Showing 174001 words to 177000 words out of 288773 words

Chapter 59 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1110

d'aya take da sauran matan daka sani ba....".
"Hum! Ai fahimtar hakan nema yasa na kasa hak'uri saida na magantu". Cewar jafar.
Wannan karon gyad'a kai Ahmad yayi kafun yace, "yayi mayen mata, toh wannan yarinyar dai matar aure ce". Wani irin kallo jafar ya mishi, kafun kuma ya sake cewa, "relax abokina abinda kake tunani sam ba haka bane, wannan sonta nake da gasken gaske aurenta zanyi, sannan Ina ganin da tana da aure khaleefa zai fad'a mun ai".
Wannan karon kafun Ahmad yayi magana khaleefa ya riga shi da cewa "toh ai baka tambayeni wannan ba....".
Mik'ewa tsaye yayi yana kallon Ahmad da khaleefa, mukhtar da yake zaune ya kyalkyale mishi da dariya, "dama na fad'a maka ka kiyayi zama tsakiyar mutanen nan biyu, ni nasan ma kawai matar khaleefa ce".
Shima jafar da son tabbatarwa ya kalle su. Khaleefa dai mik'ewa yayi don dare yaja, sai Ahmad ne yace, "of course matar khaleefa ce".
Jafar tsabar takaicin yadda suka mai dashi mahaukaci da hankalin shi yasa ya kasa cewa komai sai nuna Ahmad da hannu kawai, mukhtar da Ahmad kuwa banda dariya ba abinda sukeyi.
"Wato duk a mahaukaci kuke kallo na?". Ya tambaye su
Ahmad yace, "Haba jafar a gaban ka fa na kira khadija nace tasa matarshi ta shirya mishi wani abu yak'i cin komai, sannan ta shigo nace Madame kana nufin duk kanka bai kawo haske ba?".
Jafar zama yayi yana tuna tabbas duk anyi haka, kawai abu d'aya da ya kwashe duk tunanin shi shine yadda yaga daga ita har khaleefa basu nuna akwai y'ar guntuwar alak'a tsakanin suba koda ta gaisuwa. Sai ya sunkuyar da kanshi yana matuk'ar jin nauyin khaleefa,,,,,,
Mukhtar da Ahmad kam sun samu aikin yi a gaba d'aya daren ranar, magana kad'an zasu zolaye shi suyi dariya, tun yana taya su har ranshi ya b'aci ya bar musu gurin.

Tun daga wannan lokaci har ranar d'aurin aure jafar bai sake sakewa da kowa ba, har rawar kanshi ya rage, dama Saleem abokin shi yasha fad'a mishi idan bai bar halayyar kule kulen y'an mata ba watarana saiya jawowa kanshi abun kunya, gashi kuma ya gani.

Raihana kam tana can tare dasu ummu aphnan ta manta da babin ma wani khaleefa da matsalolin shi.
Yayinda gidan biki suke gudanar da bikin su mara hayaniya, babu event ko guda ta b'angaren su sai d'aurin aure da aka gudanar ranar juma'ah bayan an idar da sallah, a ranar ne kuma auntie da Ayman suka k'araso.
Raihana da yake tunda tazo ba suyi waya ba shiyasa bata san da zuwan taba.
Surayyah kuwa koda suka gaisa da ummie ta mata Allah sanya alkhairy, hira suka tab'a ta yaushe gamo akan yara da aiki, (da yake kusan itama tsohuwar ma'aikaciyar banki ce, data ajiye aikinta ba don lokacin barin aikin yayi ba). Ayman kuwa dama tawagar angwaye yayi.
Surayyah tana tason tambayar raihana amma ta nuna halin kara da kawaici, ita kuma ummie tana son taga wani cikin yaran gidan tasa a nemo wa auntien ita. Cikin sa'a kuwa sai ga Rabi'a, ita ta fad'awa tasa khadija ko Fatima su turo mata raihanan.
A lokacin tana kwance can k'arshen gadon d'akin, sanye da doguwar rigar shadda data sha d'inki mai azabar kyau, ba headtie sai rolling da tayi da d'an k'aramin gyale tunda ba futa waje zata yi ba, fuskarta ba komai sai powder, man leb'e da kwalli, cikin gidan ma ba wanda yayi wata heavy make-up duk kamar kwalliyar fuskar raihana ce a fuskokin su.
A lokacin da sak'on isowar auntie ya risketa da wani irin sauri ta tashi zaune tana tambayar inda take.
Fatima ce ta rakata har parlon da auntien take, da tarin farin ciki ta tafi da gudu kamar zata rungumeta sai kuma kunya ta kama ta, daga auntie har ummie dariya sukayi mata, a gefen k'afar auntien ta zauna ta d'ora kanta jikin k'afar idonta cike da hawaye. Dafa kanta auntie tayi tace, "daga gani na sai kuka kuma?".
Murmushi ta k'ak'alo a nutse ta fara gaisheta, ta amsa mata da tarin kulawa.
Gwanin burgewa ummie ta dinga kallon su kamar uwa da y'arta, tana fatan Ahmad yayi sa'ar samun halayen yesmine kamar na Raihana.

A daren ranar auntie tana zaune a d'akin da aka sauketa zata yi kwana d'aya ta koma, ta gama shirinta na kwanciya bacci tsab amma bata kwanta ba sai tagumi data rabka ta tafi duniyar tunani, idan tana lissafe yau sama da shekara talatin kenan rabon da k'afarta ta taka garin Abuja, kuma ko yanzu da tazo Allah Allah take gobe tayi ta bar garin ko hankalinta zai samu kwanciya, Zama gari d'aya da Suraj zai iya haddasa mata komai ciki hadda bugawar farat d'aya.
Knocking k'ofarta da akayi yasa ta sauke ajiyar zuciya taje da kanta ta bud'e, raihana ce d'auke da tray na shayi. Saita bata guri ta k'arasa shiga ta maida k'ofar ta rufe.
Saida suka sha shayin sudaniyyah sak da sak yadda ta koya mata sannan ta kalleta cikin tsanaki da tattara hankalinta guri d'aya ta kira sunanta, "Raihana".
"Na'am auntie". Ta amsa da bata dukka hankalinta.
Saida ta sake kallon k'afarta da hannunta ta gansu rad'au da lalle kamar sannan akayi shi sannan ta sake cewa, "wani abu nake son tambayarki game da rayuwar khaleefa! Amma kiyi mun alk'awarin zaki fad'a mun iya gaskiyar abinda kika sani".

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*


_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page forty nine4️⃣9️⃣


Raihana saida ta jinjina girman alk'awari, cike da tsoron abinda auntien zata so sani tace, "insha Allah zan fad'a miki gaskiyar abinda na sani".
Auntie tace, "Good! Nace kina yin turare dai kullum idan kika futo wanka kamar yadda na koyar dake ko?". ...
Gyad'a mata kai tayi.
Saita sake tambayar ta, "kina barin lallen jikin ki ya futa kafun sake yin wani?". Ta sake jefa mata wata tambayar.
Raihana tace, "a'a kafun ya futa nake k'ara saka wani...."
"Good girl, khaleefa yana cin abincin ki idan kika dafa?".
Tambayar tazo mata a bazata gashi tayi alk'awarin fad'ar gaskiya, tana tsoron kuma kada amsar da zata bayar ta tashi rigima tsakanin shi da mahaifiyar shi, don haka sai tayi shiru ba tace komai ba, "raihana tambayar ki nake".
Ba tare data d'ago ta kalleta ba ta girgiza kai, "ba ya ci".
Murmushi auntie tayi tace, "alright! Abu d'aya da zan sake tunasar dake dai shine, kinga lallen nan raihana, kada ki kuskura kiyi wasa dashi ki rik'e shi hannu bibbiyu kamar yadda nasha fad'a miki a baya, saboda wannan yana daga sirrin matan sudan da yasa a duniya suka shiga gaban kowanne mata musamman a gurin mazajen su, amfanin lalle a jikin mace yafi k'arfin kid'aya bare a iyakance shi, shiyasa a al'adar mu budurwa bata yin k'unshi da duk wasu sauran kwalliye kwalliye na mata har sai ranar da aka sata a lalle, daga wannan rana kuma ba za'a sake ganin k'afarta fari ba har tsufan ta, kinga lalle, kinga turare, kinga zaman iccen dukhan, girki, k'unshi, kitso, kwalliya da ladabi da biyayyah duk duniya su nasan muna rik'ewa mu zauna lafiya a gidan miji ba boka bare malam ba, toh ke girki da turare kad'ai ma kika rik'e ina da yak'inin saikin fasa zuciyar khaleefa komai taurinta raihana, ke dai kici gaba da hak'uri lokaci yana tafe da zaki juya khaleefa a hannun ki kamar masa".
Duk wannan bayanin da auntie take raihana shiru tayi tana sauraronta kanta a k'asa, nauyinta take ji sosai shiyasa ta kasa d'agowa ta had'a ido da ita sai murmushi da tayi don kalmarta ta k'arshe ta bata dariya, wai ta juya shi kamar wani d'anta, a zuciyarta kuwa tunani take ko wane irin so wannan mata take mata da yasa har take bata manyan lagon d'anta haka kyauta.
Ko a yanzu kafun ta tafi saida auntie ta k'ara mata wasu kayan lallen masu yawa tace ta k'ara akan nata gudun kada su yanke mata kafun ta kawo musu ziyara.

Raihana bata tafi ba sai can dare shima bacci ne ya cika idonta, bayan sunyi sallama da Auntien ta d'auki hanyar futa daga d'akin tana murd'e mabud'i shi kuma yana turo murfin zai shigo, abinka da namiji ma'abocin k'arfi kamar an hankad'a ta haka ta tafi taga taga zata fad'i, cikin zafin nama yayi saurin rik'o ta, yadda ta shiga rud'anin fad'uwa yasa duk jikinta ya d'auki rawa, hakan yasa khaleefa ya kwantar da kanta a k'irjin shi yana buga bayanta. Sai ajiyar zuciya take saukewa a jajjere donta saddakar sai taje k'asa a lokacin. Ayman da yake bayan su cikin wani irin mawuyacin yanayi ya tsinci kanshi kamar an watsa mishi garwashin wuta a zuciya, da kyar ya iya d'auke idon shi daga kansu ya huce cikin d'akin yana karanto duk addu'ar da tazo bakin shi don yak'ar shaid'an la'anannen Allah.
Khaleefa kuwa saida ya tabbatar nutsuwarta ta dawo jikinta sannan ya janyeta daga jikin shi ya k'arasa shiga cikin d'akin, ita kuma ta k'arasa futa da sauri.
Duk abinda ya faru auntie ta gani sarai duk da kwayar idanunta bawai tana kallon su bane direct.
A ranar khaleefa ya jima yana hira tare dasu don da gaske yayi kewar su gaba d'aya, bai tafi ba sai nisan dare sukayi mata sallama shida Ayman suka tafi makwancin su.
Sai dai Ayman ranar kasa bacci yayi sai juye juye, a duk motsin shi sai ya hango kan raihana rungume a k'irjin twin d'inshi. Daga k'arshe da yaga nutsuwa tana neman gagarar shi sai ya d'auro alwala ya fara karatun alqur-ani da k'ira'a k'asa k'asa gudun kada ya hana khaleefa bacci.

********

Washe gari su Auntie zasu bi jirgin takwas na safe su kuma raihana sha biyu na rana, hakan yasa raihana ta shirya da wuri cikin doguwar rigar atamfa wrapper, d'inkin ya mugun zauna a jikinta kamar a jikinta aka d'inka, bata sa turare ba amma duk da haka tashin sassanyan k'amshin daya zauna a jikinta take, da wadataccen gyale tayi rolling ta futo suka gaisa dasu Fatima ta gaishe da ummie da sauran mutanen gidan sannan ta tafi gurin Auntie, ko breakfast bata tsaya yiba, sai data nemi izini daga auntien sannan ta shiga cikin d'akin.
Tana zaune ita kad'ai a tsakiyar d'akin sanye da lufaya maroon colour da aka yiwa ado da manyan flowers black sai stones a jiki kamar yadda dai tazo jiya, a kullum raihana ta kalli matar nan sai taga kamar ba ita ta haifi su khaleefa ba saboda baiwar kyawun jiki da Allah ya mata, da kasancewarta ma'abociyar son kwalliya da k'alk'ale jiki kullum ba datti, iya zaman da tayi tare da ita ta fahimci duk sammakon ka ba zaka tab'a ganinta cikin datti ba, kamar ita su Yaya Ayman suka gada.
"Raihana k'araso mana ya zaki tsaya kuma". Ta fad'a tana kallon raihanan da yaba nutsuwar ta, komai nata a sanyaye bada zafi ba.
A k'asa ta zauna suka gaisa da auntien taji lafiyarta
"Raihana wanko hannun ki ki tayani mu cinye abincin nan dama yayi mun yawa".
Ba tayi mata musu ba ta tashi ta wanko hannun ta fara cin abincin a tsanake, suna ci auntie tana janta da hira, wani abun tayi dariya wani kuma tayi murmushi a haka khaleefa ya shigo bakin shi d'auke da sallama, kallo d'aya yayi musu ya d'auke kanshi ya durk'usa gefe ya fara gaishe da maman shi, ta amsa da fara'a kan fuskarta kamar babu komai. Itama raihana ta gaishe shi da girmamawa. Bai jima da zama ba Ahmad da Ayman ma suka shigo. Duk suka gaisheta, ta k'ara yiwa Ahmad Allah sanya alkhairy da gajeriyar naseeha kan hak'uri da rayuwar aure.
Ko data tashi tafiya gudunmuwa mai yawa taba ango da maman shi, raihana kam tana kuka suka rabu bayan ta mata alk'awarin tana tafe Germany nan da watanni uku insha Allah.
Babu wanda ya rakata airport cikin su don cewa tayi ta yafe tunda suma tafiyar zasu zo suyi bada jimawa ba.

Tare da aphnan raihana ta k'arasa zaman jiran lokacin tafiyarsu, wannan karon daga ita sai khaleefa sukayi sallama da kowa Ahmad ya sauke su airport suka d'auki hanya sai Germany.
Su biyu suka koma wannan karon ba kamar yadda suka zo ba, saboda Ahmad zai huce turkey ya taho da amaryarshi Yasmine ne.

Wannan karon ma sai yamma suka sauka a gajiye lik'is.
Tare suka jero suna tafiya sannu a hankali har suka isa inda zasu samu motar hayar da zasu hau.

Koda suka shiga gida babu wanda ya kalli d'an uwanshi suka raba hanya, da kyar ta iya yin wanka ta sauya kayan jikinta ta rama sallolin da suka huceta ta kwanta sai bacci.
Shima khaleefa wankan yayi ya rama sallolin da suka huce shi ya kwanta don ya huta kad'an kafun ya tafi nemo abinda zaisa a cikin shi.

Bashi ya farka ba sai nisan dare da wata irin azabtacciyar yunwa kamar ya ci babu. Yana duba agogo yasan kashin shi ya bushe don ba wani gidan abinci da zai tunkara a daren nan har ya samu abinda yake so, ruwan da baya rabo dashi a bedside ya d'auka yasha, aifa kamar wanda yasha guba haka yaji, gaba d'aya duniyar shi ta fara juyawa kamar ana hajijiya dashi, da dafa bango ya laluba ya futo daga d'akin ya zauna kan kujera d'aya dake cikin parlon ya had'a kai da gwiwa.

Itama raihana ta b'angarenta yunwar ce ta farkar da ita, sai kuma ta tuna da sallar isha'i da ba tayi ba, hakan yasa ta fad'a bathroom da sauri tayi alwalah ta futo.
Ko data idar da sallar hijab ta zura ta futo parlon donta samawa kanta abinda zata ci, a lokacin khaleefa yana zaune kan kujera ya had'a kanshi da gwiwa yana tunanin yadda zaiyi da rayuwarshi, dama tunda suka je bikin gidan su Ahmad bai iya cin wani abincin kirki sosai ba, a yau da zasu tafi ma k'in cin komai yayi yana ganin har zai ziyarci gidan abinci idan jirgin su ya sauka Germany ya samu abinda zaici, sai gashi gajiya ta hana mishi damar hakan, yanzu kuma yadda yake jinshi gani yake tak'i kad'an ne tsakanin shi da mutuwa gaba d'aya baisan abinda ya kwance mishi ba.

Raihana kuwa koda ta kalle shi sau d'aya hucewarta tayi kitchen, ta samu kitchen d'in k'ura fal kamar ta shekara bata nan, tasan dama za'a rina duba da iskar da ake bulbulawa a garin.
Abinda zata yi amfani dashi kad'ai ta duba, tea ta fara had'awa don warware hanji, kafun ya tafasa kuma ta had'a abinda zata yi sauk'ak'k'en abinda zata ci don magance yunwar cikinta a lokacin.
Tana cikin aikin khaleefa ya shigo a wani irin jirkitaccen yanayi, saida gaban raihana ya fad'i data ganshi, stool yaja ya zauna don bazai iya tsayuwa ba, ya kife kanshi jikin middle drower kitchen d'in, cikin damuwa da nuna kulawa raihana ta tambaye shi, "are you okay?". Girgiza mata kai yayi, hakan yasa ta shiga rud'ani har takai tana k'ara tambayarshi abinda ya same shi. Shi kuwa tsabar azabar da yake ji tasa ya kasa magana sai jujjuya kai da hannu kurum, abinda ya sake jefa raihana a tashin hankali har ta kaiga ta yanke hukuncin kiran auntie a waya ta fad'a mata.
Sai dai tuna nisan dare ne yanzu musamman a Nigeria da tashin hankalin da zata sasu yasa ta hak'ura, amma gaba d'aya ta kasa nutsuwa sai kallon shi take da tarin damuwa tana jero mishi sannu.
Shi kuwa khaleefa ta b'angaren shi azaba yake karb'a ba daga ko'ina ba, Kai tsaye a lokacin ba zaice ga takamaiman abinda yake damun shiba ma, abun da yake ji yana soya mishi k'irji had'e da murd'a cikin shi bai tab'a jin kwatankwacin shi a tsawon rayuwar shiba. Tun yana iya juya kanshi da addu'a har hakan ya gagara, sai kawai ya kwantar da kan ya d'auke wuta, abinda ya sake furgita raihana kenan ta d'ora hannunta aka ta fashe da kuka cikin matsanancin tsoro. Kamar me tsoron wani abu kuma haka ta dinga k'arasawa gaban shi tana k'ara volume d'in kukanta. Hannunta ta d'ora saman kanshi ta kira sunan shi a sanyaye, karo na farkon a tarihin rayuwar khaleefa da yaji sunan shi a bakinta "khaleefa!!". Bai iya amsa mata ba sai hannun shi daya d'ora saman nata don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login