Showing 180001 words to 183000 words out of 288773 words

Chapter 61 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1063

dashi ta kalleta da mugun mamaki tace, "see you don Allah! Ke yanzu ko kunyar kanki baki jiba wai kin kasa bacci sai b'arawo saboda wani can da baisan kina yiba,,,, don Allah k'awata kada ki maida kanki bagidajiya ni miji har saina tsaya neman wani yardar shi kafun aiwatar da abinda ya zamo mun dole? Bada karatun ki ya ganki ba?".
Da k'arin damuwa shaheeda ta girgiza mata kai, "ba zaki gane ba feena! The fact is mammie ce tace dole saina nemi izinin shi kafun komawa makarantar,,,, kuma ke kinfi kowa sanin abinda ya had'a mu wancen ranar,,,, da muna da guntuwar alak'ar kwanciya muhalli d'aya da kuma gaisuwa, amma a yanzu ko kallon banza ban ishe shiba bare har nace naga fuskar da zanyi mishi wata magana irin wannan....".
Mik'ewa tsaye feena tayi ta d'auko ruwa me sanyi a fridge tasha, ta sake kallon shaheeda data zuba mata ido tana jiran a sama mata mafuta, "Wai baki da wani abinci a gidan ki ne shaheeda, saboda azalazalarki fa ko breakfast ban samu nayi ba na futo daga gida".
"Allah safeenatu kina da matsala! Ya ina miki magana mai muhimmanci kina kawo mun shiriritarki, waccen ranar akan maganar maganin nan mafa haka kika yimun kika barni ba gamsashshiyar amsa".
"Ohh! Shaheeda kina nufin yunwar cikina ce shiriritar?". Feena ta fad'a tana nuna kanta
"Eh mana toh nima ko abincin ban iya ci ba tun safe, infact ban dafa komai bama yau".
Tab'e baki feena tayi tace, "ke kika ji zaki iya,,,, muyi mu gama maganar mu in tafi inda zan samu abinda zanci don akwai lukutar matsala in naci gaba da zama a haka". Saita sake zama kusa da ita tana tambayarta, "Wai kina nufin tun waccen ranar bai sake waiwayar kiba".
"Eh mana! Ba abinda nake ta k'ok'arin fad'a miki ba kenan waccen ranar da kika zo amma kika k'i saurarona,,,, wallahi feena na rasa yadda zanyi". Shaheeda takai k'arshen maganarta kamar tayi kuka.
Feena ganin yadda shaheeda ta d'auki maganar serious saita kama kanta itama ta zama serious, "yanzu ya kike son ayi shaheeda? Ni kike son naje naba mijinki hak'uri ko kuma yaya".
Cikin damuwa shaheeda tace, "haba feena ki fahimci abinda nake nufi mana, mutumin nan ko kallona baya yi fa".
Feena cikin k'osawa da jin magana d'aya a gurinta tace, "toh ke sai kace ba mace ba, kibi duk hanyoyin daya dace mana ku shirya saiki tambayeshin tunda b'uruntun bakin ki yasa kin fad'awa mammie harta kafa miki sharad'i,,,,, sannan naji kina batun wai maganin dana baki kwana ki menene....".
Shiru shaheeda tayi tana nazari kafun can tace, "na tambayeki ai yaushe zai daina aiki baki fad'a mun ba".
Dariya sosai feena ta mata kafun ta d'an tsagaita tace, "ke nifa ba wani magani dana baki tsokanarki nake wallahi,,,,".
Cikin rashin fahimtar ta shaheeda tace, "ban gane ba".
Feena tana dariya tace, "ai dama ba zaki gane ba,,, toh in banda kema taya zaki yarda da duk abinda na fad'a miki sai kace baki san wace niba.....".
Tsabar takaici shaheeda sai kawai ta fashe da kuka tana kallonta tana fad'in, "Amma feena ban yafe miki ba wallahi,,, yanzu fisabilillah taya kike tunanin zan shawo kan Imran har mu daidaita mu zauna lafiya? Kinsan fa ni ba fiye jure tashin hankali nayi ba".
Feena tana dariya har lokacin tace, "toh ni taya zan sani nida ba matar aure ba,,, abu d'aya kawai dana sani ki cire girman kai ki bashi hak'uri,,,,, shima dai don wani irin baud'ad'd'e ne in banda haka taya zai iya d'auke kanshi daga zukekiyar budurwa kamarki k'awata....". Ta kai k'arshen zancen tana share mata hawayen fuskarta had'e da bata hak'uri.
Da kyar ta samu ta shawo kan shaheedan ta hak'ura, tare suka shiga kitchen suka dafa abinda suka ci, feena bata tafi ba har saida ta kusa yin late suna ta shawarta me yiwuwa ita da k'awarta, shaheeda har bakin get ta rakata duk k'annen Imran sun ganta amma bata shiga cikin gidan donta gaishe da hajiya tafeeda ba, Koda wasa tunanin hakan baizo kanta bama.
Washe garin ranar da wuri ta tashi tayi duk abinda ya dace, tayi kwalliyarta mai kyau cikin doguwar riga y'ar gaske ta zauna dakon futowarshi, bata jima da zama ba kuwa ya futo da shirin futa office kamar kullum.
Saita tashi da sauri ta russuna tana gaishe shi, ya d'auke kanshi tamkar bai ji taba, ganin ya d'auki hanya da gaske zai futa sai tayi shahada tace, "Ina son zan koma makaranta".
Ba tare daya waiwayota ba yace, "zaki iya fad'awa mom don ita ta auro ki kuma zamanta kike". Yana gama fad'a ya dusa kanshi ya fuce.
Shaheeda a gurin ta zauna tana tuna kalmar mom daya fad'a, in banda yanzu daya ambaci sunan mom ta manta da ita gaba d'aya a cikin babin rayuwarta, tunda ya fad'i haka ba wata mom da zataje tambaya tafiyarta kawai zatayi ai aurenta ba'a hannunta yake ba.

@@@@@@@@

Washe gari shaheeda ta shirya tunda wuri ta d'auki katin cirar kud'i ta fuce a gidan tayi tafiyarta makaranta, abinda ya d'aure kan mom kenan don an tabbatar mata anga futar shaheeda a safiyar yau,,,,,, zuwa yanzu lamarin shaheeda ya fara shallake tunaninta, amma bata son yiwa mahaifiyarta magana tukun zata ci gaba da d'aga mata k'afa har zuwa lokacin da zata tabbatar da abinda yarinyar ta taka.
Bata dawo gidan ba sai dare da tulin handout da past question papers, sallah kawai tayi don taci abincinta a capteria, ta baje takardu tana duba abinda ya huce ta cikin satikan da suka gabata.
Kusan kwana hud'u shaheeda tana futa kuma duk bata dawowa gidan sai dare, don ko sun tashi lectures group discussion take zama tare da tsirarun y'an department d'insu don a lokacin kansu ya d'au zafi kowa burinta ta samu five point, don wannan tana daga second to the last year d'insu su kammala had'a degree na farko...
Shaheeda kam dama ko bayan ta dawo gidan tsinke bata iya d'aukewa, in banda wanka daya zamo mata dole ko kayan jikinta inda ta cire nan take barsu gidan duk yayi kaca kaca musamman d'akin barcinta.
A rana ta hud'u hajiya tafeeda ta gaji da wannan sabon al'amari da sam bata gane kanshi ba a gidan ta kira Imran a waya tace in ya taso kasuwa lallai lallai tana son ganin shi.

Rabon daya shiga gidan da dare har ya manta sai yau,,, su hamra ne kad'ai a parlon amma ita tana d'akinta, cikin parlon ya zauna suka dinga gaishe shi d'aya bayan d'aya, ya amsa su cikin kulawa yana kallon su da tausayin yadda mom take son shiga rayuwarsu k'arfi da yaji, don a zaune take duk abinda kayiwa d'an wani sai an yiwa d'anka.
Yana nan zaune ta futo daga cikin d'akin ya russuna yana sake gaisheta, ta amsa kadaran kadahan ba tare data zauna ba ta tambaye shi, "tun yaushe ka shigo d'an suwaiba? Don ni yanzu na tattara ka na bar mata tunda ita ka zab'a matsayin sabuwar uwarka data fini,,, yanzun ma na kira kane don naji koda d'aurin k'ark'ashin ka shaheeda bata zaman gidan nan?".
Shiru yayi yana nazari kafun can yace, "nima ban sani ba kwanaki dai tace mun tana son komawa makaranta sai nace ta tambaye ki".
"Ta tambaye ni? Ni a suwa? Ka mai dani mutum ne bare itama ta maida ni".
Imran kanshi a k'asa yace, "kiyi hak'uri mom".
Yamutsa fuska tayi tace, "daka daina bani hak'uri ma,,, don ba fasa halinka zaka yiba, abu d'aya dai dazan fad'a maka shine kabi sannu don duk matar daka hurewa kunne kasa tak'i bin mahaifiyarka kaima ba zaka ji dad'inta ba".
Ko kad'an Imran bai fahimci inda maganganunta suke son tafiya ba, tana nufin shi zai zuga shaheeda kenan ko me?
Bai dawo daga tunanin shiba yaji muryarta tana ci gaba da fad'in, "shaheeda dai y'ar k'awata ce kusan a gabana ta taso nasan halinta ciki da bai, dalilin da yasa ma na takura wajen nema maka aurenta kenan,,,, amma tunda sakayyar da zaka yimun kenan ba matsala gaka ga duniya nan, suwaeba kuma had'a kai da ita maza ka bada himma".
Tana gama yin maganarta tabar shi nan durk'ushe yana jujjuya maganganunta a cikin ranshi.


*Germany*

Cikin satin daya biyo baya Ahmad da y'an uwan shi kuma y'an uwan amaryarshi biyu suka sauka a k'asar ta Germany tare da amarya Yasmine.
Su suka sauya gidan da sababbin furnitures da sauran abun buk'ata yayi kyau dai dai da gidan sabuwar amarya.
Kwanan su uku a garin suka koma inda suka futo suka bar ango da amaryarshi.
Tunda suka tafi khaleefa bai sake ganin k'eyar Ahmad ba saida ya kwana biyar. Shima saboda ya shiga asibiti ne a yammacin ranar tare da matarshi.
A lokacin khaleefa yana shirin barin office suka shigo, saiya dakata har saida suka zauna suka gaisa, ba laifi yarinyar fara ce tas kyakkyawa da ita Masha Allah.
Sun tab'a hira da Ahmad kan abinda ya shafi harkar aikin su da maganar karatun raihana da komai ya kammala cikin satin ma zata fara zuwa d'aukar darasi.
Kusan tare suka futo shi ya huce gidan shi, su kuma zasu kewaya cikin asibitin ya gaisa da mutanen shi.

A mugun gajiye khaleefa ya shigo gidan bakin shi d'auke da sallama, babu kowa a parlon sai mayataccen k'amshin raihana daya cika ko'ina, saida ya lumshe idon shi ya bud'e wani sanyi da tarin nutsuwa suka kwaranya a ruhin shi.
Bai shiga d'akin shiba saida ya zauna a parlon ya shak'i k'amshin sosai yasha ruwa ya huta gajiyarshi.
Ita kuwa a dai dai lokacin tana d'akinta tana aikin dole data k'irk'irowa kanta saboda kad'aici da rashin abunyi, tana jin lokacin da aka bud'e k'ofar parlon aka shigo, tasan babu wanda zai shigo mata sai khaleefa don shi yake da copyn key, kasancewar Germany k'asar da babu ruwan wani da wani kowa rayuwarshi yake bare wani yazo don ya shiga rayuwarka, mamaki take yadda cikin kwanakin khaleefa baya dad'ewa a waje kamar da,,, ko aikin nasu ne yayi sauk'i a office oho. Ita rabon dasu had'u ma tun washe garin ranar da yayi ciwon nan cikin dare. Rayuwarsu suke babu ruwan wani da wani bare takurawa ko shigarwa juna hanci.
Shi kuwa khaleefa ta k'ark'ashin k'asa yake ta gudanar da binciken shi akan surajo Abdallah tofa ta hannun basudaniyar likitan k'ashin da suke aiki tare, zuwa yanzu ya fahimci mutumin yazo medical check-up tun lokacin da suka tafi Nigeria, yanzu haka sai after 4 months zai sake dawowa don a shekara sau biyu yake zuwa farko da k'arshe. A wannan karon khaleefa ya lashi takobin sai ya samu wannan mutumin insha Allah, hakan yasa ya fara tsananta addu'a da tashi cikin dare duk bayan wasu kwanaki, yana fatan ta silar mutumin nan ya ruguje tubalin ginin rehun da auntie tayi musu tsawon shekaru, ya fallasa gaskiyar abinda take b'oyewa kowa ma yaji.

Ranar data kama weekend khaleefa bai futa ko'ina ba through out yana gida don tunda Ahmad yayi aure ya daina zuwa gidan shi.
Kullum tambayar shi Ahmad yake yaushe zai kawo raihana su gaisa da yasmine, don already ya had'a su k'awance shiyasa sai damun shi take da son sanin wai wacece wannan raihanan da ganinta yafi ganin sarki tsada.
Duk lokacin da ya yiwa khaleefa magana sai yace zai samu lokaci suzo, tun Ahmad yana saka ran ganin su har ya gaji ya shirya da yammacin yau suka taho da kansu shida Yasmine d'in yau dai taga wannan raihanan.


*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*

_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page fifty one 5️⃣1️⃣


Ga zaton yasmine ta d'auka zasuyi tafiya mai nisa ne kafun suje gidan sai taga sun nufi gidan da yake fuskantar nasu, kasa shiru tayi har saida ta magantu, "ba gidan abokin ka khaleefa zamu ba?".
"Eh gashi ma har munzo". Ya fad'a yana kallonta da k'ok'arin knocking k'ofar da hannun shi.
Da wani k'arin mamakin tace, "yanzu nan kusa damu ne ya gagare su zuwa kullum ka kira shi a waya yace zai samu lokaci?".
Murmushi Ahmad yayi yace, "bakisan waye khaleefa bane".
"Na san shi mana ba wanda muka je office d'inshi ranar ba".
Wannan karon y'ar dariya Ahmad yayi kafun ya sake cewa, "bafa irin wannan sanin nake nufi ba, ba zaki tab'a ganewa ba mu bar maganar kawai".
Shiru tayi shi kuma ya lalubo no khaleefa don yaga duk bugun nan da suke tsawon lokaci daga shi har raihana basu da niyyar bud'e musu.
A lokacin dukkannin su bacci suke sadidan, ko da wasa babu wanda yaji bugun k'ofar da Ahmad yake.
Cikin tsakiyar baccin shi mai dad'i me cike da dad'ad'an mafarkai yaji ringing na wayarshi da take gefen shi kamar ta fasa mishi kunne.
Mik'ewa yayi da addu'a a bakin shi ya lalubo wayar, kiran har ya katse wani ya sake shigowa. Ganin Ahmad ke kiran sai ya d'auka ba tare da yace komai ba ya kara a kunnen shi. "Man wane irin nisa kayi ne haka da ka shanya ni a k'ofar gidan ka kamar get man zaman jiranka, hala baka son bak'uncin mu a wannan yammaci"
"Ohh! Sorry Ina zuwa" ya fad'a tare da ajiye wayar ya tashi daga kan gadon da sauri.
Saida ya wanke fuskarshi sannan ya futo a gurguje, kallon d'akinta yayi a ranshi yana ayyana bacci tayi kenan itama, don yasan ido biyu ba zata k'i jin zuwan su Ahmad ba.
Da k'orafin Ahmad ya fara bayan ya bud'e mishi gidan, "Allah saura k'iris mu tafi".
Khaleefa ya mik'a mishi hannu suka gaisa yana sake bashi hak'uri, a lokacin suka bawa yasmine hanya itama ta shigo ya maida k'ofar ya rufe.
Anan parlon suka zauna su duka suka gaisa da jin lafiyar juna.
Yasmine dai tana tsakiya sai rarraba idanu take taga ta inda wannan diamond raihana zata futo, gashi su sai hirar su suke kamar sun manta da itama a gurin.
Sake matsawa tayi jikin Ahmad tayi k'asa da muryarta dai dai saitin kunnen shi tace, "shi kad'ai ne a gidan wai".
Ahmad bai bata amsa ba sai tambayar khaleefa daya d'auke kanshi gefe don basu dama suyi maganar su da yay, "Man wai sai mun biya kud'i ne baby zata ga k'awar tata".
Shiru yayi yana kallon Ahmad kafun ya tashi ya nufi d'akinta.
Da zoben azurfar da yake hannun shi ya kwankwasa mata,,,,, tun bata jiyo shi har yaci nasarar tashin ta baccin gaba d'aya.
Doguwar riga ce a jikinta, hakan yasa ta jawo mayafi ta yafa don bata raba d'ayan biyu khaleefa ne, tunda su biyu suke rayuwa a gidan.
Lokacin data bud'e k'ofar ya gama knocking har ya juya baya, hango kawunan su Ahmad da suka juya baya da tashin k'ananun dariya yasa ta gane dalilin zuwan nashi. Hijab ta sauyo wadatacce ta rufe k'ofar ta k'araso cikin parlon, a lokacin shi har ya koma mazaunin shi ya zauna.
Da fara'a sosai akan fuskarta suka gaisa da Ahmad da yasmine ma da take ta son ganinta.
A ranta take raya (Lallai wannan itace jinta yafi ganinta, duk da ake fad'a mata raihana raihana ta d'auka zata ganta wata y'ar gayun wayayya lambar k'arshen nan, sai kuma ta ganta da wani uban zurmemen hijab tabbacin bata kai yadda take zato ba).
"Toh yasmine yau dai ga raihana matar khaleefa, raihana ga matata Yasmine da kuka kasa zuwa ganinta".
Kusan a tare duk suka sakarma juna murmushi, kafun yasmine tace, "nice to meet you raihanatu".
"Same" raihana ta fad'a a tak'aice.

Sunci gaba da zama shiru, khaleefa na aikin danna waya, yayinda yasmine kema Ahmad gulmar wai miji da matar sam basu dace ba, a wane k'auyen ma had'ad'd'en guy kamar mijinta yaje ya d'auko wannan matar.
B'ata fuska Ahmad yayi ya lakace mata hanci can k'asa muryarshi yace, "to ke Ina ruwan ki, daga mata ganin farko zaki yanke mata hukunci baby hakan babu kyau fa".
Kwantar da kanta tayi gefen hannun shi cikin shagwob'a tace, "am sorry".
Kiss ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login