Showing 204001 words to 207000 words out of 288773 words

Chapter 69 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1119

tana share hawayen daya cika idonta ta dubi Amna da take jin kamar ta shak'e ta ta mutu kota huce takaicin abinda tayi mata.
"Ke kuma zan dawo gare ki".
Murmushi Amna tayi ranta fes tace, "da zaki yi hankali wannan zai zama manuniya a gare ki dashi kanshi khaleefa na fahimtar lokaci yayi da zaku hutar da zuk'atan ku ku tunkari rayuwar gaskiya, don ke ba zaki tab'a samun mai sonki kamar muslihu ba".
Wani mugun kallo kawai Saleema ta jefa mata don ba zata iya cewa komai ba tsabar tashin hankalin data tsinci kanta ciki, da gudu gudu sauri sauri ta futa bata ko rufe mata k'ofar ba.
Murmushi mai kyau Amna tayi a fili tace, "da sannu zaki dawowa gaskiyar da kika gujewa Saleema".

*****Auntie tana kallon news taji ana tab'a door bell, a nutsenta ta mik'e taje ta bud'e k'ofar, Ahmad ne tsaye, saita bashi hanya ya shigo ciki ta maida k'ofar ta rufe.
Har k'asa ya durk'usa suka gaisa kafun ya zauna saman d'aya daga kujerun parlon, hira suke yi jifa jifa, ya fahimci kamar ita kad'aice a gidan hakan yasa ya tambayeta ko khaleefa ya futa ne.
"A'a ina tunanin bai tashi bane".
Kallon agogo yayi ya maimaita kalmar "bacci? Aikuwa yanzu zan tashe shi".
Murmushi ita dai tayi ta sake tattara attention d'inta kan labaran da take kallo.
Saida ya fara rubutawa Yasmine gajeren sak'o don yaga komai ya tafi dai dai a gidan, sannan ya fara kiran layin khaleefa.
Raihana ce taji ringing d'in, hakan yasa ta tashi zaune da sauri tana karanta addu'ar tashi daga bacci had'e da yin mik'a. Sashen da khaleefa yake ta kalla taga baccin shi yake sadidan kuma yana jin dad'in baccin da dukkan alamu.
Da sauri ta d'auke wayar tayi rejecting kiran tayi silencing wayar baki d'aya, don daren jiya bata jin ya runtsa kona second d'aya.
Fuskar wayar ta tsurawa ido har yanzu hoton Saleema ne, sai tayi murmushi a ranta tana ayyana watak'ila itace yarinyar da yake so d'in nan. Tana shirin ajiye wayar gajeren sak'o ya shigo daga Ahmad, "Ohh shine ka katse mun kira,,,, Anya ma kuwa baccin da auntie ta fad'a kake?,,, koma dai meye ya kamata a k'are shi haka azo a gaishe da tsohuwa".
Da sauri raihana ta ajiye wayar tare dajin tsananin kunyar kalaman Ahmad d'in, bathroom d'inshi ta shiga ta wanko fuskarta.
Koda taje wajen k'ofa da nufin futa kasawa tayi, na farko kunyar Auntie ce ta diro mata dashi kanshi Ahmad d'in daya sauya musu fassara, sai kayan jikinta na bacci duk da riga da wando ne wadatattu kuma da wadataccen hijab a sama amma tasan Ahmad ba muharraminta bane da zatace ba komai don ya ganta a haka.
Tana nan tsaye Yasmine ma ta shigo gidan, har suka gaisa da auntie tasha tea a kunnenta, tana jin Yasmine na tambayar auntie raihana, Ahmad yayi zaraf ya bata amsa da bacci takeyi, ita kanta saida ta kalli agogo zata k'ara magana ya harareta, ya tura mata sak'o, "ya kamata ki kama kanki kina gaban maman mune".
Had'e fuskarta tayi ta mishi refly da, "toh ina ruwan ka ai dai nima mamana ce ba taku bace ku d'aya da zaku goranta mun".
Murmushi kawai yayi ya girgiza kai, suka ci gaba da hirar su ita da auntie, rabin hirar Yasmine duk yabone ga raihana, sai jaddada mata take raihana ta iya kaza ta iya kaza a k'arshe tace kai aita iya komai ma.
Ahmad ganin khaleefa da gaske ba futowa zaiyi ba sai yayi ma auntie sallama ya futa, sai a lokacin raihana ta samu damar futowa.
Ta k'arasa har kusa da Yasmine ta durk'usa ta gaishe da auntien. Suka gaisa da yasmine ma sannan ta shiga d'akinta tayi wanka ta shirya cikin kayan da suka fi amsar jikinta, Allah ya taimaketa basu da lectures yau data gane kurenta, don ta kuskura tayi missing saita jima kafun ta fahimci abinda ya huce ta.
Koda ta futo ba k'aramin santin dressing d'in nata dashi kanshi d'inkin yasmine tayi ba, gashi yau Allah ya rufa asiri bata labto wannan uban zurmemen hijabin ba, tana zama auntie ta gabatar mata da abincin karin kumallo, ta karb'a cikin jin kunya tana godiya, tunda ita ya kamata ta tashi ta had'a abincin ba bak'uwa irin suruka ba. Koda ta yiwa yasmine tayi cewa tayi ta k'oshi. Auntie da take kallon su tace, "nima saida na zuba mata bata ciba dama haka kuke wannan rayuwar?".
Murmushi raihana tayi tace, "a'a da gaske ta k'oshin ne indai kuma ko ba kunyarkice ta hana ta ciba".
"Ah haba! Ke kin tab'a ganin y'a taji kunyar cin abinci gaban mamanta". Yasmine ta fad'a.
Duk dariya sukayi marar sauti kafun Auntie ta tashi ta koma cikin d'akin raihanan.
Matsowa kusa Yasmine tayi tace, "Ashe bani kad'ai bace bani da kunya?". Tasan me Yasmine take son cewa don haka ta katse mata hanzari da saurinta, "kar ki kaimu inda bamu jeba, ah toh makara mukayi kema kin sani".
Y'ar k'aramar dariya tayi, "yada kama kai haka da sauri".
"Ai nasan abinda zaki fad'a shiyasa na taryi numfashin ki".
Sai suka sake dariya su dukan su.
Hirar su suka ci gaba har raihana ta gama cin abincin.
Suna cikin hirar ne kuma kiran Ahmad ya shigo, Koda ta d'aga tambayarta ya fara, "daga gaisuwa kuma sai kiyi zaman ki madame? Ko kin koma can da zama ne?".
Bata bashi amsa ba ta katse kiran bayan ta mik'e tsaye ta maida gyalenta tace ma raihana, "hajiya am about to go na samu urgent call daga boss".
Dariya kawai raihana tayi, a times in Yasmine tayi abu sai taga kamar k'anwarta Salma, halin su iri d'aya kamar uwa d'aya uba d'aya.
Auntie ta k'arasa ta yiwa sallama sannan ta fuce a gidan.
Ranar khaleefa bai tashi a bacci ba saida aka kira sallar zuhr.
Raihana tana zaune gefen auntie kan darduma tana lazumi, auntien ma lazumin takeyi ya kwankwasa k'ofa suka bashi izini ya shigo.
Raihana ta kalle shi da dressing d'inshi daya taimaka wajen k'ara futo dashi a gentleman, shi kam ta b'angaren shi wani irin sanyi ne ya kwaranya ruhin shi a lokacin daya shak'i k'amshin turaren daya manne da d'akin nata.
Ta tashi a nutse ta futa daga d'akin don bashi guri ya gana da mahaifiyar shi.
A k'asa ya durk'usa ya fara gaisawa da auntien, ta amsa da fuskar ba yabo babu fallasa.
Shiru sukayi bayan hakan kafun khaleefa ya fara magana da cewa, "kiyi hak'uri auntie jiya kin same ni..... Shiyasa ma banzo mun gaisa a jiyan ba..... Amma yanzu..... am very sorry dai kawai".
"Matar ka zaka bawa hak'uri khaleefa bani ba". Ta bashi amsa still ba fara'a kan fuskarta.
Shafo sumar kanshi yayi kanshi a k'asa still yace, "ai na bata hak'uri tun jiya komai ya huce".
Gyara zama Auntie tayi taci gaba da cewa, "wato khaleefa har yanzu kana nan da halin ka na zafun rai da kasa mallakar kai a lokacin da kake cikin b'acin rai, sanadiyyar haka har gashi kana jibge buhun rashin mutumci akan yarinyar da bata jiba bata gani ba..... Gaka a haka kamar mai k'arfi ashe ta gina bata shiga bane, don annabi S. A. W yace, ""laisashshadidu, walakinnashshadidu, allazey yamluku nafsahu indal gadabi"" (fassarar hadisin da hausa shine👉🏻mai k'arfi bai zamo ba, kad'ai mai k'arfi, wanda yake iya mallakar kanshi yayin fushi) don Allah khaleefa ka dinga tunawa da wannan hadisin da kuma kiyaye b'atawa ruhin da yake kyautata maka".
Tunda ta fara maganarta har ta gama kanshi a k'asa yake, saida ta gama zancen ta kaf sannan yace, "insha Allah za'a kiyaye Auntie...".
Cikin jin dad'in yadda ya karb'i kuskuren shi da kuma son ta jarraba shi tace,
"Toh Allah yasa! Amma Ina ganin idan na tashi tafiya zan d'auke Raihana ta mu koma gida tare".
Rass! Khaleefa yaji gaban shi ya fad'i haka kurum ba tare da zato bare tsammani ba, duk da a cikin zuciyarshi babu komai.
"Kayi shiru baka ce komai ba?".
"Eh ba damuwa zaku iya komawa taren". Ya bata amsa a zuciyarshi yana ganin auntien ta fad'a ne kawai tunda dai tasan raihana ta fara zuwa makaranta ai.
Zancen ya shiga Auntie a bazata, koda yake tafi kowa sanin halin khaleefa, zai iya b'oye komai a cikin shi komai girman shi, sai in yaso aji yake futar dashi, galibi ma bai fiya fad'ar magana da baki ba sai dai ya nuna a aikace.
"Amma Auntie sai naga kamar kin rame?". Khaleefa shima ya mata tambayar a bazata, b'oyayyen ajiyar zuciya ta sauke tace, "kwanakin da suka gabata nayi fama da rashin lafiya amma ynz alhamdulillah".
Shiru ya sake yi kafun ya nisa ya tambayeta, "akwai abinci kuwa?".
"Eh yana dinning raihana zatayi saving d'inka".
"Ita ta dafa?" Ya sake tambayarta.
"In ita ta dafa ba zaka ciba kenan?". Shafo sumar kanshi ya sake yi yace, "a'a kawai nayi missing abincin kine mamana". Ya k'arasa zancen yana marairaice mata kamar k'aramin yaro.
Dariya tayi sosai khaleefa yana tayata, sunci gaba da hira har zuwa lokacin da yaji yunwar cikin shi ta fara uzzura mishi ya futa dinning, yaci abincin da yawa ba laifi don da gaske yayi kewar girkintan nan.

Da daren ranar ma raihana a d'akin khaleefa ta kwana, har tayi bacci yana aiki a system batasan nisan lokacin daya d'auka ba, ita dai ta tashi da asubah tagan shi kan sallaya yana sallah. Alwala tayi itama tayi tata sallar.
Khaleefa yana shirin komawa bacci sak'o ya shigo wayarshi da bak'uwar number, "kayi hak'uri da abinda ka gani waccen ranar, nasan zaka dinga kallona matsayin silar ganin abinda zai zamo maka tashin hankali a rayuwa, ko mai son raba ka da masoyiyar ka Saleema, sai dai hakan shine kad'ai damar da zanyi amfani da ita wajen ganin na ceto rayuwarku kaida ita, na kuma fahimtar daku abinda kuka kasa fahimta a soyayyarku tsawon lokaci..... Nagode Amna".
Khaleefa yayi ta juya maganganun amnan har zuwa lokacin da bacci ya sake sad'ad'd'afowa yayi awon gaba dashi.

Raihana bata yarda an sake abun kunya irin na jiya ba, hakan yasa tak'i komawa bacci, da kitchen ta fara, ta shiga don shirya lafiyayyen abincin breakfast. Ko zuwa lokacin da auntie ta futo ta sameta ta kusa kammala aikinta gaba d'aya. Bata yarda ta tayata ba don dole ta hak'ura ta koma ta zauna.

@@@@@

Ranar Monday tunda sassafe khaleefa ya gama shirin shi na futa office as usual, ya futo rik'e da jakar shi da wayarshi yana magana da Ahmad. Raihana tana aikin jera food warmers a dinning taga futowar shi, yayi maseefar kyau cikin shigar tashi ta yau fiye da kullum ma.
K'asa tayi da kanta a lokacin daya k'araso gurin, baice mata komai ba yayi knocking k'ofar bedroom d'inta aka bashi izinin shiga.
Ya samu auntie suka gaisa tare da yi mata sallama.
"Amma zaka karya kafun ka futa ko?".
"Ehh! A'a gaskiya ba lokaci zan iya yin late in na k'ara wasu mintuna".
"Toh Allah ya tsare ya bada sa'a".
Ya amsa da ameen yana fucewa.
Da kallo ta bishi a ranta tana tunanin abinda yasa baya son cin abincin, ko har yanzu baya cin abincin raihanan? Koda yake ai tana nan da sannu zata kama shi.

Yana zaune a office aiki yasha kanshi, wasu uban files ne yake ta dubawa yama kasa gane wannene ainahin wanda yake nema a ciki, saboda rarraba hankalin shi da yake yi.
Ganin ba fahimtar komai zaiyi ba daga k'arshe sai kawai ya matsar da files d'in gefe ya kifa kanshi jikin table d'in da yake gaban shi, hoton abinda ya faru waccen ranar yana dawowa cikin kwakwalwar shi dalla dalla yana hucewa kamar video, shi yasan cikin kwanakin k'arfin hali kawai yake yi amma abun yana cikin zuciyarshi, yini baya farawa ya k'are bai tuna ba, dole ba yadda zaiyi abun so yake ya zama wani yanki na b'acin ranshi, ko abin bak'in cikin rayuwarshi da baya son tunawa.
Ya lula duniyar tunani shiyasa har aka turo k'ofar office d'in aka shigo bai sani ba. Itama bata damu ba ta k'arasa har gaban shi taja kujera ta zauna.
Zuba mishi ido tayi tana kallon shi tare da jin wani mugun kishin sa, a duniya babu abinda zai hanata samun khaleefa, kuma ko meye zata iya kau dashi kota wacce hanya wannan alk'awari ne........

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*

_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page fifty eight 5️⃣8️⃣


Bak'on k'amshin turaren da yaji cikin office d'in ne ya taimaka wajen dawo dashi hayyacin shi, a nutse yake binta da kallo fuska sam ba annuri.
Itama kallon shi take yi shakkun shi na shigarta.
"Tashi ki futar mun a office don baiyi kama da gurin shirme da shirita ba".
Marairaice fuska tayi ta mik'e daga kujerar ta fara k'arasawa har gaban shi tana magana da sigar ban tausayi, "me yasa zaka yimun haka khaleefa? Kasan kuwa adadin yawan son da nake maka da kishin ka? Amma shine har kaje ka auri wata kake rayuwa da ita bayan alk'awarin da kayi mun......" Ta k'arasa fad'a cikin rawar murya tana nufar shi kai tsaye zata d'ora hannunta jikin shi.
Da wani mugun sauri ya hankad'a ta har saida kanta ya daku da jikin bango, cikin tsawa yace, "ki futa Saleema! Ki futar mun a office!! Na tsane ki bana son ganin ki, bana son jin muryarki.... Banza ballagaza, ke yanzu har kina da bakin magana akan aure na bayan duk abinda kikayi....."
Yadda ya rufe Ido ya balbaleta da maseefa kad'ai ya tabbatar mata da zai iya aikata komai gareta a lokacin, jikinta gaba d'aya yayi lakwas takaicin Amna da nadama ta cika zuciyarta a karon farko, amma fa koda ha maza ha mata saiya aureta tunda har ya kuskura ya lasa mata zumar soyayyarshi toh sai dai fa ya rayu da ita kad'ai bai Isa ya rab'i watan ta ba.
Jiki a sanyaye fuska sharkab da hawaye taci gaba da tsayuwa a offishin tama kasa d'aga k'afa bare ta iya futa kamar yadda yake buk'ata. Yayinda shi kuma hannun shi ke mata nuni da k'ofar futa.
A haka doctor andal ta shigo office d'in ta tsaya tana kallon su su duka biyu kafun ta tambayeshi, "tsayuwar me patient take a office d'in likita?".
Khaleefa k'asa yayi da kanshi a sanyaye yace, "ita ba patient bace".
"Toh me takeyi kenan ko batasan yanzu lokacin aikinka bane".
Saita dawo da dubanta ga Saleema da take faman rabzar kuka tace, "hajiya u can wait for him somewhere in ya tashi office ya same ki a can".
Bata iya cewa andal komai ba ta fuce a office d'in da mugun sauri bayan ta k'aro k'arfin sautin kukanta.
Doctor andal taja kujerar gaban table d'inshi ta zauna, shima zaman yayi amma kanshi a k'asa
"Be careful khaleefa". Doctor andal ta fad'a ba wasa akan fuskarta.
Gyad'a mata kai kurum yayi yana k'ok'arin saita yanayin shi.
Tsabar tashin hankalin da yake ciki doctor andal tana iya ganin yadda physique chest d'inshi yake up and down.
"Wash your first and calm down your mind tafe nake da magana me muhimmanci".
Ba musu yabi umarninta yaje ya dawo ya koma mazaunin shi ya bata dukka nutsuwarshi.
"Akwai wani patient d'ina da yake zuwa check up 2 times a year kwana ki mun tab'a maganar da kai remember?". Khaleefa ya gyad'a mata kai. Tace, "good! Toh shine yayi accident ya samu karaya a hannu, an mishi aiki a k'asar shi cikin nasara har hannun yaci gaba da aiki normal, bayan lokaci mai tsayi Kuma yanzu ya dawo yana mishi ciwo, duk da ciwon ba wai ya mishi zafi bane amma hannun yana damun shi sosai, yanayin aikin shi yasa ba zai samu damar shigowa check up ba wannan karon ga kuma ciwo, Soo Ina ganin zanyi magana da doctor raazee Upper week kuje kaida Muhammad da kuyi mishi aiki har k'asar shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login