Showing 87001 words to 90000 words out of 288773 words
Chapter 30 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
gaishe ta kafun ya fad'a mata cikin shine yayi ciwo, zama tayi gefen bed d'in tana kallonshi kafun ta fara magana cikin fusata fusata, "Ayman ne baya ji wallahi khaleefa, na hana shi zama da yunwar nan amma yak'i, idan yaci abincin safe baya sake cin wani abu sai yamma ko dare, ba dole ulcer ya rik'e mishi k'irji da ciki ba, akwai wasu magungunan shi cikin drower can yasha?".
"A'a na sauya mishi wani shine ma yaji dama dama, saboda wad'an can d'in..... Ni bansan ma wane shashashan likitan bane ya bashi su". Kwalin maganin khaleefa zai d'auka sai kuma ta riga shi d'aukewa, Saida ta duba maganin ta karance kwalin tsaf sannan ta mik'awa khaleefa. Ya karb'a ya zura cikin drower.
Haka Auntie tayi ta mita kan rashin son cin abincin shi khaleefa na bata hak'uri.
Da kanta tasa shaheeda ta kai musu abincin karin kumallo har d'akin Ayman d'in. Duk da babu datti ko d'igo a jikinta, amma saida ta sake gyara jikinta ta shafa turarenta, taja siririn gyalen dake kanta ta d'auki trayn abincin tayi d'akin.
Saida ta nemi izini khaleefa ya bata, lokacin shima Ayman ya tashi yana zaune dai kan bed bai tashi zaune ba. Ta cikin glass khaleefa ya kalleta, bai manta taba itace tazo d'aukar su waccen ranar a airport, sai ya maida kanshi ga abinda yake yi, a kusa dashi ta ajiye abincin ta fara gaishe su d'aya bayan d'aya ta d'ora da yiwa Ayman sannu, ya amsa cikin kulawa.
Tana futa khaleefa ya dawo da duban shi kanshi, "sannu da jiki, hope yanzu kana jin jikin naka da sauk'i dai". Murmushin k'arfin hali yayi yace, "da sauk'i sosai ma, nayi mamaki kaida kake likitan k'ashi amma kasan wancen maganin na ciwon ciki". Murmushi shima yayi don tambayar d'an uwanshi ta bashi dariya ne, "ba maganin daya kamata yake baka ba, wannan dana rubuta maka shine wanda zaka dinga sha a duk lokacin da kaji alamun tasowar ciwon, sannan auntie tayi complain akan baka son cin abinci, magani bazai tab'a yi maka amfani da yunwa a jikin ka ba, ka tabbatar ka tsayawa cin abinci akan lokaci insha Allah zaka samu lafiya a jikin ka ko baka sha maganin ba, kayi k'ok'arin fara tsira da wannan saika zauna lafiya".
Cikin jin dad'in kulawar khaleefa Ayman yace, "insha Allah zanyi yadda kace nagode da kulawa....."
Katse mishi hanzari yayi, "Kada kace komai na had'a maka ruwan wanka masu zafi shiga ka futo mu karya kumallo, kafun nan nima zanje na shirya na dawo, cikin na'am Ayman ya lallab'a ya mik'e. Shima khaleefa mik'ewar yayi.
Ko bayan duk sun shirya tare suka had'u suka ci abincin, abinda ya jima bai faru ba tun tsawon lokaci kafun tafiyar shi Germany. Yadda khaleefa ya bawa Ayman cikakken lokacin shi sai ya taimaka wajen warwarewar garkuwar jikin shi ta dawo normal da wuri.
Ranar wuni sukayi tare cikin farin ciki suna hirar su ta zumunci da abubuwan da suka faru a bayan idon khaleefa, har futa auntie tayi ta dawo, haleema ta tabbatar mata tana aikinta tsakanin parlour da kitchen duk futar su sun dawo suna tare a ciki. Sai taji wani sanyi ya kwaranya ruhin ta, yau ga yaranta kansu yana shirin sake had'uwa su koma kamar yadda suke da farko.
Suna parlon d'akin su, khaleefa yana kwance yana saita sabon sim d'in da Ayman ya kawo mishi tun jiya a wayarshi, shi kuma Ayman yana zaune yana kallon wani program da ake gabatarwa. Tana yin sallama duk suka mik'e zaune suna yi mata sannu da dawowa, Zama tayi a kusa da Ayman ta ajiyewa khaleefa mukullin mota a gaban shi, "kyauta ta na tayaka murnar kammala karatun ka cikin nasara". Wani d'an ihu Ayman yayi yace, "khaleefa irin motar da kake mafarkin samu tun muna yara, auntie thank you, thank you Soo much we really appreciate.... We have no one like you sweet mum".
Murmushi tayi hankalinta na kan khaleefa don taga yadda zai karb'i kyautar tata, ta mishi ko batayi ba. Shikam juya mukullin motar kawai yake a hannun shi, cikin nutsuwa da sanyi yayi mata godiya, ba irin nuna farin cikin nan da ihu kamar yadda Ayman yayi don ta mamaye su ba zato.
Kallon Ayman tayi ashe shima ya kalleta sai suka had'a ido, shi kuwa khaleefa mik'ewa yayi rik'e da mukulli da wayar ya sake mata godiya ya huce bedroom d'inshi, a jikin k'ofar ya kifa kanshi ya fara kokawa da zuciyarshi, so yake ya daure ya danne abinda yake ji a kanta a duk lokacin daya tuna Saleema da yadda zai rasata saboda ita,,,,,
Auntie kuwa ajiyar zuciya ta sauke mai tsayi tacewa Ayman, "ya fad'a maka yana da yarinyar da yake so?". Girgiza kai Ayman yayi, nan auntie ta labarta mishi komai da ya fad'a mata. Yayi murna sosai ya nuna farin ciki da jin dad'in shi a fili, abun da bai tab'a zato ba ko a mafarki shima.
Kwana biyu a tsakani binciken khaleefa ya kammala, hakan yasa ya shirya futa wajen iya da malam. A d'akin auntie ya samu Ayman yana breakfast nuriyyah a gefen shi suna hirar su cikin farin ciki. Tana ganin khaleefa ta durk'usa tana gaishe shi, ya amsa kai tsaye ya d'auke kanshi daga kansu gaban shi yana fad'uwa, baya son alak'ar Ayman da yarinyar nan, haka kawai yake jin wani abu a kanta mai kama da zargi, tsoron shi d'aya kada ta karyawa d'an uwanshi zuciya irin yadda Saleema tayi mishi, ya fahimci yanzu a rayuwar nan ba wanda zai basu auren y'ay'an shi ba tare da ya san asalin suba, ganganci ne da kuskure auntie take shirin aikatawa. Koda yake ta hakane zata gane duniya taci gaba, mutanen cikinta sun waye, kowanne d'a da ubanshi yake ado.
Ganin yadda yake neman part d'in auntie sai Ayman yace mishi, "tana ciki mammie ce tazo suna tare". Kan d'aya daga kujerun parlon ya zauna yace, "akwai abinda kakeyi yanzu?". "a'a wani abu ne?". Ayman ya tambaye shi, khaleefa shafa sumar kanshi yayi yace, "eh gidan iya nake son zuwa". Mik'ewa Ayman yayi "da gaske! ai ko akwai abinda nake yi zan barshi saboda uzurin ka yana gaba da komai nawa.....". Shima khaleefa murmushin yayi, yana nan zaune har Ayman ya sake futowa cikin shiri, sai ya fara sauka k'asa don ya basu guri suyi sallama da juna. Ba suyi doguwar magana ba Ayman yayi sallama da Nur ya futo ya same shi, saida suka tsaya gurin Auntie da mammie suka gaisa sukayi musu sallama sannan suka futo. A sabuwar motar khaleefa suke tafiya, Ayman yana tuki yayinda hankalin khaleefa ke gefen window yana k'arewa garin kallo, jinshi yake kamar bak'o a garin musamman daya lura da sababbin gine ginen da akayi akan hanya. Babu laifi an samu ci gaba kad'an akan sanda ya tafi.
Juyowa yayi ya kalli Ayman da yake tuk'in shi hankali kwance yana bin wakar turanci ta love you baby, rage sautin wakar yayi yace, "Ayman wannan dana ganku yanzu itace Nur". Ayman da yake jinshi yau cikin farin ciki na haka kawai yace, "Eh itace princess d'in yaka ganta bro". Shima murmushin ya mayar mishi, "tayi!! ba laifi tana da kyau, gata fara gata doguwa kyakkyawa dai ta k'arshe, sai dai ina fatan Allah yasa yadda fuskarta take haka zuciyarta take". Rage gudun motar shi yayi ya d'an kalleshi da wani yanayi mai kama dana sanyin jiki da sagewar gwiwa yace, "da kayi wannan maganar saika tuna mun da raihana, itace mai yawan fatan zuciya iri d'aya da fuskar mutum, toh ni dai gaskiya tunda nake da Nur ban tab'a ganin abu makamancin mummunan hali ko rashin tarbiyyah ba, ba wai don auntie tana tare dasu ba a'a sai don gaskiya duk inda tazo a fad'e ta, kaf y'ay'an mammie sun samu tarbiyyah irin wadda addinin islama yazo da ita, shiyasa nake fatan rayuwa cikin farin ciki bayan auren mu da Nur". Nazarin kalaman shi khaleefa yayi kafun ya nisa yace, "Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairin shi". Ayman yace, "ameen".
K'aro mishi volume din wakar shi yayi, basu sake cewa juna komai ba har suka k'arasa gidan iya. Khaleefa ya bud'e murfin k'ofa ya futa shi kuma Ayman ya tsaya yana kallon gidan su raihana ba tare daya futo daga ciki ba........
_Na kasa fahimtar Ayman ni kaina, shin sabo ne yake sashi jin kewar raihana ko kuma dai akwai wani abu da yake shirin faruwa dasu_
_Bazan fasa jinjina muku ba masoyan asali, Maryam sulaiman, ummee sa'eed abdallah, khadija maman khaleefa, maman mu'awiyya, mardiyya mai damashi, k'awata, aminiyata, in-identical sis d'ina Dr Ferhyeez m usmern, Fatima Abdullahi...... da dukkannin d'aukacin members na JARUMAR UWA fans group da sauran masu bibiyar novel d'in mu, comment d'inku shike sake k'ara mun k'arfin gwiwa a koda yaushe, na jinjina muku dukkan ku, much love_
_*littafin JARUMAR UWA tun daga farko har k'arshe sadaukarwa ne ga mahaifiyata, farin cikina, best & close friend to me, first love d'ita, lovely ummata......... I'm froud of you mom like no other*_
Happier Jumu'at Kareem to oll Muslim umma
A sama zaku ga link na group d'in *DARAJAR HAK'URI* ne domin samun littafin mahadin jarumar uwa akan kari. Ngd
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page twenty five2️⃣5️⃣
"Me kake kallo kuma?" Khaleefa ya tambaye shi, sai ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace, "ba komai" tare suka jera har cikin gidan iya.
Iya da take parlour tare da bak'i suna magana sama sama kamar fad'a, ganin su yasa ta futo da sauri da fara'ar ta tana musu marhaba, ganin da mutane a d'akin sai basu shiga ba suka tsaya daga tsakar gida khaleefa ya nemi kujerar roba fara ya zauna, Ayman ma kusa dashi ya zauna, sun gaisa da iya tana tambayar su yadda suka baro surayyah, sukace "tana lafiya alhamdulillah". Daga nan bata ja dogon zance ba ta koma d'aki ta sauyawa bak'in ta masauki zuwa sitting room na gidan, kamar ma bata so su khaleefan suka gansu ba, dangin sune dai na can k'auyen su a karo na farko da wani ya biyo bayan su tunda suka zo maraya, khaleefa yabi su da kallo bayan sun gaisa yana sake tabbatar da zargin shi akan iya da mahaifiyar su. Cikin parlon tasa suka shiga, suka zauna kan kujera, gidanta fess kamar a zuba ruwa a k'asa asha, dama tun can sun shaida iya a b'angaren tsabta, macece mai tsabta da yin komai tsab tsab, gidanta ko shirgin nan babu kamar ba gidan tsohuwa ba, ruwa da lemuka ta kawo musu masu sanyi, ta k'ara da zubo musu d'umamen tuwon shinkafa ne miyar kub'ewa da yasha man shanu da yajin daddawa. Ayman saida ya lumshe ido a lokacin daya shak'i k'amshin abincin, "daga jin k'amshin tuwon nan nan dole ma zaiyi dad'i". Duk dariya sukayi mishi, khaleefa yace, "tun kafun kaci ka fara santi". Iya tace "aikuwa dai kam", ruwan wankin hannu ta kawo musu suka wanke sannan suka fara cin abincin da Bismillah. Shi kanshi khaleefa tuwon ya mishi dad'i, in banda abincin iya da auntien su a da ba abincin wanda yake iya ci komai iya girkin mutum kuwa, kuma har gobe ba kowanne abinci yake iya ciba saina wad'an da ya aminta dasu.
Yaci tuwon da yawa don bai yi breakfast ba yau duka, kafun ya zare hannun shi ya wanke, iya da ta shimfid'a tabarma saman carpet tana k'ullin gyad'a ya tambaya, "yau malam baya nan ne?". tace, "yana ciki akwai abinda yake yi kana son ganin shine?".
"Eh Ina son akwai maganar da zamuyi dashi in ya gama". Iya tace, "ba damuwa yana gamawa zan fad'a maka sai ka shiga ku gaisa". Ayman saida ya sid'e kwano har iya na tambayar shi ko ta k'aro mishi ne, yace, "a'a iya in kika k'aro wani kuma ai cikina saiya fashe". Iya tayi dariya khaleefa kuma da yake gefe yayi murmushi, sunci gaba da hirar su shida iya shi dai khaleefa danna wayarshi kawai yake sai in sunyi abun dariya yayi murmushi, suna hirar iya ta ciko plate da gyad'a ta ajiye musu, aikuwa Ayman yana ganin gyad'a ya soma murmushe ta yana aikawa cikin shi, sai khaleefa ya tsaya kurum yana kallon shi, kafun ya magantu, "Dole ka zama Mr fat ashe in kazo gidan iya komai na gidan saika cinye kake tafiya". Shi dai Ayman gyad'ar shi yake taci sauri sauri yana satar kallon iya kamar mara gaskiya. Itama maganar khaleefa ce ta d'auki hankalinta har ta d'ago tana kallon Ayman d'in, "a'a yau nake ganin mugun abu! Ya zaka cinye gyad'ar dana baku ku biyo? Kai magaji kana kallon shi fa....". Da sauri Ayman ya d'auke wayar shi da plate in gyad'ar yaja baya kusa da d'akin gadon iya sannan yace, "kin manta iya khaleefa baya cin gyad'a tun muna yara". Aikuwa iya ta saki baki tana salati da tafa hannu, shaf ta manta khaleefa baya cin gyad'a tun da can, ta yink'ura zata tashi da nufin karb'e gyad'ar ta, ya shige d'akinta da gudu ya rufo. Saita koma ta zauna tana fad'in, "ai shi kenan! Amma gaskiya bazan yi shiru ba laifin kane magaji, fisabilillah kasan na manta baka cin gyad'a dazan baku ba sai ka tuna mun ba? Shi wancen kamar an mishi k'auri da kurege goman wannan ta gabana ma sai ya cinye ba gajiya yake ba, ka barni kana kallo na dunguje mishi ribar gaba d'aya". Banda dariya ba abinda khaleefa yake ciki ciki Cox iya da Ayman sun bashi dariya matuk'a yau, Ni kam sai na tsaya kurum Ina kallon wani b'oyayyen kyawun shi da banbancin shi da Ayman wanda sai mutum ya nutsu zai iya gani, duk da a yanzun ma sun banbanta sosai.
_Kwanaki biyu kafun yau_
Raihana ce zaune kan sallaya da talatainin dare tana kai kukanta ga mai duka, sarkin da babu wani sarki a gaban shi ko bayan shi, sarkin da yake da k'arfin iko da mulkin sarrafa kowa da komai na wannan duniyar, shi kad'ai ne zamu rok'a yayi mana mu sake rok'on shi ya sake yi mana, koda zamu k'are rayuwar mu muna rok'on shi ba zai gajiya wajen yi mana ba, rabbil izzati ubangijin sammai da k'assai. A yau raihana Kukanta take kai mishi akan ya magance mata matsalolin da suke tunkarota, a wannan karon ta fara damuwa da maganganun mutanen gari da dangin su, so take tayi aure kota kawo k'arshen matsalar nan su huta ita da ummienta haka, koda ace Imran zai sake ta a washe garin auren su ta amince zata aure shi muddin zasu shaida cewa ta tab'a aure ko a tarihi, ta fahimci cikin datsin ummie kanta hankalinta a tashe yake da wannan sabon ibtila'in daya tunkaro su, duk da koda wasa Imran bai tab'a sub'utar bakin fad'a mata cewa maman su bata son ya aureta ba, ya b'oye mata komai hakan yasa ta sakankamce har tana tunanin k'arshen matsalolin tane suka zo, sai gashi rana tsaka ana sake shirin tada musu zaune tsaye, mahaifiyar Imran da kanta take aiko musu da mugayen bak'ak'en maganganu akan ta rabu mata da d'anta, in ba haka ba zatayi dana sani don karo da ita ba dad'i, tabi guri guri ta fad'awa mutane da y'an dubiya cewa raihana ce me bak'ar k'afa tunda Imran ya had'u da ita masifu suke ta bibiyar rayuwar shi daga wannan sai wancen, bar gashi yanzu rayuwar shi tana shirin salwanta ata sanadiyyarta, saboda binciken y'an sanda ya nuna musu wani akayi harin poisoning Imran ya fad'a tarkon. Kuka take sosai tana rok'on ubangiji ya kawo mata d'auki a cikin wannan rayuwar, bata fasa neman zab'in Allah ba don har gobe lamuran ta gaba d'aya ta mik'a su gare shi.
Ta jima tana addu'a da kuka akan sallaya kafun ta shafa, bata iya komawa kan gadon ba ta kwanta a nan k'asa tana tunane tunanenta har bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.
@@@@@@
Washe gari ta tashi jikinta duk a mace, haka dai ta lallab'a tayi duk abinda zatayi a gidan, ta yiwa jidderh wanka ta shiryata cikin uniform, ta zaunar dasu suka karya suka huce makaranta, itama wankan tayi, bata son cin komai amma tasan fad'an auntie in ta tabbatar bata ci komai ba, haka dai ta tuttura, abban su kafun ya futa da kanshi ya kirata ya dinga K'arfafa mata gwiwa da ban hak'uri akan abinda yake faruwa, taji sanyi a ranta ba kad'an ba, koba komai ya bata sabon hope.
Da yammacin ranar tana kwance a parlon su tana kallon wani series wayarta da take gefen kanta ta d'auki ringing, da sauri ta d'auko zata duba tunaninta ko Ayman ne ya tuna da ita yau, ko kuma Imran ne ya samu faragar kiranta in maman shi ta futa. Ba d'aya a cikin su, k'awar tace raheelatu, sai tayi picking da sauri tasa handsfree ta ajiye wayar a gefenta, sun gaisa cikin farin ciki tare da tambayar lafiyar juna da y'an uwa, sun d'auki lokaci k'alilan suna waya kafun suyi sallama, bata ajiye wayar ba saida ta kira Fatima itama suka gaisa taji lafiyar ta da y'an gidan su sannan, itama kamar raheela ta tambaye ta ya maganar bikinta, ta fad'a musu da saura zata fad'a musu in lokaci yayi.