifinta ya kirata yayi mata tambayoyi akan zuwan Imran ta kuma tabbatar mishi da tasan da zuwanshi. Abu na gaba daya tambayeta shine, "ko tana son shi ta amince da auren shi, saboda shi yayi dukkan bincike baiji an fad'i wani abu na aibu a gurin wanda suka tabbatar da sun sanshi sunsan mahaifin shi wasu har mahaifiyar shima, itace kuma take da d'an matsala itama bame zafi ba, matsalar kawai saboda ta bashi wata y'ar k'awarta ya aura yak'i ne, shine ta cire hannunta akan lamarin auren gaba d'aya. Shida mahaifin shi suke kid'an su suna rawar su. Raihana ta amince da auren Imran saboda ta duba ta hanga bata ga wata makusar shiba, haka kuma yana iya bakin k'ok'arin shi wajen nuna mata so da kulawa, a duniya tasan burin mamanta d'aya taga ta aurar da ita, shiyasa itama ta tattara dukkan attention d'inta yanzun akan aure.

An kawo kud'in auren raihana dubu d'ari biyu da hamsin a karo na shida, kud'i mafi yawa a cikin duk kud'ad'en da ake kawowa na aurenta, an tsaida rana nan da wata shida masu zuwa, mutane sunso su bashi shawara me zai hana a d'aga na khausar sai a taru ayi lokaci d'aya, Abba yace Sam ba zai yiwu ba ba'a haka ai kowa da lokacin ta, zasuyi bikin khausar da wata uku ayi na raihana.
Lokacin da matar Abba abubakar taji labarin yaron da ya kawo kud'i a wannan karon hankalinta sake tashi yayi, ta shiga damuwa da tunanin yadda kullum yarinyar take k'ara samun masoya da yin gaba, banda haka ace duk wanda ya tafi wanda zai zo sai ya fishi kud'i da komai, yanzu ga irinta nan d'an abubakar Muhammad Imran da kanshi yake son yarinyar, kowa a anguwar yasan familynsu masu kud'i ne gaba da baya. Ranar kasa bacci tayi sai sake sake da tunanin yadda zata tunkari wannan tashin hankali sabo na saurayin da raihanan ta kawo.
Ko da Wasa raihana bata fad'awa Ayman abinda ke faruwa ba saboda shi yayi fushi da ita tun waccen ranar data tura mishi text da dare tace ta koma makaranta yayi dogon fushi irin wanda yakan jima baiyi irin shiba. Ta kira shi ba adadi baya d'agawa, sai kawai ta tattara shi ta ajiye a gefe taci gaba da harkokinta amma Allah kad'ai yasan yadda ta damu da al'amarin a cikin zuciyarta, saboda fushin da Ayman yayi yasa lahadi biyu tana hucewa ko zuwa mata baiyi ba.
Hakan ya sake d'ingimata har Imran yaso fahimta in suna waya, saboda sai yayita magana bata amsa mishi tana can tana tunani. Shi kuma Imran yanzu damuwarshi d'aya ne yana son ta bashi dama yazo su gaisa sai kewarta yake, tunda fa Suka had'u sau d'aya basu k'ara had'uwa ba, in suna chat ko video call k'in d'agawa take pic d'inta kuwa basu huce uku yake dasu ba har yanzu.
Ita kuma tana sone saita fad'awa ummienta abinda tace shikenan.

@@@@@@@@


_After one month_

Safiya ce misalin k'arfe 10 da rabi na safe, raihanatu sanye take cikin riga da skirt na les pink colour, kanta babu d'ankwali sai tulin gashi da tayi parking a k'eyarta, fuskarta ko powder babu sai siririn gashi da suka kwanto har gaban goshinta da gefen fuskarta, kallon kanta tayi a mirror sannan ta dubi raheelat tace, "yae nayi kyau ne?".
"Sosai ma kuwa banda tsabar iskanci mijin da zai aure ki yazo ganin ki tun daga cikin gari amma ki futa fuska ko powder babu sannan wai don k'arfin hali har tambayata kike wai kinyi kyau".
Dariya raihana tayi ta dafa kafad'ar raheelat tace, "raheelatu tawa toh kwalliya itace me?".
Fatima ta galla mata harara tace, "oho miki dae amma Allah ki sauya hali, bani powder na shafa mata raheela" raheela ce ta d'auko powder suka zaunar da ita gefen bed suka gyara mata fuska hadda wetlips, ita dai raihana ta zama y'ar kallo sai yadda suka ga dama suka yi da fuskartata a yau. Ta tsaya saroro tana kallon kanta a mirror Fatima ta jawo hannunta, "zo mu tafi ni inba so kike ya gaji yayi fushin zuciya ya koma inda ya futo ba".
Duk su ukun suna dariya suka futo raheela ta rufe k'ofar d'akin.
Suna tafe suna hira har suka isa inda ya kwatanta mata yana jiranta, ya sha wankan shadda light blue kanshi babu hula amma sumar tasha gyara sai d'aukar take. As usual yanzun ma k'afar shi d'aya a cake take jikin dalleliyar motar daya zo cikinta.
Fatima ce ta dank'e hannun raihana dake cikin nata da kyau


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login