Showing 45001 words to 48000 words out of 288773 words

Chapter 16 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1049

yace, "dis girl was very stubborn". A zahiri kam ce mata yayi, "Wai ke heedayar mammie baki da maganar komai sai a baki chocolate?". B'ata face tayi tace, "toh ai kaine kace zaka zo har gida ka kawo mun chocolate na!".
Ayman sani idan ba lallab'ata yayi ba zata yi mishi haramiyar jin muryar Nur yau sai ya kwantar da kai yace.
"Ayyah afwan heedaya Zan kawo miki k'aton vanilla ice cream and 🍫 idan zanzo gidan ku amma yanzu ki kaiwa baby waya zamuyi magana". Aikuwa heedaya na jin haka ta daka tsalle ta hau ihun murna, sai a lokacin Nur ta d'ago saboda ihun heedaya da ya d'auki hankalinta har ta juyo tana kallonta, "heedaya ki kama kanki tun kafun na......". Saita fasa k'arasa waccen maganar saboda ganin wayarta a hannunta tana juyi da ita.
"Au wayar tawa ce a hannun ki?".
Matsawa baya tayi tare da mata gwalo, aikuwa Nur ta bita suka zuba tsere har gaban mammie a parlour, bayanta heedaya tayi ta b'oye tana fad'in, "mammie kinga auntie Nur zata dake ni ko?". Nur data tsaya daga bayan mammie tace, "mammie wayata fa ta d'auke mun tana tsalle tsallen ta dashi salon ya fad'i ya fashe".
Juyowa mammie tayi ta kalleta, "me yasa kika d'auke mata waya babie?".
Shagwob'e fuska tayi kamar zatayi kuka tace, "mammie gaisawa fa mukayi da Yaya Ayman". Saita harari Nur da take faman kumbura baki tana fad'in, "Allah mammie she's lying". "yanzu donta gaisa da Ayman d'in kike binta ki doketa! Shikenan bamu wayar mu bata tsoro takeyi wai kada ki kwace mata shi". Mammie ta k'arasa fad'a tana karb'ar wayar a hannun heedaya, duba screen d'in da zata yi sai taji nauyi ganin har lokacin yana kan layi, "karb'i mu ki b'ace mana a nan" ta mik'awa Nur, Nur tazo ta karb'a tana hararar heedaya don ba damar duka ta fuce, wayar ta kara a kunnenta tace, "hello lovely...". Ayman kam k'ayataccen murmushi yayi akan fuskarshi yace, "Ina jinki nuriyyah ta, me ya d'auke mun hankalin ki kika manta dani gaba d'aya".
Zama tayi kan kujera kamar tana gaban shi ta zaro ido, "nifa ban manta dakae ba, akwai dai wani abu da nake shirya maka na musamman Kuma bazan yarda ka gani ba sai lokaci yayi shine ya maidani busy?".
"Lokacin me! Nurienerh nidai ki fad'a mun yanzu kawae please".
"Shiyasa na fara fad'a maka ba zai yiwu ba, kayi hak'uri kawae saboda idan kaji yanzu lovely ai ya dawo ba surprise ba kenan, a'a nidai riga na yiwa raina alk'awari".
Murmushi ya sake yi komai na Nur mai sauk'i da k'ayatarwa, shiyasa rayuwarta take burge shi.
"Tom yanzu dae albishir d'inki".
Da sauri cikin son jin abinda zai fad'a Nur tace, "goro fari k'al ma".

_Dear fans Muna fatan kuna bibiye da littattafan in-identical twins cikin littafan mu naπŸ‘‰πŸ» JARUMAR UWA da kuma DARAJAR HAK'URI, Wanda muka shirya tsab don futar muku da wani salon labari na musamman da zai jijjigaku ya girgiza ku a k'arshe kuma ya k'ayatar daku ya Kuma saku nishad'i_

*Dubun godiya da jinjina gare ku masoyan asali da nake ganin comment d'inku babu kaukautawa, wanda yake sake k'ara mun kwarin gwiwar muku typing koda kuwa Ni Zan takure kaina ne. NagodeπŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ˜*



_Comment and share_
24/03/23, 2:02β€―pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*πŸ§•
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page thirteen1️⃣3️⃣


"Har da saurin ki?, toh nima na fasa fad'a miki sai kin fad'a mun abinda kike shiryawa idan ba haka ba kuma.... Kowa ya bar komai a ranshi".
Cikin had'e rai Nur tace, "Allah dama ba kayi niyyar fad'a ba".
Murmushi ya sakeyi kafun yace, "yaushe ya kamata na shigo na ganki? Kwana biyu aiki bai barni na nutsu ba, kuma ni kunyar mammie nake, ke kuma yanzu ko d'an kwana biyun ma da kike zuwa yiwa auntie kin daina".
Y'ar k'aramar dariya tayi, "Zan zo mata kwanan nan jira nake auntie shaheeda ta dawo daga gidan Aunty suhaila saina zo, ai munyi magana da auntien ma rannan da tazo".
Ayman d'an k'aramin tunani ya tafi akan shaheeda, duk a gidan su ba wadda jinin su bai had'u bama kamarta, shiyasa har mantawa yake da ita, tana da alfahari da mugun d'aukar kai wata tsiya shiyasa kwata kwata basa shiri da ita, "kaji me nace kuwa lovely?". Da sauri ya dawo daga d'an k'aramin duniyar tunanin daya fara tafiya "da naji dad'i kuwa! Allah yasa ta dawo da wuri ma".
Nur tace, "ameen amma ni dariya kake bani duk lokacin da zaka ce wai kunyar mammie ke hanaka zuwa sosai".
"Humm ba zaki gane ba Nur".
Sunci gaba da tattaunawa kafun bacci ya cika mishi idanu fal suyi sallama ya kwanta, ranar ko auntie bai je yiwa gud night ba. Sai itace da taga motar shi take tunanin yaushe ya shigo, tazo d'akin shi taita knocking shiru, tana bud'ewa ta ganshi kwance saman bed yana baccin shi hankali kwance, k'arasawa tayi har gaban gadon ta dafa goshin shi ta karanta mishi addu'o'i sannan ta futo taja mishi k'ofar d'akin tayi nata guri.


@@@@@@@


Raihana kuwa ranar da aka cika sati da yin bikin gidan su tana zaune k'ofar kitchen tana yanka salad da cabbage saiga yaro ya shigo wai ana kiranta waje inji wani yace sunan shi Imran, "Imran?". Raihana ta maimaita sunan a bakinta da mamaki, "eh haka dai yace". Ummie da take jin komai tsakanin su tace da yaron, "kace tana zuwa".
Yaron ya futa ita kuma ta shiga d'aki ta sauya riga armless da 3 quarter skirt da yake jikinta a lokacin ta futo cikin wasu kayan da zunbulelen hijab, makullin sitting room ummie ta bata tace, "ki kula". Da toh ta amsawa ummie sannan ta nufi k'ofar futa.

Yana tsaye jikin motar shi yana danne danne a waya, da fuska kadaran kadahan, bata k'arasa inda yake ba tayi tsayuwarta a k'ofar gidan su hard'e da hannu tana nazarin anguwar tasu, a haka Imran ya lura da zuwanta ya zura wayar aljihu ya k'arasa inda take.
Kallon kallo suka fara yi kamar zasu ce da juna wani abu sai kuma suka basar, Imran ne ya fara ajiye kanshi gefe yace, "amincin Allah ya tabbata a gareki raihana".
Raihana cikin d'auke kai tace, "tare da kai, mu k'arasa ciki ko". Ba musu tayi gaba yabi bayanta ita bata yi tsammanin ma zai shiga ba.
Madaidaicin parlour ne zagaye da kujeru da center carpet a tsakiya sai fridge a gefe da table. A two seater ya zauna ita ma ta nemi kujerar dake gefen shi ta zauna, cikin nutsuwarta ta soma gaishe shi, ya amsa yana kallonta, shiru yayi na a k'alla wasu mintunan, fahimtar da yayi zasu iya k'are zaman su anan har su tafi bata ce dashi k'ala akan rashin zuwam shiba saboda miskilancin ta, sai shi ya sauke nashi na aro yace, "sai kika jini shiru kwana da yawa, bana kiran wayarki, banzo inda kike ba kuma in kin kirani bana d'agawa alhali ina gani, baki ji duk kina son sanin me yasa ba?".
Girgiza mishi kai raihana tayi tace, "ko kad'an, ai mutum baya yin abu babu hujja musamman wanda yasan abinda yake yi kamar ka". Imran ya jinjina d'aurin talalar da tayi mishi cikin hikima, sai ya sake gyara zaman shi ya ce, "hakane sai dai raihana ni fushi nayi". Saita kalle shi a bazata, "fushi da me kuma?".
Imran yace, "very good! Raihana na fahimci har yanzu ni kad'ai nake kid'ina da rawata a kanki, da farko kenan, na biyu nayi mamaki yadda kika rufe mun wayarki tsawon kwana biyu bakiji daga gareni ba kuma kina yin rayuwarki ko a jikin ki? Haka nayi ta kiran wayarki kamar tab'ab'b'e har abokan aikina nayi mun dariya, na uku nazo d'aurin aure tare da mahaifina muka had'u da k'anwar ki tace bari ta nemo mun ke, nace a'a ta barshi kawai amma ta fad'a miki ki kunna wayarki zamuyi magana, shima kikayi burus! Toh a barshi kina cikin uzurin biki na hak'ura da hakan, sai dai abu na k'arshe daya tabbatar mun da zargina kuma yasa jikina sanyi zuciyata ta karaya, na kasa cikakken bacci saboda tunanin ki raihana, hakan yasa na gwada kiran ki a lokacin da ban tab'a gwada kira ba, infact ban tab'a tunanin in na kira ma za ki d'aga saboda lokaci ne da kowanne d'an Adam yake kwantar da hak'ark'arin shi don ya huta, sai dai kash na same ki busy kina waya a dai dai wannan lokaci, ban yarda ba ban hak'ura ba haka nayita jera kira har saida na had'a miki 3 missed call". Ajiyar zuciya Imran yaja sannan yaci gaba da maganar shi idon shi na kallon glass table dake gaban shi d'auke da drinks data kawo mishi "raihana a wannan daren na d'auka ko uzurin k'arya ai kya kirani don ki bani a matsayina na wadda kika amince zaki aura ku shimfid'a rayuwar aure me kyau da tsabta har mutuwa, sai baki yi hakan ba, Ina tunanin a lokacin ma Sam baki San na Kira ba sai washe gari da misalin k'arfe hud'u da minti talatin da uku, me kike tunanin zan d'aga na saurara daga gareki? Me zaki fad'a mun kuma?".
Raihana shiru tayi jikinta a matuk'ar sanyaye tana sauraron shi, tunda ya d'auko maganar da farko ta fahimci inda zancen ya dosa, tasan dai dama ba zai huce ya tuntub'i ba'asin wayarta da Ayman ba. Sai ta rasa abinda zatayi a lokacin, gashi ya zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma, da jiran jin amsar da zata bayar donta kare kanta. "Kayi hak'uri". Ta fad'a da jiki a sanyaye, murmushin takaici Imran yayi kafun yace, "kad'ai! Kina nufin nayi hak'uri shine amsar duk wad'annan jerun gwanon maganganun nawa?".
A sanyaye raihana tace, "toh aini bani da abinda zance maka bayan hakan".
"Ke kuwa kike da abun fad'a, ko baza kice komai ba tunda wani abun sirrin kine bance dole sai naji ba amma a k'alla ki fad'a mun da waye kike waya a waccan ranar", dam! Dam! Taji luguden bugu a k'irjinta, tana tsoron ambaton sunan Ayman a gurin Imran saboda ya d'auki dangantakar ta da Ayman da zafi fiye da zato.
"Kinyi shiru ko matsayina bai kai naji waye shi ba?". Ganin abun zai sake tsamari gashi bata iya k'arya ba sai tace, "Yaya Ayman ne shima akwai maganar da yake son zamuyi dashi bai same niba sai a wannan lokacin dana kasa bacci na kunna wayata, kuma ni bana waya da kowa cikin dare, shima ranar kawai a katari ne......"
Imran jikin shi har rawa yake wajen d'aga mata hannu ya mik'e tsaye a mugun zafafe yana fadin, "idan har naci gaba da jin maganar Ayman daga bakin ki ko shakka babu zuciyata zata iya tarwatsewa, na kasa fahimta! Na kasa fahimtarki har yanzu raihana, ta Yaya ma za'ayi mace ta k'ulla alaqa da wani d'a namiji da sunan friendship? Ni wallahi har gwara kice mun shi saurayin kine akan jin wannan mummunar kalma ta aboki a tsakanin ku".
Har tsorata raihana tayi saita sake takurewa gefe tana kallon yadda k'irjin shi yake up and down, matsalar shi kenan zuciya, a d'an zamanta dashi ta fahimci mutum ne mai azababben kishi. Shi kuwa Imran tsam ya mik'e ya koma gefen kujerar da take zaune ya had'a hannuwa biyu a gabanta, "don Allah ki taimake ni raihana, ba don niba ba don na Isa ba sai don darajar soyayyar da take tsakanin mu indai har da gaske kina jina a ranki koda rabin cokali ne ki rabu da wannan Ayman d'in", wani irin kallon kana hankalinka kuwa raihana ta wurga mishi, shi kuwa cikin rufewar ido yaci gaba da maganar shi, "yess ki rabu dashi raihana, ki bani sim d'inki na taune ki daina bin duk hanyar da zata had'a ku tunda ai ba a anguwar nan yake ba na sani, kinga shikenan daya kwana biyu baiji daga gare kiba zai hak'ura, hankali kwance alaqa tazo qarshe".
Mik'ewa tsaye raihana tayi cikin b'ata fuska tace, "bazai yiwu ba Imran, sai dai kayi hak'uri amma Sam bazan iya aikata abinda kake so ba, Yaya Ayman ya huce duk yadda kake tunani, kamar Yaya d'an uwa na jini yake a gurina, tarin alkhairan shi da d'awainiyar da yake yi a kaina ma baza su iya bari rana tsaka na watsa k'asa a ido na rabu dashi ba, sai dai kayi hak'uri.......". Ai Imran da yake jin kalamanta kamar tana watsa mishi garwashi kasa jure har takai k'arshen zancenta yayi, hakan yasa cikin zafin nama ya had'e ta da jikin shi ya rungume ta tsam tsam unexpected, "hasbunallahu wani'imal wakeel". Raihana ta fad'a a zuciyarta tana jin yadda zuciyarshi take kaiwa da kawowa a dai dai wannan lokacin, gashi yayi mata wani mugun rik'on tsauri da bata isa ta kwaci kanta cikin sauk'i ba saida dabara, sai dai a yadda take a fusace d'in nan sam ba zata iya tsayawa wani b'ata lokaci ba. Cikin zafi da k'una ta fara k'ok'arin barin jikin su ta hanyar soma ture shi, Imran kuwa jujjuya mata kanshi yake a goshin su daya had'e tare da fad'in, "Ina so kiji yadda nake ji a zuciyata raihana, raihana Ina sonki ta yadda bazan iya jure ganin ki tare da wani namiji ba komai k'ank'antar shi, Ina sonki Ina son ki da yawa har ni kaina bansan adadin ba, raihana nayi soyayyah da y'an mata daban daban amma ban tab'a samun wadda nake sonta koda quartern yadda nake son kiba, raihana ban k'iba na kewaya garin Kano Ina ambaton sunan ki da bayyana adadin son da nake miki ga kowa babba da yaro k'arami ko babbba, Ina sonki raihana wallahi Ina tsananin sonki sosai".
Raihana cikin fushi da fusata tace, "naji ka sake ni". Ba musu ya sake ta ya koma mazaunin shi ya zauna tare da dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu. Raihana kam ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jejjere a jejjere kamar wadda tayi tsere. Kafun Imran ya ankara har tabi hanyar futa daga sitting room d'in sai k'arar rufe k'ofar ta kawai yaji. Allah ya taimake ta bata had'u da kowa cikin familyn gidan ba har ta kewaya d'akinta ta shiga ta fad'a kan katifa ta fashe da wani irin kukan takaici, me yasa Imran zai mata haka? Me yasa zai nuna cewa jikinta yake so a aikace bayan a bakin shi kullum yana furta ita yake so? Ashe shima mayaudari ne kamar ragowar matasa masu kawo caffa ga rayuwarta don su ruguzata, shine ya sauya hanya ya turo da kud'in aure don ta saki jikinta dashi tunda aurenta zaiyi? "Imran me yasa".
Haka tayi ta kuka tana katse kiran daya ke jera mata, kafun daga k'arshe ya mata, text kamar haka, "shikenan raihana tunda kin kasa fahimtata kiyi yadda kike so, sai dai Ina so ki sani ko gaisawa kukayi dashi bayan igiyar aure na ta hau kanki toh bazan tab'a yafe miki ba! Nina tafi ki turo su jidderh su d'auki sak'o a inda na tashi".
Raihana ta karanta massage d'inshi yafi sau uku, mamaki take yadda yayi maganar shi hankali kwance tamkar baisan ma akwai wani kuskure daya aikata mata ba yanzun.
Da sauri ta mik'e ta shige bathroom jin alamun tahowa da maganar ummie. Sai data saisaita yanayinta ta wanke fuskarta sannan ta futo, lokacin ummien ma ta futa. A parlour ta same ta zaune tana duba text book d'in jidderh dake zaune gefenta.
"Na shiga kina ban d'aki".
Raihana tace, "alwala na d'auro".
"Imran d'in ya tafi Ina makullin?" Sai ta mik'e kawai ta futa daga parlon, a jikin k'ofar taga makullin, sai ta k'arasa rufewa ta zare key d'in kawai.
Ta mik'awa ummie bayan ta shiga parlon.

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…

Toh tun daga wannan rana sai Imran ya kasa gane kan raihana, ta sauya gaba d'aya ko wayarshi bata d'agawa, haka in yazo data futo sun gaisa take komawa gida tayi zamanta, sai dai ya k'ara ci tsayuwarshi har ya gaji ya tafi.
Tun yana share ta da tunanin zata sauko sai gashi ya zamana abu kullum hauhawa yake, dole daga k'arshe ya dinga rubuta mata text na magiyar ta fad'a mishi abinda ya faru don Allah. Kamar ta kyale shi sai kuma taga makaho fa baisan ana ganin shiba sai an zungureshi, sai ta rubuta mishi abinda yayi wanda Sam bata so. Shi dariya ma abin ya bashi, yasan ba zata d'aga wayarshi ba, sai ya sake mayar mata da amsa ta hanyar text massage d'in, "emoji na dariya, kin bani dariya wallahi babie, aini ban d'auka d'an hug d'in dana miki wancen ranar ne ya haddasa wannan fushi da gabar ba, na d'auka kina yin hakane saboda nace ki rabu da saurayin ku, yanzu don Allah ki fad'a mun meye laifi dan ka tab'a jikin matar da zaka aura? Ai ba wani abu bane, balle ma ni nayi ne cikin zafin zuciya bansan ma nayi ba".
Wannan text d'in sai yafi na farkon kona mata rai, wato baisan ma yayi ba, a gurin shi ashe k'aramin abune hug?.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login