Showing 57001 words to 60000 words out of 288773 words

Chapter 20 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1121

ata sama wanda ya sauka mata ya b'oye k'irjinta gaba d'aya.
Zama sukayi gefen bed Saleema ta kwantar da kanta jikin khaleefa tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren shi. Hira suke yi k'asa k'asa wadda su kad'ai suke jin abinda suke fad'a kafun khaleefa ya d'auke ta cak ya dire akan gadon. Kwanciya yayi bayan ya kashe globe d'in d'akin duka rungume da ita a k'irjin shi.
Ya karanto musu addu'ar bacci ya tofe duk kusurwowin d'akin ya sumbaci forehead d'inta. A haka wani sumamemmen bacci yazo ya tafi da su mai cike da dad'ad'an mafarkai.

Asubah ta gari American cooples..


_Noo comment noo update tomorrow🤗_



_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page sixteen1️⃣6️⃣


Saboda dad'in bacci har kusan kwace musu sallar asubah tayi, Allah dai yasa khaleefa ya fara tashi ya tashe ta itama. Alwala suka d'auro ya jasu jam'i, saboda yasan tana da lectures 7 am wannan ranar, shikam yana hutun final semester wadda da sun dawo zasu zana final exam su jira sakamako. Saida ya gama morning azhkar sannan ya mik'e daga kan sallaya, ya kalleta nad'e abinta akan gado tana lazimi da hannunta rabi kuma tana gyangyad'i.
"Gud morning Cherie". Ta fad'a cikin magagi, "morning" khaleefa ya fad'a yazo a nutse ya shafa gashin kanta zuwa kuncinta, d'ora hannunta tayi akan nashi tana kallon shi da idanunta da suke cike da bacci, "kiyi bacci na minti 30 kawai". Gyad'a mishi kai tayi cikin bacci ta maida idonta ta lumshe.
Khaleefa gyara mata kwanciya yayi yaja mata bargo ya tafi kitchen.
Abincin k'asar Nigeria ya had'a mata mai sauk'i na break. Ya gyara mata d'akin tsaf ya kammale komai a muhallin shi kamar mace, ya saita mata alarm, yana gamawa keyn d'akin ya d'auka ya futa, d'akin shi yaje yayi wanka da brush ya shirya cikin wasu kayan farare Sol. A rayuwar khaleefa yana son farin abu, yana daga abinda yasa saleema take k'ara burge shi, kusan sunyi tarayyah wajen son abu iri d'aya mabanbanta.
Lokacin daya shiga ta tashi harta yi wanka tayi shirinta ta had'a komai na tafiyarta school.
Tattausan murmushi ya sake mata a lokacin da yake k'arasowa cikin d'akin, "I thought Zan tarar har yanzu baki tashi ba ai". Ya fad'a Yana zama gefenta.
Itama murmushin ta mishi tace, "ba alarm ka saita ya tashe niba, yanzu na fahimci yadda akayi kake yin komai kan lokaci, ashe lissafa komai kake yi, to wai a gurin wa kake samun irin wad'annan dabarun ne?" Shiru yayi yana kallonta da murmushi a idon shi still kafun yace, "a gurin Auntiena, she's very reasonable person me tafi da rayuwarta cikin taka tsantsan, komai tana yin shi with seriousness, lokacin da nake gida kafun na taho nan karatu, idan muka kwanta bacci da rana ita kuma zata futa, bata tab'a had'a iya (kakarmu) da aikin tashin mu bayan cikar adadin mintunan data d'aukar mana, saboda kota fad'a iya was busy doing her work mantawa take, fak'at sai ta saita mana alarm. Alarm na k'adawa zan tashi a baccin da nake komai nauyin shi. Tunda nake a gida ban tab'a yin baccin cikakken hour biyu ko uku da rana ba sai in bani da lafiya, a haka har na saba, kasancewar twin bro na muna kama sak dashi, ga wad'an da basu gama tantance muba idan Suka zo gidan mu suka kwana biyu, da yawan baccin rana suke gane Ayman dani, Cox Ayman yaga dama auntie tasa mishi alarm ya tashi ya kashe yaci gaba da baccin shi har sai in anyi sallah ni ko iya mun tashe shi tukun........". Tunda khaleefa ya fara magana da yaren jamus Saleema ta zuba mishi ido tana kallon shi ko k'iftawa babu tamkar mai d'aukar darasi, for the first time daya tab'a yi mata magana akan familyn shi, ko Ayman tasan d'an uwan shine amma bata tab'a sanin twins d'inshi bane sai yau, Auntie ma sunan take ji yana yawan ambata in suna waya a wasu lokutan, haka iya.
Ganin kallon k'urillar da take mishi sai ya d'an tafa hannuwan shi, "ya dai madame kallon meye duk hakan?".
"Uhm! Cherie Ina kallon mamakin yadda kake iya shanye komai a cikin ka da ranka ne? Don Allah ka koya mun ajiye muhimman abubuwa irin yadda kake yi? Da naji kad'an daga labarin auntien ma yanzu, sai naji Ina son nasan abubuwa da yawa game da ita, don Allah ka bani labarinta nasan itama dole zata zama y'ar gayu kamar dai kai?".
Murmushi khaleefa yayi yace, "kiyi hak'uri time is coming da zaki san tarihina da komai game da Auntiena, abu d'aya da zan iya yi miki a halin yanzu shine in nuna miki hoton ta, shima sai mun fara yin break kada abincin nan su huce".
Ba musu Saleema ta gyara zamanta cikin happie suka fara cin abincin tare dashi bayan sunyi basmala.
Toasted bread ne with eggs da chips, sai tea na zallar ganye. Saleema taji dad'in cimar hakan yasa taci da yawa fiye da yanda take cin abincin safen ta. Saida suka gama ya nuna mata wani pic d'in Auntien da Ayman ya tura mishi, asalin hoton sameera ce ta d'auke ta a wani occasion, tana zaune kan kujera nad'e da lipaya mai shegen kyau orange colour an yi mata adon lace a k'asanta maroon da milk. Hannunta rik'e da Jakarta tana dariya, hoton bai huce 4 to 5 weeks ba. Saleema kasa d'auke idonta tayi akan pic d'in tana al'ajabin yadda wannan zata kasance mahaifiyar zabgegen saurayin dake gabanta, idan khaleefa yace mata yayar shice wannan ko da wasa ba zata musa ba? Kuma ko yanzun don tasan bai kasance ma'abocin k'arya ba da sai tace ya raina mata hankali ne kawai. Sake juya wayar tayi a hannunta tana kallonta, duk yadda mamanta take ji da kwalliya da ado wannan ta damata ta shanye, da kallo d'aya ta fassara ta da rik'ak'k'iyar y'ar gayu da bokon da aka tsabtace da wadataccen ilimin addini, sannan mace mai tsayayyen ra'ayi akan komai, basa kama da khaleefa sai ta jini amma a kwayar idonta tana iya kallon wasu abubuwa dake tare da khaleefa.
Lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya a lokacin da taji an zare wayar a hannunta, "duk me kike kallo haka?".
Bud'e idonta tayi akan khaleefa da yake kallonta shima tace, "Ina kallon tushe, asalin Abdallah khaleefa, da gaske wannan itace ta haife ka?".
Murmushi yayi yana duba lokaci yace, "kingan ki ko? Zaki jawa kanki late fa, oya tashi muje ki huce". Mik'ewa tayi ta d'auki duk wani abun buk'ata na makarantar ta.
Tare suka futo ita da shi, ya rakata har inda ta shiga mota sannan ya dawo.
D'akin shi ya gyara yayi d'an sauran abinda zaiyi ya kwanta baccin mintuna 40.
Yana tashi ya soma k'ok'arin had'a lunch saboda saleema na gab da dawowa makaranta yasan kuma hungrily zata dawo.
Yana cikin had'a easy recipe tayi mishi knocking, ko daya bud'e mata k'ofar rungume shi tayi, "I miss you future husband".
Rik'e ta yayi shima yace, "I miss you too". Yana fad'in haka ya janye ta a jikin shi ya karb'i jibgegiyar jakar bayanta ya maida k'ofar d'akin ya rufe.
Zaunar da ita yayi saman sofa ya shiga bathroom sharp sharp ya had'a mata ruwan d'umi mai d'an yawa.
Gurin ta ya dawo ya zauna tare da rik'e hannunta ya sumbata, "nasan yau kin gaji sosai, kiyi wanka ga can ruwan masu zafi na had'a miki".
Saleema zuba mishi ido tayi tana kallon shi cikin narkewa a so da k'aunar shi tace, "kana ji dani futuruhus! Nagode sosai...". Girgiza mata kai yayi, "bani keyn d'akin ki wane kaya zaki sauya?".
Mik'a mishi mukullin tayi tace, "duk wanda kaga yayi maka". Murmushi ya sake yi ya mik'e ya fuce. Ita kuma ta shige bathroom d'inshi, galala Saleema ta saki baki tana kallon yadda ya shirya d'akin wankan kamar wani gurin da za'a dawwama ba abu na lokaci d'aya a futa ba. Tsabtar khaleefa tana burge Saleema, shiyasa a wasu lokutan take ganin komai nasu a opposite, in aka d'auke hali na miskilanci da jin kanshi.
Sai tace kusan ta jima batayi wanka mai dad'in wannan ba, ga wasu irin body wash masu k'amshin dad'i mai tsayawa a rai da zuciya.
Ta jima kafun ta sake futowa d'aure da d'aya daga cikin bathrobe nashi da suke ajiye cikin kayan towels da innerwears d'inshi. Yana zaune yana operating system ta futo gashin kanta na d'igar da ruwa, kallo d'aya yayi mata ya maida kanshi ga abinda yake yi saboda wani irin yarrr da yaji a duk ilahirin jikin shi, itama ganin haka sai ta d'auki kayan daya ciro mata a gaggauce ta koma bathroom d'in ta shirya kanta, wasu riga da wando ne ya d'auko mata, wandon tight yayinda rigar kuma ta kasance mai fad'i da girma ta sauka mata har gwiwarta. Sosai tayi kyau musamman data yane kanta da siririn gyalen daya had'o cikin kayan donta sirranta gashin kanta da bai bushe ba har lokacin. Shi kuma a bashi da kayan gyaran gashi irin nasu na mata.
Wani irin k'ayataccen murmushi khaleefa yayi mai nuni da aji da zallar izza, "kinyi kyau princess".
Itama murmushin ta mishi k'asa k'asa tace, "thank you futurehus". Gefen shi ta zauna, shi kuma ya tashi ya nufi kitchen, zuba ma computern ido tayi tana kallon wani video da yayi playing yana kallo kafun ya tashi, shiru tayi tana kallon yadda k'ashin d'an Adam ke had'ewa bayan yayi broken, sosai ta duk'ufa tana kallo har jikinta na rawa don razana. A haka ya futo da trayn abinci, daga yadda take kallon shi tana zare ido ya gane abinda take yiwa hakan, rufe system in yayi ya kamo hannunta suka zauna k'asa gab da juna, zatayi magana ya d'ora yatsar shi saman labbanta, dole taja bakinta ta tsuke suka fara cin abincin daya had'a. Suna cikin cin abincin ne k'ofar shi tayi k'ara. Tsam ya tsame hannun shi yaje ya bud'e, Ahmad ne tsaye kare da waya a kunne, cikin farin cikin ganin juna suka mik'awa juna hannu tare dayin side hug. Bashi guri khaleefa yayi ya shigo ciki shi kuma ya rufe d'akin. Yana Shirin zama gefen bed ya ankara da Saleema da take zaune da trayn abinci a gabanta, sai sannan ya ankara da abinci suke ci tare ashe. Katse wayar da yake a lokacin yayi suka gaisa da ita sama sama, saboda itama bata wani sakewa mutane sosai, mik'ewa yayi yace, "yeah ni zan huce sai munyi waya ko?". B'ata fuska khaleefa yayi yace,
"Ahmad ka tsaya muyi lunch mana tare yaushe rabon dana ganka ma da idona, yanzu kuma kazo ko minti biyu bakayi ba kace wani zaka huce, haba mana". Ahmad Kallon agogon hannun shi yayi yace, "I'm in hurry but later zamuyi dinner tare ma, saboda Ina son ganin ka dama".
"Alright Allah ya tsare sai mun had'u d'in". Daga haka suka yi sallama ya tafi shi kuma ya dawo gurin Saleema.
Ko da suka gama cin abincin sun jima suna hira kafun ya rakata har nata apartment d'in, da kyar suka rabu tana ta zuba mishi shagwob'a yana rarrashinta.


**********


_8:25pm Northtown coffee, Arcata, CA, United state_
Zaune suke a babban gurin cin abincin sun tattara hankalin su da nutsuwar su kacokan ma juna. Khaleefa ne ya gyara zaman shi bayan gama sauraron doguwar maganar da Ahmad yazo da ita, "Ina ganin shawarar ka tayi Ahmad, babu laifi idan har zasu biya mu da kyau fiye da na k'asar mu Nigeria, sai muyi aikin tare dasu, Auntie zata zo cikin watan nan insha Allah sai mu tattauna da ita".
Ahmad yace, "Kai khaleefa kana da damuwa, yanzu ya kamata kayi mata maganar ba wai sai lokaci yazo gab ba, toh idan tace bata amince bafa?". Da sauri khaleefa yace, "ya da mugun fata da wuri Ahmad? Insha Allahu zata amince". "Toh amma idan ka duba zaka ga saida aka matuk'ar kai ruwa rana kafun ta yarda muzo Germany karatu, shine yanzu kake zaton zata barka ka dawo aiki na dindindin sai dai kaje musu da ziyara ka gan su". Shiru khaleefa yayi yana nazari kafun can ya nisa yace, "mu barshi sai tazo d'in Ahmad kafun nan zanyi addu'a ka tayani kaima Allah yasa muyi rinjaye akan ta". Ahmad yace, "ameen insha Allah zan taya ka mu duk'ufa addu'a khaleefa".
Duk shiru suka sake yi kafun Ahmad yace, "sai magana ta biyu akan Saleema, yanzu kana ganin babu matsala a soyayyarka da yarinyar nan da kuma yanayin yadda kuke tafi da mu'amular ku?". Shiru khaleefa yayi, Ahmad ya sake dafa kafad'ar shi, "kayi hak'uri idan nayi maka katsalandan da rayuwarka, ba komai yasa na shiga cikin abinda baka saka niba sai guje maka heart broke da rashin tabbas na mata yanzu, saboda Amna k'awar Saleema ta tabbatar mun akwai wani da suke soyayyah ra'ees babu irin soyayyah da kulawar da bai nuna mata ba, amma tana samunka lokaci d'aya ta watsa mishi k'asa a ido ta rabu da shi......"
Tunda Ahmad ya fara magana khaleefa ya kafe shi da ido yana kallon shi kamar ya wanke shi da mari, lallai Ahmad ba don yasan shi d'in mai k'aunar shi bane daba abinda zai hana yaja mishi layi take yanke, toh amma yasan lallai Ahmad yana yin maganar nan da kyakkyawar niyyar kubutar dashi, bayan sharri ne da gadar zare, sai ya saisaita yanayin shi yace, "calm down and cool your mind, Sam Saleema ba irin y'an matan da kake tunani bace, nasan kaima don bakasan komai bane shiyasa, toh amma alhamdulillah da kanta ta bani labarin yadda suka rabu da ra'ees da abinda ya raba su, har ita k'awar tata da takai maka wannan maganar yanzu haka basa tare, too ba wani abu bane duka zamu iya cewa rashin fahimta aka samu".
Ahmad yace, "toh Ina fatan haka, sai maganar hot love na....." Sai kuma yayi dariya. Shima khaleefan dariya yayi ya gane abinda Ahmad yake son fad'a sai yace, "shima kada ya dame ka khaleefa yana kiyayewa ako da yaushe, duk wani abu da kake tsoro bazai kasance ba Ahmad insha Allah".
Ahmad yana dariya yace, "Allah yasa kam, abokina naga alamun ka zamo expert a soyayyah fa zamu zo a bamu formula". Mik'ewa tsaye khaleefa yayi, "Hum let's go zan kira auntie da Ayman a waya kada suyi bacci kuma".
Mik'ewa sukayi kusan a tare suka futo daga eateryn suna magana suna had'a hannuwa da dariya abun gwanin burgewa.


@@@@@@@@



Kusan tun daga wannan lokaci soyayyar khaleefa da Saleema ta sake zama hot and romantic, sosai suka k'ara d'inkewa sau goman yadda suke a da, zasu ci abinci tare, hira tare, karatu tare, futa guraren shak'atawa tare, yawo bridge bridge ma tare, har takai yanzu komai khaleefa zai siya biyu yake siya na maza dana mata, haka itama takan zage wajen kyautata mishi da bakin alhihunta. A iya zaman shi a Germany har rasa yadda zaiyi da kud'in account d'inshi yake, amma yanzu sai gashi yana neman yiwa kanshi karkat akan Saleema. Soyayyar su tayi shura ta karad'e lungu da sak'o na makarantar sai gashi suna shirin k'afa tarihin zama masoyan da suka kusa danne kowanne masoya shak'uwa da iya soyayyah a Humboldt university, ko sau d'aya basu tab'a samun rashin jituwa ba bare ta kaisu ga yin fad'a, tuni sun k'aryata, sunyi fancakali da maganar da masu iya magana suka ce wai duk soyayyar data cika soyayyah sai an samu fad'ace fad'ace da rashin jituwa a cikinta. Sun d'auki kiss as the only way to express sad or happiest moment, and the only way to thank each other a duk lokacin da wani ya kyautatawa wani cikin su.
Rik'e hannu kuwa sun mai dashi tamkar farilla, ko tafiya suke basu sark'afe hannuwan juna ba basa jin dad'i, sukan d'anyi light romance amma ba koda yaushe ba, saboda khaleefa baya son su k'arar da soyayyar tun kafun auren su. Sau biyu suka tab'a kwana a gado d'aya, daga ranar da tayi murnar cikar shekararta sai wata rana da tayi wani rashin lafiya. Soyayyar su takai gejin da ko ciwo d'ayan su yake sai d'an uwan shi ya kwanta irin ciwon, haka zasu taru suyi jinyar tare.

Rayuwar su a hankali ta dinga tafiya, d'an lokacin daya ragewa khaleefa na zaman karatu a k'asar yana k'arewa a kullum wayewar garin Allah. Tuni ya gama tsara yadda zai gabatarwa da auntie abubuwa biyu a lokaci guda, wato soyayyar shi da Saleema sai kuma maganar aikin shi a general hospital german. So yake idan ta amince aje a nemo mishi auren Saleema a can zinder sai taci gaba da karatun ta tana gidan shi har Allah yasa ta kammala shi kuma yana aikin shi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login