Showing 159001 words to 162000 words out of 288773 words

Chapter 54 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1086

ba, don yayi abun da bata tab'a zato ba.
Mahaifin shi kam ya tattara ya zuba musu ido, yaga iya gudun ruwan hajiya tafeeda, dama tun daga fasa auren raihana da Imran yayi afuja'atan yasan akwai wata a k'asa, bai sake tabbatarwa ba saida maganar shaheeda ta shigo,,, saiya zab'i yin shiru yaga iya gudun ruwanta akan yace komai.

Sameera kam har office d'in surayyah taje a wani yammaci tana gab da tashi daga aiki.
Ta zauna kan kujerar da takan ga patient tace, "sannu da aiki doctor surayyah". Surayyah da take aiki a system d'inta tace, "yauwa sannun ki". Sameera tace, "nasan zakiyi mamakin ganina a office d'inki ko?".
Surayyah ba tare da tabar aikin da take yiba tace, "ba abun mamaki bane sameera, tunda nan asibiti ne, maybe kinzo ganin likita, duk da baki bi tsarin da ake bi na ganin likitan ba...".
Murmushi sameera tayi ta sake cewa, "zaki iya tunanin haka tunda kin manta wacece ni a gurin ki".
Rufe computer gaban ta tayi ta fuskanci sameera tana kallonta da kyau tace, "meya kawo ki?". Duk da sameera taji ba dad'i da tambayar da surayyahn ta mata, amma saboda ita sulhu take nema saita dake tace, "zuwa nayi in fad'a miki an tsaida maganar auren Imran da shaheeda".
A hankali ta zame farin medical glass d'in idonta ta mik'e tsaye hannunta biyu hard'e a k'irjinta tace, "Allah ya sanya alkhairy yasa abokin arzik'in tane....". Sameera tace, "ameen, kece mutum ta farko dana fara fad'awa saboda a cikin k'awayena bana da kamark har gobei".
Murmushi surayyah tayi tace, "kina da wadda ta fini mana, ko hajiya tafeeda a yanzu aita fini a gurin ki sameera... Shawara d'aya dai dazan baki shine,,,, *kibi komai a sannu, akwai alak'ar da sam bata buk'atar kusanci me yawa ko ja a jiki, Ni kaina bansan haka ba sai cikin shekarar nan data zomun da tarin sauye sauyen alkhairy da sabon karatun mutanen duniya*"
Sameera da tayi tsam tana sauraronta cikin son rarrabe abinda take nufi da kowacce kalma d'aya data fad'a amma ta kasa, murmushi tayi tace, "kamar kina son cewa wani abu kan maganar auren Imran da shaheeda zatayi?""
dogon numfashi surayya taja kafun ta sake cewa, "sameera rayuwa da kike ganinta ta huce duk yadda muke tunani da tsammaninta, magana ta ba akan shaheeda ko Imran nayi ba......". Ta k'arasa fad'a tana had'a jakarta don lokacin barinta office yayi.
Sameera kam sake tara hankalinta tayi, tasan surayyah ta fita wayewa, ilimi da gogewa a harkar jama'a, bata kasance ma'abociyar shagwub'e da k'ananun maganganu ba, sai dai batasan dalilinta na fad'a mata magana me harshen damo ba a yanzun.
Bata da wani zab'i wanda ya huce ta kama hanyarta, don surayya ta rataya Jakarta tuni tana neman key ta futa a office d'in.
Tabi bayan surayyah da har ta kusa k'ofar futa tace, "Nima tafiyar zanyi ai, Nagode da shawara k'awata, na barki lafiya".
Gyad'a mata kai surayyah tayi tana murmushi, har ta fuce idanunta suna kanta, tana iya ganin wauta tsirararta cikin mu'amular sameeran, sai dai masu iya maganar bahaushe suka ce duniya tafi bagaruwa jima kuma bari ba shegiya bace da ubanta. Saita girgiza kai ta k'arasa futa daga office d'in a tsanake.

Ya rage kwana uku raihana su tafi Germany, auntie ta wakilta khaleefa ya kaita tayi sallama da duk wanda ya kamata, sannan ya jirata har ta futo, inda ya dace a ganshi a sanshi kuma ya shiga ya kwashi gaisuwa.
Khaleefa ji yayi kamar ya d'ora hannu aka ya rushe da ihu lokacin da yaji tsattsauran takunkumin da auntie ta d'aure shi dashi, Babu yadda ya iya haka ya wuni yana yawo da raihana da uban zundumemen hijabin daya rasa ubanda take b'oyewa a cikin shi, ta gidan su ta fara, bayan ta gama kukan yadda zatayi kewar su inta tafi, ummie ta had'a ta da d'an abinda take tunanin zai bata wahalar samu a can, ta kuma tursasa mata ta shiga gidan wan mahaifinta ta gaishe su tayi musu sallama, dama daga nan tace direct ta k'arasa gidan Innah.
Ba don ran raihana yaso ba ta k'ara neman wasu mintuna a gurin khaleefa ta shiga gidan, rabonta da gidan harta manta, muneer yana zaune a tsakar gidan yana cin abinci, ummukulsum kuma tana wanke wanke. Duk turus sukayi suna kallonta, daga gefe d'aya ta rakub'e tana gaishe da muneer, ya amsa mata babu yabo babu fallasa, ganin shiru shiru gidan kamar sai su biyu a ciki saita tambayi ummukulsum, "ummah salaha bata nan ne?".
Ummukulsum tace, "eh ta futa asibiti ganin likita".
Raihana tace, "ayyah in tazo kice ina yi mata sannu".
Ta yink'ura zata tashi Ali ya futo ashe yana ciki, Saida gaban raihana ya fad'i data ganshi don basa kwasheta ta dad'i dashi, ya tsaya a gabanta yana tambayarta, "uwar me kika shigo yi mana a gida...".
Bata tanka shiba don tuni cikinta da yake murd'awa kad'an kad'an ya sake hautsinewa, sai ta fara neman hanyar da zata rab'a ta futar musu daga gidan su. Sai dai Ali ya hana ta wai lallai saita fad'a musu uban da ta shigo yi gidan.
Ga muneer a zaune yana kallo amma ya d'auke kai kamar baya gurin.
Ganin in bata zage ta kwaci kanta a gurin Ali ba zai iya yi mata haukar shi sai tace, "zuwa nayi in gaishe da umma salaha kuma tunda bata nan ka bani hanya in huce....".
Wata uwar tsawa ya daka mata, "k'arya kike munafuka ba abinda ya kawo kiba kenan.... Zuwa dai kikayi kinji k'ishin k'ishin Yaya muneer ya dawo toh ta Allah ba taki ba, kwanan nan zai koma ba dawowa yayi dindindin ba ehe, sai aje a fad'a musu wad'annan munafukan guda biyu na gida da suke ganin kowa a banza suna ganin kamar ku kad'ai zaku ci gaba....".
Nau'ikan cin mutumcin da Ali yake yasa ta silalewa ta gefen shi kamar zata gogi jikin shi ta fuce ba tare data saurare shiba, madadin ya rabu da ita tunda ta futo saiya biyota har k'ofar gida yana wasu maganganun na rashin mutumci.
Khaleefa tun tana ciki yake jin zantukan Ali sama sama, baisan da raihana yake ba saida yaga ya biyota har waje yana maganganun.
Bata saurare shiba taci gaba da takawa har inda khaleefa yake jiranta a saman mota, ta bud'e murfin da nufin shiga ciki ko zai rabu da ita, yayi saurin datse k'ofar, "dallah malama ki saurara, ke har kin isa Ina magana ki share ni? Wacece ke? Me akayi aka yiki banza a wofi...". Dafe kanta tayi da hannunta d'aya tana Allahumma ajirni fil musibati waklifni khairan minha, khaleefa da yake gefe yana kallon su baiyi yink'urin sa musu baki ba don baisan alak'ar da take tsakanin suba, watak'ila family issue ne irin nasu da bai shafe shiba.
Mutane har sun fara tsayawa, ganin haka sai raihana ta sake k'ok'arin bud'e murfin motar a karo na biyu, wannan karon da k'afa ya buga motar yace, "ki saurara mun keda wannan banzar gwangwanin da aka siya da kud'in Haram, kud'in zinaaa! Mijin naki duk garin nan waye baisan uwarsu karuwa bace data haife su shegu,,,,, ko bakisan munsan shida wancen d'an uwan shed'ancin naki da kuka gama gantali hotel hotel basu da uba ba......".
Raihana wannan karon kasa hak'uri tayi don ya gama k'ure hak'urin ta, tace cikin fushi har idonta na sauya kala, "ka fad'i duk abinda zaka fad'a a kaina amma kada ka sake ka tab'a Auntie, don banga had'in ka da ita ba, baiwar Allahr da bata jiba bata gani ba....".
Kamar abinda yake jira kenan ya d'aga hannu zai zabga mata mari aka rik'e hannun shi ta baya babu zato. Tare duk suka waiwaya, khaleefa ne tsaye yake kallon shi fuska ba wasa, yau raihana taga abinda bata tab'a gani daga gare shiba wato fushi, yana da wani irin ra'ayi na baud'ewar hali da rashin fahimtar komai a yadda yake, amma zaiyi wahala kaga fushin shi cikin sauk'i, don yana da shanye abu.
Da wata irin murya me fudda sautin fushi yace, "ka fad'i duk abinda zaka fad'a a kaina da mahaifiyata amma kada ka sake kace zaka tab'a ta,,,, don ita ba tsarar ka bace".
Yadda yayi maganar kad'ai ya firgita Ali ya shiga rawar jiki daga ta ciki, zubi, tsari da zarrar duk ba irin nashi bane, ya tabbatar ya shiga hannun wannan giant d'in bazai sha ba. Sai ya fara k'ok'arin warce hannun shi, sai dai ba rik'on wasa khaleefa ya mishi ba, gashi sai wani irin kallon gargad'i yake jefa mishi. Saida ya tabbatar yayi ladab sannan ya saki mishi hannu ya bud'ewa raihana front seat ta shiga ta zauna, shima ya kewaya mazaunin driver ya shiga.
Har suka bar layin Ali bai ce k'ala ba sai ajiyar zuciya da yake ta saukewa a b'oye. A ranshi yana fad'in, Wannan karon kam tasha amma next time suka had'u babu wannan guy d'in sai ya yagata yaga uban daya tsaya mata. _nikam nace inka ganta kenan😜 lolll_

Suna tafe tana satar kallon khaleefa daya cika mak'il. Da kyar ya iya bud'e baki ya tambayeta anguwar da suka nufa, ta kwatanta mishi har suka k'arasa.
Ko data shiga gidan innan duk zuba mata ido jama'ar gidan sukayi suna kallonta, mutane k'alilan suka iya amsa sallamarta.
Saida ta gaishe su sannan ta tambayi ko Inna tana ciki,
Inna tana daga ciki amma kunnenta na waje, sai kuwa cewa tayi, "eh Ina nan waye yake nemana?".
Raihana salin alin ta nufi d'akin, sai dai daga bakin k'ofa ta dakatar da ita, "tsaya daga nan.... Yau kuma wanne sharrin da gayyar maseefar aka d'ebo aka taho mun dashi gida? Dama da farko kar ki fara fad'a mun mijin ki ya sake ki kinzo nan yaji, gidana beyi kama da mafakar y'an iska ba, Ni dama nasan a rina wannan uban lefe akwati Sha hud'u kamar me yankan kai ai wallahi nasan da walakin goro cikin miya, ba iya rik'e ki zaiyi ba atohh! Shiyasa dai a rayuwar nan ka dinga ajiye kanka inda Allah ya ajiye ka, bawai ka dinga zurma kai kana shiga inda Allah bai kaika ba".
Tunda ta fara magana raihana tayi shiru tana kallonta ko kwakkwaran motsi ta kasa yi, har yanzu ta kasa yarda wannan ita ta haifi Abban ta.
Saida taja mata addu'o'i sannan ta russuna ta fara gaisheta,,,, aikuwa nan ma ta d'aga mata hannu da sauri, "ki fad'i abinda ya kawo ki ba sai kinji lafiyata ba, Ni banson tsugudidi da munafurcin banza".
"Haba innah aikya bari kiji abinda ya kawota tukun ko? Ina ganin zuwa fa sukayi su gaishe ki tare suke da mijinta yana k'ofar gida". Wata daga cikin y'an uwanta da suke gidan ta fad'a.
Sai a lokacin Inna ta sassauta tace, "wato shine kika barshi a waje salon kija ya tafi dani a baka yana barbad'awa mutane bani da mutumci, toh ai sai ki ce masa ya shigo ko?". A nutse raihana ta juya ta futa, khaleefa yana tsaye a k'ofar gidan ya tokare k'afar shi d'aya jikin gini, a gefe ta tsaya cikin taushin murya sosai tace, "ka shigo ku gaisa da Inna". Kallonta yayi kafun ya yamutsa fuska yace, "wacece innah".
A tausashe tace, "ita ta haifi Abbana".
Wayar shi ya mayar cikin aljihun shi kusan duk abinda ta fad'a akan kunnen shi, don ba a hankali take maganar ba, kuma gidan duk da an zamanantar dashi ba'a k'ara mishi tsayin katanga ba, "muje".
Ta sauke b'oyayyar ajiyar zuciya, don da khaleefa yace bazai shiga ba nan ma wata ce daban, abun har ummienta sai ya shafa.
Mutanen gidan kallon su suka dinga yi, don da yawan su sun futo ne su ganshi, suga wanene ya auri raihana, tunda lokacin biki basu samu ganin shi ba gaba d'aya.
Saida ya gaggaisa dasu sannan suka k'arasa ciki gurin innah suka bar su nan suna k'us k'us.
Wani abun mamaki Inna har da shimfid'awa khaleefa darduma ya zauna, itama saita rab'a gefen shi taci albarkacin shi. Tarba ta mutumci hadda ruwan Sha me sanyi a fridge.
Shikam tunda suka gaisa bai iya cin komai ba. D'akinta fes fes kamar a yada tuwo aci, ga ko'ina a gyare kamar ba gidan tsohuwa ba, (saboda Abba ba k'aramin gyara yayi mata a gidan ba).
Inna ta shangare baki tana ta bawa khaleefa labarin dangin su da mutumcin kowanne mutum ciki, tana ta kushe raihana da mamanta kuma, shi dai yana jinta kawai. Da suka tashi tafiya ya ajiye mata kud'i masu yawa, raihana gudun kada taji labarin tafiyarsu ta bar mamanta cikin matsala saita tsaya ta fad'a mata batun tafiyar su Germany nan da kwanaki k'alilan.
Ai da gudu Inna ta futo ta tara jama'ar gidan tana fad'a musu raihana zata tafi k'asar waje,,,,, "gaskiya dai rukayya munafuka ce, ashe tun asali kunsan da maganar tafiyar amma kuka ja baki kuka tsuke saboda bak'in mugun abu,,,, Kai Allah ka raba mu da sharrin rukayyah....". Ita dai raihana shiru tayi kanta a k'asa ta kasa cewa komai.
"Toh yanzu da kika fad'a mun, me kike son ni nayi akai". A sanyaye raihana tace, "ba komai dama.... dama sallama zanyi miki"
Sake kyab'e baki tayi tace, "oh! Toh Allah ya kiyaye hanya".
Jiki a sanyaye raihana tace, "ameen, sai anjima".
"Toh sai a gaida gida ko" y'an gidan suka fad'a, a lokacin da take huce su jiki a sanyaye.
Khaleefa yana tsaye jikin bangon gidan, sai dai duk abinda ya faru akan kunnen shi wannan karon ma yaji komai.
Koda suka fara tafiya raihana kasa rik'e hawayenta tayi, saita kife kanta a gwiwarta ta fashe da kuka mai ban tausayi, ta rasa wannan wane irin bala'i ne, dangin uban su amma kamar basu had'a komai ba, a hankali khaleefa ya rage gudun motar yana kallonta da tausaya, don shi a rayuwarshi ya tsani sautin kukan mace gaba d'aya, saboda shine abu na farko da yake nuna rauninta.
A hankali ya gangara gefe yayi parking motar, shiru motar ba sautin komai sai sheshshekar kukan ta. Kuka takeyi irin mai ban tausayin nan. Hannun shi ya d'ora saman kanta ya d'ago fuskarta da take sharkaf da ruwan hawaye.
"Kiyi hak'uri don Allah! Amma kukan ki.... Komai yayi farko dai yana da k'arshe raihana, da sannu gaskiya zata fallasa kanta.... Soo kiyi hak'uri kawai....". Khaleefa ya samu bakin shi da fad'a cikin sigar rarrashi bayan ya d'ago kanta ya jingina ta da jikin kujerar da take kai. Da tafin hannun shi ya dinga share mata hawaye yana sake bata hak'uri.
Kamar wata sakarai haka raihana ta zuba mishi ido tana kallon shi, sam bata d'auka ya iya magana da tattausan harshe irin haka ba.
Janye hannun shi yayi ganin tayi shiru ya fara k'ok'arin tada motar yana tambayarta, "sai wacce anguwa kenan?".
"Layi na gaba da wannan". Ta bashi amsa fuskarta na kallon gefe.

Baisha wahalar gane gidan ba, saboda tsiran ba yawa sosai, saida ta sake daidaita yanayinta zata futa daga motar ta tsinkayi muryar shi yana cewa, "in kin shiga ki fad'a musu zan shigo mu gaisa".
Gyad'a mishi kai tayi a sanyaye ta nufi cikin gidan.
Khaleefa ya bita da kallo har ta shige, haka kurum yaji yana son sani da ganin da yawa daga cikin danginta, yana son rairaye da tantance abinda yake wakana cikin rayuwarta, ta wata fuska rayuwarta abun tausayi ce kamar tasu, duk da bata tab'a ce mishi ga matsalar taba amma yau d'aya ya fara wani karatu cikin rayuwarta, ya kuma sake cin k'udurin inganta rayuwarta ta yadda watarana duk sai sun raina kansu idan suka ganta, suka ga mijin da take aure, sai ya sake kwantar da kanshi jiki yana duba kiran da yake shigowa wayarshi akai akai, Muhammad ne sai dai baya jin d'aga kiran kowa a cikin su a halin yanzu.
Raihana kuwa koda ta shiga ummah tana d'aura alwalar sallar la'asar a bakin famfo, da murnarta ta taryeta tana yi mata lale marhabin.
Har cikin parlonta ta kaita sannu da zuwa tak'i k'arewa.
Saida suka gaisa raihana take fad'a mata tare suke da khaleefa a waje.
Aikuwa Ummah ta kora ta taje ta shigo dashi. Raihana ta futa tana dariyar fad'an da ummah takeyi bilhak'k'i kan me tabar khaleefa a waje ai shima d'an gida ne.
Yana cikin mota tayi knocking glass d'in side dinda yake.
Kusan tare suka jero har cikin gidan. Raihana ta shige d'akin gadon ummaa ta barsu tare nan a rumfa suna gaisawa.
Kwanciyarta tayi har saida taji ummah tana kwad'a mata kira sannan ta futo, a kusa da ita ta durk'usa tace, "gani ummaah".
"Maza ki zuba mishi ruwa a buta zaiyi alwala, ki shimfid'a mishi darduma yayi sallah". Da toh ta amsa, ta kalli inda khaleefa yake zaune, by lucky idanun su suka fad'a cikin na juna. Sai taga ya sakar mata murmushi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login