Showing 210001 words to 213000 words out of 288773 words
Chapter 71 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
a d'akin tana hasaso lokacin da yake bin bayanta, da lokacin da yazo daf k'amshin turaren shi ya dabaibayeta. Ta ko ta ina khaleefa ya cika cikakken namiji da mace zata so, toh amma meya had'a shi da wannan budurwar har ta bibiyeta da neman rigima??? Ko kuma ya b'oye mata gaskiyar maganar auren su yanzu taji labari shine tazo mata warning har makaranta?? Kai Anya kuwa???
Tunane tunanen da tai tayi kenan bata futa ba har saida taji alamun futowarshi.
Ta kwasa da gudu gudu ta bar d'akin ba tare da ko waige ba.
Lumshe idanun shi yayi bayan gama binta da kallo, murmushi na escaping kan lips d'inshi.
Raihana tana futa auntie ta had'a tray na abinci tasa ta kai mishi, ba musu ta d'auka sai dai ta kasa shiga saboda tasan yanzu yana tsaka da sauya shiryawa ne, inda Allah ya taimaketa auntien ta shige bedroom d'inta, sai ta dawo parlon ta ajiye trayn har zuwa lokacin daya futo ya nufi harabar gidan rik'e da wayarshi, a lokacin ta faki ido ta shiga da trayn d'akin shi ta ajiye ta futo.
Da dare khaleefa yana zaune ya tasa wayarshi a gaba yana kallon wani abu da batasan ko meye ba, ta jima da kwanciya amma bacci ya kasa zuwa mata sam sai tunane tunanen duniya da kewar ummienta, koda tana hostel bata tab'a d'aukar kwana ki biyu ba tare da taji muryar ummienta ba, amma sai gashi a yanzu da tafi buk'atar ji daga gare su hakan ya gaza samuwa.
Tana kwance har khaleefa ya ajiye wayarshi tsakiyar su ya maida dim light.
Saida ta kintaci dai dai lokacin da take zaton yayi bacci sannan ta tashi zaune da kyau ta jingina da fuskar gadon, kamar barauniya haka ta soma lalubar wayarshi har ta samu, juya baya tayi ta tsurawa pic d'inta idanu. Da gaske budurwar shice, toh ita meye had'in ta da ita zata bita har makaranta? Shiru tayi tana nazari kafun ta maida k'afarta cikin bargon ta juyo da nufin mayar mishi da wayarshi inda ta ganta.
Cak! Ta tsaya ganin shi a zaune yana kallonta sai tama kasa ajiye wayar, haske ya k'ara cikin d'akin ya mik'a mata hannu, ba musu ta zura mishi cikin hannun shi ta sunkuyar da kanta cikin jin tsananin kunyarshi don zaiyi tunanin ko wani abun ne daban.
Shiru ya biyo baya kafun khaleefa yayi magana cikin taushin murya, "d'azu munyi waya dasu ummie sunce basa samun layin ki in sun kira". Bata d'auka da ita yake ba saida ta d'ago suka had'a ido dashi, shiru tayi don batasan amsar da zata bashi ba, bayan shiya fasa wayar da kanshi.
Shima abinda ya tuno kenan yasa ya share zancen.
Sunci gaba da zama shiru kafun Raihana tayi magana, "dama Ina son tambayarka wani abu idan ba zaka damu ba".
Sake jingina kanshi yayi jikin fuskar gadon yace, "fad'i tambayarki ina ji".
Saida ta saci kallon shi sannan ta fara maganar da in bata yita ba zata iya hana ta runtsawa da kyau, don ta tsaya mata a k'ahon zuci haka kurum take son jin ba'asi, "amm me zai hana ka bani labarin soyayyar ka da saleema?".
Zancen nata a bazata yazo mishi, ya kuma bashi mamaki had'e da d'aure mishi kai, saiya gyara zaman shi yace, "me yasa kike son sani?".
"Kawai Ina son ji ne" ta bashi amsa tana kallon kai tsaye cikin kwayar idon shi.
Shima ita yake kallo, lokaci d'aya yanayin shi ya k'ara sauyawa. Da irin kallon da yake mata ta fahimci lallai ba zai aikata abinda ta fad'a ba, don haka salin alin tayi kwanciyarta had'e da juya mishi baya.
Ta b'angaren shi kuwa saida ya sake nisawa sannan ya fara magana, "Saleema itace mace ta farko data fara d'aukar hankalina har na fara sonta, saboda tazo cif cif da tatsuniyar karatun zuciyata irin wanda yakan faru a zuciyar kowanne matashi ko budurwa. Na had'u da Saleema a wani yammaci da bazan tab'a mantawa ba, sai dai na kasa tunkararta a lokacin saboda ban san me zance mata ba. Bayan wannan ban sake ganinta ba har na fara tunanin ko aljanace tazo take son bud'e mun ido, Allah da ikon shi sai gashi mun k'ara had'uwa a wani yammacin har ma ta nemi na taimaka mata k'ofar ta tak'i bud'ewa, tun daga nan gaisuwar mutumci ta fara tsakanin mu har muka fad'a soyayyar juna, munyi soyayyah tsantsa irin wadda ta zarce tunanin hankali, munyi abubuwan kuskure duk da sunan soyayyah ba tare da tunanin akwai wani abu da zai iya zama shamaki wa auren muba......".
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya sake duban raihana data gama tattara mishi duka hankalinta tana sauraron shi.
Yaja gwauron numfashi kafun yaci gaba da bata labarin soyayyarshi, bai b'oye mata komai har love romance da sukayi da yadda lokaci d'aya ta juya mishi baya daga Jin tarihin rayuwarshi, dawowar shi gida Nigeria da musabbabin aurenta da yayi har kan dawowar su Germany da binciken y'an uwan mahaifin shi da yake yi a b'oye ba tare da auntie ta sani ba.
"Na d'auka yadda na adana kaina nake tattalin rayuwata haka itama take yi a bayan idona, na d'auka bata tab'a sanin irin waccen soyayyar ba saita sanadiyyata,,,,,,, Ashe ita yaudara ce tab cikinta da jininta take bin ko'ina na jikinta, Ahmad shiya tunasar dani akan naje gareta na mata tuni kan soyayyahta, Amna k'awarta kuma tayi mun jagora zuwa gareta, tasa nayi mummunan ganin da har yanzu ya kasa b'acewa kwayar idona,,,, Amna tasa naga Saleema kan cinyar matured namiji saurayi yana kissing d'inta, hak'ik'a nayi nadamar saninta da tarayyar da nayi da ita a baya, na yanke hukuncin barinta har abada tun daga wannan rana.......".
Sai ya kwantar da kanshi fuskar gadon ya d'ora duka hannun shi a kanshi, ya dad'e a haka kafun ya d'ago yaci gaba da cewa, "raihana Ina da matuk'ar kishi! Ina da kishi irin wanda ban yarda matar da zanyi rayuwar har abada da ita ba tazo mun da guntun tabon wani namiji ya tab'a rik'e hannunta ko jikinta bare har a kaiga irin abinda na gani sunayi ita da wani namiji.... Bazan tab'a shiring mace da jikin kowanne banza ba, dole matata ta zamo tawa ni kad'ai...... Shiyasa na hak'ura da Saleema har abada ko sunanta ma bana son tunawa wani lokacin Cox na tsane ta! Na tsane ta bana sonta kwata kwata......".
Ya kai k'arshen zancen yana wulli da wayar shi ta daku da tiles, tsoro ya kama raihana shi kuma haka b'acin ranshi yake na jawo asara. Tana son mishi magana amma tana tsoron yanayin shi, gaba d'aya jikin shi ba inda baya rawa musamman k'irjin shi sai up and down yake, ga idon shi yayi ja....... Sun jima a haka kafun taga ya dire k'afafun shi ya had'e kanshi da gwiwa. Daga inda take zaune tana fara fad'in, "Allahumma la sahala illa ma ja'altahu sahala wa anta taja'alul hazini iza shi'ita sahala....". Abinda tayi ta maimaitawa kenan har shima ya d'auka yana taya ta suna fad'a tare.
Tun kanshi yana k'asa sai gashi ya d'ago ya tsura mata ido yana kallon yadda bakinta yake futar da harrufan a tare da nashi.
Saida ta tabbatar ya dawowa nutsuwarshi sannan tayi shiru, shima shirun yayi yana sauke ajiyar zuciya a jejjere....
Shiru ya wanzu a d'akin kafun raihana ta fara magana da cewa, "Ni kuma da naji tarihin soyayyarku sai naga kamar babu soyyayar juna a tare daku, da farko ita ta rabu da kai akan k'aramin abu, sannan tasa kana zargin matar data sadaukar da rayuwarta a kanku, muje ma a yadda ta fad'a d'in ku baku da cikakken asalin, shin ita da take sonka fisabilillah ya kamata aji haka daga gare ta? Na d'auka masoyi shine wanda zai b'oye sharrinka komai girman shi, ya yayata alkhairin ka komai k'ank'antar shi, Na biyu taya zata yankewa mahaifinta hukunci tun kafun ta kaika gare shi? Idan akace soyayyah toh anje k'arshe za'a iya fuskantar komai cikin yak'i da so, ni nan naga budurwar da ta dinga futo na futo da iyayenta ba tare da tasan ma kuskure take aikatawa ba saboda soyayyah ta rufe mata ido, amma ita one time ace ta tuna hakan sunan tana cikin soyyayah kuma? Toh wace irin soyayyah take maka data kasa makantar da ita duk wad'annan abubuwan kenan?".
Har numfashi khaleefa yaji kamar ya d'auke yana kallonta cike da mamakinta.
Murmushi tayi don tasan bazai fahimci komai da take fad'a ba yanzu, ita kuwa taci gaba da maganarta, "kaima bawai kana asalin sonta bane tunda dai har ka iya cewa ka rabu da ita don tayi maka k'aramin kuskure, Ina matan da suke wulak'anta kansu? Ina matan da suke irin soyayyar da kukayi da samari bila adadin? Ina matan da k'arewa ma suke rayuwa a gidan karuwai, duka ansan da wannan lambar amma cikakkun masoya gare su suke auren su, in hakane suce sun daina son su ba zasu aure suba tunda dai sunyi so so so so and so thing. Amma madadin haka sai suka gyara su suka inganta rayuwarsu ta hanyar aure. Abu na gaba Ina ganin abin duk da kasan baka so toh kar ka fara yiwa wani, ita d'in ba matar kaba amma ka dinga rayuwar da ranka yake so da ita, ba tare da tunanin abinda zaije yazo gaba ba, ashe kaga duk wanda ya aureta a k'a'ida kai da ita sai kun nemi yafiyarshi kun kuma sanar dashi abinda ya wakana tsakanin ku a bayan idon shi. Amma a shawarce abinda zaifi muku ku sasanta tsakanin ku kuyi aure, Ina ganin duk duniya babu masalahar da tafi muku wannan, sannan ni ban cika maka baki ba amma sai ka kusa kewaye duniya yanzu kafun ka samu irin matar daka fad'a, don rabin y'an matan wannan zamanin koma ince fiye da rabin su zaka same su da irin tabon da baka so, macen da ko hannunta wani namiji bai tab'a rik'ewa ba Ina ganin zaka wahalar da kanka ne kurum,,,, rayuwar da kukayi da Saleema ta kewaye ko'ina birni da karkara......".
"Kina nufin harke duk nutsuwarki da kamun kanki?". Ya samu bakin shi da fad'a ba shiri.
Murmushi tayi tace, "kar muzo maganata yanzu, don tsarin rayuwata da naku ba d'aya bane".
Shiru yayi a zuciyarshi yana ci gaba da nazarin maganganun ta. Itama koda ta kwanta ta jima tana juya labarin soyayyar khaleefa da Saleema, dama sun d'auki tsarin da ba zai kaisu ko'ina ba, kuma ko aure sukayi ba zasu zauna lafiya ba sai sun had'a da hak'uri.
Da irin wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.
@@@@@@@@@@
Kwanaki biyu a tsakani raihana tana lissafin rayuwar khaleefa, ta rasa ma ta inda zata iya kawo mishi gyara a al'amuran shi kamar yadda take so.
Shi kuma ta nashi gurin maganganun Raihana yake ta juyawa cikin ranshi, meyasa a lokacin da yake bulayin neman masoyiya bai tab'a dogon tunani kan abinda zaije yazo ba? Meyasa kyawun fuskar Saleema ya rud'e shi har ya hana shi banbance tsakanin nutsuwa da wadataccen ilimin addini, meyasa bai tab'a k'iyasta adadin had'arin da wani kyawun fuskar yake dashi ba? Me yasa bai nemi mace irin raihana ba, ma'abociyar nutsuwa, kamala, kaifin kwakwalwa da wadataccen ilimin addinin daya danne na zamani har ya b'oye wayewarta, mai kiyaye dokokin ubangijinta da gujewa son zuciya da gudun fad'awa halaka?...... Astagfirullah wa'atubu ilaik ya Allah ka yafe mun kurakuraina! Kaji k'aina ka bani yarinyar da zata zamowa y'ay'ana uwa ta gari.
Irin tunanikan da khaleefa yake yawan yi kenan a gida ko a office.
******Raihana kuwa cikin kwanakin ta samu lokaci ta maida lallenta, tare da yasmine sukayi don tana maseefar son lallen jikin Raihanan, ga duk yawonta a garin ta kasa samun inda ake henna mai kyau black or red one bare taje a mata.
Duk da raihana a d'arare tayi lallen saboda khaleefa hakan bai hanata shiga kitchen ta had'a dinner ba, gashi yau suka dawo office da wuri tare da alamun yunwar da suke matuk'ar ji, koda ta gama ta shirya table ita ta kai musu har parlour shida Ahmad bayan ta b'oye hannayenta cikin gyale. Bai kawo komai cikin ranshi ba har suka cinye abincin shida Ahmad.
Ranar ma har dare Yasmine bata tafi ba suna ta hirar su ita da auntie raihana na sauraron su, in anyi abun dariya tayi in na takaicine tayi har Ahmad ya gaji ya kira wayarta.
Tare suka futa da raihana bayan duk sun yiwa auntie sallama. "sau d'aya kika tab'a zuwa gidan mu amma yasmine kullum tana tare dake a gidan ki". Ahmad ya fad'a cikin sigar zolaya.
Murmushi tayi tace, "ai insha Allah nima zanzo bada jimawa ba, zan rako auntie ma kafun ta tafi".
"Toh Allah yasa!". Mata da mijin suka fad'a kusan a tare, duk sai sukayi dariya banda khaleefa da yake tsaye gefe hard'e da hannuwan shi biyu a k'irji.
Har waje raihana ta raka Yasmine sannan ta dawo, ta same shi yayi relax kan kujera, kitchen ta nufa zata had'a mishi sabon tea don sun shanye duka na gidan.
"Raihana" ya kira sunanta... Bata amsa ba sai dawowa da tayi ta dafa jikin kujerar da yake zaune. Ya shak'i k'amshin turaren ta ya lumshe idon shi ya bud'e sannan ya jawo jakar dake gefen shi ya mik'a mata, ta karb'a tare da kewayowa ta zauna da kyau. Koda ta bud'e laptop ce mai kyau da waya da agogo da sauran complete.
Koda ta d'ago ta kalle shi da neman k'arin bayani murmushi ya mata yace, "naki ne don jin dad'in karatun ki".
Har k'asa ta durk'usa bakinta ya gaza rufuwa saboda farin ciki ta fara jero mishi godiya, d'aga mata hannu khaleefa yayi, saita tsaya tana kallon shi har yanzu bakinta a bud'e.
"Kiyi mun addu'a Allah ya bani mace kamarki".
Shiru tayi bayan ta maida kanta k'asa tana nazari kafun can ta nisa tace, "Allah yasa Saleema ta koma nagartacciyar macen da zakayi alfahari da ita a rayuwarka....".
Kujerar da yake zaune a kai ya daka da k'arfi yace, "noo! Saleema ba zata tab'a zama kamarki ba,,, kawai kimun addu'a na samu kamar ki raihana".
Kasa cewa komai tayi sai tunanin abinda take dashi da har zaiso matar da zai aura ta kasance kamarta? Sai take ganin maganarshi kamar gaisuwane da rok'on iri, duk da tasan khaleefa ba zai tab'a sonta ba.....
"Addu'ar ba zata samu ba ko Raihana?". Ya fad'a da sigar ban tausayi
Murmushi tayi ta d'auki jakar kyautar daya mata, "toh Allah ya baka wadda tafi ni,,,,, Ina sake godiya". Ta k'arasa fad'a tare da juyawa ta nufi d'akin gadonta, ta samu auntie har tayi bacci. Bata iya hak'uri ba saida ta duba cikin wayar, ga mamakinta sai taga an saita mata komai nata sim card d'inta kuwa tuni dama ya dad'e da tsufa a ciki.
Ranar data kama weekend khaleefa dole zasu shiga office saboda doctor andal da ta buk'aci ganin su su uku, itama raihana tana da abinda zatayi cikin makaranta a ranar hakan yasa data shirya futa ta jira shi suka huce tare bayan sun yiwa auntie sallama.
Dressing d'inta na yau ya matuk'ar ba khaleefa mamaki don baiyi kama da irin wanda ta saba futa dashi ba, doguwar riga ce jikinta ba laifi kuma ta futar da well shape structure ta, saita kawo madaidaicin gyale tayi rolling kanta dashi.
Da Ahmad suka had'u a gaban gidan zai shigo gurin khaleefan, hakan yasa ta basu guri bayan ta gaishe shi.
"Yea! Man ba dai office ba?". Ahmad ya tambayeshi da sigar mamaki.
"Eh amma bazan huce 1hour ba".
"Tare zaku dawo da madame kenan?". Ahmad ya sake tambayarshi.
"Anya kuwa!" Ya fad'a yana duban gurin da take tsaye.
"Ni kuma sai nake ganin ka biya ta makarantar su bisa b'oyayyen dalilin da nake son ka gani da idon ka idan ka futo office".
Shiru khaleefa yayi yana kallon shi, a zuciyarshi yana tunanin akwai wata a k'asa kenan don tabbas hakanan Ahmad ba zaice mishi yaje makarantar su raihanan ba, koma dai meye Allah yasa ya zamo alkhairy ba irin wancen bak'in ganin da yayi ba.
"Alright zanyi k'ok'ari na je". Ya fad'a tare da sake bawa Ahmad hannu suka gaisa.
Hakanan khaleefa ya samu kanshi da rakata har makarantar, ya bata kud'in da batasan me zatayi dasu ba ya mata sallama ya huce office.
A gurin meeting Doctor andal take sanar dasu soke tafiyar su Nigeria da doctor raazee yayi saboda k'in aminta da hukumar asibiti tayi, sakamakon hakan patient zai shigo Germany k'arshen watan amma su zasu jagoranci aikin Kamar yadda ta fad'a da farko. Duk sunyi na'am don an sauk'ak'a musu aikin su gaba d'aya.