Showing 18001 words to 21000 words out of 288773 words
Chapter 7 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
kikayi ko kuma in ture fadar taki in aza ummaaa".
"Kyaci gidan ku ja'ira zan had'u dake ne". Iya ta fad'a tana wullo mata dak'uwa da hannu, ita kuma ta huce gaba tana dariya.
Ummie tana zaune kan k'aramar kujera tana d'auraye ragowar kwanukan dasu jidderh suka ci abinci, gidan shiru duk sun tafi islamiyyah.
"A'a kece da yammacin nan kuma". Ta fad'a da mamaki tana kallon raihana.
"Eh ummie sannu da gida bari na k'arasa miki aikin" kawai saita ajiye kayanta a gefe ta nad'e hannun riga da gyale ko kafun ummie tace wani abu har ta tsunbula hannunta cikin ruwan d'auraya.
"Ki barshi kawai aina kusan gamawa ma, amma raihana wannan wane irin zuwa ne ba sanarwa? Kina ganin abbanku ya dawo ya ganki bazai yi fad'a ba?".
Raihana tace, "A'a ummie ki barshi kawai na k'arasa ni bazan iya zama Ina kallon ki kina aiki ba, Abba kuma na fad'a mishi a waya kafun na taho". Dole ba don ummie taso ba ta kyaleta suka k'arasa aikin tare, raihanatu ta sharce gurin sannan Suka k'arasa cikin parlour. Kamar yadda na fad'a a baya Mahaifin raihana ba mai kud'i bane amma yana da rufin asiri, sannan ya tsare musu komai kama daga abincin da zasu ci, har zuwa kan karatun su da suttura data zame musu kana.
(Ban gama fasalta gidan suba d'azu, bayan parlor da d'akuna akwai wani babban d'aki a gefe na abban su sai sitting room, da harabar da yake ajiye motar shi da machin)
Ruwa ta d'auko a fridge tana sha ummie tace mata,
"Sai kika ji Salma ta haihu"
Ajiye gorar ruwan tayi tace, "eh wallahi kuma fa jiya da rana ma Saida mukayi waya da ita, ashe ita a lokacin ma bata da lafiya tak'i fad'a mun".
Ummie tace, "Ai kinsan halinta, balle ga abinda ya faru cikin satin ni kaina fa bata fad'a mun ba ita da mijin ta suka tafi asibiti saida ta haihu ya kirani yake fad'a mun, nace aiba ni ya kamata ya kira ba sai su nemi uwarsu hajara".
(Hajara yayar ummie ce, itace ta biyu a gidan su daga babbar yarsu Aisha sai ita sannan ummie da k'anin ta Isma'eel da yuseep sannan saratu da autar su hapsat, duk ummansu ta aurar dasu sai jikoki da suke lek'o ta, marayu ne mahaifin su ya rasu tun da dad'ewa suma.)
"Ummie kina nufin baki je kinga baby ba har yanzu?"
"Toh yaushe ma ta haihun da zaki ce wani har yanzu banje ba, kuma yanzu ke tunda kinzo ai sai kije a madadina".
Dariya raihana tayi ganin ummie tana yi mata kallon wata mara hankali tace, "Allah ummie nasan ma ba zuwa bakiyi ba".
"Kinga mu ajiye wannan maganar a gefe, sai kika ji gidansu ilyas sun karb'i kud'in auren d'an su suma ko?".
Take yanayin ta ya sauya duk data shanye kaso talatin a ciki, "eh Abba ma ya kirani washe garin ranar da mukayi waya dake".
"Raihana Ina fatan baki sa wani abu a ranki ba, dama tunda akayi haka nake ta damuwa nasan halinki, zaki iya zama kiyita wannan kukan na maseefa ki k'i ci ki k'i sha, duk ki damu kanki". Sunkuyar da kanta k'asa tayi tace, "banyi kukan ba ummie, ni komai ya huce ma a gurina har abada don na dad'e da deleting duka no's d'inshi a wayata ma". Ummie tana lura da yanayinta tace,
"Naji dad'i da kika fahimci komai daughter dama kowanne d'an Adam da irin jarrabawar da Allah yake mishi, idan kayi hak'uri sai ya saka maka da abinda yafi alkhairy a rayuwa, Ina fatan wannan ya zamo na k'arshe a gareki, kullum Ina yi miki addu'a insha Allah ba zaki wulak'anta ba a rayuwa".
Had'iye abunda ya tokare k'ahon zuciyarta tayi, tace, "insha Allah ummie ko bana kusa dake idan na tuna irin wad'annan kalaman da suke futowa daga bakin ki sai Inji kwarin gwiwa da sanyi a raina"
Ummie tace, "Masha Allah fatan Allah yayi mana jagora, ki shiga kitchen ki zuba abinci kici in babanku ya dawo nasan zaki tafi gidan masu jego ko". Raihana tace, "Toh ummie amma ni ba yau zanje bama sai gobe"
"Toh Allah ya kaimu".
Raihana mik'ewa tayi taje ta zuba abincin ta dawo parlor, tana cin abinci suna hira da ummie har ta kammala, a haka su jidderh suka taso school, aikuwa da gudun su suka rungume ta suna mata oyoyo. Tsarabar chocolate da Ayman baya rabo da kai mata tayo musu, aikuwa sukaita tsallen murna suna godiya.
Da yamma abbansu ya taso kasuwa, shima yaji dad'in ganinta sosai, sai da suka zauna cin abinci abban yake tambayarta yanzun data taho babu matsala?, ta fad'a mishi babu matsala attendance ne kuma akwai wata k'awarta zatayi mata.
A daren ranar take shaidawa Ayman tana gari fa saboda Salma ta haihu, yace eh yaji a gurin iya, zai zo su gaisa kafun ya tafi office gobe.
***********
_Da asuba_
Raihana tun data yi sallah bata koma bacci ba saida suka tsabtace gidan tsab ita da khausar suna aikin suna hira har suka kammala. Wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa d'inkin kuwa ya zauna das a jikinta, wayarta da take kashe ta kunna bayan ta duba lokaci, 7:00 am yaran gidan har lokacin bacci sukeyi, khausar tasa ta tashe su su shirya tafiya school. Ita kuma ta zauna tana yin abinda ta jima batayi ba wato kallo. Jinta take free cike da farin ciki da annashuwa, lallai tayi kewar gida don rayuwa a gida babu abinda ya kaita dad'i, tana nan zaune tana lazimi at the same time idonta a kan tivi wayarta tayi ring, as she expect Ayman ne, da sallama ta d'aga bayan ta kai volume d'in tivin k'arshe, "Ina fatan kin tashi lafiya ya kwanan babyn mu"
"Lafiya qalou nake fatan kaima".
Ehh to ni kaina zuwa yanzu ban sani ba amma gani k'ofar gidan ku Ina sauri zan huce aikine na kusa late".
"Okay to minti biyu". Ajiye wayar tayi ta kasa kunne ko zataji motsin ummie, fahimtar da tayi bata tashi ba sai kawai ta fad'awa khausar zata futa su gaisa da Ayman koda ummie zata futo yanzu.
Yana tsaye a k'ofar gidan jingine da motarshi ya hard'e duka hannunshi a k'irji.
Tana futowa Abba abubakar shima yana futowa.
Dam gaban raihana ya fad'i.
_Comment and follow_
24/03/23, 1:59 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyeart lerwerl*
Page six 6️⃣
Raihanatu bata san dalili ba amma duk lokacin da zataga d'aya daga iyalan gidan ko masu gidan takan tsinci kanta cikin tashin hankali mara misali. Cikin ladab ta durk'usa k'asa tana gaishe shi, da sakakkiyar fuska ya amsa mata har yana tambayarta an samu hutu kenan, dama shi mutum ne simple kamar abbansu, matar shi da y'ay'an shi sune matsala, sai Inna da sauran yaran kishiyarta masu shiga shara ba shanu da kuma zuciyar hassada, ziyada ma bata shiga sam tana tsaka tsakiya haka yaranta, batace tana tare dasu ba kuma bata ce tana tare da hajiya Inna ba. Shima Ayman har k'asa ya durk'usa yana gaishe shi kamar yadda Raihana tayi.
Kasancewar Ayman ba b'oyayyen shi bane sun gaisa har yana tambayar shi mahaifiyar shi mutuniyar kirki da akayi zaman mutumci da Amana.
Bayan tafiyar shi, matsawa raihana tayi kusa dashi tana sakin mishi tattausan murmushi, "Ina kwana ya Ayman". Sai ya had'e rai
"Da ban kwana zaki ganni, aini fushi nake da kema in baki sani ba....."
"Fushi kuma Yaya Ayman? Toh me nayi kuma?". Sake had'e fuska yayi yace, "Ba sau d'aya ba na fad'a miki times without no cewa ki dena kamo hanyar garin nan cikin motar haya, amma kinsa k'afa kin shure saboda Sam baki d'auke ni yadda na d'auke kiba, meyasa raihana?"
"K'asa tayi da kanta tana mamakin wannan k'arfin hali na Ayman, for what reason zata dame shi watak'ila ma yana wajen aiki lokacin da zata taho amma wai ta kira shi don neman magana da rigima, toh aikin zai baro yazo d'aukarta "ka gafarceni yaa Ayman insha Allah Zan kiyaye". Raihana ta fad'a carmly.
Ayman yace, "Gud Allah yasa! Yanzu Yaushe zaki je ki gano mana babyn?".
"Anjima kad'an" ta bashi amsa.
"Kwana nawa zakiyi ki koma scul".
"Umm nida sai bayan suna zan tafi ma".
Zaro ido Ayman yayi yace, "karatun naki fa?, haba ina laifin idan kinga baby yau gobe da sassafe na mayar dake, in yaso ranar suna da safe again nayi alk'awari zanje na taho dake na mayar dake washe garin suna hakan ba yafi ba".
B'ata face tayi tana juya yatsun hannunta, "kina son wasa da karatun ki raihanatu gashi kina mafi hadarin watanni, yanzu every slice mistake zasu iya jangwalar abinda zasu lalata miki duk wancen shekarun da kikayi", ganin tana sake had'e rai sai yace, "Amma fa kiyi hak'uri idan da damuwa a magana ta kiyi yadda kike so".
Juyawa yayi ya d'auko wata leda a back seat na motarshi ya mik'a mata, "Auntie tace na kawo miki tun waccen ranar mantawa nayi". K'in karb'a tayi tana kallon shi tace "I'm sorry....".
"Shhh! Is okay" Ya katse mata hanzari. Ganin ba zata karb'i ledar ba sai kawai ya ajiye mata kan k'afarta ya shige mota abinshi ya tafi.
Jiki a sanyaye raihana ta d'au ledar ta shige gida, duk yaran gidan sun tashi har sun shirya cikin school uniform sai hayaniya suke yi kamar za'ayi dambe.
Zama tayi k'asan carpet ta dubi khausar da take ta aikin ganin ta raba rigimar da ake yi tsakanin muhibba da al'ameen, "Ashe har yanzu yarannan suna wannan rigimar ta k'a'ida?".
Y'ar dariya khausar tayi tace, "ai Auntie raihana Ina ganin sai abinda yayi gaba ma, yanzu ma kinga wai muhibba ce bata wanke socks d'inta ba ta d'auki na al'ameen tasa wai itace tata, shine ake ta rigima, ita muhibba tasan ba nata bane amma don neman rigima taki bayarwa, shi kuma ya kafe saita bashi saboda bashi da wanda zaisa ya tafi school kuma an yaje ba socks d'in duka za'ayi mishi".
"Wannan shine abinda ya had'a fad'an?". Ta tambaye su su duka ukun.
Matsowa muhibba tayi zata fara mata zayyana ta dakatar da ita. D'akin su ta shiga ta d'auko jakarta akwai farar safa sabuwa dal ta mik'awa al'ameen, "bar mata wancen kasa wannan kaji k'anina".
Hadda dariyar shi ya karb'a yasa a k'afar yace, "wannan ma tafi wadda ta d'auke kyau Auntie Raihana".
Raihana tace, "wannan shi ake kira da hak'uri mai cimma rabo". Khausar tace, "aikuwa".
Kicin kicin muhibba tayi ko shayin ma tak'i sha sai faman hararar al'ameen take a sace har suka fuce.
Gidan yayi tsit daga ita sai khausar da ta d'an jima da kammala waec d'inta tun satittikan da suka huce, hira sukeyi jifa jifa har Allah yasa ummie ta futo.
Suka durk'usa suna gaisheta, ta amsa musu cikin so da kulawa. Kusan a tare suka nufi d'akin abbansu shima suka gaishe shi.
Sun sake tab'a hira yanzun ma da ummie akan karatun ta da yadda komai yake tafiyar mata.
Bayan abbansu ya futa, sai da hantsi ya d'aga sannan ta d'auki ATM card da hand bag wayar ta a ciki ta yima ummie da khausar sallama ta tafi gurin y'ar uwarta.
A POS ta tsaya ta ciri y'an kud'ad'en ta da take saving a duk lokacin da abbanta ya turo mata da kud'in amfani taga bata buk'atar komai, da wanda Ayman ya d'orawa kanshi duk watan duniya wai ko wani abu zai taso mata ba sai ta fad'awa Abba ba.
wani k'aramin store na kayan babie tayi burki, ta siyama baby tsala tsalan riguna kala biyu da saitin mayukan jarirai ta had'a da overall farare tass, har zata fuce wani k'aramin Teddy pink ya d'auki hankalinta, sai ta koma da baya tana duba kud'in jikinshi.
Shigowar shi shagon kenan yayi tozali da ita tana duba jikin teddy, lokaci d'aya ta d'auki hankalin shi har yaji bazai iya hak'uri ya rasa wannan tsaleliyar budurwa ba.
"Amincin Allah ya tabbata gareki y'an mata". Ya fad'a bayan ya k'arasa inda take tsaye
Saida gaban ta ya fad'i taja tsaki can k'asan ranta, shiyasa ta tsani futa waje sam saboda maza da sun ganta basa iya kauda kai sai sun kula ta ko lura da d'aurewar fuskarta basa yi, "kiyi hak'uri idan na shiga rayuwarki amma don Allah ki bani no ki sai muyi magana".
Sake d'auke kanta tayi tabar siyan teddyn ma tayi hanyar futa, bin bayanta yayi da sassarfa yana fad'in, "kinga! Am babie pleeze just one mint".
Napep take k'ok'arin tarewa amma ya hana sai korar masu napep d'in yake, dole at last ta fusata har tayi mishi magana, "don Allah malam ka kama kanka".
"Kamun kan ne ai bazai yiwu ba y'an Mata, na baro kan tun a cikin store inda na fara ganin ki".
Duk yadda take cikin fushi saida maganar shi ta bata dariya, amma dai ta gintse gudun kada ta bada kanta yaga lagonta.
"Yanzu dai no ki kad'ai nake son ki bani y'an mata, ko har yanzu baki aminta dani ba saina tsugunna nayi magiya a gabanki?".
"Bani wayar in saka maka". Raihanatu ta fad'a ganin yana Shirin yin abinda bakin shi ya furta.
Da hanzari ya bata phone in, ko a hannu data rik'e wayar tasan waya ce mai tsadar gaske, ita dai ta samu ta zuba mishi no ta mik'a mishi, k'in karb'a yayi yace, "kira muji".
Da b'acin rai tace, "kana ganin zan saka maka wrong ne?".
Nifa bance ba amma dai ki kira kalas na, danna kiran tayi ba tare da bin la'akari da wanne sim ba, sai kuwa ga wayar ta tana ring a jaka. Ya sauke ajiyar zuciya gami da yin hamdala ga Allah.
"Meye sunan gimbiyar?". Ya tambayeta bayan ya karb'i wayar, "duk abinda kasa".
"Woow an bani zab'i kenan, godiya mai yawa yanzu sauranki abu d'aya, kizo muje na sauke ki a gida don Allah"
Wai anya mutumin nan yana da hankali kuwa? Ta tambayi kanta a zuciyarta.
"Princess can we?". A zafafe tace, "what?".
Kama kunnen shi yayi yace, "I'm sorry I mean let's go".
Fuuu ta hucesa don tana ganin laifinta nema data tsaya magana dashi har wannan lokacin, shi kuma tunda yaga guri ba dole yayi yadda yaso ba.
K'aramin gidane sama da k'asa mai d'auke da ginin safe content matattakalar ta sauko ta cikin parlour. Koda tayi knocking mijin ne yazo da kanshi ya bud'e, yana ganinta ya bata hanya ta huce yana mata sannu da zuwa, ta amsa mishi da yauwa.
A parlon k'asa ta zauna ta ajiye ledar hannunta tana kallon komai na gidan tsaf tsaf, shima shigowa yayi bayan ya kulle k'ofar, nan suka gaisa har tayi mishi barka.
Shiya turo mata Salma da take parlon shi suna breakfast a lokacin, da hanzarinta kuwa ta sauko tana kwala kiran "Auntiena, shiyasa nake ji dake saboda nasan duk kinfi sona"
"Ki dai tafi a hankali wallahi inba so kike ki b'arowa kanki wani sabon ciwon ba, kiyi double double".
Rungume ta tayi ko damuwa da maganar y'ar uwar batayi ba, "nayi kewarki auntie raihana".
"Nima nayi kewarki sosai salmaty".
Sake ta tayi tana tambayar, "Ina babyn nawa ma kika wani zo kika mak'ale ni god'ai god'ai dake kamar bake kika haihu shekaran jiya girma ya kama ba".
"Tana gurin ummaa". Ta bata amsa, "toh Ina ummaan". Tana ciki watak'ila ma bacci tayi da kin ganta ta futo, huce Salma tayi ta shiga neman inda umman take, a d'aki na biyu kuwa ta sameta kwance kan katifa tana bacci yarinyar a gefenta, raihana d'auko babyn tayi kawai ta futo. Nan suka baje a parlour Salma na faman bata labarin irin wahalar da tasha wai saura k'iris ta mutu, yayinda ita take sauraronta cike da tausayawa ta kasa ajiye yarinyar sai juyata kawai take cike da so da k'auna.
Lokaci d'aya taji son yarinyar ya shiga zuciyarta har tana jin kamar karta bawa uwarta ita.
Kayan data siyowa babie ta mik'awa mamanta, tsabar mamakinta Salma sake baki tayi tana kallonta, "kin tuna mun jiya fa Yaya Ayman yazo yayi ma yuseep barka da dare baki ga uwar hidimar da yayi ba".
Raihana cike da mamaki tace, "wane Ayman kuma?".
"Ayman dai naki wanda kika sani y'an biyun Auntie