Showing 168001 words to 171000 words out of 288773 words

Chapter 57 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1073

kan d'aya daga fararen kujeru biyu da suke a harabar gurin, hannunta rik'e da wayarta ta lula ciki da alama chat take, kallo d'aya zaka fahimci mabayyanin farin cikin da take ciki.
Tana nan a saleemarta babu wani sabon abu ko bak'o tare da ita.
Ta jima a gurin kafun k'awarta Amna ta k'araso a gajiye ta ajiye jakarta gefe tana cewa, "sannu da zaman jira! Na barki kina ta jirana ko?".
Saleema murmushi ta wanzar a saman fuskarta ta ajiye wayar hannunta kan table d'in daya raba kujerun su tace, "ba komai nasan akwai abinda ya rik'e ki".
Amna tace, "wallahi kuwa".
"Ke nifa jiya da kyar na iya bacci, so nake kawai kizo don tunda naji kince akwai maganar da zamuyi nasan muhimmin al'amari ne ya taso....".
Amna tace, "humm! Sosaima kuwa, amma kafun na fad'a miki maganar nan dai da bakya so zan k'ara jaddada miki, ki dinga yin dogon tunani kafun aiwatar da komai na rayuwarki, kiyi hak'uri ba wai shishshigi zanyi miki ba amma.......".
Saleema ta d'aga mata hannu da sauri tana kallonta, kafun cikin had'e girar sama data k'asa tace, "don Allah muyi magana akan abinda ya kamata! A ganina zaifi ko?".
Amna tace, "hakane tunda bakya son gaskiya! Toh khaleefa dai ya dawo k'asar Germany zaiyi aiki a matsayin physiotherapy doctor............."


🤦‍♀️sai hak'uri not edited


_fans please kuyi hak'uri da jina shiru kwanaki da yawa, na shiga matuk'ar uzuri yanzun ma dakyar na samu lokacin dana muku wannan, gashi nan dai ba yawa_.


_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page forty six4️⃣6️⃣


Murmushi tayi me kama da yak'e, ta mik'e tsaye ta juyawa Amna baya tayi taku biyu zuwa uku sannan tace, "nasan da labarin dawowar shi, tun a ranar da jirgin su ya sauka.....". Saita juyo ta kalli Amna data zuba mata ido itama tana kallonta kafun taci gaba da cewa, "inda nasan wannan labarin zaki bani.... Da bazan fara b'ata awowi cikin muhimman lokutana ina jiran ki a nan ba".
Tana gama fad'ar haka ta d'auki wayarta zata bar gurin, da sauri Amna ta dakatar da ita, "ai baki ji k'arshen labarin ba, mufi muhimmanci a ciki kuma, ko kinsan dame khaleefa ya dawo Germany a wannan karon??....".
Sake d'aga mata hannu tayi, wannan karon a d'an zafafe tace, "me yasa dole sai kinsa raina ya b'aci ne Amna????, Tuntuni nasan akan me kike duk wannan y'an kewaye kewayen. Toh ya ishe ki haka ki barni nayi rayuwata yadda naga dama tunda ba taki bace,,,, khaleefa bake kika had'a ni dashi ba, kuma baki Isa kice zaki raba muba".
Da wani mugun mamaki Amna take kallonta, kafun cikin jin zafi tace, "ki dinga sanin abinda bakin ki zai furta mun Saleema? Wace irin maganar banza ce zaki ce Ina k'ok'arin raba ki da khaleefa!". .
Saleema bata bata amsa ba sai tsaki da taja ta d'auki hanyarta.
Da kallo Amna ta bita tana magana cikin d'aga murya yadda zata iya jiyo ta, "Saleema Ina ganin lokaci yayi daya kamata mu raba hanya kowa yaje yayi rayuwarshi, don banga amfanin zaman mu tare ba tunda ba zamu iya amfanar juna da komai har shawara akan abinda ya kamata da zai amfani rayuwar mu kuwa.......".
Ko waiwaye Saleema bata yiba duk data jita sarai, sai a ranta da tace, "sai yanzu kika san haka kenan.... Aikin banza".

*NIGERIA*

Tafe take sannu a hankali cikin motarta tana tuk'inta cikin tsanaki, a gajiye take tibus burinta kawai ta Isa gida ta kwanta ta huta don cikin satin gaba d'aya bata jin dad'in jikinta k'arfin hali kawai take yi da office d'in ma baza taje ba.
Tana k'arasowa Ayman daya dawo aiki a lokacin shima yana shirin cusa hancin motarshi cikin gidan, saita jira ya shiga itama ta bi bayan shi.
Kusan tare suka futo, ya k'araso gurinta yana mata sannu da zuwa.
Ta amsa da murmushi tana kallon shi da yadda ya sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa, hakan na mata dad'i a koda yaushe inta ganshi.
Koda suka shiga cikin gidan mama haleema tana zaune cikin shirin tafiya, jira take kawai cikin auntie ko Ayman wani ya dawo ta tafi gida.
Aikuwa auntie tana zama gaisawa kawai sukayi ta bata sak'on da wata yarinya ta kawo a ajiye mata, ta mata sallama zata tafi.
Auntie ta karb'a tana tambayarta, "da wuri kuma yau?".
Mama haleema tana dariya tace, "Eh wallahi akwai abinda zanyi a gidan kinsan in kana da y'ay'a kullum cikin raba case".
Auntie tace, "aikuwa damma Allah yasa ba fitinannu a ciki". Mama haleema tace, "duk da haka sai godiyar Allah kinsan sha'anin yaran yanzu ". Auntie tace, "Toh Allah dai ya k'ara shiryawa"
Mama haleema ta amsa da "ameen" ta sake mata sallama, har ta kai k'ofa auntien ta tsayar da ita, "wannan sak'on baki fad'a mun ko daga Ina ba kuma?".
Shiru tayi tana nazari kafun can tace, "toh ni dai wata yarinya ce ta bani shi, haka dai take doguwa me matsakaicin jiki, fuskarta har ta bani ta tafi a rufe da takunkumi".
Itama auntien shiru tayi tana nazarin ko zata iya gane wacece, kafun ta fara duba ledar don koma waye in taga sak'on zata iya ganewa.
Ko data bud'e invitation card ne guda uku da kwalin chewing gum, sai pass na event har hud'u.
Sunan shaheeda data gani yasa ta gane sak'on daga k'awarta sameera ne.
"Bikin yazo kenan? Toh Allah ya sanya alkhairy". Ta fad'a a zahiri kafun ta tashi ta shige bedroom.

Suu kuwa gidajen biyu ta ko'ina shirye shiryen biki suke babu kama hannun yaro, akwatuna sha biyun da aka kaiwa raihana aka karb'o aka sake kaiwa shaheeda bayan an sauya wasu daga cikin kayan da wanda suka fisu tsada da kyau.
Ango dai kam sai yadda akayi dashi, tun da aka fara maganar bikin bashi da wani abu guda d'aya a cikin tsare tsaren daya yishi don ra'ayin kanshi, komai yayi musu shi yadda suke sone, akan abu guda yaja da maman shi da tace shaheeda zata zauna a sabon gidan shi inda ya tsara zai zauna da raihana, yace sam sam ba zai zauna a can ba sai dai su zauna tare da maman a nan gidan mahaifin shi.
Ran hajiya tafeeda da sameera kuwa ba k'aramin b'aci yayi ba da sukaji abinda yace, kuma koda hajiya tafeeda taso ta matsa masa kan lamarin, nan da nan abban su ya takawa abun burki da saurin shi, a cewarshi ai akwai rufaffen b'angaren da ba'a amfani dashi sannan ko a saman gidan zasu zauna meye laifi in akayi haka.
Dole tana ji tana gani ta amince da tsarin Imran ba don ranta naso ba sai don ba yadda zatayi.

Ta b'angaren sameera kuwa daga mijinta har mamanta sun zuba mata ido suga iya gudun ruwanta.
Saboda mahaifiyar ta har gida ta kirata da taji labarin abinda ya faru tsakaninta da surayyah, ta bata shawara tun wuri taje ta janye abinda ta furta ta bar yara suyi auren su, amma baiwar Allahn nan tayi funfurus tayi watsi da maganar don tana ganin itace akan gaskiya ba surayyah ba, Kuma har asibiti taje ta bata hak'uri amma ta nuna sam bata buk'atar Nur da Ayman tare, gashi yanzu ma ta raba hanya da ita k'arshe kenan, toh meye kuma zata sake je mata da maganar a karo na biyu.

Amarya shaheeda tasha shiri da gyara in and out.
Musamman aka ajiye mata me gyaran jiki bayan hajiya tafeeda ta caji kud'i daga Imran.
Abin ka da farar mace nan da nan tayi d'au sai walwali take.
Sun shirya event kala kala ita da k'awayenta ranar farko zasuyi lunching, sai rana ta biyu henna, rana ta uku kuma bridal sai dinner da za'a gabatar last. (Amma fa duka ita da k'awayenta kad'ai zasuyi ko dinner ango ya bada uzurin ba zai samu damar zuwa ba)
Ta b'angaren iyaye suma sunyi shirin su kama daga kamuu,,, shagalin su na ranar iyaye,,,, da yini.
Ba k'aramin kud'i suka futar wajen yin shagalin bikin nan ba, y'an uwa da abokan arzik'i kuwa na kusa dana neesa duk sunzo ba'a cewa komai sai son barka.

Tunda suka fara taron bikin sameera take sakaran ganin surayyah amma babu ko inuwarta har sai ranar da aka d'aura aure da yamma tazo mata Allah sanya alkhairy.
Aikuwa ta rasa inda zata ajiyeta saboda karramawa.
Abinci kuwa cikin na bak'i na musamman ta kawo mata haka ma drinks.
Ita kam dama a k'oshe take bata iya cin komai a gurin ba sai ruwa.
Data tashi tafiya ta bata kyautar mayun turarukan sudanniyyah masu tsada da wani set d'in flask.
Har wajen motarta sameera ta rakata tana ta mata godiya.
Ita dai ta kama hanyarta, daga nan ma gidan su iya tayi don kwana biyu basa nan sunyi tafiya ita da malam zuwa garin su sai jiya suka dawo.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya, y'an uwa da k'awaye sun raka amarya gidanta lafiya.
Sai dai sun kwafsawa hajiya tafeeda, don tana can ta kwafe a parlonta ita da hamshak'an k'awayenta tana jira a bata girma ta hanyar shigo musu da amarya ta nemi albarkar su sai suka ga sab'anin haka. Aikuwa ba tayi wata wata ba ta dokawa sameera kira tana tambayarta bata fad'awa y'an uwanta yadda tsarin yake ba, da farko bata gane abinda tafeedan take nufi ba sai daga baya da tayi mata dalla dallar bayani. Hak'uri ta bata tace suyi hak'uri zata kira su zasu zo yanzun nan.
Hajiya tafeeda ta ajiye waya tana fad'awa k'awayenta yanzu za'a kawo amaryar. Sameera kuwa koda ta kira k'anwarta ta fad'a mata maza maza su kai amarya b'angaren surukarta ba musu suka amsa mata, sai dai Amarya tana jin batu ta buga tsalle ta dire tace ita ba inda zata, suka kad'a suka raya shaheeda tace ba zata iya jure sake sauka da hawa ba. (Da yake ita a sama take)
Daga k'arshe suka kira sameera tace a had'a ta da ita a waya, nan ma tak'i karb'an waya. Dole sameera ta kashe wayarta tana takaicin shegen taurin kai da kafiyar shaheeda, shiyasa kwata kwata bata so aka had'a su gida d'aya da tafeeda ba, don tasan k'awarta sarai ba hak'uri gareta ba, ita kuma shaheeda taurin kai da bak'in rik'o, gashi komai k'ank'antar abu akayi mata bata yafiya, dama ba don Nur tak'i ba itace lafiyar Allah.
A gidan amarya kuwa Tsabar haushin abinda tayi yasa y'an uwan mammie sukayi fushin zuciya suka dundungure mata kai sukayi tafiyarsu ba'a bar mata ko mutum guda ba sai k'awaye.
Suma har k'annen mammie sun futa suka sake shawara suka dawo suka sallamu kowacce cikin su ta kama gabanta aka barta ita d'aya.
Itama hajiya tafeeda kafun su tafi suka biya suka bata uzurin k'arya na cewar amarya bata da lafiya sun baro ta dai a kwance tasha magani.
Ba don ranta yaso ba ta karb'i uzurin, don yau taso k'awayenta suga surukarta ta nunawa sa'a, ko ta futa kunya itama, toh amma ko yanzun ai babu laifi tunda zasu had'u da an kwana biyu, zasu k'ara ganta.

Ranar babu wanda yaga k'eyar Imran sai nisan dare, a lokacin shaheeda ta dad'e da sauya kayan jikinta zuwa na bacci ta kwanta tuni.
Saida ya shiga bedroom d'inshi da yake kallon nata ya shirya tsab sannan ya d'auko ledar daya shigo da ita ya nufi d'akin ta.
Ya murd'a handle a hankali ya shiga cikin d'akin da baya tashin komai sai wani irin k'amshi me dad'in shak'a.
Saida ya kunna glove haske ya mamaye d'akin sannan ya ajiye ledar hannun shi gefe, shi kuma ya jingina da bangon da aka jingina gadon yana k'arewa matar da ake cewa tashi kallo.
Baccinta take sadidan, ta rufe daga k'afarta zuwa rabin cikinta, uban kitson gashin dokin da aka mata ya zubo har gadon bayanta saboda sake shi da tayi.
Fara ce tas kyakkyawa shi kanshi zai iya shaida hakan, sai dai kwata kwata baya jinta a ranshi ko kad'an, saboda shi a rayuwarshi mace kalarta bata tab'a burge shiba, raihana yake so da komai nata, itace tsarar shi tsarar soyayyar shi, tsarar auren shi, a itane kad'ai yake ganin natural beauty ba wanda kyale kyale ko hasken fata ya k'ara futar dashi ba.
Sai ya sauke ajiyar zuciya me tsayi, ya k'arasa gaban gadon sosai yana k'ok'arin tashin ta, don yayi alk'awarin bazai tab'a wasa da duk wani hakkinta da yake wuyan shiba, don baya son abinda zai kaishi wuta ranar gobe kiyama.
Cikin magagin bacci ta bud'e idonta tana kallon shi dishi dishi kafun ta mik'e zaune da sauri tana kallon shi.
Gefen gadon ya zauna ba tare daya kalleta ba yace, "ki tashi ki d'auro alwala zamu yi salllar nafila raka'a biyu".
Banza tayi dashi kamar bata jishi ba har saida ya maimaita abinda ya fad'a sannan tace, "zaka iya yi kai amma ni bazan yiba".
Imran baisan lokacin daya waiwayo ya kalleta ba jin amsar data bashi kai tsaye da tsayayyen harshe.
Ta juya fuskarta gefe d'aya kuwa kamar ba ita tayi maganar ba.
Sai bai sake ce da ita komai ba yaja sallaya ya shimfid'a yayi sallarshi, ya jima yana addu'o'i kafun ya sallame ya d'auko ledar daya shigo da ita.
"Zaki iya tasowa muci abinci?". Ya nemi sani don yaga saida tambayar.
Girgiza mishi kai tayi tace, "Ni na k'oshi".
Bai damu ba ya mayar da komai gefe ya ajiye tunda shima ba wai yunwarce dashi ba, kafun ya baro gidan auntie saida ta cika mishi shi da abinci mai kyau.
Ya kashe kwan d'akin yabi gefen gadonta ya kwanta daga can k'arshe, da farko shaheeda sauka tayi daga gadon tana kallon shi da kaifafan idanunta, shi kuwa ya juya baya ma sam baisan tana yiba don abinda take tunani ba shine a ranshi ba, ko kad'an baiji komai a kanta ba, duk daya ganta daga ita sai wannan fingilalliyar rigar bacci.
Ta dad'e a tsaye kamar y'ar patrol, bata sake kwanciya ba kuma saida taji yana sauke numfashi tabbacin yayi bacci.

*Imrana ango*😜

*Germany*
Tun washe garin ranar khaleefa kamar yadda ya fad'a ya kawo mata sim na k'asar ya saita mata. Aikuwa ta kwashe kaf contact d'in y'an uwanta na kusa dana nesa, haka k'awayenta su fatima babu wanda ta bari wai don tayi aure, don a rayuwar makaranta sun yiwa juna amfanin da ba zata iya yada su donta fara taka matattakalan nasara ba, ko me ta zama a rayuwa ba zata sauyawa y'an uwa da k'awayenta ba wannan alk'awarine ta yiwa ranta.
A ranar kasa hak'uri tayi har saida taji muryar ummienta, Auntie da abbanta, sannan tabi ragowar y'an uwa duk taji lafiyar kowa.
Ta jima da raheela suna waya tana bata labarin abubuwan da suke faruwa game da auren Fatima da gurbin karatu da zata samu ita kanta ta had'a degree a A. B. U zariya bada jimawa ba.
Sosai raihana ta taya su murna da fatan alkhairy kafun suyi sallama kowa ya ajiye wayarshi.
Rayuwar raihana a Germany ta kasance lami ba wani armashi, sai ta kwana biyu ba tayi magana da khaleefa kota gaisuwa ba, saboda a kullum ya taso aiki gidan Ahmad yake shiga baya dawowa sai dare, haka weekend ma a can yake yini, ita harta fara tunanin ko aikin nasu har weekend ne ba hutu ma.

Bata fara zuwa makarantar da khaleefa yake k'ok'arin sama mata gurbi ba sai bayan da suka share watanni hud'u a k'asar ta Germany da zama.
Admission d'in yazo dai dai da lokacin bikin Ahmad da aka k'arawa wata guda, kamar wancen karon haka wannan ma ya shirya mata tafiya ba cikakken bayani, ita dai tana kallon ikon Allah, saida ya saura kwana biyu su tafi Nigeria a d'aura auren Ahmad khaleefa ya shirya tunkararta da zancan don tayi shiri kafun ranar.
Tana kitchen tana had'a abincin da zata ci a daren ranar, don girkin ma yanzu ba kullum take yiba tunda cikinta ita d'aya.

Sanye take da doguwar riga mai fad'i tayi rolling da k'aramin gyalen rigar, hakan yasa gashin kanta data tubke tuli guda ya samu damar zama a k'eyarta har ya bada shape me kyau.
Aikinta take tayi kanta a k'asa batasan da shigowar shiba sam, kuma koda wasa bata d'ago ba.
Khaleefa kuwa abinda ya sake bashi damar zubawa fuskarta ido da son gano


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login