Showing 150001 words to 153000 words out of 288773 words
Chapter 51 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
Ball d'in ta taya su kallo 4 de first time a tarihin rayuwarta data tab'a kallon ball.
Suna zaune kamar kurame sai ihun y'an ball daya cika d'akin taf, koda auntie ta futo da kallon mamaki ta bisu kafun tace, "toh aini ban d'auka akwai mutane a parlon ba, Ina ta sauri in gama lissafin can in zo in sama muku abinda zaku ci sharp sharp".
Raihana ce tayi magana, "ayyah auntie ai da kin gama aikin ki a tsanake, na dafa mana abincin tun d'azu ma...".
Auntie tace, "Toh Allah dai yasa kada aci tara na, na tura Amarya kitchen tun yanzu....". Murmushi tayi tana rufe fuska, ita kuma Auntie tayi y'ar dariya... Daga k'amshin abincin auntie tasan zaiyi dad'i kwarai.
"Akwai wanda zaici abinci cikin ku yanzu?". Auntie ta tambaye su.
Ayman ne ya fara cewa, "aini zaman jiran shima nakeyi...". Khaleefa kam yamutsa fuska yayi, auntie ta tambaye shi, "Kai baza kaci ba?". Yace, "noop am okay".
Ayman ta zubawa abincin ta kai mishi har inda yake, itama ta d'auki kad'an don bata jin yunwa Sam. Ta zubawa raihana nata ta mik'a mata da ruwan lemon.
Ta karb'a itama ba don tana jin wata shahararriyar yunwa ba. Tana jin auntie suna ta hirar su da Ayman har ta gama cin adadin wanda gurbin cikinta zai d'auka ta ajiye ragowar a gefe.
Ta d'auki wayarta da Mukullin k'ofar part d'inta tace, "Auntie Yaya Ayman saida safen ku".
Duk suka amsa da Allah ya bamu alkhairy. Saida ta futa da adadin wasu mintuna sannan khaleefa ma ya tashi zai tafi, bayan ya musu sallama auntie tace, "gobe tunda safe dama ka fad'awa raihana ta shirya kuje gurin d'inkin nan ayi measuring d'inta ga kayan nan ta kawo, daga nan har passport ayi mata".
Da toh ya amsa ya dusa kai ya huce abin shi. Bayan futar shi Ayman yake tambayar auntie, "tare zasu tafi Germany ne?". Auntie tace, "toh me yasa ya aureta". Gyad'a kai Ayman yayi yana nazarin wasu abubuwa a cikin zuciyar shi, ko iya zaman da sukayi yanzu a parlon auntie ya dad'a fahimtar abubuwa da yawa a rayuwar auren su.
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page forty two4️⃣2️⃣
Kamar kullum yauma raihana bayan ta gama gyaran d'akinta ciki da waje, tayi wanka ta shirya cikin atamfarta mai kyau da tsada, bata d'aura d'ankwali ba saboda gashin kanta data tubke a k'eyarta himili guda, yanzun ma hijab ne a jikinta take shigowa parlon da yake ta d'aukar ido kamar mirror saboda gyara da yake samu, kusan sau uku kenan tana zuwa duba auntien bata samunta, duk sai ta shiga damuwa da tunanin ko lafiya....
Yana tsaye jikin windown parlon hard'e da hannu a k'irji, yadda ya zubawa harabar gidan ido kad'ai zakasan akwai abinda yake tunani.
"Ina kwana". Raihana ta gaishe shi bayan ta russuna,
Saida yaja iska ya furzar sannan ya bata amsa da "lafiya". Gaba tayi zata shige d'akinta sautin muryar shi ya katse mata hanzari, "ke nake jira zamu futa". Kallon kanta tayi, tako ta ina ba makusa a shigar jikinta, saita juyo kawai tace, "okay". Kallonta yayi kamar ya tambayeta wai ita bata da kayan sawa sai irin wad'an nan zunbula zunbulan hijjaban, sai kuma yaga ba hurumin shi bane ita taji zata iya.
Shiya fara yin gaba ita Kuma tabi bayan shi.
Da catin hannun shi ya lalubo katafaren gurin d'inkin, daga waje ta cikin glass robot ne na mace kusan guda shida an saka musu kaya daban daban na mata, kallon y'ar tsanar yayi yana yaba tsarin d'inkin dake jikin kowacce d'aya a cikin su, ga surar jikinta well shape, yana tunanin a duniya babu mata masu irin wannan shape d'in sai dangin su robbot d'in. Take Saleema ta fad'o mishi a rai, itace yasan jikinta ciki da bai, ko ita duk kyawunta a iya fuska ya tsaya, amma ta surar jiki bata da wani shape irin wannan, siririyace ajin k'arshe, koda yake shi ba komai nata yake kallo ba ita d'in gundarinta yake so da k'auna.
Wayarshi ya zaro ya zuba numbobin jikin katin yayi dialing, bugu hud'u akayi picking, "muna waje". Abinda raihana taji khaleefa ya fad'a kenan, Daga can b'angaren aka ce, "okay kune doctor surayyah ta kawo kayan ku d'azu ba?". "eh" khaleefa ya bata amsa a tak'aice. "Ina futowa yanzu". Ta fad'a suka ajiye wayar gaba d'aya.
Kwantar da kanshi yayi baya ita kuma raihana ta k'ame har zuwa sanda taji ana knocking murfin motar.
Wata macece y'ar gayu ta ajin k'arshe kamar Auntie take tsaye daga gefen mazauninta, "sannu da zuwa Mrs Abdallah khaleefa" matar ta fad'a a lokacin da raihana ta futo, ita dai k'asa tayi da kanta ta russuna tana gaisheta, shima khaleefa futowa yayi ya d'an durk'usa kad'an yana gaisheta, Saida ta gama yi mishi kirarin rashin zumunci sannan ta amsa tana sake yi mishi Allah sanya alkhairy.
"Zaka bamu 30 mint muna dawowa". Kai ya gyad'a mata ya kalli direction d'in da raihana take, sai ya ganta daban a gurin kamar irin typical matan auren nan na ajin k'asa.
Sai ya d'auke kanshi yana kwab'ar kanshi da shishshigi wa lamarin rayuwarta. Matar ita ta fara yin gaba raihana tana bin bayanta har suka shiga gurin, babban shagon d'inki ne da suka kware wajen futar da kowanne design na mata daya gaji da had'uwa, a kujera suka zaunar da ita aka gabatar mata da drinks masu sanyi.
Matar tasa an futo da kayan zuwa gaban raihana ta tambayeta yadda za'ayi mata da kowanne d'aya, raihana tace, "kuyi shi duk yadda ya kama".
"An bamu wuk'a da nama kenan". Matar ta fad'a tana dariya k'asa k'asa.
Wata matashiyar ta k'ara kira tazo zatayi measuring d'inta, ganin duk mata ne a gurin sai hankalinta yafi kwanciya ta cire hijab aka aunata sosai.
Suna gamawa ta maida hijabinta, tare suka futo yanzun ma bayan tayi sallama da y'an shagon masu kirki da suke ta nan nan da ita.
Yana zaune saman mota kunnen shi d'aya sak'ale da Bluetooth yana danna waya hankali kwance.
K'arasowar su gurin yasa shi d'ago kai yana duban su, "mun gama doctor surayyah tace kai zaka biya duka kud'in ko?". Duk da ba suyi haka da auntie ba amma yasan dama ba zata futar da ko kwandalar ta ta hidimtawa matar shiba, baisan dalilinta ba. A take ya yiwa matar transfer na duka kud'ad'en data lissafa, sukayi sallama ta tafi su kuma suka shiga cikin mota.
Tak! Babu wanda yace da d'an uwanshi har suka k'arasa wani gurin hoto, wannan karon saida ya futa sannan itama raihana ta futo, tabi bayan shi a lokacin har ya fara mata nisa.
Nan ma shi yayi magana da mutanen gurin, batasan ko akan me ba ta daiga sun buk'aci ta shiga cikin gurin, hoto akayi mata akace ta d'an jira na wasu mintuna. Ta samu gefe d'aya ta zauna har aka mik'o mata hotunan a envelope. Ta karb'a ta futo. Yanzun ma yana jikin motar shi a tsaye, yana ganin ta k'araso ya mik'a mata hannu, duk da bece komai ba amma tasan dai bazai huce hotunan ba, saita mik'a mishi su, ko a yanzu daya kalli yatsun hannunta saida yaji takaici fal zuciyar shi, abubuwa da yawa a rayuwar raihana da take yi da yana da iko daya haramta mata su saboda shiya tsane shi..... D'auke kanshi kurum yayi ya zagaya driver seat ya zauna, bata da zab'i itama sai bin bayan shi.
*****. "Yae engineer wai meye sirrin ne yau tunda kazo naga sai kyalli kake, kumatun ka har sun ciko". Wani kwakkwaran naushi Ayman ya kai mishi a gefen kafad'a, ya goce yana dariya,,,, shima dariyar yayi ya huce office d'in kaamil. Bai zauna ba ya mik'a mishi hannu suka gaisa, "yau ba zaka zauna ba". Kaamil ya tambaye shi yana kallon shi.
Ayman yace, "Kai ai ko office ban shiga ba zaman nan bazai yiwu ba, zuwa nayi dai na fara maka godiya,,,, nagode kwarai naji dad'in shawarar daka bani". Kaamil y'ar dariya yayi yace, "yana aiki kenan". Ayman yace, "ahh sosai ma, sai dai nayi mamaki kaida ba likita ba Ina ka samu irin wad'annan dabaru?".
Kaamil saida yayi dariyar shi son rai sannan yace, "Wai bakasan soyayyah ba department d'in da ba ta shiga ta koyar ba? Tana jin kowanne yare har da wanda ba me jin irin shi a wannan duniyar da muke ciki". Cikin gamsuwa Ayman yace, "na yarda da kai kam". Sai ya dubi agogon hannun shi, ya gyara zaman tabaran fuskarshi yace, "kaamil ya kamata na tafi muna da meeting nan da 2 hours soo yana da kyau na shirya kafun lokacin". Sake gaisawa sukayi Ayman ya futa shi kuma ya sake duk'ufa kan system d'inshi.
****Yana gama daidaita parking ta bud'e k'ofar zata futa, "dakata" ya fad'a da dakakkiyar muryar shi, saita janye hannunta ta saci kallon shi, waya yake dannawa, "meye account d'inki". Shiru tayi kamar ba taji abinda ya tambayeta ba, har saida ya sake maimaitawa, "ki fad'a mun account number ki zan dawo miki da kud'in da nasa ki aramun waccen ranar".
Girgiza mishi kai tayi cikin sanyi da taushin muryarta tace, "Ni ba rance na baka ba,,,, ka bar shi kawai".
Khaleefa fuskantarta yayi sosai yana kallonta, "bana son kyautar ki fad'a mun account d'inki nace......".
Yadda yayi maganar yasa taji shakkar shi sosai, amma sai ta dake saboda tana ganin don yasa ta bawa y'an uwanta kud'in mota har sai ya biyata.... "Ni kuma nace na yafe".
Ganin kamar tana jin dad'in jayayya dashi saiya zare wayarta dake kan cinyarta, tabi wayar da sauri zata rik'e yayi gefe da ita cikin zafin nama, ya wani irin zare mata ido yana mata kallon gargad'i, "ki kama kanki yarinya,,,, baki san waye Abdallah khaleefa ba ko? Tom". Fucewa tayi daga motar a nutse tana tab'e baki, a ranta tana maimaita maganar shi, "Wai batasan waye shiba, waye shi kuwa in ba wani kwallin mutum mai bak'ar zuciya da nunk'ufurcin maseefa ba kullum fuska a d'aure, nikam kada Allah ma ya bani miji irin shi....".
Shima a nashi b'angaren abinda yake ayyanawa a ranshi shine, "Lallai yarinyar nan sai yayi da gaske zama da ita, don yaga take takenta tana da raini da rashin kunya....".
Wayar ma bai samu abinda yake so a cikinta ba saboda tayi locking d'inta. Ganin lokacin sallah yazo dab sai ya juya ya futa daga gidan.
Yini guda yau Auntie bata nan bata san inda ta tafi ba amma taje yafi sau hud'u ma'aikatan gidan suna fad'a mata bata dawo ba, ga mama haleema yau bata zoba itama, suma y'an matan da suke nan lokacin tafiya islamiyyar su yana yi suka shirya suka tafi sai kuma gobe, dama su haka tsarin aikin su yake, mama haleema ce dai take yini wata rana ma har ta kwana.
Sai taji gidan yayi mata tsit duk ba dad'i.
Yau ma ita tayi girkin rana a kitchen d'in auntie, ta d'auki nata ta ajiye musu nasu a warmers. Parlonta ta koma rik'e da plate d'in abincin ta zauna zata ci, har kallo ta kunna don ya d'ebe mata kewa, tana cin abincin tana kallonta a tivi har ta kammala ta ajiye plate d'in zata tashi ta d'auko ruwa.
Turus tayi ganin shi zaune a parlon ya zubawa tivin idanu shima yana kallon firm d'in da ake haskawa. A d'arare ta kewaye shi ta huce, saida ta d'auko ruwan ta dawo zata sake hucewa sannan khaleefa ya mik'a mata wayarta da wasu kud'i. Tasa hannu ta karb'a k'asa k'asa tace, "nagode Allah ya k'ara rufa asiri".
Bai d'auka zata karb'a har tayi mishi addu'a irin wannan ba, sai yaji zuciyarshi tayi sanyi, salin alin ta warware k'udurin da yake ranshi har ya dinga tunanin sauk'in kai gareta haka ko kuma shi d'in ne ta gani babu wasa ta kama kanta shi dai kam bai sani ba.
@@@@ Ranar auntie bata dawo da wuri ba har sai yamma, kusan da matuk'ar farin ciki raihana ta taryeta tana mata sannu da zuwa.
A daren ranar auntien take shaida mata ta koma bakin aiki, sai dai tana son zata nuna mata wasu sirrika irin na matan sudaniyya a kullum daga k'arfe bakwai na dare zuwa tara har na tsawon sati biyu, sannan akwai gyaran jiki na musamman da take so ta had'a mata dashi.
Raihana duk da batasan ko akan meye ba amma tayi na'am, don tasan bazai tab'a zama cutarwa a gare taba. Washe gari ma kafun ta futa saida ta turo musu da karin kumallo. Raihana har kunya taji data gani, tana ganin tunda ta koma aiki ya kamata ta dinga hutawa ita ta karb'i girkin.
A ranar ma saida suka futa da khaleefa, shirye shiryen tafiya ake mata ba tare data sani ba, bai kuma yi mata bayani ba.
@@@@@ kwanaki da yawa sun shud'e, abubuwa suna ta faruwa a rayuwar gidan, raihana sun daidaita da Ayman suna zaune lafiya da gaisuwar mutumci a duk lokacin da suka had'u, koda wasa basu ji a ransu zasuyi wasa da aurenta na boge da khaleefa ba, basa nuna wata alama ta soyayyah a tsakanin su, saboda Ayman ya ajiye komai har zuwa lokacin da game d'in da suke bugawa da khaleefa zai zo k'arshe.
Wani lokacin in ya taso aiki da yunwa, yakan yi mata text message yace ta sama mishi abinda zaici kafun ya dawo, majority ma wainar fulawa yake sawa tayi mishi. Kafun ya dawo kuwa ta had'a mishi ita ta kammaleta a dinning na parlon auntie tayi nata guri.
Duk da khaleefa yana ganin yadda take b'ata lokaci wajen girki a kitchen, ta ajiye Ayman yazo ya cinye amma hakan bai tab'a damun shiba, baya jin komai akan duk yadda taga dama tayi da rayuwarta bazai sa mata ido koya takura taba. Sai a yanzu yake gane da tun can akwai kyakkyawar alak'a tsakanin ta da Ayman, wadda ba zaice ga abinda ya raba su yanzun ba.
A kullum dare auntie tana koya mata wasu sirrikan gyaran jiki da turare kala kala na jiki masu kama zuciyar namiji ya tsaya bisa ra'ayi guda.
Haka girki ma kalar na mutanen Sudan ta nunnuna mata, gaba d'aya ta tashi maida ita wata rik'ak'k'iyar y'ar gayun jinsin Arab cikin kwanakin, sirrikan data ajiye kunya ta bata a naira million ba za'a bata shiba.
Mata me d'inki ta kawo mata kayanta har gida, lokacin ma auntie bata dawo gidan ba saboda biyawa ta gidan su iya da zatayi, sai raihana ce ta taryeta ta karb'i kayan, koda auntie ta dawo taga tsarin yadda akayi d'inkin ta yaba sosai, wasu riga da zani, wasu da skirt, wasu kuma akayi mata dogayen riguna.
Komai ya kammala har dana shirye shiryen tafiyar su Germany. Ya rage saura kwanaki k'alilan auntie tasa khaleefa suje da dare ya gaishe da iyayen raihana, daga nan yayi musu bayanin tafiyar su da kanshi.
Da dare raihana tana zaune a parlonta tana waya da ummienta bayan tayi sallama da auntie ta taho nata b'angaren, mita take yiwa auntien akan dalilin rashin zuwan su al'ameen gidanta har yanzu. Tana wayar khaleefa ya shigo parlon da sallama, ta d'aga idonta ta kalleshi, as usual yana sanye da white shirt da ash trosser, sumar kanshi a kwance luf yasha gyara sai d'aukar ido yake yi, tana daga inda take amma k'amshin turaren shi yazo har inda take tun kafun ya k'araso.
A d'aya daga kujerun parlon ya zauna ya kalleta a lokacin da ita kuma ta d'auke kanta daga kallon shi, itama kamar kullum bazai iya tantance kayan jikinta ba saboda wani uban zundumemen hijab data kirma ko zafi bata ji. Sai ya d'auke kanshi yana sake gargad'in kanshi da shiga hurumin ta.
Ganin kamar khaleefa yana son magana da ita sai ta tak'aita wayar tayi sallama dasu, a lokacin ma da hibba take waya tana ta biyewa shagwob'ar ta.
Tun tana waya take ganin kamar kira yana shigowa bata maida hankali ta duba ba har ta gama, khaleefa ya bud'e baki zaiyi magana kenan wani kiran ya sake shigowa. Saita kai dubanta ga screen d'in wayar, zatayi rejecting kiran ya hanata ta hanyar cewa, "ki d'aga amma kar kiyi maganar sama da minti goma da koma waye, saboda nima ina son magana dake......".