Showing 276001 words to 279000 words out of 288773 words

Chapter 93 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1085

Bayan sun k'arasa gidan ma saida suhaana ta tashe ta sannan, ko sallama ba ta iya yiwa Ayman ba ta bud'e k'ofar sashenta ta shiga. Suhaana tabi bayanta ta d'auki kayanta zata tafi, hanata futa raihana tayi wai lallai saita kwana a nan, ita kuwa tace ba zai yiwu ba, ita kuma ta tubure, ganin abun nata bana k'are bane sai ta lallab'a tayi guduwarta.
Suhaana tana futa ko kayan jikinta bata sauya ba ta maida dim light ta kwanta dama duk abinnan da take bacci ne fal idonta, k'arfin hali kawai take.

Khaleefa kam sun d'an jima tare da Abban su suna hira, kafun ya musu sallama ya nufo sashen, yana shiga wanka yayi ya sauya kayan jikin shi zuwa tausasan kayan bacci, har ya kwanta ya jishi in complete ya tashi ya futo daga d'akin bayan ya rufe ya nufi nata.
Sai daya k'ara haske ya gano ta a farkon gado juyi d'aya zata iya fad'owa, ya k'arasa da sauri ya gyara mata kwanciyar, saida yaita tunani sannan ya shiga cikin bathroom ya had'a mata ruwa masu d'umi, ya zuba mata turarukan wankanta ya futo.
Cak ya d'auke ta bai dire ta a ko'ina ba sai cikin ruwan wankan daya tara mata bayan ya rufe mata gashin kanta da shower cap, kafun ta tantance a yanayin da take har ruwan ya fara ratsa ta, d'umin shi ya sake dilmiyata cikin wani sabon bacci mai dad'i, abun ma dariya yaba khaleefa, sai ya fara shafa mata ruwa a fuska har yayi nasarar tashin ta a baccin. Ta kuwa zabura zata futo ya sake dannata yana girgiza mata kai. Da lalube ya zura hannun shi ta bayanta ya zuge mata zif d'in rigar, ta kuma zabura cike da tsoro, ya d'ora hannun shi akan leben shi yana gargad'in ta, "kada kice komai! Kiyi wanka kurum". Dole ta koma cikin ruwan tana kallon shi zuciyarta na bugawa faster.
Bata samu nutsuwa ba saida taga ashe futa ma zaiyi a d'akin wankan, ta sauke ajiyar zuciya ta maza ta murza key sannan ta samu nutsuwar wankan.
Bayan ta gama ta d'auki bathrobe daya ajiye mata tasa, sai dai fa ta kasa futowa, ta tabbatar yana cikin d'akin gashi ba komai a jikinta dama kayan jikinta sun jima da jik'ewa. Dole saita futo zata sauya kayan.
Kamar munafuka haka ta bud'e k'ofar tana lek'a cikin d'akin, sai taga bata ganshi ba, ta k'arasa futowa da sauri ta nufi jikin wardrobe d'inta, sai dai abun mamaki a rufe take gam kuma babu ko key d'aya da aka bar mata. Saita fara laluba drower kota manta ta mayar ciki, sai dai nan ma babu, har ta yanke hukuncin komawa sai taga kaya saman bed d'inta. Ta tafi da sauri ta d'auka zata saka sai kuma ta fara juya kayan a hannunta, ohh Allah ta fad'a a ranta ganin irin sexy night wears daya kawo mata. Nan fa ta rarraba zuciyarta tasa ko kada tasa, jin kamar ana tab'a k'ofarta saita watsar da kayan ta koma jikin bango ta takure kamar wadda ta yiwa sarki k'arya tana faman zaro ido. Ganin ba'a shigo ba saita fara k'ok'arin saka kayan da sauri sauri, wando ne iya cinya da rigarshi sharara iya gwiwar k'afarta amma bata rufe komai na jikinta ba. Ta shafa turaren da taga ya had'a mata cikin kayan, nan da nan ta d'auki sirrin k'amshi. Bayan ta d'aure gashin kanta da ribbom tsayawa tayi gaban mirrow tana kallon kanta, ita kanta sai data ji kunyar kallon kanta cikin kayan, "taya ma zan iya tsayawa gaban shi a haka". Ta fad'a a fili, aikuwa tana rufe bakinta yana shigowa.
Cak ta tsaya ta kasa ko kwakkwaran motsi, shi kuwa Masha Allah Alhamdulillah yake fad'i cikin zuciyarshi. Ya murzawa k'ofar key ya fara takowa ciki zuwa gare ta idonshi a kanta ko kiftawa ba yayi har ya k'arasa wajen da take tsaye, ya tsaya daga bayanta ya dogare hannun shi jikin mirrown, ya sata a tsakiya yana kallonta ta cikin mirrown, kawai runtse idanunta tayi don bata ga banbancin a ganta da wannan kayan da tsirara ba.



_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy eight 7️⃣8️⃣


"Kinyi kyau". Ya fad'a da husky voice yana kallonta still ta cikin mudubin. Ita kuwa k'ok'arin kaucewa take daga gurin amma ya hana ta damar hakan fafur, tuno abinda ya faru tsakanin shi da suhaana d'azu sai ya harzuk'ata da k'ara mata k'arfi cassa'in cikin d'ari, (kunsan kishi k'arfin mata💪) ta kuwa d'aga hannun shi ta tafi da gudu zata futa a d'akin gaba d'aya.
Shi kuwa sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi, ganin ta dage da gaske tana ta kokawa da k'ofa sai ya kad'a mata mukullin hannun shi. Ta juyo tana kallon shi dai dai lokacin da shima ya juyo yana kallonta.
Da sauri ta d'ora hannunta kan switch ta kashe wutar d'akin gaba d'aya.
Ta cikin duhun ya fara lalubenta tana b'uya, kamar wasa sai gashi sunata wasan b'uya ya kuma kasa samunta. Raihana tun tana b'uya cike da tsoro sai gashi abun ya zamar musu wasan gaske, har yana sasu cikin nishad'i da tuno lokacin da suke yara ita dasu Salma irin wasan su kenan, in akayi nasarar kama mutum ayi mishi dundu hud'u.
Murmushi ne ya sub'uce kan fuskarta ta cikin dahun, sai kuma ta gimtse fuska ganin k'afar shi kusa da inda take durk'ushe, da yake ya juya baya tana mik'ewa yaji k'amshinta kusa dashi ai kuwa taku d'aya ana biyu ta jita cikin jikin shi gaba d'aya.
"Wana kama?".
Cikin marairaita tace, "kayi hak'uri don Allah".
"A'a sakin fad'a mun abinda ya hassala ki kika rufe ni da maseefa d'azu".
"Nifa Allah ba komaiii....".
Da sauri ya katse ta, "kar ki fara yimun k'arya ko jawabin rehu mai yawa, bazan iya zama da yawa ba cikin duhu".
Shiru tayi bata ce komai ba, "ki fad'a mun gaskiya before the count of three" sai ya fara k'irga d'aya, biyu, uku, da sauri tace, "Ni fa ba komai".
"Baza dai ki fad'a ba kenan?".
"Da gaske ba komai sai hana ni inga Abbana da kayi".
"shikenan let's sleep".
A hankali ta zame jikinta tana kallon shi ta cikin duhun tace, "okay saida safe".
Ya jingina da bango yana kallonta yace, "sleep tight dear".
Madadin ya tafi sai taga yaci gaba da tsayuwa, gashi so take ya futa ta kwanta. Saita gyara tsayuwarta tace, "so nake ka futa zan rufe k'ofar".
Ya maida hannun shi aljihu yace, "muje". Yayi gaba tana bin bayan shi har yaje kusa da k'ofar kamar zai murd'a handle sai kuma ya juyo unexpected ya jawo ta jikin shi ya rungume ta tsam tsam a k'irjin shi, Ya zura bakin shi cikin kunnenta da husky voice yace, "kin tab'a ganin inda macen arzik'i ta kori mijinta.....? Raihana zan baki dama ki fahimci zuciyata da abinda ke cikinta game dake a wannan daren, open your heart and read it clearly....".
Ko kafun ta samu kwarin gwiwar aikata wani abu ya d'aga ta cak....... Ya maida d'akin k'ark'ashin dim light.....
Abinda ya biyo bayan wannan dare ya kasance mai girma ga wad'annan bayin Allah guda biyu, the gentle love making under the dim light, abun yazo fiye da zato ko hasashen raihana. A ranar ta san zahirin Abdallah khaleefa, jajirtacce kuma gwarzon namiji da yasan sirrin soyayyah da yadda zai sarrafata, indai har da gaske his action express what's in his mind ta gama tabbatar da soyayyarta mai yawa dankare cikin zuciyarshi.

***Washe garin ranar suka tashi cikin jin matsananciyar kunyar juna, musamman raihana data kasa futa ko gaishe da mutanen gidan kamar yadda ta saba a kowacce safiya. Tana nad'e a gado tun bayan da tayi sallah ta kasa aiwatar da komai sai tuno scenes d'insu na jiya tana fudda sautin murmushi, babu abinda tafi tunawa kamar tsadaddun kalaman da khaleefa ya dinga furta mata. Tana wannan tunane tunanen bacci b'arawo yayi gaba da ita.

Lokacin data farka rana ta d'aga sosai, ta mik'e da sauri tana ambaton sunan Allah. Bathroom ta fad'a shap shap tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, tayi d'aurinta mai kyau da simple make-up kamar koda yaushe, ta shafa turaren ta mai sanyin k'amshi da sai in tazo dab ake jinshi.
A nutse ta fara takawa tana kallon yadda aka gyare ko'ina tsab, ba tayi mamakin ganin warmers ba tasan break ne auntie ta aiko musu kamar koda yaushe, sai dai kamar ba'a tab'a komai dake dinning d'in ba, tabbacin bai karya ba shima? Sai ta nufi d'akin shi ta d'ora hannu zata mishi knocking sai kuma tayi tunanin maybe bacci yake kada ta tashe shi kuma, saita tura d'akin a nutse tana lek'en cikin d'akin daga inda take. Yana kwance ya rufe jikin shi da duvet sai kace sanyi ake a garin. Ajiyar zuciya ta sauke ta juyo da nufin janye kanta sai taji muryarshi cikin dodon kunnenta, "in kin gama lek'en ki shigo ki had'a mun ruwan da zanyi wanka". Sam bata d'auka yana jinta ba saida yayi maganar, saita shigo a nutse kamar bata son taka k'asa har bedroom d'inshi ta had'a mishi ruwa kamar wanda tasan yana so a wanka. Bathroom d'in ba datti ko digo amma duk da haka bata futo ba saida ta tsaya goge mishi mirrow da sauyawa abubuwan shi da yawa muhalli kamar wadda aka sa🤔, tana cikin aikin ya shigo d'aure da towel daga kugun shi zuwa gwiwar k'afar shi, ta ajiye duster da sauri zata fuce ko kallon shi ta kasa tun sau d'aya daya shigo suka had'a ido a tsautsayi.
Da hannun shi d'aya ya tare ta, "Ina zaki kuma baki k'arasa aikin kiba madame".
"Zan gyara maka d'akin gadon...". Ta fad'a a marairaice.
Khaleefa yayi wani miskilin murmushi yace, "ohh aikin goge tiles da katakwaye har yafi na mijin ki muhimmanci?".
Ita dai bata ce dashi komai ba ta silale ta futo tana sauke ajiyar zuciya, tana jinshi yana fad'in, "matsoraciya kawai". Murmushi tayi ta fara had'a mishi d'akin da kayan daya cire sauri sauri. Lokacin daya futo ta jona burner da turare a ciki kenan. Wannan karon ma guduwa taso yi amma bai barta ba, duk rikicinta da tsoronta haka dai ta hak'ura ta taya shi shafa mai a jikin shi, ya gama da taimakonta ya saka kayan data zab'a mishi shadda sky blue da agogo takalmi da hula. Yayi kyau sosai har saida ta fad'a, "kayi kyau fa".
"Kinyi k'ok'ari zaki ce ba nayi kyau ba". Tayi murmushi ya kashe mata ido d'aya.
Tare suka futo suka zauna a dinning tayi saving d'insu da lafiyayyen break da aunty tasa a kawo musu. Nan ma cike da soyayyah sukayi feeding juna. Bayan sun gama ta tattare gurin tass gyalenta ta d'auko da flat shoe, yana zaune cikin parlon yana danna wayarshi ta k'araso ta dafa saman kujerar daga ta bayan shi tace, "Zan je mu gaisa dasu auntie da Abba".
Wayar ya mayar cikin aljihu ya dube ta, "ki d'auko kayan ki set biyu da duk wani abun da kikasan zaki buk'ata a kwana ki biyu kacal". Raihana kamar ta tambaye shi wani gurin zasu, sai kuma dai tayi yadda yace.
Shiya karb'i jakar kayanta ita kuma ta futo rik'e da hand bag ta rufe k'ofar parlon.
Saida suka fara gaisawa dasu Abba sannan suka haura sama gurin su auntie, bayan sun gaisa da doctor andal da momma da take ta zolayar su wai irin mijin irin matar, murmushi kawai khaleefa yayi ya tambayi Auntie, momma ta fad'a mishi ta d'an futa taje ta dawo. "Okay in ta dawo ki fad'a mata raihana tazo yi mata sallama ne zata d'anyi tafiya ta kwana biyu".
Momma tace, "lafiya dai ko?". Khaleefa yace, "lafiya alhamdulillah". Momma tace, "toh Masha Allah! Allah ya tsare hanya raihanatu ya dawo dake lafiya".
Khaleefa ya amsa da "ameen" yana mik'ewa. Itama da batasan komai akan maganar tafiyar ba ta mik'e tabi bayan shi.
Bayan sun futo suka had'u da mama haleema ma suka gaisa har khaleefa na tambayarta suhaana yaga bai ganta cikin parlon ba. Wani abu ya soki raihana har kwakwalwar ta ta tafi mata tariyar abinda ya faru jiya.
"Tana bacci ko a taso ta?". Yace, "a'a barta kawai in na dawo zamu yi magana". Ya k'arasa fad'a yana kallon raihana da har ta huce su tuni, sai ya yiwa mama haleema sallama yabi bayanta.
Mama haleema tabi su da kallo tana murmushi.
Khaleefa tunda suka futo ya fahimci sauyawar da raihana tayi amma baice mata komai ba saida suka d'auki hanya, "madame what's going on naga kin sauya". Ranta a had'e tace, "nothing". Sai yayi murmushi bai sake ce da ita komai ba, sun tsaya a k'aramin supermarket dake kan kwanar layin su yayi siyayyah sannan ya k'arasa da ita k'ofar gidan su. Yana yin parking ta soma k'ok'arin futa, lock yasa, sai ta tsaya tana kallon shi, shima kallonta yake, "a garin ku haka kika ga ake yi? Kawai daga parking sai ki fuce? At least dai kya tsaya muyi sallama ko?".
Gefen windown da take zaune ta juya kanta ba tare da tace mishi komai ba.
Shima bai sake ce mata ba ya fara k'ok'arin yin reverse zai bar layin, da sauri ta d'ora hannunta akan nashi tana girgiza mishi kai idonta fal ruwan hawaye tace, "don Allah kada ka fasa abinda kayi niyya, Allah kad'ai yasan ladan da zaka samu".
Tsayawa yayi yana kallonta yace, "Amma me yasa dana miki magana kika share ni? Ki kalleni da kyau kinga nayi miki kama da irin mazan da suke d'aukan rainin hankali irin wannan? Tun jiya nake tambayarki in nayi miki wani abu kince ba komai, dubi yadda kike kuka.....". Ya k'are maganar da juya kanshi gefe yana fatan jin abinda yake son ji daga gareta cikin kwanakin.
Ita kam share hawayenta tayi ta d'auko powder a jakarta ta gyara fuskar hadda k'ara wetlips.
Duk abinda takeyi yana kallonta ta cikin mirrow, saida suka d'auki tsayin wasu lokuta sannan ya bata damar futowa, ya mik'a mata ledar shopping da jakar kayanta. Ta karb'a ta russuna tana mishi godiya da tambayar, "kwana nawa zanyi?". Ya furzar da iska mai huci daga bakin shi yace, "biyu". Ta sake russunawa a gaban shi tace, "nagode".
Ya gyad'a mata kai yana kallonta da danne k'in amincewa da wani b'angaren na zuciyarshi yake sonyi yace, "zanyi kewarki raihanatu, nasan ke mantawa ma zakiyi dani da kin samu y'an uwan ki". Ba tace komai ba sai tsayawa da tayi tana kallon shi da wani irin bak'on yanayi, daga kwayar idonta ya fahimci abinda ke cikin zuciyarta. "Zan k'arasa gidan sai Allah yayi mun dawowa?".
"Sai kin dawo ko sai nazo d'aukar ki?". Saita tsaya ba tare data juyo ba, shi kuma yayi tattaki zuwa gareta ya tsaya dab da ita yana kallonta, saboda kusancin da sukayi saita d'an janye jikinta baya, shi kuwa cikin tsare gida yace, "ban yarda kije ko'ina ba bayan gidan khausar da Salma, hajiya ummaa da Inna da kaina zan kai ki gidan su kafun tafiyar mu tofa". Ta gyad'a mishi kai cikin matuk'ar jin dad'in abinda ya mata, "ki gaishe da ummie dasu al'ameen".
"Zasu ji nagode". Ta fad'a a sanyaye ta d'auki hanyar shiga gidan, saida takai k'ofar gidan ta juyo ta kalle shi, saita samu kanta da mishi murmushi da d'aga mishi hannu. Ya d'aga mata shima bai matsa gurin ba har ta shige.
Ya sauke k'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya shige motarshi.
Bai koma gidan ba haka yayi ta shawagi cikin gari, tun kafun aje da nisa ya fara gane kuskuren shi, don sosai ya shiga cikin kewarta amma yayi alk'awarin zai danne zuciyarshi ya bata damar sakewa tare da ummien ta da sauran k'annen ta.

***Ita kuwa ummie ba k'aramin mamakin ganinta tayi ba, koda ta fad'a mata yadda sukayi da khaleefa fad'a ta mata sosai da tunanin ko takura shi tayi ya dawo da ita, har saida ta mata bayanin komai dalla dallah sannan ta barta. Sunsha hira kuwa sosai ita da ummien irin wadda suka jima ba suyi ba. Sai a lokacin take warware mata dalilin zuwan su da abinda ya kawo su, ummie tayi al'ajabi kuma ta taya auntie murnar sake komawa gidan mijinta, tace da an kwana biyu zata je mata Allah sanya alkhairy.
Da dare Abbanta daya dawo ya ganta yaji dad'in ganinta shima, dama tun jiya ummie take fad'a mishi tazo k'asar. Sun tattauna game da abinda ya shafi karatun ta, a nan ma Abba saida yayita sawa khaleefa albarka da yabawa k'ok'arin shi.
Ranar sai nisan dare ta bar cikin su al'ameen ta shige d'akinta.

****A tak'aice kwana ki biyu da raihana tayi a gidan su ya mata dad'i tare da y'an uwanta, taje gidan Salma inda ta sameta tana laulayi sai rigingimu take yi wai daga haihuwa sai haihuwa ba hutu shikenan kuma ita haka zata k'are. A lokacin yasmine ce ta fad'o zuciyar raihana, sai taga sak yadda sukayi da ita farkon laulayinta. Haka dai ta lallab'ata da nasihohi ta gudu ta barta.
Khausar kuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login