Showing 93001 words to 96000 words out of 288773 words
Chapter 32 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
ya amsa da, "ameen". Wani rubutu ya d'auko irin wanda ya yiwa raihana ya bashi jarka d'aya da wani a k'ok'o "ka shanye yanzu a gabana sai ka tafiwa Ayman dana jarkar" khaleefa ya karb'i bak'in ruwan tawwada a hannun malam yana k'are mishi kallo kamar zai ga wani abu ya lissafa ya futar mishi da branch branch, "shiyasa nace a gabana zaka sha saboda nasan halin bokayen nasara ba komai suka yadda dashi ba.....". Murmushi yayi ya d'auki kokon ya kafa a bakin shi bayan yayi basmala ya shanye rubutun ciki tass sannan ya ajiye kwaryar, lallai ba don kada malam yaga ko bai yarda dashi ba ko wani abu daban, da ba abinda zaisa yasha wannan rubutun, shifa duk wad'annan abubuwan bai yarda dasu ba tun da can, ko ciwo ne ya dame shi gwara yayi tofi, tofin ma yanzu baya sha sai dai ya karanta kawai.
Malam ne ya katse mishi tunanin shi da fad'in, "Yaushe za'ayi maganar aure khaleefa kaga d'an uwanka cikin satin nan za'a kai kud'in auren shi". Ya kalli malam shiru kafun yace, "me auntie tace daka tambayeta ni nawa auren sai yaushe?". ""Kamar yana gurin mukayi magana da ita,,, malam ya fad'a a ranshi, a zahiri kam sai yace, "cewa tayi akwai wadda kake so amma da sauran lokaci kafun ka gabatar da ita".
"Hakane abinda ta fad'a haka yake, akwai abinda nake son ya kammala kafun auren, ga maganar komawarmu Germany aiki". Malam yace, "au da gaske ne kenan da tace kace mata zaka koma aiki can k'asar masu jajayen kunnuwa inda ka futo?". Khaleefa yace, "da gaske ne malam sai dai naga kamar batayi na'am ba". Malam ya gyara zama, "ba amincewa ne batayi ba, hankalinta ne yake tashi a duk lokacin data tuna kana son barin k'asar nan zuwa wata uwa can duniya ba matar aure, nima kuma abinda bai kwanta mun ba kenan, ba wai muna yi maka kallon wani mutum marar nutsuwa bane, a'a nayi Imani ko kafun ka dawo muna da kyakkyawan yak'ini a kanka zaka rik'e kanka bisa jagorancin nutsuwarka da addinin ka, yak'inin da nake dashi a kanka bani dashi akan Ayman d'an uwan ka, nasan zaka iya rayuwa a k'asar da babu namiji ko d'aya tsakiyar mata ba tare daka fad'awa haramci ba, toh amma duk da haka shi aure daban ne, martabar shi daban ce, mutum baya cika cikakke idan babu mace a gefenshi duk kud'in shi duk ilimin shi da limancin shi kuwa". Wani irin nauyi khaleefa yaji a kanshi kamar malam ya d'ora mishi wani mugun gungumen dutse, kalaman shi sun mishi nauyi aka, sai yake ganin kamar malam yasan irin haramtacciyar soyayyar da sukayi shida Saleema a k'asar Germany, wadda yayi imanin da sunsan akwai idon wani da suke shakka a kusa tare da ba zasu fara kai ga aikata abinda sukayi ba, tun wancen lokacin sai yanzu yaji wani abu mai kama da nadama ta tsirga mishi karo na farko a tarihin soyayyar shi, sai yake ga kamar a gaban malam suke love romance shi da Saleema watanni kad'an da suka gabata, iska ya furzar me huci daga bakin shi ya gyara zaman shi da kyau yace, "malam da gaske auntie tana nufin zata amince idan har na gabatar mata da matar dazan aura?". Malam da yake sake nazarin duk wani motsin shi yace, "Ina kyautata zaton haka, Allah yayi muku jagora a dukkan al'amuran rayuwar ku". Ya amsa da "ameen".
Daga nan basu ja wani dogon zance da tsayi ba ya yiwa malam sallama ya futo.
Iya kad'ai ya tarar a parlon, a tsaitsaye itama yayi mata sallama ya tafi, ta raka shi har tsakar gida tana mitar baza su tsaya suci abinci ba gashi ta kusa saukewa. Khaleefa yana tafiya kad'an yace, "yanzu Ina sauri ne sai wani lokacin iya kada ki damu".
Addu'a ta mishi suka k'arasa sallama ya huce, shi ya manta ma tare da Ayman suka zo saida yaci karo dashi akan dakalin k'ofar gida ya zubawa guri d'aya ido, "yaeh zamu tafi ne ko a nan zan barka?". Khaleefa ya tambayi Ayman, sai ya mik'e zaune yana karkad'e k'urar kan gurin daya zauna yace, "a'a mu tafi kawai".
Wannan lokacin khaleefa ne yake driving Ayman a gefen shi, tafe suke kowa da abinda yake tunani a ranshi har suka k'arasa gida. Kamar a haukace haka khaleefa ya dinga had'a stairs bibbiyu yana tsallakewa har ya haura saman, auntie da mama haleema suna zaune a parlour sai wasu mata uku bak'inta, kaya ne da yawa zube a gabanta tana y'an rubuce rubuce da lissafin kaya, da farko d'auke kanshi yayi zai huce saida mama haleema ta kira sunan shi, ya saita yanayin shi kad'an ya dawo da baya ya gaishe da matan, Ayman da yake bayan shi sai lokacin ya k'arasa shigowa parlon, shima ya gaishe su, sai suka saki baki suna tambayarta dama twins ne d'an tannan namiji, murmushin yak'e kawai ta musu ta k'ara nazarin su d'aya bayan d'aya musamman khaleefa da kwayar idon shi ta soma sauya launi, ganin yadda take duban shi saiya tambayi mama haleema, "kina nema na ne"
Mama haleema tayi y'ar dariyarta tace, "a'a auntie ce take son ganin ka, yanzu tasa na duba ka ashe kun futa kaida Ayman".
Kallon auntien yayi, tace, "ka jira ni a d'akina".
Bai bata amsa ba ya huce d'akin nata shi kuma Ayman ya tambayi mama haleema ko Nur tana nan, tace, "a'a sun tafi da mammie". Har ya tafi saiya juyo, "shaheeda fa". "Ina tunanin ita wannan ta tafi makaranta ne".
Khaleefa tun kafun ya d'aga labule k'amshin turaren d'akin ya shiga kafofin hancin shi, har yanzu auntie tana nan da wannan k'amshin nata, shiba mai sanyi da yawa ba, bame hawa kai ba, k'amshin turare ne me sanya nutsuwa da kwantar da hankali, saman sofa ya kwanta tare da lumshe idon shi yana shak'ar daddad'an k'amshin daya jima da kama komai nata, a hankali nutsuwa ta soma saukar mishi har yaji yayi k'asa sosai ba b'acin rai da tashin hankalin nan da suka tsiro from no where, shi dai malam ba zagin shi yayi ba, ba fad'a ya mishi ba magana kawai sukayi, maganar ma da kwantaccen murya bada gargagi ba, amma tuno saleema kawai da yayi yasa duk yanayin shi ya zama haka, d'an k'aramin tsaki yayi a fili kamar me magana da wani yana tuna yadda ta iya rufe ido ta fad'a mishi maganar da bai tab'a zato bare tsammani ba, har yanzu ya kasa tantance a ajin da zai ajiye Saleema,,, bare ya fahimci tarin soyayyar da kullum take kururuwar tana yi mishi. Well shikam yana sonta kuma baya jin zai iya barinta no matter what,,,,,
Da wannan tunanin bacci b'arawo ya sad'ad'o yayi wuff dashi.
Auntie kam saida ta sallami kowa suka d'auki kayan da zasu karb'a suka tafi sannan tasa mama haleema ta had'a musu lunch saboda sameera tana dawowa anjima.
Da fuskarshi ta soma tozali, bacci yake amma ranshi a b'ace sai cin d'aci yake, a kusa dashi ta zauna ta d'auki kanshi a hankali ta mayar kan cinyarta ta dafa kanshi tana k'are mishi kallo na tsab da tsanaki kamar zata iya fahimtar damuwar shi, tabbas Suraj yayi gaskiya ya mata illar da ba zata tab'a iya mantawa dashi ba, amma kuma ya bata kyauta, kyautar da zata dinga kallo tana godewa Allah a duk ranar duniya, wad'annan yara guda biyu tana jin ko kanta bata so yadda take son su yanzu, zata iya hak'ura da komai ta sadaukar da komai, ta rayu babu dangin iya bare na baba a duniya mabanbanta indai tare da sune, tana son su tana k'aunar su Allah ma ya sani, sune sanadin baro kowa da komai ta taho zuwa wannan rayuwar. Ta manta da soyayyar Suraj tuni, haka ta manta da wawakeken ramin daya gina a cikin zuciyarta, ta shafe babin shi a cikin rayuwarta ya zamo tarihi, sai dai ta kasa mantawa dashi kamar yadda ya fad'a a rana ta k'arshe da zasu rabu, Allah ya azurtata da yara biyu sai dai basu d'auki komai nata ba, sai guda d'aya daya keda irin d'abi'un ta da sanyin halinta, amma don khaleefa ko motsi yayi Suraj take gani a tare dashi, yanayin sa! Tafiyar sa! Maganar shi ta kai tsaye! Da miskilancin shi na maida kowa ba kowa ba da baud'ad'd'en ra'ayin shi duk na Suraj ne! Saika rayu da Suraj tsawon lokaci bakasan abinda yake cikin zuciyar shiba, da irin haka itama ya zurma ta ta d'auka da gaske yana sonta, ta saki jiki ta afka kogin soyayyar shi, ta saki jiki dashi k'arshe ya kaita ya baro ta...... Wasu irin zafafan hawayen takaici da bak'in ciki ne suka dinga futa daga idanunta suna sauka kan fuskar khaleefa da kanshi yake saman cinyarta, tun tana kukan silently har ta gagara, k'arshe haka ta duk'ar da kanta ta dinga kuka, amma da yake khaleefa yayi nisa a duniyar bacci duk wannan abun bai jiba, Saida tayi kukanta son rai sannan ta fara magana da raunatacciyar murya, "Allah ya Isa tsakanina da kai Suraj! Allah ya Isa tsakanina da hauwa data kasance ummul'a'ba'isin fad'awa ta cikin wannan rayuwar, da yanzu Ina rayuwata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali tare da yayana sauban". Wani kukan ta sake fashewa dashi kafun ta tsagaita ta d'ora da maganarta, "Ashe d'an Adam zai iya aikata kuskure sau d'aya hukuncin yayi ta bibiyar shi har k'arshen rayuwar shi? Wayyohh Allah ni surayyah......". Yadda take kuka da sambatu saida ta bani tausayi. Haka ta gama kukanta ta rarrashi kanta da kanta tayi shiru, wayar khaleefa da take gaban aljihun shi ta d'auka, tunda ya dawo ta kasa gane kanshi, yanzu lafiya anjima ba lafiya ba, tayi iya yinta amma ta gaza, shine yau zata yi abinda bata tab'a aikatawa wani a rayuwarta ba wato *bincike*. Wayar ba tsaro ko d'aya, kan fuskar wayar tana dannawa hoton wata kyakkyawar yarinya ne fata sol, half d'inta ne amma duk da haka tayi kyau kwarai, hoton anyi shine cikin flowers tana watsa musu ruwa tana dariya, kayan jikinta farare Sol. Ta jima tana kallon yarinyar kafun ta fara tafiya kan applications na wayar, ba game ko d'aya ba duk wasu kafafen sada zumunta na social media, de de da watsapp babu shi a ciki, toh me zata bincika ta gano bakin zaren matsalar d'an nata, wata zuciyar ce tace ,,ki shiga ma'adanar hotuna mana,, aikuwa tayi na'am, hotuna iri biyu ne dashi kacal, daga wattsapp image sai na camera, na watssapp d'inshi ta shiga sai dai yak'i bud'ewa watak'ila saboda ya goge watsaapp d'in ne ko kuma wani dalilin oho, saita koma na camera, eqyawanci duk pics d'inshi ne, wasu taree da Ahmad wasu da matasa abokan karatun shi su da yawa haka! Wasu kuma a gurin surgery, duk gasu nan dai kuma kaf ciki babu inda ta ganshi da mace shi kad'ai sai ko suda yawa a cikin lab ko wani gurin practice da duka course mate d'insu, mafi yawa ma su bakwai take ganin sunyi rukuni duk maza, har ta fudda tsammanin samun wani abu sai taga wani folder tsakiyar camera pics d'in. Tana bud'ewa ta fara tozali da wani hoto da sukayi kan bridge, hoton basu suka d'auke shiba yi musu shi akayi, Saleema ce tsaye khaleefa yana tsaye gab da ita kamar zasu shige jikin juna, ya rankwafo da fuskarshi kad'an hannun shi da k'afar shi tokare jikin k'arfen gadar da take jingine, duka suna sanye da kaya farare k'al, hannunta rik'e da red flowers, daga kallon da suke jifan juna auntie da take neman bakin zaren ta samu zaren gaba d'aya.
Ta jima tana k'arewa hoton kallon zuciyarta na tsananta gudu, sai ta fara tambayar kanta, wace irin rayuwa khaleefa yayi a Germany? Wacece wannan yarinyar da suke kallon juna haka tsirara, ko a iya nan ta tsaya zata iya fassara wannan soyayyar tasu da haramtacciyar soyayyah, har zata d'ora hannunta ta jawo hoto na gaba sai ta dakata, ""Wala ta jassasu"" zuciyarta ta kwab'e ta, "akul kefa uwace, bai kamata ki dinga tsananta bincike akan abinda ya zai d'aga miki hankali ki kasa zaune ki kasa tsaye, baya ga haka kowa yana da personal secret nashi da baya so wani ya gani, watak'ila khaleefa shima hakane". Sai ta rufe mishi wayar ta mayar da ita inda ta d'auka ta zuba mishi ido tana kallon shi da zarge zarge iri iri a kanshi, tsoronta d'aya kada tarihi ya maimaita kanshi..... Duk wahalar da tasha akan su, tak'i aure ta sadaukar da gaba d'aya lokacin k'uruciyar ta saboda su da lokacin ta data k'arar wajen ganin ta basu tarbiyyah irin wadda kowacce uwa da tasan kanta take bawa yaranta ta tashi a banza ko me? koda yake hadda soyayyar Suraj ta hanata aure, duk namijin data kalla sai taga kamar be kai Suraj ba, a hali da dabi'a da tsarin tafiyar da rayuwa Suraj yayi mata karantsaye tako ta ina, duk da kasancewar shi bahagon mutum haka take son shi har kwanan gobe, da farko tana tunanin saboda abinda ya had'a su ta daina sonshi, amma daga baya ta fahimci soyayyar shi a jinin jikinta take sai dai ta mutu da ita amma bawai ta cire ta daga rayuwarta ba. "Allahumma ajirni fil musibati.... Waklifni khairan minha". Ta fad'a da k'arfi a fili tana zubda sabon hawaye
A haka Ayman ya shigo parlon ya same ta, aikuwa tayi saurin share hawayenta da duka hannuwanta, tayi k'asa da kanta kamar wani abu ya fad'a mata ido. Shima yau jikin shi a sanyaye yake ya k'araso har gabanta ya zauna ya d'ora kanshi jikin k'afarta ya fashe da kukan da shi kanshi baisan takamaiman na meye ba, ji yake a duniya in bai futar da abinda yake ji game da raihana ba a wannan karon bazai tab'a samun nutsuwa ba.
Ngd da addu'o'in ku mah fans, Ina ganin tarin comment d'inku na K'arfafa gwiwa na jinjina muku kyautaππππ
_Comment and share_
24/03/23, 2:05β―pm - Merhreeyaertou βπ»βπ»: *JARUMAR UWA*π§
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page twenty seven2οΈβ£7οΈβ£
A hankali auntie ta soma k'ok'arin zame kan khaleefa daga cinyarta, sai dai ya hana mata damar hakan ta hanyar rik'e hannuwanta kamar me rok'o yana magana k'asa k'asa, saida tasa kunne sosai sannan taji abinda yake fad'a, "kada ki tafi, don Allah kada ki tafi kema ki barni..... rayuwata bata tab'a shiga rud'ani ba sai datsin had'uwa ta dake, sannan kin zamo kamar haske me yaye duhun dake cikin zuciyata.... Don Allah ki kasance tare dani har k'arshen numfashin mu..... Duk da kina ganin har yanzu bansan meye so ba, amma indai abinda nake ji a kanki shine Soo! Toh tabbas Ina sonki! Ina sonki so me tsanani!!
Auntie tana d'ago kanta yana mik'ewa zaune firgigit kamar wanda aka zabura, doctor surayyah ta bishi da kallo, shima kallonta yake yana yamutsa sumar kanshi da fuskarshi, abinda ya kanyi a duk lokacin da kanshi ya d'au chargy, a lokaci guda kuma ya zaro wayarshi ya duba hoton Saleema da yake kan fuskar wayar, saiya fara sauke ajiyar zuciya ajejjere atleast yasan zai sameta watarana wancen kawai mafarkine. Ayman kam kuka yake baji ba gani kamar wanda aka turowa da sak'on mutuwa, sai Auntie ta dawo da hankalin ta gare shi ta d'ago shi kusa da ita cikin kulawa take tambayar shi abinda yake faruwa dashi, bai iya ce mata komai ba sai share hawaye da yake, sai suka jefa auntie a rud'ani ta rasa dawa zataji a cikin su, Ayman da yake kuka ko kuwa khaleefa da ya d'ora hannu aka yana jujjuya kai kamar wanda aka turowa da wani mummunan sak'o, kawai data rasa yadda zatayi sai ta fashe da kuka, a mugun gigice da d'imauce duk sukayi kanta suna tambayarta lafiya take kuwa? Sai a lokacin khaleefa ya fahimci kuka Ayman yake d'azu kenan? Shi kuwa Ayman dama da muryar kukan yake bata hak'uri, khaleefa ma ji yayi zuciyarshi ta tsinke, amma dai ya daure baiyi kukan ba sai basu baki ita da d'an uwanshi, da haka suka lallab'a ta tayi shiru. Khaleefa ta fara tattarawa duka hankalinta ta tambaye shi meye damuwarshi, me yake bibiyar rayuwarshi, cikin dakiya da shanye komai yace, shi babu wani abu da yake damun rayuwar shi, tasan bazai fad'a ba ko zatayi me, don haka sai ta koma ga Ayman, "kaifa meye sanadin kukan naka?". Shima Ayman kukan da yayi yasa yaji sanyi ba kad'an ba, sai yaji damuwar tashi ta lafa har yaji ya hak'ura da fad'a mata abinda yayi niyyah da farko, to amma don ya kwantar wa da auntie hankali sai yace, "auntie yaushe za'ayi maganar auren mu da nuriyyah?". Saida ya fad'a ya fahimci sub'ul da bakan da yayi, sai ya basar ta hanyar wulla kanshi gefe kamar bashi yayi maganar ba, duk da auntie bata cikin mood d'inta sai da tayi dariya, tasan Ayman ya dad'e yana son aure ita da malam sun dak'ile shine kawai saboda khaleefa, yanzu kuma tunda taga khaleefa yana Shirin yin wala wala ba zasu k'ara tsayawa jiran shiba, auren shi zatayi mishi, hannunta ta d'ora a kanshi da cool voice tace, "nasan kana son aure tuntuni Ayman ko baka fad'a ba, sannan kana son Nur ma, shiyasa nake son anjima kad'an sameera tana zuwa zamu k'arasa tattaunawa da ita akan maganar auren ku insha Allah, murmushin jin dad'i yayi ya yima auntie side hug yana dariya, shima khaleefa kanshi ya d'ora a d'aya b'angaren kafad'ar ta yana murmushi cikin jin dad'i yace, "congrats Man!". Ayman mak'e kafad'a yayi yana dariya. Haka