Showing 81001 words to 84000 words out of 288773 words
Chapter 28 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
ya d'auki mukullin motar shi, khaleefa na zaune a d'akin shi ya tankwashe k'afa yana duba abinda yake bincikawa ta cikin system d'inshi lokacin da Ayman ya shigo. Daga bakin k'ofa yayi mishi sallama bayan ya fad'a mishi zai tafi d'aurin aure ne ba jimawa ya dawo, da tak'aitacciyar addu'a khaleefa ya raka shi yaci gaba da abinda yake yi. Shi kuma fucewa yayi Yana k'ara mamakin d'an uwan nashi, a kowanne motsi na khaleefa sauyi yake gani, sai ya dinga ganin kamar ba asalin khaleefa nashi da ya tafi Germany shekaru tara zuwa goma baya ba.
@@@@@@@@
Raihana tana zaune a parlon gidan su, ta zubawa television ido kamar tana fahimtar abinda akeyi, nan kuwa tayi nisa ne cikin duniyar tunani, a cikin kwanakin har rama tayi saboda shiga damuwa da yawan tunani, ga Imrana a asibiti har yanzu yana karb'ar allurai, ga Ayman ya futa daga harkar ta gaba d'aya, ko y'ar wayar ma da suke gaisawa bayan kwana biyu yanzu ta gagara, gaba d'aya ta rasa abinda yake yi mata dad'i cikin kwanakin nan, kenan Ayman yana nufin daga haka zasu rabu? Kamar wasu maƙiya ko alagar nesa, ita Kam bata so haka ba, ta sone suyi rabuwa ta mutumci dashi ba irin wannan ba. Sai taja doguwar ajiyar zuciya ta sauke idonta kan ummie da take shigowa parlon rataye da jakarta, hannunta rik'e da jidderh. Saita mik'e tsaye tana fad'in, "sannu da zuwa ummie ya kuka baro su?". Ummie ta fad'a kan sofa tare da cire gyalen jikinta tace, "lafiya lou suna gaishe ki". Raihana tace, "aikuwa Ina amsawa".
Kitchen ta tafi ta kawo wa ummie ruwan lemon data had'a da rana. Ummie ta karb'a tana sha sanyin shi na ratsa y'ay'an hanjin ta, ta sha da yawa kafun ta ragewa jidderh da take zaune gefenta saura. Kallon raihana tayi ta sake cewa, "na shiga gidan iya mun gaisa har tana tambayar ki". Raihana tayi y'ar dariya tace, "Allah sarki iya zan shiga ai mu gaisa cikin satin nan" ummie tace, "da kin kyauta dai kam".
Daga nan suka ci gaba da tab'a hirar su har zuwa lokacin da ummie ta shige d'akinta, ita Kuma ta tafi wajen wayarta. Tayi zaton zata samu missed call d'in Imran sai taga babu sai text massage daya mata, "yakike raihanata fatan kina lafiya, hak'ik'a addu'ar ki tana tasiri sosai a kaina, yanzun haka likita yace zai iya sallamata nan da kwana biyu ko uku masu zuwa, naji sauk'i alhamdulillah kuma ina futowa ke zan fara zuwa na gani, saboda nayi kewarki fiye da yadda ke da kowa kuke zato.... I love you Soo much raihana".
Koda Imran ba kiranta yayi ba amma taji dad'i da taga massage d'inshi, ta fahimci idan yana tare da maman shi baya tab'a kiranta, itama kota kira ba zai d'aga ba, tun wani lokaci sau d'aya daya kirata suna cikin waya taji muryar maman tana ta maseefa har yau bai k'ara yadda ya kirata in tana kusa ba, bai fad'a mata baki da baki ba amma kasancewarta mutum mai saurin fahimta tuni ta d'ago shi.
Sai da ta mishi refly sannan ta sake dawowa parlon hannunta rik'e da wayarta.
Tana zama kamar jira sai ga alart daga Ayman, saida ta jinjina kafun tayi dialing no shi, kamar kullum yau ma bai d'aga ba, sai ta mishi text na godiya kawai ta ajiye wayarta.
******** ********
Auntie kuwa a yinin ranar ta had'awa khaleefa d'akin shi kamar yadda ta had'awa Ayman, k'aramin gado da k'aramin carpet a k'asa sai wani madaidaicin table a gaban gadon, sif mai biyu sai drower. Yana zaune a parlour har suka gama had'awa suka yi mishi sallama suka tafi, auntie kuma da kanta ta kawo mishi duvets fari da mayafin rufa da duk sauran abinda tasan zai buk'ata.
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: https://chat.whatsapp.com/CKR7E0qHjy0L9W04t8Acc2
*JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page twenty three2️⃣3️⃣
Da yammacin ranar yana zaune still a parlor yana operating system akan aikin da yasa gaba a yanzun, ya fara jiyo hayaniyar mutane da yawa suna nufo d'akin. Yana daga kanshi suna fara shigowa cikin d'akin, auntie da sameera ne sai baby heedaya da Nur a baya.
Suna shigowa heedaya ta daka tsalle tayi inda khaleefa yake zaune ta d'ane bayan shi, "na kama ka, yau sai ka biya mun duk chocolate d'ina da kullum kullum kake yimun alk'awari ta waya kak'i kazo ka kawo mun". Murmushin gefen baki yayi ya janye ta daga bayan shi ya zaunar da ita gefen shi, su kuwa duk guri suka nema suka zauna a kujerun parlon. Nur dai ta kasa daina kallon shi, a dole ita so take ta fahimci Ayman d'inta ne wannan ko kuma khaleefa, bata fahimci komai ba har taji muryar shi yana gaishe da mammin su.
Ta amsa mishi tana k'ara kallon shi itama, kallon surayyah tayi bayan sun gama gaisawa da khaleefa tace, "wato surayyah tunda nake ganin twins ban tab'a ganin masu tsananin kama da juna kamar su Ayman ba, kinga ni yanzu ban fahimci waye a cikin suba fa". Dariya auntie tayi tace, "ba kums zan fad'a miki ba sai dai ki canka da kanki".
Nur dai tana gefe tayi shiru tana kallon yadda ya d'auke kanshi yana ci gaba da abinda yake yi a cikin system, a ranta tace Anya wannan Ayman ne kuwa? Tasan Ayman be kai hasken wannan ba kuma bashi da shariya irin haka.
Heedaya kuma ganin ya share ta bai biye mata kamar Yaya Ayman ba sai tasa hannunta a screen d'in system d'in ita ala dole ta rufe tace, "Ni dai ka fara bani chocolate d'ina sai kaci gaba da aikin ka irin na Yaya haeydar". Khaleefa ganin zata dame shi sai kawai ya nemo wayarshi da take gefen shi ya dannawa no Ayman kira, ringing uku hud'u ya d'aga, "yae man ka futo Ina ganin kana da bak'i fa". Yana gama fad'ar sak'on shi ya ajiye wayar gefe yaja kumatun heedaya data zuba mishi ido, "ya sunan ki?" Ya tambayeta yana kallonta, cikin iyayi da iya reto tace, "heedaya". Murmushi ya kuma yi yace, "Nice name baby heedaya me bakin kwad'ayi, yanzu zai kawo miki chocolate d'in naki". Y'ar dariyar jin dad'i tayi, a maganar shi bata fahimci komai ba sai za'a kawo mata chocolate. Sameera tana shirin fad'awa auntie ta gane su sai kuma ga Ayman ya futo. Aikuwa heedaya na ganin shi ta tashi da gudu ta b'uya a bayan auntie tana fad'in, "aljani, auntie aljani mai kama da Yaya Ayman b'oye ni kada ya kamani".
Sai a lokacin Nur da mammie suka gane lallai wanda ya futo yanzu shine Ayman. Shi kuwa heedaya da take lek'o shi daga bayan auntie ya zarowa ido yana fad'in, "Bari kiga nazo na d'auke ta zuwa duniyar aljanu gaba d'aya.....". Aikuwa ta rintse ido tana sake mak'ale auntie da faman kiran ta b'oye ta. Cikin jin nauyin mammie ya durk'usa suka gaisa daga inda yake, itama a haka ta amsa mishi. Kusa da khaleefa ya koma ya zauna. Sai a lokacin sameera tace, "Masha Allah khaleefa an zama physiotherapy Doctor saura aiki da aure kuma......".
Shiru yayi jim kafun ya d'ago kanshi yace, "Aure ai da sauran lokaci, aikine dai munyi magana da wani likitan k'asar Germany zamuyi aiki tare dashi a wani asibitin k'ashi dake Berlin inda mukayi karatu". Saida gaban auntie ya fad'i, ta d'ago kanta daga danne dannen wayar da take ta zuba mishi ido tana kallon shi, shi kuwa tuni ya maida kanshi ga abinda yake a system d'inshi. Kallonta sameera tayi suka had'a ido sai ta gyad'a mata kai, meaning taci gaba da maganarta. Sai tayi gyaran murya again ta sake cewa, "Allah sarki Allah yayi jagora yanzu can Germanyn zaka koma da zama kenan?". Sai ya rufe system d'in gaba d'aya ba don ya samu matsaya kamar yadda yaso ba yace, "eh to kusan hakan dai". Mamie tace, "okay fatan nasara toh amma zakayi auren ne kafun ka bar k'asar nan ko? Ina ganin dai kamar zaifi ai?". Sai a lokacin ya kalli Auntie ta d'aure fuska tamau ba alamun annuri. D'auke kanshi yayi cikin basarwa. Ayman da yake rakub'e gefe saboda wanzuwar mammie a gurin kallon shi kawai yake, wato duk burin da yaci akan yana dawowa k'asar suyi aure shine zai watsa mishi k'asa a ido? Lallai khaleefa akwai abinda ya taka duk wannan d'abi'un da yake timming ne, don yasan khaleefa farin sani ciki da bai, mutum ne me rik'e abu a rai yayi ta riritashi b tare daya fad'awa kowa ba har sai an matuk'ar kai ruwa raana sannan.
Yana sauraron duk hirar da suka dinga yi shida mammie akan karatun su da banbance banbancen kowanne a cikin karatun likita a k'asa Nigeria, abun ya burge auntie kwarai a lokacin da take sauraron yadda yake bayani da zallar kwarewa kan abinda ya karanta, yanzun ta sake tabbatar da ba'ayi asarar kud'in da aka kashe akan karatun nashi ba.
Saida aka kira magrib sannan suka mik'e su duka har Nur da baby heedaya da tayi bacci jikin auntie tun tsoratar da tayi na ganin Ayman. Shima d'akin shi ya shige don ya d'auro alwalar sallar magrib data k'arato.
Ayman ma alwalar ya tafi ya d'auro yabi d'an uwanshi suka tafi masjid tare.
Auntie tana zaune a parlon ta tayi shiru tana kallon sameera da take zaune kusa da ita, "matsalolin khaleefa kullum gaba suke k'ara yi sameera, kinsan tunda ya dawo nake ganin bak'in halaye tare dashi kuwa? Gaba d'aya nema yake ya ware kanshi daga cikin mu shiyasa ya k'irk'iro tafiya aiki Germany,,,, da yake ban isa ba a gurin shi ko amincewa ta bai nema ba shi da kanshi ya yankewa kanshi hukunci, tunda shi d'an kanshi ne....". Sameera da take zaune kusa da ita tace, "kiyi hak'uri surayyah, ni gani nake kamar miskilancin shine yafi futowa yanzu, kuma kinsan namiji dama yana girma yana sauya halaye, dole kiyi hak'uri da bak'in halayen da zaki gani daga gare shi har zuwa lokacin da zaki lallab'a shi yayi abinda kike so, sannan abu na biyu kada mu shiga hak'k'in shi akan maganar auren nan, mu ajiye maganar shaheeda a gefe ki tabbatar ya futar miki da matar da yake so kafun komawarshi Germany, shine kad'ai hanyar da zaki samu nutsuwa bayan tafiyarshi k'asar da uwa ba kwab'a uba ba harara..... Sannan kada ki hana shi aikin nan...". Doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon sameera still da damuwa a fuskarta ta sake cewa, "kina nufin na soke zab'in da nayi mishi na matar da zai aura? Toh aikuwa sameera indai khaleefa ne sai dai zuciyata ta buga da bak'in ciki na mutu shi bashi da asara da dai yayi abunda nake so, don bazai tab'a aure cikin datsin nan ba Ina mishi magana zaice bashi da zab'in irin matar da yake son aure".
Murmushi sameera tayi tace, "kada ki fara fassara shi zuwa ga abinda baki sani ba k'awata, ki bari dai kiji daga gare shi tukun, sai dai bada hayaniya ba, ki bishi a nutse da y'an dabaru, in kika so ma kice mishi zaki amince ya tafi Germany amma ba zaki yarda ya tafi ba matar aure ba, a wannan lokacin sai ki ji abinda zaice miki, yadda na fahimci yana son aikin nan tsab zai amince da zab'in matar da zaki mishi don ya samu cikar burin shi cikin sauk'i,,, sannan ni banga abun damuwa da komawar shi Germany ba".
Cikin gamsuwa da shawarar k'awar tata tayi na'am lokaci guda, shiyasa lokuta da yawa idan kanta ya kulle game da matsalolin yaranta sameeran take samu su shawarta, da yake ta fita yawan yaara nan da nan zata d'ago mata bakin zaren.
Shaheeda kuwa da take tsaye jikin windown bedroom d'in da Auntie ta bata na jikin d'akinta, tashi hankalinta yayi da jin furucin auntie da kuma irin shawarar da mamanta ta bayar, sai taji kamar ta futo ta yak'i komai ta nemi shiga a gurin khaleefan, daga jiya zuwa yau data ganshi gaba d'aya ta kasa samun nutsuwar ruhi, haka kurum ya shiga cikin zuciyarta ya zauna da baud'ad'd'en ra'ayin shi da halayen shi, ba don komai ba sai don abu guda data fahimta tun farkon ganinta dashi, Dole zai zama daban a cikin maza, kuma mai kwakwalwa, ita Kuma irin mijin da take so kenan tun da jimawa, take mafarkin had'uwa dashi oll dis time, yanzu kuma ta samu mamanta tana shirin yi mata..... Sai ta daki k'arfen window da hannunta d'aya cikin takaici. Ta lashi takobin duk hanyar da tasan zata bi don tasa khaleefa ya sota sai tabi, kuma tana ji a jikinta dole zai sota ma tunda batayi kala da matan da namiji zai k'i ba duk aji da kyanshi ko kud'in shi kuwa, saboda tasan ita d'in mai kyau ce tun tasowarta, haka k'awayenta suke yawan kod'ata bata gasgatawa har zuwa yanzu data mallakin hankalin kanta ta tabbatar da gaskiyar abinda suke fad'a game da ita. Murmushi tayi a zahiri bayan ta tsaya gaban mudubi ta sake k'arewa kanta kallo, a zahiri ta furta, "khaleefa da sannu zaka so ni ba tare dana yarda ka fahimci soyayyarka da take cikin zuciyata ba, zanci gaba da jan girma da ajina har zuwa lokacin da zaka zube k'asa a gabana kana neman soyayyata". Sai ta sake sakin wani murmushi na K'arfafawa kanta da kanta gwiwa.
_(Toh fans ga shaheeda da jin kanta zata fad'a mafarkin ido biyu, ga khaleefa wanda ya fita baud'ewa yayi nisa cikin soyayyar Saleema a gefe)_
@@@@@@@@
Khaleefa kuwa yayi nisa cikin binciken family of Abdallah tofa, binciken shi ya tabbatar mishi da cewa Abdallah tofa wani shahararren d'an siyasa ne daya rik'e muk'amai da yawa a k'asar Nigeria, ya tab'a rik'e ambassador Nigeria a k'asar turkey ma, hakan yasa ya daina harkar siyasa gaba d'aya, ya zauna a k'asar turkey kusan shekaru goma sha tara kafun a sauke shi ya dawo Nigeria da zama din din din. Abdallah tofa ya rasu shekaru talatin da uku wannan shekarar ta silar accident a hanyar zuwa Kano daga Abuja. Khaleefa yaci gaba da bincikawa sai dai baisan sunan y'ay'an shi ko guda d'aya balle yabi diddigi yaji tunda shi Wanda ya fara bi a matsayin kakan su ya rasu, duk da dai khaleefa tuni ya sare jin k'aton familyn da binciken shi ya kaishi, yana ji a jikin shi ba daga babban family irin wannan suka futo ba. Sai ya zubawa computer gaban shi ido kawai yana nazarin ta inda zai b'ulla ko Allah zaisa ya dace da abinda yake nema, zuciyar shi ta bashi shawarar ko ya rubuta sunan mahaifin su??? Knocking k'ofar shi da akayi yasa cikin sauri ya rufe system d'in ya tura ta gefe sannan ya tashi da kanshi yaje ya bud'e. Ayman ne tsaye hannun shi duka biyu goye a bayan shi yana fuskantar k'ofa, "sannu da dawowa daga aiki Mr engineer" khaleefa ne yayi wannan maganar, Saida yayi kamar ba zaice mishi komai ba sannan yace, "ban futa aiki ba yau saboda Ina hutun k'arshen shekara na wata d'aya". "okay" kawai ya fad'a ya bashi hanya ya shiga cikin d'akin sannan ya maida k'ofar ya rufe. Duk zama sukayi a gefen gado sukayi shiru kowa da abinda yake tunani a ranshi kafun Ayman yace, "me yasa ka fad'i abinda ka fad'awa mammie jiya". Kai tsaye khaleefa ya bashi amsa, "saboda abinda na fad'a shine abinda yake raina kuma ban iya k'arya ba kaima shaida ne bare na shirya mata k'arya don na burge ta". D'an jim Ayman yayi yana son yaga ko zai iya fassara abinda khaleefa yake nufi, bai fahimci komai ba hakan yasa ya sake cewa, "na fuskanci kamar kana son nisanta kanka damu shiyasa ka nemo aikin k'asar Germany". Numfashi ya sauke me tsayi kafun ya ci gaba da magana, "nasan ka reasonable person baka tab'a yin abinda babu cikakken hujja ko dalili, sai dai nayi iya nazarina don ganin na nemo kuskuren da mukayi maka nida auntie har yanzu ban iya tunowa ba, shine nazo na rok'e ka don girman Allah khaleefa ka taimaka ka fad'a mana sai mu nemi yafiyarka muci gaba da zama lafiya kamar yadda muke da farko......". Zuba mishi ido khaleefa yayi kamar zaice wani abu sai kuma ya basar cike da tausayin d'an uwan shi rabin ranshi, Ina ma Ayman yasan abinda auntie take b'oyewa game dasu, Ina ma yasan da gaske basu da cikakken asali?? Da bazai k'ara mishi kallon zargi akan duk wani bak'on hali da zai nuna ba, sannan ya tabbatar bazai sake ganin farin auntie ba har abada. Sai ya durk'usar da kanshi yana tuna kalaman Saleema da suke mishi amsa kuwwa a cikin kunnenshi kamar yanzu take furta mishi su, wannan kalma ta da uba ake ado ta kasa barin ranshi, k'ona shi take da kowanne motsi ko yink'uri da zaiyi, ba don Saleema ta kasance macen daya fiso a duniya in aka d'auke mahaifiyar shiba, da har abada shida sake kallonta bare ma har ya fara tunanin aurenta a yadda ta jefe shi da mummunar kalmar da babu wanda ya tab'a jifan shi da kwatankwacinta, toh amma soyayyah!! Allah ya d'ora mishi