Showing 189001 words to 192000 words out of 288773 words

Chapter 64 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1071

Ita kanta kukan take yi na tausayin su shida d'an uwan shi, tana tsoron ta mutu ta barsu a wannan halin, shin ya rayuwarsu zata ci gaba da kasancewa cikin wannan al'ummar ma'abota gutsiri tsoma da shiga hurumin da bai shafe suba bayan ba ranta?. Shin Ayman zai samu matar aure da bak'in tambarin da aka lik'a mishi na rashin uba kamar yadda khaleefa ya samu da kyar?
Shin zasu yafe mata bayan ranta idan suka gano mahaifin su yana raye ta b'oye musu tsawon shekaru saboda wani dalili nata da alk'awari data d'aukar wa ranta ita d'aya? Hak'ik'a tana tsoron ta mutu ta bar baya da k'ura ga yaran da basu jiba basu gani ba, hasalima basu suka samar da kansu ba, tako wacce hanya samar dasu akayi.......

_ina jinjina da nuna goyon bayan ku masoya littafin JARUMAR UWA, comment d'inku shine kwarin gwiwa ta a koda yaushe, sai dai masu jin haushin Saleema ku koma ku bincika ainahin yadda ake soyayyah ta gaskiya, sannan lamarin raihana sannu sannu bata hana zuwa, komai da takeyi akwai dalilinta, zaku gane hakan bada jimawa ba insha Allah_

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*


_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page fifty three 5️⃣3️⃣


"Oohhh Allah ka kawo mun d'auki a cikin wannan rayuwar". Ta fad'a a zuciyarta, a zahiri kam cikin son kwantar wa Ayman hankali tace, "me likita yace akan ciwo na?".
Da kyar ya iya had'a lab'b'an shi biyu yace, "zazzab'i.... Jinin ki kuma ya hau da yawa, sai stress da yake damun ki". Shiru yayi kafun yaci gaba da cewa, "am sorry Mom amma lokaci yayi daya kamata ki ajiye komai ki huta saboda shekarun ki sun fara nauyi,,, idan nace komai Ina nufin har aikin ki da harkokin kasuwancin ki.... Alhamdulillah hak'ar ki ta gama cimma ruwa, yanzu duk muna da rufin asirin da zamu ci gaba da d'aukar nauyin rayuwar ki da tamu ma har zuwa k'arshen numfashi...."
Murmushin yak'e tayi tace, "ka kwantar da hankalin ka Ayman kabi komai a sannu".
"Taya hankalina zai kwanta auntie bayan kinsan bazan iya jure rashin ki ba, kece mahaifiyar mu, mahaifin mu, babbar abokiyar da tafi kowa sanin kowa a cikin mu, abokiyar shawarar mu,,,, shin kina ganin zamu iya jurar rashin mutum guda da yafi mutum goma muhimmanci da amfani a tare damu,,,, ya kike tunanin rayuwarmu zata kasance idan akace yau babu ke.......?".
Ya kai k'arshen zancen yana kifa kanshi jikin k'arfen gadon ya fashe da kuka mai cin rai.
Ita kanta kukan take yi saboda maganganun shi sun tab'a zuciyarta ainun.... Haka suka taru sunata kuka har mama haleema data farka kusan lokaci guda da auntien take sauraron su tuntuni.
Tabbas surayyah ta kasance bango majinginar bayin Allah da dama, wanda suka santa da wanda ma basu santa ba, wanda ta bayyana da wanda ma ta barwa kanta, a girme tasan zata yiwa surayyah fintinkau a shekarun haihuwa, amma tayi mata abinda ko uwar data haifeta iyakar abinda zata mata kenan, ta d'auki nauyin cinsu, shansu, suturar su harma da wasu nauye nauye na rayuwar mutane ta yau da kullum, y'ay'anta mata uku data aurar duk bata sanin lokacin da auntie take zuwa ta d'auki amarya ta zab'i furnitures masu kyau da sauk'in kud'i sai dai kawai taba mama haleema resit taji da siyan sauran kayan kitchen. Sannan taja da baya ta gyara jikin amarya ta had'a ta da turarukan Sudan masu k'amshi da d'aukar hankali. Lallai rashin wannan mata a gareta dai dai yake da fallasuwar asirinta da yake rufe tsawon shekaru, duk da a yanzu y'ay'anta itama sun kawo k'arfi kowa ya samu abinyi cikin su alhamdulillah.
Ita ta sulale ta kira wata nurse tazo don duba yanayin jikin auntie, ta kuwa dinga zabgawa Ayman fad'a don ya mugun b'ata mata rai, suna iya bakin k'ok'arin su yazo zai dawo musu da aiki baya ta hanyar wannan kukan da yasata, duk da wani lokacin kuka ma rahama ne, akwai tashin hankalin da in yakai k'ololuwa ba'a iya mishi kuka.
An sake yi mata allurai masu k'arfi, ba jimawa kuwa bacci ya sake kwasheta.
A washe garin ranar mama haleema ta fad'awa su malam, duk da auntie tayi warning kar a fad'awa kowa, sai dai sanin in suka ji daga baya ba zasu tab'a jin dad'i ba sai ta fad'a musu, su kansu har kuka sukayi da suka zo asibitin suka ganta. Duk yadda take K'arfafa kanta da zuciyarta wajen ganin tayi yak'i da ciwon hakan ta gaza cimma ruwa yayi.
Sai gata da shafe sati guda har da d'oriyar wasu y'an kwanaki tana jinya a gadon asibiti, yayinda suka b'oyewa su khaleefa basu sanar dasu komai ba.
Tun a lokacin da khaleefa ya damu da rashin samun layinta ya tambayi Ayman yace wayarta ta samu matsala ne sai bai sake tambayar shiba duk da yadda abun yake damun shi ya shanye,,, raihana kam ba waya sukeyi da Ayman ba sai gaisawa ta hanyar text massage, Koda ta kasa samun layin auntien ma bata tambayi kowa ba ta bari a ranta ko wayar ce ta lalace.
Mutane da yawa sunzo duba ta ciki hadda sameera da bata san inda ta samu labari ba, su doctor seera kuwa zuwan su ba zai k'irgu ba. Ayman da mama haleema kamar su suke jinyar saboda yadda suka sawa ransu damuwa da tashin hankali akan ciwon.
Alhamdulillah zamu ce don jikin auntie yayi sauk'i sosai har an bata sallama ta dawo gida, sai dai likita ya kafa mata wasu tsauraran matakai da zata bi akan hawan jininta in tana son d'orewar lafiyarta.
Tunda ta dawo take yak'i da Ayman kan komawa office amma fafur yak'i, tun tana lallab'a shi har ta dawo mishi fad'a, ba don ranshi yaso ba ya shirya a safiyar yau ya tafi office, amma fa wuni yayi kiran wayarta data bud'e a safiyar ranar yana jin yanayin jikinta.
Da yamma kuwa daya taso hold up ya rirrik'e shi a hanyar komawa gida ba k'aramin cinkushewa ranshi yayi ba.
Tunda ya shawo kwanar layin yake kallon yarinyar kamar ya santa, matashiyar budurwa ce data sha kwalliya cikin suttura ta hausawa, riga da zani na atamfa sai gyale data yafa a kafad'arta ta rik'e hand bag a hannu, ta rufe rabin fuskarta da mask shiyasa ba'a gane ta sosai.
Ayman koda ya k'araso bai ko sake kallon inda take ba ya fara danna horn yana addu'ar Allah yasa tukur yana kusa ya bud'e mishi ba sai ya futo ba.
Addu'ar shi bata karb'u ba don yayi horn kusan sau uku ba'a bud'e mishi gate d'in ba, hakan yasa ya futo da kanshi zai bud'e.
Da sassarfa ta k'araso gare shi duk da a tsorace take kada wani ya ganka ya kaiwa mamanta rahoto.
"Assalamu alaikaa?". Fuska a d'aure ya amsa, "wa'alaikissalam".
Shiru tayi ta rasa abinda zata ce gashi har ya fara k'ok'arin huce ta, da sauri ta zare face mask d'in ta kira sunan shi da murya me taushi, "Ayman.....". Tsayawa yayi ba tare daya juyo ba, sai tayi taku kad'an zuwa bayan shi ta fara mishi magana da rawar murya, "yanzu kana nufin shi kenan, duk soyayyar da muke yiwa juna wani k'aramin abu ya raba mu?......".
A matuk'ar fusace ya juyo tana dire zancenta ya fara bata amsa da, "ba k'aramin abu ne ya raba mu ba Nur, babban abune da yafi k'arfin kan mu nida ke bare wata soyayyar mu ta rehu, kije ki tambayi mahaifiyarki kiji kota shirya bawa shege marar asali y'arta a yanzun...... Sannan wannan ya zama karo na k'arshe da zaki dinga nema na guri guri kamar wanda yaci muku bashi".
Yana gama yin maganar ya huce ta da sauri ya barta nan tsaye ko bi takan ta baiyi ba.

Yammacin ranar gaba ki d'aya haka ya kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali,,,,, duk yadda ya dawo da zumud'in son ganin auntie ta cire mishi haka a ranshi, k'arshe bai shiga ganinta ba sai dare, tana kishingid'e kan doguwar kujera tana waya da raihana,,,,, sun jima suna hirar kafun suyi sallama ta nemo layin khaleefa da shima take ganin kiran shi yana shigowa a lokacin da take wayar.
Shima sunyi hira dashi ba mai tsayi ba kafun suyi sallama ta ajiye wayar, hankalinta ta tattarawa Ayman d'ungurungum tace, "Ina fatan dai lafiya" squeezing face yayi kad'an yace, "lafiya qalou, me zan samu a gidan yau".
"Mama haleema zaka tambaya kasan itace a kitchen yanzu".
Tashi yayi yaje ya zubo abincin ya dawo nan kusa da ita ya fara ci, gaba d'aya Nur ta gama jagula mishi rai, ganinta da maganar data tuna mishi suka taru suka sake tuna mishi matsayin su da ya fara mantawa.
Auntie data ke can wata duniyar ta tunani ma nisawa tayi ta dawo da dubanta gare shi tace, "tafiya ta kamani zuwa Germany cikin satin nan da zamu shiga".
Da kyar ya iya had'iye abincin bakin shi ya tambayeta, "wani abu ya faru ne a can".
"A'a".
"Toh me yasa! Daga futowarki asibiti sai d'aukar doguwar tafiya kuma?, Ni ina ganin ki bari sai an kwana biyu kin sake warwarewa".
Murmushi tayi ganin yadda duk ya fututtuke baya son ta d'ara ko nan da can.
"Ba zai yiwu bane Ayman! Na yiwa raihana alk'awari kuma wannan tafiyar a gare ni ta dole ce".
Ganin yaja taja bata saki ba sai ya sawa zuciyarshi salama ya kyale ta kurum, Amma kwata kwata baya son tafiyar nan tata.

Kamar yadda ta fad'a Cikin satin aka kammala mata komai na tafiya sai lokaci kawai da take jira.

*********

Kamar kullum yau ma bayan ya tashi office bai koma gidan ba sai bayan sallar magrib, ya karb'i abincin da zaici a eve eno ya d'auki hanyar gidan.
Tana zaune tayi baja baja da littattafanta tana nazari ya murza key ya shigo gidan, bata d'ago kanta ba tayi mishi sannu da zuwan da batasan ba ko ya amsa, ko bai amsa ba don ita bataji komai ba sai k'arar rufe k'ofar d'akin shi da k'arfi. Saita fara had'e kayanta gudun kada ta aikata laifi a gare shi kafun wani lokaci ta b'ace wa ganin su.
Shi kuwa b'acin raine ya kama shi da ya bud'e k'ofar d'akin shi yaga komai a hargitse yadda ya barshi, gaba d'aya cikin satin baya samun lokacin da zai gyara muhallin shi, ko yanzu daya shigo a mugun gajiye yake ga maganar da sukayi da Ahmad d'azu. Tsaki ya dinga ja har yayi wanka yayi sabon shiri cikin kaya marassa nauyi, yayi sallar isha'i da shafa'i da wuturi. Tun kafun ya gama lazimi kiran Ahmad yake ta shigowa wayarshi yana katsewa har ya gama, wani sabon tsakin yayi a k'asan ranshi yana mitar Ahmad ba dai azalzali ba.
Koda ya futo bai sameta a parlon ba yasan maybe ta kauce zuwa d'akinta, sai ya nufi d'akin ya mata bugu uku zuwa hud'u.
A lokacin ta idar da sallah tana muraji'ar karatunta na al-qurani bugun k'ofar shi ya katse ta.
Riga ce doguwa a jikinta milk wadatacciya, saita yafa k'aramin gyalen rigar a saman kanta taje ta bud'e mishi k'ofar.
Kallo d'aya yayi mata yace, "in ba abinda kike zamu futa yanzu".
Gyad'a mishi kai tayi ta koma ciki ta d'auko wayarta ta dawo inda yake jiranta. Har suka futo a gidan bata daina tambayar kanta inda zasu da wannan daren kamar wasu munafukai ba.
Gidan da take kyautata zaton na Ahmad ne suka nufa, daga gaban gidan suka tsaya khaleefa ya kira shi ya shaida mishi isowar su.
Aikuwa a tare Ahmad da yasmine suka bud'e musu gidan, yasmine har ta kasa hak'uri saida tazo ta rungume ta tana mata oyoyo!
Karo na farko da raihana ta ziyarci gidan su, ba k'aramin farin ciki Yasmine da Ahmad sukayi ba da ganin su. Ina jin komai na gidan saida ta kawo musu duk a sonta na ganin ta tarye su da kyau irin tarba ta mutumci. Ruwa kad'ai raihana tasha, shi kam khaleefa ko ruwan k'in sha yayi (kunsan dai mutumin naku😜)
Suna gama gaisawa Yasmine ta janye raihana zuwa d'akin barcinta suka basu guri, ta bita da abinciccikan data shirya dominta kusan kala uku, kallon abincin raihana tayi tace, "nifa Saida naci abinci na futo".
"Niba ruwana da kinci abinci, wannan dana shirya da sunan ki ko baki ciba sai kin tafi dashi gidan ki...". Sanin hali akace yafi sanin kama, tsab zata aikata abinda ta fad'a. Sai ta d'auki abincin salin alin ta fara ci tana sauraron hirar da Yasmine take yi mata.


Khaleefa da Ahmad ma hirar su sukeyi akan abinda ya shafe su na k'ashin kansu, cikin hirar ne Ahmad yake mishi k'orafin rashin samun auntie a waya kwana biyu, ya k'are da tambayar, "Ina fatan dai tana lafiya".
"Lafiya lou Ayman yace kasan koba lafiya ba zasu fad'a ba, yanzu zaka sameta ta bud'e layinta jiya har munyi waya ma".
Ahmad yace, "insha Allah zan kirata zuwa gobe koda safe ne". Kallon agogo khaleefa yayi yace, "yea! Man dare fa ya fara nisa".
Ai shiyasa kuka k'i zuwa da wuri saida dare ya fara yi don ku gudu da wurwuri, Ni dai gaskiya ban karb'i wannan zuwan wayon ba".
"Hum! Ba zaka gane bane".
"Taya zan gane bayan ba'a yimun bayani yadda zan gane d'in ba".
Murmushi khaleefa yayi a wannan karon yace, "toh Allah ya huci zuciyarka". ya mik'e tare da yin doguwar mik'a, da gaske bacci yake ji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi.
Shima Ahmad mik'ewa yayi yace, "tom mun gode da ziyara Allah ya bar zumunci, bari na kira madame, ko zaka barta a nan su kwana da k'awarta". Khaleefa baice mishi komai ba, hasalima yi yayi kamar baiji shiba
Ahmad lalubo no Yasmine yayi cikin wayarshi ya fad'a mata raihana tazo zasu huce.
A lokacin har ta fara gyangyad'i sak'on su ya iso gareta ta hanyar Yasmine. Kamar jira take kuwa ta tashi da hanzari har yasmine na fad'in wai gidanta ba dad'i duk ta k'agara ta tafi ko, tayi murmushi kurum suka jero tare.

Har waje suka rako su suna ta musu godiyar ziyara.
Raihana dai duk a tsorace take da yanayin anguwar data sake zama tsit ba'a jin motsin komai sai haske tarwai daya haske ko'ina. Tsoronta yasa ta kasa nesa da khaleefa take binshi daf da daf.
Har sun fara tafiya Ahmad ya mishi magana da yaren jamus, "ba kaji ba". Juyowa yayi ita kuma raihana taci burki ba tare data juya ba.
"Wai kuwa kana nan akan bakan ka game da Saleema?".
Tambayar saita zowa khaleefa a bazata, kwata kwata bai d'auka abinda Ahmad d'in zaice ba kenan.
"Me yasa ka tambaya?". Khaleefa ya fad'a yana kallon shi.
Murmushi yayi ya sake cewa, "saboda naga ka daina bibiyar ta da lamuranta gaba d'aya, wanda naga hakan yana da kyau a matsayin ta na matar da kake son aure watan watarana, shareta ba itace mafuta ba yana da kyau tasan matsayinta a gurin ka".
Ajiyar zuciya khaleefa ya sauke yaci gaba da bashi amsa da yaren German, "kasan fa a inda muka ajiye zancenta ni da kai tun a wancan lokacin, meyasa zaka dawo da maganar yanzu bayan kana sane da ban samu komai cikin abinda zai kaini ga samun ta ba".
Wani kalar bahagon murmushi Ahmad yayi, a zuciyarshi yana ayyana abubuwa da yawa masu girma da k'arfin gaske, Sam khaleefa baya fahimtar abu cikin sauk'i, shiyasa gaskiya take wahalar dashi kafun ya ganta ya santa a yadda take.
Takowa Ahmad yayi har kusa dashi ya dafa kafad'ar shi, "khaleefa shiru ba amsar da zata wadatar bace, babu wanda zai fahimci abinda ka ajiye a cikin ranka in bakai ka fad'a da bakin kaba, masu iya magana suka ce waiwaye adon tafiya..... Ya kamata ka waiwayi Saleema ka mata tuni game da alak'ar soyayyar ku......".
Duk shiru sukayi kafun khaleefa ya gamsu da shawarar Ahmad d'in suyi sallama ya shige gidan shi, su kuma su k'arasa nasu gidan.
Yana bud'e k'ofa ya kunna haske ya gauraye ko'ina, a parlon ya zauna ya had'a kanshi da gwiwa yayi shiru yana nazari. Raihana dai dama suna shiga bata tsaya ba saida ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login