Showing 249001 words to 252000 words out of 288773 words

Chapter 84 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1109

kike turowa kawo mun abinci mai suna raihana?". Ya k'are maganar idon shi cike da ruwan hawaye kamar zaiyi kuka.
Wani irin sanyi jikinta yayi, tabbas ta karb'i nadamar sooraj a sarari duk da har yanzu zuciyarta bata gama hucewa da sakin k'awarta da yayi ba. Sai ta sauke ajiyar zuciya tace, "yaushe doctor jurgen Zai rubuta maka sallama?".
"Kwanaki biyar masu zuwa".
"Toh insha Allahu zan fad'a maka iya abinda na sani nan da kwana ki biyar d'in in muna da rai da numfashi".
Ganin yayi shiru sai ta sake cewa, "banga surayyah ba amma insha Allah akwai hanyar da zamu bi mu sameta wannan alk'awari nane".
Sai a lokacin ya d'an ji nutsuwa kad'an har ya sauke ajiyar zuciya, yasan ba zata tab'a yaudarar shiba.
Akan haka suka rabu ya tafi ya fara lissafin kowacce second, minute da hour har a kaiga wuni.

****Raihana kuwa ranar data kama weekend da safe tana kwance cikin bargo tak'i futowa parlon sam bare ta had'u da matsalolin khaleefa da baya rabo da neman magana yanzun, shiyasa tana gama had'a karin kumallo tayi shigewarta d'aki ta kwanta tana ta tsokanar yasmine ta wattsapp, a haka k'aramin sak'o ya shigo daga gurin likitar su khaleefa, sak'on da saida tayi ta juya shi a ranta da tunanin hanyar da zata cika umarnin likitan kafun can tayi k'undunbala ta rubutawa khaleefa gajeren sak'o kamar haka, "Assalam! Fatan ka tashi cikin k'oshin lafiya, Ina ta son maka wata magana amma tayi mun nauyi gashi bansan ta yadda zaka d'auki abun ba..... Shin kasan kuwa mahaifin ka yana rayeee?".
Khaleefa yana kwance, gaba d'aya tunda ya tashi sallar asubah bai koma bacci ba yana ta lazumin shin har yunwa ta fara sakad'ar cikin shi ya kasa jurewa.
Hakan yasa ya zura takalmin shi ya futo, sanye yake da jallabiyyah maroon colour data haska shi sosai, yana duba dinning yaga ta jere mishi abincin masu rai da lafiya.....
Ya fara bud'e pulasan k'amshin abincin na dukan hancin shi yana sake tunzira yunwar shi. Yana saving kanshi zai fara cin abincin sak'on ta ya riske shi, sai ya ajiye cokalin ya bud'e ya fara karantawa.....
Lokaci d'aya kanshi ya sara zuciyarshi ta harba, sai ya mik'e tsaye ko neman izininta baiyi ba ya shiga d'akin kamar an wurgo shi ya k'arasa har gaban gadon da take kwance yace, "ke kika turo mun sak'on nan?". Ta gyad'a mishi kai, sai ya durk'usa a gabanta, "ya akayi kika san haka? And kina nufin duk tsawon shekarun nan auntie k'arya take mana".
Sauƙe k'afarta k'asa tayi tace, "tayi hakane saboda b'acin rai da alk'awarin data d'aukar wa ranta, kamar yadda yanzu da kanta ta bud'e wannan babban sirrin ta kuma so kuji....".
"Innalillahi wa'inna ilaiji raji'un" ya fad'a had'e da dafe kanshi da hannuwan shi yana faman maimaitawa ko zaiji dad'i a ranshi. "me yasa auntie zatayi mana haka? Me yasa! Me yasa!!" Sai kawai ya fara kuka, a karon farko da raihana taga raunin shi har taji matuk'ar tausayin shi ya sake ninkuwa a cikin zuciyarta.
Inda ta adana diaryn nan taje ta d'auko ta dawo gaban shi ta durk'usa ta mik'a mishi, ya kalli littafin yana tuna sanda raihana take kan karatun shi harta dinga b'oye mishi, yasa hannu ya karb'a jikin shi a sanyaye ya fara karantawa, Koda ta yink'ura da nufin futa ta bashi guri hanata yayi, haka taci gaba da zama a gaban shi har ya karance abinda yake ciki tas ya fara sauke ajiyar zuciya, wani gefen na zuciyarshi na nuna tsananin tausayin mahaifiyar shi da kishin abinda mahaifin shi ya aikata mata.
"Lahaula walak'uwwata illah billahil aleeyul azeem". Sai kuma ya d'aga hannun shi sama yana fad'in "alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah na gode maka daka sa bata haramtacciyar hanya mahaifiyar mu ta samar damu ba...". Sai ya juyo ya kalli raihana kwayar idon shi harta sauya launi, tunanin shi shine meya kamata ya yiwa wannan yarinyar da dubun alkhairan ta gare shi? Ya kalli yadda duk ta kasa sakewa a gaban shi saboda suturar jikinta, riga ce iya cinya da wando tight jeans kanta ba d'ankwali sai tubkar gashinta data sauka har dokin wuyanta, ga gashin yasha gyara sai walwali yake. Sai ya fad'ad'a murmushin fuskarshi yace, "get ready nan da minti biyar kacal". Ko jiran amsarta baiyi ba yayi hucewarshi ya barta nan zaune tana bin bayan shi da kallo.
Doguwar riga kawai ta d'ora saman kayan jikinta ta yane kanta da gyale ta zauna tana jiran shi don kada ta b'ata mishi lokaci, zamanta ba jimawa shima ya futo cikin sabuwar shigar data k'ara futo dashi a asalin matashin saurayi mai ji da ilimi da kuma nasaba.
A motar haya suka futa sukaje wani babban shopping mall Gropius passagen ya dinga jidar mata kayan duk da hannun shi suka kai kai, tun raihana bata gane ita yake jidarwa wannan uban tulin kaya ba har ta fahimta ta fara k'ok'arin dakatar dashi. A lokacin kallonta yayi ido cikin ido yace, "Raihana! U deserve more than dis".
"Na gode sai dai wannan kayan sunyi yawa, inji da wanda na bari a gida ma....".
Murmushi kawai ya mata yana ganin duk yadda zai mata bayani ba zata tab'a ganewa ba, daga nan itama fara d'aukar mishi kayan maza tayi masu shegen kyau da tsada har ya gama ya taho gurin da take ko lura da kayan data cika basket d'inta dashi bai yiba. "Ke zaki tayani d'aukar wasu fa". Ya fad'a yana kallonta, "nima baka ga ina da wanda zan d'auka ba?". Sai a lokacin ya ankara da lodi lodin kayan data jibgo na maza, "ke zaki biya hala?".
"Eh amma ta hanyar rage wasu daga cikin kayan daka d'auka mun...". Murmushi kurum yayi yana ganin ba zata gane ba. Yana jinta a bayan shi tana cewa ya za'ayi ma kai ba zaka siya komai ba. Bai kula taba yaci gaba da tafiyarshi tana bin bayan shi.
Koda suka dawo gida yaga zata shiga kitchen hana ta yayi, sallah kawai sukayi ya sata ta k'ara futa suka tafi wani babban gurin cin abinci. Bata iya cin komai a gurin ba saboda banbancin d'and'ano da yawaitar idon mutane, k'arshe sai biyawa yayi Mc Donald's ya siya mata burger, pizza and chips, ya k'arasa da ita delabuu ice cream ya k'ara mata da kayan chocolate dasu ice cream d'in sannan suka koma gida.
Haka ya tara mata kaya na uban kud'i kuma a haka gani yake kamar basu wadatar ba, duk da kayan snacks da sweet basu wani dameta ba sai bata k'i ciba gudun kada ta sare mishi gwiwa. Taci burger da yawa tasha ice cream duk a gaban shi tana had'awa da mishi godiya.
Har dare khaleefa yak'i barta ta matsa nesa dashi sai labarin Auntie yake sake jaddada mata, gashi ta hana shi fad'awa Ayman a cewarta a bari sai an samu lokacin daya kamata, ko dinner tare sukayi cikin farin cikin daya wanzu a rayuwar shi daga safe zuwa daren ranar, lallai raihana ta gama musu komai a rayuwa tunda har ta silarta auntie ta bud'e musu babban sirrin da babu kamarshi.

*****Washe gari tunda yayi sallar asubah bai koma bacci ba kona 30 mint da yake yi in ya saita alarm yau babu shi sam a idon shi, haka ya shirya da wurwuri ya shiga kitchen neman ruwan da zaisha na safe kamar yadda yake bisa al'adarshi zai sha ruwa kullum da safe kafun yaci komai.
Tana tsaye d'aure da afron ash tashin ta kenan daga bacci yau a makare saboda yawon da khaleefa ya jata jiya data kwanta gajiya ta lullub'e ta sai yanzu da kyar ta samu ta farka, tayi sallah a gurguje ko azkhar bata tsaya yiba tayo kitchen gudun kada ya tafi bai sa komai a cikin shiba. Tana fara aikin sai gashi ya shigo, saita russuna tana gaishe shi, ya amsa yana kallonta tun daga k'asa har sama wani abu na tsirga mishi ata jinin jikin shi har ya haddasa mishi lumshe ido ya bud'e kan tulin gashinta da d'ankwalin ya zame k'asa saboda sauri bata tsaya d'auka ba.
Sit yaja ya zauna ya tsiyaya ruwa a cup yasha yaci gaba da kallon yadda take aikin da taka tsantsan. Fahimtar da gaske in yaci gaba da kallonta a haka za'a samu lukutar matsala sai ya koma parlon ya bud'e datar wayarshi ya shiga chat na k'arfi da yaji, tun yana d'an fahimtar abinda yake yi har ya gaza gane komai, idon shi ya rufe tsohon tsumin shi ya tashi matarshi kad'ai yake hangowa a idon shi, sai ya dinga jin haushin kanshi daya shiga gurinta har ya tsaya kallonta. "Mtsss!". Yaja tsaki shi kad'ai ya kife wayarshi kan kujerar da yake zaune ya kwantar da kanshi baya yana jin yadda komai yake son cakud'e mishi da yarinyar daya yiwa ranshi alk'awarin bar wa twin d'inshi don shi yafi cancantarta bashi ba.
Har ta gama aikin ta jere mishi abincin a dinning tana duban lokaci da yiwa Allah godiya data gama abincin taga yana da sauran lokacin karyawa a tsanake.
Bayan tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar material ta sake gyare gashinta daya hargitse gurin bacci, ta shafe jikinta da turare mai k'amshi, ta yane kanta da k'aramin gyale ta futo ta same shi yadda ta barshi, sai ta k'ara duba lokaci, toh yana da sauran mituna goma sha biyar za'a ce, cikin kulawa ta k'arasa gab dashi kamar zata dafa kafad'arshi tace, "kana lafiya kuwa?".
Ya bud'e idon shi suka sauka a kanta, k'amshin sassanyan turaren ta na kaiwa cikin hancin shi, baice komai ba ya tashi zaune da murya mafi k'asa yace, "kawo mun abincin nan, kiyi saving d'ina bada yawa ba". Ta juya cikin karb'ar umarnin shi ta kawo mishi abincin har inda yake ita kuma ta koma dinning zata karya a can. Bai wani ci na kirki ba ya mata sallama ya tafi aikin shi yau ko Ahmad bai jira ba yayi tafiyarshi.

****A yammacin ranar doctor jurgen Ya rubutawa Suraj takardar sallama bayan an tabbatar daba wata matsala cikin gyaran da akayi mishi, yayi sallama da kowa har su Ahmad ya tafi gurin andal da zumud'in jin labarin inda zaiga surayyan shi.....
Ya sameta suka tattauna, bata fayyace mishi komai ba saboda wasu dalilan, ta nuna mishi wannan raihanar matar d'an surayyah ce amma zuwanta na k'arshe gurin shi mijinta ya d'auke ta sun huce Saudi zasuyi umrah na sati d'aya daga nan su huce Nigeria. Sai ta k'ara da cewa, "Ni nan da kaina nayi maka alk'awarin zanje Nigeria gurin su na tabbatar na Nemo maka inda surayyah take don yarinyar nan ta bani tabbacin tana kan alk'awarin tane shiyasa tak'i neman ka duk tsawon wannan shekarun".
A wannan karon hak'urin sooraj ya k'are, ta kaishi limit d'in da bazai iya jurar ci gaba da sauraron labaran tatsuniya daga gare taba, sai kawai ya mik'e tsaye gabanta da raunatacciyar murya tace, "ya kamata ki daina yaudarata haka andal, ba dai don naji dad'i hankalina ya kwanta kike k'irk'irar duk wannan labarin ba? Toh ya isa haka don Allah! Na hak'ura nasan watak'ila nida surayyah har abada, sai dai ko in mun had'u a laheera za'ayi mana hisabi......".
Jikinta yayi sanyi fiye da kullum tausayin shi na ratsa ta, sai dai a halin yanzu muddin tace zata had'a shi da khaleefa zata had'a jagwal don hutun data d'aukar musu ita da khaleefa sai sati na sama, and so take har wancen d'an uwan nashi yazo, so take yaran su same shi a family house d'insu kowa ya gansu.
"Kayi hak'uri amma wallahi summa tallahi nayi alk'awarin zan zo tare da wanda suka san inda surayyah take har garin ka gidan ka.... Amma kafun nan ina son na d'auki hutu don bazai yiwu na yanke aikina ba tare dana ajiye kwakkwarar hujja ba....".
Sooraj shiru yayi bayan gama sauraronta, ya yarda da rantsuwarta amma yana shakkun zuwanta da addu'ar Allah yasa ba yaudara bane, cikin wannan k'ila wa k'alan ya mata sallama ya futa daga cikin asibitin, kwana biyu kacal zai k'ara ya bar k'asar.

**** Ya dawo aiki da yamma lis lokacin raihana bata dawo gidan ba, d'akin shi ya shige ya rufo ya kwanta akan gadon shi ko takalmin k'afar shi bai iya cirewa ba. Yana jin wayarshi nata sharara ringing amma ya kasa picking haka kiran ya dinga shigowa yana katsewa ba k'auk'autawa.
Raihana koda ta dawo bata fahimci yana gidan ba tayi duk abinda zatayi a gurguje ta shige d'akinta don tara hankalinta ga mutanen da suke ta son magana da ita.


_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy one 7️⃣1️⃣


Hirar data jima ba tayi da kowa ba ta samu dama a yau, aikuwa ta gaisa da mutane da yawa da tayi nesa dasu, a k'arshe suka k'are hirar su ita da doctor k'awar doctor inda take fad'a mata ya kamata a tsara tafiyar har Ayman.
Suka jima suna tattauna yadda komai zai tafi kafun suyi sallama ta ajiye wayar, tana jin wata matashiyar budurwa na yiwa likitar magana kafun wayar ta katse, kusan duk lokacin da zasuyi waya a gida sai taji maganar matashiyar yarinyar, tana kyautata zaton y'arta ce ko surukarta don tasan a shekarunta zaiyi wuya a rasa d'aya cikin biyun data ayyana.
Koda raihana ta duba lokaci sai taga ashe dare ya fara nisa, ta d'auro alwala ta shige cikin bargo tare da wayarta, k'aramin sak'o ta rubutawa khaleefa duk da zaton yayi bacci.
"Assalam! Zaka iya sa Ayman ya shirya cikin satin nan ku had'u a Abuja ganin mahaifin ku? Amma fa ba buk'atar ka bud'e mishi komai ya kamata a mishi bazatan dai....".
Tana tura sak'on ta wulla wayar gefe ta karanto addu'o'in ta na bacci ta k'ara rufe har kanta.
Ba jimawa kuwa wani sumammen bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Lokacin da sak'on ta ya riske shi yana kan darduma ne idar da sallar shafa'i da wuturin shi kenan yana lazumi yaji k'arar shigar sak'o, ya mik'a hannu ya d'auka don tun daya dawo gidan bai duba wayar ba, yasan maybe cikin wanda suka gama jera mishi kiran nan d'azu wani ya kasa hak'uri saida ya mishi txt.
Sab'anin tunanin shi daga gurin raihana ne, sai dai ya karanta sak'on yafi sau hud'u bai fahimci abinda take nufi ba, sai kawai ya yanke hukuncin danna kiran no ta don yaji gundarin abinda take nufi, cikin rashin sa'a tayi bacci kuma wayar a silent ta barta.
Bazai iya hak'uri ba sai yaji komai duk da tunanin shi ya bashi barci take. Kamar wanda ake azalzala haka ya zura soft sliffas d'inshi ya futo daga d'akin hasken parlon ya haske shi tarwai, ya tsaya ya rage wutar sannan yaci gaba da takawa gently har cikin d'akinta. Ya tura k'ofar ya shiga kamar b'arawo yana bin komai na d'akin da kallo wata nutsuwa na kwaranya ruhin shi, dawwamammen k'amshin d'akin da yake son a dinga sammi shi a nashi d'akin shima na k'ara tsuma shi. Cikin duhun daya mamaye ko'ina ya isa har gaban gadonta ya durk'usa ya fara janye lallausan bargon data rufe jikinta gaba d'aya har fuskarta ta bayyana, sai ya tsurawa fuskarta idanu yana kallonta da yadda take sauƙe numfashi cikin nutsuwa da jin dad'in baccin nata. Ya d'auki lokaci mai yawan da baisan iyakarshi ba a gabanta yana kallon innocent face d'inta sannan yaja mata bargon ya mik'e ya fuce daga d'akin gaba d'aya.
Saida yasha tea sannan ya koma d'akin shi, a daren ranar ya jima kafun bacci yayi awon gaba dashi.

****Asubar fari duk suka tashi a gidan ba tare da kowanne cikin su ya sani ba, khaleefa duk da yadda ya kwana da tunanin sak'on ta bai nemi ganinta ba sai bayan daya idar da sallah yayi azkhar d'inshi cikakke, yayi wanka yayi duk abinda yake gabatarwa da safe kafun futarshi aiki.
Lokacin daya futo har ta shiga kitchen gidan tsit sai b'uruntun ta kawai da k'amshin girkinta ke tashi, sai ya nufi kitchen d'in bakin shi d'auke da sallama. Tana tsaye tana firar dankali sai dai jikinta a suturce da wadatacciyar sutturar data b'oye surar jikinta gaba d'aya. Tana ganin shi ta russuna ta fara gaishe shi, ya amsa yana kai kofun ruwan daya tsiyaya bakin shi.
Daya gama shan ruwan ma saida ya d'auki wasu mintuna sannan yace, "me kike son cewa a sak'on ki na jiya?".
Rage gudun futar gas d'in da take aiki dashi tayi tace, "hala baka duba abinda na rubuta ba da kyau?".
"Ni abinda ban fahimta ba shine, wa yake shirya komai ta hanyar amfani dake?".
Shiru tayi ba tace komai ba, sai yayi murmushi ya sake cewa, "koda yake ba buk'atar na sani yanzu, bari muga har zuwa lokacin da zata fashe ko?,,," ya k'are maganar da sigar zolaya. K'asa tayi da kanta ba tare data yarda ta sake kallon kwayar idon shiba. Har ta gama aikin yana kitchen d'in, danne danne yake a waya rabi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login