Showing 141001 words to 144000 words out of 288773 words
Chapter 48 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
Da kallo auntie ta bita kafun ta mik'e tana yiwa su ummie maraba, ta basu guri suka zauna aka gaggaisa, sukayi mata ya me jiki. Shima Ayman har k'asa ya durk'usa ya gaishe su, sukai mishi sannu da jiki. Sun d'an zauna jimm kafun su tashi tafiya. Fruits da drinks suka ajiye, aikuwa auntie tayi ta godiya. Har wajen k'ofa ta raka su sannan ta dawo.
Wannan karon gefen gadon da Ayman yake ta samu guri ta zauna ta kira sunan shi da sanyi a muryarta, "Ayman" bai amsa ba amma dai ya d'ago kai ya kalleta, bata damu ba taci gaba da cewa "kasan dai ni d'in nan mahaifiyar kace ko?" Sai ya gyad'a mata kai, "sannan kasan a duniya baka da kamarni ko". Sake gyad'a kai yayi, "kasan da haka amma kake nuna mun halin ko'in kula, baka fad'a mun matsalar ka bare wani abu daya shafi rayuwarka mai muhimmanci da zan iya taimakon ka, tun kafun kazo nan nake yi maka fad'a kan ka rage damuwar da take ranka kak'i, yanzu ga likita ma abinda yake fad'a kenan, ko kafi son na rasa kane Ayman?".
Kanshi a k'asa yake sauraron kalamanta har ta gama, bai iya ce da ita komai ba. Itama tayi shiru na wasu sakanni kafun taja gwauron numfashi tace, "game da maganar daka fad'awa Nur in na fahimceka kana nufin ka hak'ura da ita kenan?".
Sai yanzu ya kalleta, "Auntie Nur dama zab'in kice, yanzu kuma da kika nuna bakiyi ammana da ita ba, ni bani da wani zab'i sai bin yadda kika so".
Gaba d'aya maganganun shi sun kashe mata baki, ya d'aureta da jijiyar jikinta har batasan me zata ce ba kuma, tabbas ta dad'e tana bin takun Ayman abinda ya fad'a haka yake a gurin shi, bai tab'a d'aukar Nur da wani matsayi sab'anin na zab'in mahaifiyar shiba, baya ga haka yana da mugun zuciya in yabar abu ya barshi kenan har abada, yana da sauk'in kai yayi wasa yayi dariya, gashi da bala'in hak'uri ba komai ne yake b'ata mishi rai har yayi magana ba,,,, amma fa zuciya,,,,, banbancin shi da khaleefa komai son da yake yiwa abu zai iya barshi muddin ya zamana da matsala, shi kuma khaleefa yana da naci akan abinda yake so sam baya zuciya, sannan bashi da yawan magana ko shiga shirgin mutane, saboda bashi da hak'uri, bazai iya jurar abinda Ayman zai jura ba, sai dai abinda bata gama fahimta ba har yanzu shine, shin Ayman ya shiga damuwa ne saboda gorin da sameera ta mishi ko wani abun daban ne yake damun shi?
******* A yini guda da suka k'ara a asibitin Mutane sai zuwa sukeyi y'an dubiya, likitan ya sallame su tuni amma tafiya ta gagara saboda cikowar mutane, wasu ma batasan inda suke samun labari suzo ba, su Muhammad duk sun dawo duba shi hadda abun arzik'in su. Kaya Kam a asibitin rasa inda surayyah zata zuba su tayi, k'arshe dai ta had'a wasu cikin patient d'in asibitin dasu suka tattara suka tafi bayan iya ta k'araso.
Ahmad yana zaune a parlon su Khaleefa dasu Muhammad da suka taho nan daga asibiti, hira suke irinta tuna baya, rayuwar makarantarsu suke tunawa, wani abun suyi dariya wani su jimanta.
A lokacin khaleefa yana bacci ya dinga jin tashin hirar su ta cikin mafarkin shi, tun yana ji sama sama har ya dawo shiga kunnen shi tangaran k'arshe ya tashi ya zauna.
Agogon hannun shi ya fara dubawa, 02:50pm sai ya mik'e da sauri yana kallon kayan jikin shi zuwa kanshi, sai ya dafe kanshi da hannun shi kafun ya mik'e da sauri.
Wanka yayi ya d'auro alwala sannan ya shirya cikin riga da wando na shadda ruwan madara, suma suna cikin sababbin kayanshi da bai tab'a sakawa ba, saida ya gabatar da sallar zuhr yayi addu'o'in shi sannan ya k'arasa shafa mai ya taje sumar kanshi data d'an taru, yabi jikin shi da mayen turaren shi sannan ya fara takawa gurin y'an maganar shi k'afar shi ba takalmi.
Su uku ya tarar a parlon ragowar sunyi nasu guri tun farkawar shi, sai ya rage saura Ahmad! Nazeer! Da Muhammad.
A kujerar da take kusa da inda suke ya zauna yana kallon su. Ahmad yace, "ka tashi kenan?".
Hannayen shi ya mik'ar yace, "ehh ya kuke ya k'ok'arin ku? Nagode sosai Allah ya bar zumunci".
"Ah haba meye wani abun godiya da fatar baki, ai Man rama mana kawai zakayi in auren mu ya tashi, ga Ahmad nan dama shine angon gobe".
Murmushi yayi ba tare daya sake ce dasu komai ba.
Sunci gaba da hirar su kamar gaske kafun ya fara jin wata muguwar yunwa tana taso mishi da shirin yiwa rayuwarshi illa, har ya d'auki wayarshi sai ya kalli Ahmad yace, "Man akwai wani abu a gidan kuwa?".
Ahmad yace, "au ni zaka tambaya ma?". Khaleefa yana laluben cikin fridge d'in parlon yace, "toh wa zan tambaya?".
"Ah matar ka mana, ko ka manta yanzu kai d'in me iyali ne?". Ahmad ya fad'a mishi yana kallon shi.
Khaleefa da baya ya dawo ya zauna don shi shaf ya manta ashe wai yana da wata mata ma, kuma ko yanzu daya tuna ba wani amfani tunawar zatayi mishi ba, tunda shi dai yanzu ko karen hauka ne ya cije shi bai isa ya tunkareta da maganar wani abincin shiba tunda baya daga cikin k'a'idojin auren su.
Ganin ya tafi wani tunanin sai nazeer yace, "Ahmad ina ganin fa mutumin ya manta yayi aure ga dukkan alamu, kasan sabo da rayuwar gwauran taka".
Muhammad yace, "tabbas naga alamun haka kam nima".
Shi dai khaleefa bai ce dasu komai ba. Ahmad hadda gyaran murya kafun yace, "taya kuke tunanin khaleefa zai tuna yayi aure bayan ya kwana a hospital cikin sanyi da sauro tsakiyar tashin hankali".
Aikuwa suka fara mishi dariyar shak'iyanci suna zolayarshi. A wannan karon shima sai daya murmusa yasa hannu yana shafo sumar kanshi, yana ganin basu san dawar garin bane shiyasa suke kallon shi cikakken ango.
Ganin inya biye ta tasu yunwa zata kaishi k'asa bai shirya ba sai ya mik'e ya nufi kitchen.
Kitchen d'in tas tas dashi babu ko d'igon datti, mama haleema da sauran ma'aikatan gidan suna ta hada hadar had'a abincin da zasu taryi auntie da mutanen gidan.
Suna ganin shi suka fara russunawa suna gaishe shi, ya amsa kamar koda yaushe da fuska kadaran kadahan.
Gefe guda ya tsaya ya cewa mama haleema, "sannu da aiki". Mama haleema ta juyo tace, "yauwa sannu khaleefa ya gajiyarka?".
Yace, "ta huce, nace ko zan samu ruwan tea me zafi da wani abinci sauk'ak'k'e".
D'an Jim tayi kafun tace, "za'a iya samun tea amma abincin ku yana b'angaren amarya cikin sitting room naga kana da bak'i".
D'an jim yayi kafun ya sake cewa, "don Allah ko zaki iya sawa a dawo mana da abincin parlon mu na sama?".
Mama haleema tace, "ai tana da bak'i y'an uwanta sun kawo kayan gara, yana da kyau ma kaje ku gaisa dasu tunda auntien bata nan".
Har ga Allah shi baya son wannan yawan gaishe gaishen da shige shigen mutanen da baka sani ba, toh amma ya ya iya tunda ya kama shi.
Juyawa yayi ya futa kitchen d'in.
Su Ahmad ya tarar inda ya barsu, Ahmad yana ganin shi ya tari numfashin shi da cewa, "yauwa yanzu mukayi waya da doctor namu yana maka congrats, ga sauran mate d'in muma duk suna taya ka murna, ya kamata ka kunna wayar ka naba wasu new no ka nasan zasu kira ka.....".
Khaleefa baisan lokacin daya zauna bai shirya ba, ya dafe kanshi da duka hannuwan shi yana nazarin wannan uban aiki da Ahmad yake jik'a mishi.
Mik'ewa yayi ya d'auki wayarshi ya dube su, "am Ina ganin zamu k'arasa can zan gaisa da y'an uwan raihana ance sunzo, sannan abincin muma yana can".
Duk mik'ewa sukayi suna mamakin abinda ya sosa ranshi har yanayin shi yana sauyawa.
Kusan tare suka futo, sai dai har sun fara tafiya khaleefa ya jawo rigar Ahmad baya yace, "Wai wa yace maka ka fad'awa kowa da kowa???? Kai kana d'aukar auren nan kamar na gaske ne ko?....". Da mamaki Ahmad ya tsaya yana kallon shi yace, "toh da na wasan yara ne". Bai tanka shiba yayi gaba ya barshi a nan, shi kam murmushi yayi yabi bayan shi.
******A dai dai lokacin Raihana tana zaune kusa da auntie hajara tana sauraron bayanin sak'on da ummie ta aiko mata tana rik'e da hannun shukura . Ko a yanzu sanye take da k'aton hijabin sallarta daya saukar mata har k'asa.
A waya ta rubuta abinda ba zata iya rik'ewa ba gudun samun matsala, duk da tana ji a ranta ba iya shan wad'annan tarin itacen zatayi ba.
Su uku ne suka rage a cikin wad'an da suka kawo gara da mahaifinta yasa ayi, ragowar sun tafi sai Auntie Sarah, Auntie hajara da Auntie hapsert k'arama.
Suma sun gama komai har y'an gyare gyaren da zasuyi mata a gidan, sun maida mayafan su suna shirin tafiya raihana ta tsaida su da sake tambayar yadda za'a had'a maganin da ummie tasa a kawo matan, su suka bata shawarar tayi saving a waya tunda ta kasa haddacewa.
Ta gama tattare ledar magungunan kenan khaleefa ya shigo parlon da sallama, cak raihana ta tsaya daga shirin mik'ewa tsayen da take, har ya k'araso tsakiyar parlon bata iya d'aga idonta ba bare ta kalle shi.
Daga gefe ya durk'usa ya fara gaishe su, suka amsa da fara'a akan fuskar su. Bai mik'e daga tsugunnen ba har suka tashi zasu tafi, yarinyar Auntie hapsert k'arama me suna shukura ta tafi gurin raihana tana yi mata Byeee, da yake koyon magana take bata iya bye bye d'in ba sai bibibi, saita tafi kamar gaske saita sake dawowa ta d'agawa raihana hannu ta sake cewa, "bibibi". So take raihanan ta tayata ita kuma wanzuwar khaleefa a gurin ya hanata kwakkwaran motsi bare ta taya ta kamar yadda ta sabar mata.
Tun uwar tana jiranta har ta gaji ta futa zuwa wajen parlon ta tsaya ta a can saboda nauyin khaleefa da take ji. Khaleefa kam yarinyar burge shi tayi, yanayin yadda take tafiyar taje ta dawo tace, "atti bibibi" yake burge shi, hakan yaja hankalin khaleefa har yake binta da kallo yana murmushi, a lokacin ta koma tana jawo raihana kan tazo su tafi tana kiran sunanta. Ganin tana shirin mata kuka saita ajiye ledar hannunta ta d'auke ta, khaleefa ya bisu da kallo ita da yarinyar har ta fuce, sai lokacin ya mik'e yana murmushi kan fuskarshi, yarinyar ta shiga ranshi lokaci d'aya da gwarrarriyar hausarta. Shi dai yana son yara ko don basu rayu tare da yara a gidan suba.
"Masha Allah raihana amma mijin ki mai kyau dashi d'an gayu, kamar Ayman wallahi muryar suce kad'ai ta banbanta sai yanayin maganar su. Sai dai kamar ba raihana dana sani me aji ba daga ganin shi duk kika wani diririce zaki bada kanki a gaban shi....". Auntie hapsert ce keyi mata wannan maganar k'asa k'asa tana karb'ar shukura a hannunta, ita dai murmushi kawai tayi, suka k'arasa sallama tace su jirata minti biyu tana zuwa, da hanzari ta tura k'ofar parlon ta shiga.
Bata ganshi a parlon ba, hakan yasa ta d'auki ledarta zata nufi bedroom d'inta da sauri ko zata samu abinda zata bawa baby shukura kafun su tafi.
"Yauwa nace ko akwai kud'i a hannun ki?" Tambayar data shiga dodon kunnenta kenan har ta assasa mata tsayawa tana kallon direction d'in da maganar ta futo. Yana tsaye daga wani sashe na d'akin, "idan akwai ki aramun 7k zan mayar miki dasu".
Cikin kud'in da suka kawo mata ta zari 7k d'in ta tafi zata kai mishi maganar shi ta sake katse ta, "ki basu suyi kud'in transport".
Saita juya da sauri ba tare da tace mishi komai ba, a lokacin har sun gaji da tsaiwa sun kusa futa daga harabar gidan ta k'arasa da hanzarinta ta d'anka kud'in a hannun shukura tace ku hau napep, da mamaki suka tsaya suna kallonta, "raihana ba zamu karb'i ko kwandalar kiba....". Auntie hajara ta fad'a. D'aga hannayenta tayi tace, "Auntie bani na baku ba, cewa yayi kuyi kud'in mota".
Jin haka sai suka yi godiya suka ce ta musu godiya a gurin shi.
Tana d'agawa shukura hannu har suka futa daga gidan.
Koda ta dawo bata same shi a parlon ba bare ta mishi godiya, kuma bata bi ba'asin komai ba ta d'auki ledarta tayi cikin d'akin gadonta.
A sitting room ya samu su Muhammad da suka shiga ta k'ofar baya, shiya musu saving abincin suka fara ci, suna hira suna zolayarshi har suka gama.
Saida aka kira sallar la'asar sannan suka futa don sauke farali, shi kuma yayi amfani da wannan damar ya kira auntie yaji ko lafiya suka dad'e haka basu dawo ba......
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page forty4️⃣0️⃣
Suna tare har su Auntie suka dawo su hud'u, Auntie! Doctor seera! Iya sai Ayman.
A parlon auntien aka saka mishi pillow ya kwanta saboda bawai jikin shi yayi kwari bane har lokacin.
Duk sunzo sun musu sannu da zuwa, tare da yiwa Ayman fatan samun lafiya dawwamammiya.
Basu bar gidan ba sai after magrib, ya rage daga khaleefa sai Ahmad da yake son shima ya tafi nan da kwana uku ko biyu in komai ya daidaita.
Iya ma saida malam ya kawowa Ayman tofin da yayi mishi, sannan suka tashi zasu tafi, sai a lokacin iya take tambayar khaleefa, "Wai Ina raihanatun ne magaji! Tunda nazo kai kad'ai nake gani ban ganta ba ita, ko kullenta za'ayi mana".
Kafun ya bada amsa Auntie ta riga shi da cewa, "taci abinci ma kuwa? Baiwar Allah d'azu da safe ma saida ta bini taga jikin Ayman".
Iya tace, "ai raihana ba dai kirki ba, naji dad'i da kika samu suruka ta gari irinta, zaku zauna lafiya da ita kwarai".
Auntie tana murmushi tace, "ai daga dukkan alamu, ni ko da can nasan yarinyar ta samu tarbiyyah, fatana d'aya Allah yasa khaleefa ya rik'e ta bisa gaskiya da Amana".
Khaleefa da yake sauraron duk maganganun su baice dasu kanzil ba, hasalima yi yayi kamar bai tab'a sanin wadda suke magana a kanta ba, Ayman kam sake rintse idon shi yayi gashi ba damar ya hana kunnuwan shi sauraron maganar su.
Malam yayi addu'o'i sosai, kusan abinda su auntie suka fad'a shima shiya d'ora, kyawawan halayen raihana suka dinga kwad'aita mishi had'e da shawarar ya kula da ita yadda ya kamata.
"Insha Allah raihana ba zatayi kuka dani akan komai ba". Kacal abinda ya fad'a ya maida kanshi, malam yace, "Toh Allah yasa".
Tana daga cikin d'akinta gefenta gado tana amsa wayoyi daban daban daga y'an uwa da abokan arzik'i, wanda basu samu damar zuwa ba suke ta mata Allah sanya alkhairy, wasu kuma ta text massage.
Bayan ta gama dasu, saita fara kiran wanda suka zo tana musu ban gajiya da godiya had'e da addu'ar Allah ya bata ikon rama musu tarin alkhairan da sukayi mata.
Suma sunata godiyar kayan cosmetics da ta bayar aka kai musu.
Ba ita ta samu kanta ba sai bayan sallar magrib, ta d'aura alwala tayi sallarta.
A hankali ta tura k'ofar parlon ta shiga bakinta d'auke da sallama, daga Auntie sai mama haleema a parlon da Ayman da yake zaune kusa da ita yana sipping tea.
"A'a raihanatu". Cewar Auntie. Da sauri Ayman ya had'iye shayin bakin shi ya ajiye sauran.
K'arasa shiga tayi ta zauna daga k'asan parlon ta fara gaishe su, duk suka amsa Auntie har tana tambayar ya gajiyarta.
Murmushi tayi bisa al'adarta a ranta tana mamakin yadda Auntie bata gajiya da tambayarta gajiya duk k'ank'antar aikin da tayi.
Mama haleema ce ta kawo mata tray me d'auke da k'ananun cup da tea flask akai.
Kad'an tasha shayin bayan ta zuba mata ta ajiye saboda rashin sabo.
Sai hira