Showing 12001 words to 15000 words out of 288773 words
Chapter 5 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
mata duhu na daga aikin makaranta, duk wannan alak'ar da suke amma ko magana d'aya bata tab'a had'a ta da khaleefa ba, kuma itama bata damu ba.
Toh kwanan su Ayman uku da bikin sauka Auntie ta tare a katafaren gidanta da ta gina, kowa ya yaba sai son barka, ranar da zasu koma gidan ma sunsha koke koke ita dasu iya da sukayi musu rakiya, da kyar iya ta iya zuk'ewa ta tafi gidanta ta barsu cike da kewar su da zatayi, halima kam dama ranar a gidan ta kwana saboda aikace aikace da sukayi musu yawa, wannan gida na surayyah ya assasa matsaltsalu da dama a cikin anguwa, inda mutane suka yita maganar su ta bak'in ciki da hassada akan tana mace zataje tayi zaman kanta, bayan tana da masoya masu sonta amma son duniya yasa ba zatayi aure ba, tana yawon bariki tana samun kud'i tana kashewa y'ay'anta a banza, abinda basu sani ba shine surayyah iya kud'in da tazo dasu a account d'in tama lokacin ya isa ta gina biyun irin wannan gidan, kuma alhamdulillah wannan ba asu tayi ba a ribar kasuwancin ta tayi, don kud'in aikinta shi suke ci, kud'in ta suna ajiye har yanzu ba tare da ko kwandala ta girgiza ba, karatun khaleefa kad'ai yasa ta tab'awa.
Rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, Ayman yana karatun shi na engineering in ya taso makaranta ya zauna mata a boutique, idan wata yazo k'arshe ta sallame su kai d'aya da haidar. Ta b'angaren khaleefa ma yana rayuwa bisa tsari da taka tsantsan kamar yadda auntien ta yi mishi naseeha, a shekara uku da tafiyar shi auntie ta je ganin su sau d'aya, ta kuma yaba da tsarin yadda suke rayuwar su a Berlin komai dae dae, Ayman yaso ace tare suka je a lokacin amma sai akayi rashin sa'a a lokacin suna da exams hakan bai yiwu ba. Surayyah bata tafi ba saida ta sake bar musu kud'i masu yawa na abinci da sauran hidimar karatu.
@@@@@@@
*AFTER SEVEN YEARS*.
Abubuwa da yawa sun faru dasu cikin wad'annan shekaru masu dad'i da marassa dad'i, Ayman ya gama karatun shi tuni har ya soma aiki, kuma har lokacin shagon surayyah yana nan saima ci gaba da ake ta k'ara samu, don tuni sun daina zama shida haidar sai wasu amintattun yaran ta samu ta zuba a ciki suke ci gaba da kular mata da kasuwancin. Ayman ya Zama cikakken matashi magidanci, ya k'ara kyau ya dad'a haske, gentle dashi ga nutsuwa ga haiba ga kamala da kyakkyawar zuciya mai iya zama da kowa lafiya.
Zuwa lokacin soyayyah mai k'arfi ta k'ullu tsakanin Ayman da nuriyyah y'ar sameera k'awar surayyah, bisa jagorancin iyayen su da Suka k'ulla zumuncin tun basu Kai haka ba, sosai Ayman yake son Nur haka itama, soyayyah sukeyi tsabtattacciya wanda suke fatan ta kaisu bisa turbar aure, nuriyyah fara ce sol kyakkyawa ba laifi, tana da matsakaicin jiki da tsayi dai dai nata, tana da nutsuwa da hankali ga kunya da yakana, duk wasu qualities da ake son mace ta gari ta had'a Nur ta had'a sai son barka. (Bayan haidar da k'anwar shi Khadija da tuni tayi aure shekaru uku da suka gabata, shekaru biyar tazarar tsarin iyali kafun sameera ta k'ara haifar shaheeda wadda daga itane sai Nur bayan wasu shekarun kuma ta haifi auta heedaya)
Ta b'angaren rayuwar Ayman kuma har gobe bashi da kamar auntie don ita kad'aice yake iya fad'awa abinda yake cikin ranshi ba b'oye b'oye, bashi da abokai hargitsae sai abokan karatu da aka sake had'uwa cikin aiki, sai raihanatu data kasance wata kwallin mutum guda tal da yake iya hira da ita as his best and closed friend. Itama ta zama budurwa saboda mak'erin y'an matanci tuni ya gama k'erata da a k'alla shekaru goma sha tara zuwa ashirin a lokacin, ita ba fara bace kuma ba za'a kira ta bak'a ba, kalar skin d'inta irin chocolate me haske, ba zaka kirata kyakkyawa k'arshe a fuska ba, haka ba zaka tab'a had'a ko kiranta da mummuna ba, tana da dirin jiki irin na cikakkun mata,doguwace ma'abociyar nutsuwa da kamala, ba mai surutu ba haka bata kasance shiru shiru ba, Soo cool, classy and gentle tana da wadataccen ilimin arabiyyah ana fafutukar neman na boko, ta gama secondary school tuni har mahaifinta ya Samar mata nursing school da ta ke garin bichi a lokacin saura watanni k'alilan ma ta kammala, abinda ya haddasa ja bayar alak'ar ta da Ayman kad'an, madadin da da take gida a kullum yammaci saiya zo gidan iya ya kirata a waya ta shiga sunyi hira, sai ya zamana yanzu sai dai suyi iya waya a kullum safiyar Allah ba fashi kafun ya futa aiki, sannan weekend yana ajiye duk uzurin shi yaje ya ganta, kuma ba zai tafi haka nan ba saida lifidi lifidin hidimomi har kunyar shi raihana take ji, da yawa daga friends d'inta na karatu da suka Santa da Ayman suna tunanin soyayyah suke yi tana b'oyewa ne kurum.
A tsayin rayuwar da Ayman yayi tare da raihanatu ya fahimci akwai wani b'oyayyen al'amari mai girma da yake bibiyar rayuwarta, amma saboda zurfin ciki bata tab'a yarda duk yadda suke ta fad'a mishi wani abu ba, duk da yana yawan ganin ta cikin damuwa wasu lokutan ma har tayi kuka a gaban shi, amma ba zata tab'a fad'a mishi kanzil ba sai rok'on ya sakata a addu'o'in shi, kuma baya tab'a mantawa da ita kamar yadda baya mantawa da shak'ik'an shi irin su Auntie, iya, malam, nuriyyah da khaleefa.
Alak'ar Ayman da nuriyyah kuwa ta zarce dukkan tunanin mai karatu, sonta yake irin sonda baya iya b'oyewa a gaban kowa, a yini idan baiji muryar taba yakan iya riskar kanshi cikin damuwa mai yawa har yaji shi kamar bashi da lafiya. Haka idan bata da lafiya ya dinga jin kamar ciwon a jikin shi yake kenan har sai ta warke.
_Wannan kenan_
@@@@@@
Ta b'angaren khaleefa kuwa rayuwarshi yake single, ya had'a degree d'inshi na farko dana biyu wato masters degree yanzu haka yana wani course ne da zai d'auke shi shekaru biyu kafun ya kammala.
khaleefa wani irin bahagon mutum ne, murd'ad'd'e da hali mai wuyar fahimta, sai kayi iya rayuwa tare dashi bakasan inda yasa gaba ba. A kamanni sak kamannin shi da Ayman babu wani banbanci har sumar kai da saje, abu biyu khaleefa yafi Ayman, murd'ad'd'en k'irar jiki irinta ma'abota k'arfi, sai dogon hanci da hasken fatar daya samu ta sanadiyyar zaman wata k'asa ma'abociya lumana da kwanciyar hankali.
Y'an mata course mate d'inshi da yawa suna tsoron shi da shakkar shiga shirgin shi saboda sunayi mishi kallon juyayyen mutum mai girman kai, mara mutumci, yayinda a gefe guda wasu da yawa suka mato a kan sonshi da begen shi, abu na uku daya sake banbanta khaleefa da Ayman shine halayyar su, Ayman yana da faram faram da sakin fuska ga kowa, khaleefa kuma bashi dashi, saurin fahimta da sauk'ak'k'en ra'ayin gami da hak'uri a kan komai na rayuwa ga Ayman sab'anin haka ga khaleefa. Wannan tarin abubuwa sune kad'ai zasu banbanta maka wad'annan zaratan matasa idan aka had'e maka su guri guda, shima fa bisa lura da nazari na musamman.
Shi khaleefa ko a apartment tunda yaje bai tab'a yarda yayi sabo da kowa ba in aka d'auke Ahmad wanda yake jin hirar shi har yaga murmushin shi, Babu yadda matasa basu so janshi cikin wani gang da sukayi creating na shan shayi da yin dinner tare ba amma furr yak'i, Ahmad ma daya fara zuwa da hikima ya janye shi ta hanyar nuna mishi kuskuren cakud'uwar maza da mata har a addininan ce ma da sunan wani abota, shiyasa shi bashi da wata k'awa mace a cewar shi babu inda mace da namiji akace su dinga cud'anya, a addini ba wani abota Allah ya raba tunda basu zo a jinsi d'aya ba.
Kamar yadda kowanne d'an Adam yake da buri da zab'in irin matar da yake so haka khaleefa ma ba'a barshi a baya ba kasancewar shi d'an Adam mai lafiya da numfashi, ya tsara yadda Angel d'inshi zata kasance tun kafun ya kai haka, da farko dai khaleefa yana son mace fara, y'ar siririya ba me k'iba ba, sannan ta zama ma'abociyar kwalliya da k'amshi, ta zama wayayyiya no d'aya kuma me aji. Wannan lissafi yana ajiye a zuciyar khaleefa tun kafun shekarun shi sukai haka, kuma har yanzu daya mallaki hankalin kanshi bai sauya ba.
Ranar wata litinin bayan ya dawo school yana zaune a harabar k'ofar d'akin shi, sanye da shirt da dogon crazy trouser, ya kife kanshi da hular sak'a kunnen shi kare da waya, sosai yayi kyau komai nashi gentle and cool, dariya yake yi yana sauraron yadda Ayman yake ta zuba mishi shagwob'ar ya daure inya samu hutu yazo musu gida, tunda shi Allah bai nufi zai je Germany ba. "Ai man sai hak'uri kawai don ni yanzu bazan sake samun hutu ba daga nan har mu kammala, kasan yadda kan mu ya d'au zafi cikin kwanakin nan ma kuwa?".
Ta d'aya b'angaren sake had'e rai Ayman yayi (a lokacin yana kwance saman doguwar kujera hannun shi dafe da kanshi, baya jin dad'i wani irin ciwon kaine yake damun shi kwana biyun nan, amma bai yarda d'an uwan yaji ba saboda zai shiga damuwa sosai). "Toh shikenan khaleefa inayi maka fatan sa'a". Khaleefa yana murmushi yace, "no one like you bloody".
Daga haka sukayi sallama suka ajiye wayar dukan su. Ci gaba da tsayuwa yayi a gurin yana gaisawa da student maza da suke mak'otaka dashi a gidan suna giftawa jefi jefi.
A gajiye ta shigo gidan, daga yadda take yarfa hannu da d'aga k'afafu na gane hakan, sanye take da riga da skirt na material pink ta yane kanta da k'aramin gyale match da takalmin k'afarta, tana goye da jibgegiyar jakar makaranta, hannunta kuma rik'e da wayar ta da LC. Fara ce tass kyakkyawa irin kyawun da kallo d'aya zaka iya ganin shi a tare da mamallakin farar fata. Idonta ne ya fad'a karaf cikin na khaleefa ba tare da zato bare tsammani ba, wannan shine kusan karo na uku da take ganin shi a gurin sai dai shi bai tab'a lura da ita ba har sun had'a idanu ba sai yau, hasalima a wancen lokacin har ta huce baisan da wucewar ta ba, ci gaba da takawa tayi har ta Isa apartment d'inta da yake kusa kusa da na khaleefa.
Khaleefa binta yayi da kallo har ta bud'e ta shiga sannan ya sauke ajiyar zuciya, karo na farko a tarihin rayuwarshi da wani abu ya tab'a faruwa dashi makamancin wannan, hasalima shi duk kyawun mace kallo d'aya ne yake raba su.
Komawa d'akin shi yayi shima ya rufo yana sake ganin hoton fuskar yarinyar data gifta shi a lokacin. Wasa wasa sai ga wani abu mai girma yana shirin riskar shi, abinda bai tab'a jiba a kan wata d'iya mace, k'arashen yinin ranar kasa tab'uka komai yayi har abinci bai iya ci da dare ba, domin samun nutsuwa dole ya kulle d'akin shi ya tafi gurin Ahmad, sun raba dare suna hira amma duk da haka baya cikin hayyacinshi, har Ahmad d'in yaso ranfo akwai damuwa a tattare dashi, amma ya fuske.
Kwana biyu a tsakani khaleefa sam baya cikin walwalarshi, burin shi kawai ya sake ganin koda giftawar yarinyar nan ne amma sama da k'asa bat tayi b'atan dabo ba ita ba alamunta, bai kasance mutum mai sa ido ba amma a y'an kwanakin nan har abinda yafi k'urilla ya koya, haka zai tsaya yana kallon hucewar kowanne d'alibi a harabar d'akin shi duk da sunan nemanta.
Sannu a hankali sai ga khaleefa yana neman had'a sati guda ba ita bare labarinta, har ya soma tunanin ko aljana ce tazo donta sashi a wahala ta bud'e mishi idanu.
Yau ma tun safe da Suka shiga lectures basu futo ba sai da rana ta take, ko break baiyi ba ga gajiya da take nukurkusar shi, yana ganin idan har sukace sai sun koma gida sunyi girki shida Ahmad zasu ci wani abu to lallai kafun lokacin shi ya jigata, bisa shawarar shi suka nufi wani k'aramin gidan cin abinci dake daura da makarantar su.
"ki rabu dashi kawai Amna ni sam bazan iya d'aukar tension d'in shiba, daga wancen sai wannan ni na gaji soyayyah aiba hauka bane mtsss!".
"Kada ki zama butulu saleeema ra'ees yayi miki k'ok'ari dai dai gwargwado, kada kuskuren shi d'aya yasa ki zab'i wofantar dashi ki manta duk wad'an can tarin alkhairan nashi, ki daiyi tunani Allah".
"Hum kinga ni tashi mu tafi na gaji da jin magana guda". Wannan hirar wasu y'an mata ne da suke zaune gaban table d'insu khaleefa, duk hirar nan akan kunnen sune sai dai basu ji abun ko kad'an a ransu ba, kamar ance da khaleefa d'ago sai kuwa idanun shi suka fad'a cikin nata karaf, take wani reaction yayi aiki na a k'alla dak'ik'a biyar kafun kowa ya basar ta hanyar d'auke kanshi, har suka futa bai sake d'agowa ba sai dai yaji ranshi fess kamar an yaye mishi duk wata damuwar shi. A k'alla dai yaga tana k'asar kuma ba aljana bace.
@@@@@@@
_Nigeria_
Sassanyan yammacin damuna ne, iskar hadari na kad'awa kad'an kad'an tana busar da ganyayyakin bishiyar da suke zaune k'asan ta. Raihanatu ce sanye cikin riga da wando na Pakistan ta yane kanta da gyalen kayan, ba'a ganin fuskarta saboda kanta yana durk'ushe kan gwiwarta, Ayman na zaune gefenta ya zuba mata ido yana nazarin maganar data fad'a mishi har cikin ranshi, so yake ya rarrasheta ta daina wannan kukan amma baisan ko ta ya ba, ya yarda k'addarar ta mai girma ce duk da bata bud'e baki har yanzu tace dashi komai ba. Numfashi yaja mai tsayi sannan ya soma magana cikin kulawa, "kiyi hak'uri raihanatu a kullum rayuwar kowanne d'an Adam tafe take da kalubane iri iri, da k'addarori masu rik'e da akalar kowacce nassara, Ina ji a jikina duk wannan abun da yake faruwa dake wata rana sai labari kuma kina gab da futa daga cikin wannan tsattsauran yanayin, hak'ik'a Allah yana tare dake".
Share hawayenta tayi da tafukan hannayenta, ta k'ak'alo murmushi ta d'ora saman fuskarta, mik'ewa tayi cikin sanyin muryar da taci kuka tace, "muje na taka maka yaa Ayman kaga hadari a garin ga kuma yanayin da muke ciki ba zanso kayi tafiyar dare ba".
Mik'ewa yayi ya tsaya kurum hannun shi zube cikin aljihun shi yace, "har yanzu kink'i amincewa dani a matsayin d'an uwa kuma amini raihanatu, shiyasa kika kasa amincewa dani har naji damuwarki, koda yake ba komai lokaci, muje ki taka mun". Sannu sannu suka dinga tafiya har suka k'arasa inda motar shi ke fake, kamar kullum yauma tsaraba yayo mata me yawa ta abun buk'ata na daga abinci da sauran kayan amfani na yau da kullum. "Don Allah ya Ayman ka daina hidimar nan haka,na last week ma daka kawo har yau bai k'are ba....".
Da sauri ya d'aga mata hannu nan da nan yanayin fuskarshi ya sauya yace, "ba ruwanki tunda ai bake kika sakani ba, and I don't want to hear any complain, har yanzu baki San muhimmancin abokin kwarae mai irin halayen kiba, sa'a tace dana same ki as mie closed friend raihanatu".
Dole ba don taso ba taja bakinta ta kulle har godiya yak'i saurara, tana ji tana gani ya shiga mota yayi reverse ya bar gurin yana hangen ta ta side mirror ya d'aga mata hannu, itama d'aga mishi tayi.
"Allah sarki Ya Ayman Allah ya saka maka da mafificin alkhairy". Raihana ta fad'a tana share hawayenta da gefen gyalenta.
Wacece raihanatu salees abdallah ne??
_barkan mu da daren Jumu'at babbar rana, fatan Allah ya had'a mu da dukkan alkhairan dake cikinta ameen_
_Comment and share_
24/03/23, 1:59 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lawal and doctor Ferhyeez m usman/ as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page five5️⃣
Raihanatu y'a ce ga ruqayyatu lameer da salees abdallah, dukkannin su haifaffun anguwar yakasai ne anguwa d'aya tsiran su layi biyu, salees ya had'u da ruqayyah ne a hanyar shi ta dawowa daga kasuwa da wani yammaci, ita kuma ta dawo daga makaranta, kamar da wasa soyayyah mai k'arfi ta k'ullu tsakanin su wadda itace har ta kaisu ga aure.
Ruqayyah taso fara aiki bayan karb'ar kwalinta na diploma bayan aurenta da wata biyu, sai dai sam salees ya nuna bai amince ba, idan har zata dinga futa kullum toh waye zai kula musu da tarbiyyar yaran da zasu haifa nan gaba, dole ta hak'ura tunda dama bata nemi komai ta rasa ba, salees matashi ne hazik'i mai k'ok'arin neman na kanshi a koda yaushe, kuma mutum ne mai d'aukar ragama, tun kafun yayi aure ya saba da hidin dimun gida, shiyasa ko bayan auren sa, d'aukar dukkan nauyin matar shi da gidan su bai gagare shiba duk da kasancewar shi mai k'aramin k'arfi.
salees tun kafun ya fara zuwa kasuwa ya had'a degree d'inshi na farko amma kasancewar aiki ya zama abinda ya Zama a k'asar mu sai bai tsaya jiran aiki ba ya fara harkar kasuwancin shi a kasuwar kantin kwari,