Showing 84001 words to 87000 words out of 288773 words
Chapter 29 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
soyayyarta a k'ok'on ranshi har yana jin idan bai same taba bazai sake rayuwa cikin farin ciki ba har abada......
Ayman sake matsawa kusa dashi yayi ya had'a hannuwa biyu yana rok'on shi kamar ya zubar mishi da hawaye, "khaleefa ba don niba, ba don na isa ba, ka taimake ni don Albarkacin soyayyar tagwaitaka da take zukatan mu da mak'otakar zaman wata tara a ciki guri guda ka amince da maganar auren mu ko nima na samu Nur cikar burina, kada ka zamo silar da zan rasa Nur saboda Ina sonta da gaskiya kamar yadda itama take sona, sannan ka soke maganar komawarka Germany don girman Allah......". Hannuwan shi biyu yasa ya saukewa Ayman hannun shi k'asa daga alamun rok'on shi da yayi, "ka daina had'a ni da girman Allah Ayman, ko yanzu zaka iya yin auren ka ba dole sai tare dani ba, maganar aikina kuwa bakin Alk'alami dad'e da bushewa..... amincewar auntie kawai nake nema....idan har bata amince ba na hak'ura zanyi aiki a k'asa ta, amma fa idan ta amince ko second bazan k'ara a Nigeria ba zan b'acewa ganinka".
Kallon shi kawai Ayman yake kafun ya mik'e don ya futa daga d'akin, don baiga amfanin ci gaba da magana dashi ba, har yakai k'ofa ya dakata ba tare daya juyo ba yace, "auntie tana son magana dakai, tace ka same ta a parlonta".
Bai amsa ba hasalima kamar bai jishi ba ya mik'e jiki a sanyaye yabi bayan Ayman d'in, shi a nan parlour ya kwanta, shi kuma khaleefa ya tafi don amsa kiran auntie.
Lokacin daya shiga parlon babu kowa sai shaheeda zaune saman sofa tana rubuce rubucen ta. Sanye take da doguwar riga y'ar kanti sai gyalen rigar data d'aura a kanta, fuskarta ba hayaniyar kwalliya daga powder sai pink jan baki. Zama yayi daga kujerar da take nesa da inda take, tunda ya kalleta da farko ya fahimci ba auntie bace bai sake duban inda take ba koda wasa, ita kuwa shaheeda da kyar ta iya d'auke kanta ga barin kallon shi, ba don kar tayi k'arya ba da sai tace tun ranar da suka karya a dinning da safe bata sake ganin shiba sai yau. Cikin basarwa da d'auke kai ta gaishe shi, ya amsa ko kallon inda take baiyi ba.
Ya d'auki adadin wasu mintuna kafun auntie ta futo rik'e da wayarta me shegen tsada da kyau, waya take yi, saita samu guri daga gefen inda yake ta zauna tana kallon wayar hannun shi, yana daga abinda yake burge ta da khaleefa, bai fiya damuwa da abubuwa irin na matasan zamani ba, wayar nan ta hannun shi tare ta siya musu da Ayman, bayanta Ayman ya lalata wayoyi hud'u ko biyar ma, amma shi har yanzu tana nan rik'e a hannun shi, ga k'aramin misali kud'in da take tura mishi duk k'arshen wata, baya almubazzarantar dasu a banza, sai dai in siyayyar abu na dole ta taso mishi yayi amfani dasu, kyale kyale ko kyallin duniya basa d'aukar hankalin shi kuma basu dame shiba, sannan bashi da zarmewa a son abun duniya kwata kwata, shiyasa har gobe ta kasa fahimtar abinda ya d'auki hankalin shi da aiki a k'asar Germany, tabbas tasan ba don abinda zasu biya shi ya amsa tayin wannan aikin ba.... To don meye??? Wasu lokutan idan ta kalli rayuwar khaleefa da kyau tsarin yadda yake tafi da rayuwar shi Soo simple sai taga kamar tana kallon rayuwar Suraj mahaifin sune. Haka yake mutum mai aiki da hujja amma me shegen taurin kai da zurfin ciki. Jin ana faman kira mata hello hello a kunne sai ta dawo daga tunaninta ta tuna ashe fa waya take,,, "I will call you later" ta fad'a tare da datse kiran, "Ayman ya fad'a maka Ina son magana da kai?". Ta tambayi khaleefa, "eh ya fad'a mun" ya bata amsa shima, shaheeda da take ta harkar gabanta ta kalla tace, "shaheeda ko zaki bani guri nayi magana da yayanki". Ba musu tace toh ta had'a tarkacen littafanta ta shige d'aki.
Sake fuskantar shi tayi da kyau kafun taci gaba da maganarta, "khaleefa na kira kane saboda naji meye takaimaman matsalarka, kada ka fara yimun k'arya kasan ba dabi'ar ka bace kana yi zan gane gaskiya daga nan bazan k'ara yarda da duk abinda zaka fad'a mun daga baya ba, komai muhimmancin shi kuwa har abada... Sannan zan fasa abinda nayi niyyar yi maka". Shiru khaleefa yayi kanshi a k'asa yana jinjina girman matsalar shi da yadda zata fahimci gaskiyar koya fad'a, sanin bazai samu abinda yake so daga gare taba yasa ya gwammace yin shiru da bata amsar tambayarta.
Ganin sun d'auki lokaci bashi da niyyar bud'e baki bare ya furta wani abu sai ta fahimci ba zai bata amsa ba kenan, sai ta d'auki tambaya ta biyu, "tunda baka da amsar wannan, ya batun maganar da kayiwa mamanka sameera jiya, shin gaskiya ne abinda kuka shirya aiwatarwa kenan kaida Ahmad?". Sai a yanzu yaji zai iya magana, "Eh auntie duk abinda na fad'a mata babu k'arya a ciki ko zolaya, toh taya ma zan zolayeta tana matsayin uwa a gurina, a cikin wad'an da mukayi course d'in nan dasu, an zab'e mu mu bakwai zamuyi aiki k'ark'ashin wani team don mu k'ara samun kwarewa, kuma sunyi alk'awarin zasu yi mana kyakkyawan biya, bance zanyi aiki abadan dasu ba, amma akwai abinda nake timing dana samu zan baro k'asar na dawo gida Nigeria a amfana da abinda na karanta, sai maganar aure da mammie tayi jiya, shima bance bazan yiba don mutum baya cika cikakken mutum saida iyali, kuma ni tun watanni shida baya Ina da zab'in matar da nake Soo in aura, shima akwai abinda nake so ya kammala bada jimawa ba zan gabatar miki da ita".
Duk maganar da yake auntie shiru tayi tana sauraron shi har ya kai aya, Amma fa tayi shock da taji cewar yana da matar da yake so ya aura, babu zato taji wannan maganar, koda yake dama amma dama itama bata shirya yi mishi dole akan ya karb'i shaheeda ba sai dai zata so ya auri matar da aka santa a k'asan asalinta, ba wai ya d'auko mata daga wata duniyar ba, su basu san halinta da d'abi'un ta ba itama ba tasan nasu ba, ya kawo musu ita cikin su ta zame musu k'arfen k'afa. Astagfirullah ta fad'a kuma da sauri a ranta tana addu'an Allah ya nisanta su daga irin wannan matar.
_shin kune biye da littattafan in-identical twins? Albishir gare ku masoyan mu, litattafan mu sunzo muku da wani sabon salon soyayyah da sadaukarwa ba irin wanda kuka sani a wannan duniyar ba, ku dai kuci gaba da kasancewa da 👉🏻 *Doctor Ferhyeez m usmern DARAJAR HAK'URI* & *merhreeyeart lerwerl JARUMAR UWA, together as in-identical twins*_
_i need your prayers plzz Ina kwance bani da lafiya, k'anwar sisi nama tana kwance bata da lafiya a asibiti_
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: https://chat.whatsapp.com/FL6vlC2CnStDUNk6BOW3Ob
*JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page twenty four2️⃣4️⃣
Shawarar sameera ce ta fad'o mata zuciya a take, sai ta gyara zamanta kamar babu komai a cikin ranta tace, "Masha Allah naji dad'in hakan matuk'a kayi mana bazata mu duka nida Ayman, nasan shima in yaji labari zaiyi farin ciki sosai, na amince da komawarka Germany a karo na biyu, sai dai da sharad'in zaka gabatar da ita a nema maka aurenta sai ku tafi tare".
Khaleefa duk da yaji Damm da farko amma amincewarta da aikin shi sai yaji kwarin gwiwa, yana fatan ya samu madafa kafun lokacin da aka d'iba musu na hutu ya k'are, sai ya russuna a gabanta yace, "Ina godiya auntie insha Allah zan kammala duk shirin daya kamata na gabatar miki da ita nan bada jimawa ba, saboda watanni biyu suma suka bamu a can duk wanda bai koma bayan wad'an nan watannin ba cikin sauk'i ya bayyana cewa bai amince da aiki tare dasu ba"
Wani murmushin cin galaba auntie tayi a ranta tace, ""Kaine no one cikin wanda za'ayi cancelling kuwa don babu inda zan yarda ka koma"". A fili kuma addu'ar samun nasara tayi mishi tare da sanya albarkarta. Da haka sukayi sallama ya tashi zai futa, har ya kai k'ofa ta kira sunan shi a sanyaye, "khaleefa!". Saiya juyo da raunananniyar zuciya ya kalleta ba tare daya iya amsa kiranta ba, itama a yanayin data ke kallon shi kenan cikin sigar tausayi ta fara mishi magana, "don Allah khaleefa ba don niba ba don na isa ba, ka sauke duk wani abu da kake ji k'asa ko don Ayman ya bar damuwa akan ka da sababbin halayen da kake gwada mishi, khaleefa tun kafun ka dawo 9ja rabon da naga walwalar shi, Ayman da a duniya bashi da zancen daya huce naka!! Amma shine mutum na farko da zaka fara kuntatawa da hukuntashi akan laifin da bai san dashi ba,,,, shin ka yiwa kanka adalci kenan?....".
Tun data fara magana ya sunkuyar da kanshi k'asa bai yarda ya d'ago ba har ta dire, a nutse itama ta mik'e ta k'ara taku kad'an zuwa gaban shi ta tsaya goye da hannaye a baya kafun taci gaba, "nasan halinka, fiye da yadda nasan halin Ayman da nake kwana dashi kullum nake tashi dashi.... Tabbas wannan laifin nawa ne ko baka furta da bakin ka ba zan iya fahimtar hakan daga kwayar idon ka.....". Khaleefa rintse ido yayi ya d'ago da idon shi da suka sauya colour ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya murd'a handle ya futa da sauri.
Ita kuwa ajiyar zuciya ta sauke bayan futar shi ta koma inda ta tashi ta zauna tana al'ajabin wai khaleefa yana da wadda yake son gabatar mata tuntuni matsayin matar auren shi?? toh wacece wannan yarinyar kuwa??? A wace duniyar ma ya had'u da ita tukun shida bai rufe sati da dawowa k'asar ba. Da wannan tunanin auntie ta k'arasa yinin ranar gaba d'aya.
Shima ranar yuni yayi yana juya maganganun ta a cikin zuciyar shi, tabbas auntie tayi gaskiya shi kanshi yasan a duniya ba wanda yasan halin shi irin yadda ita ta sani, a shekarun baya ko abinci zasu ci daga kallon da yakewa abinci take gane zaici ko bazai ciba.
Sai abu na gaba daya kamata zuciyar shi tayi laushi a kanshi shine, kowanne mutum tafe yake da k'addarorin shi da bai Isa ya tserewa ba, sannan har yanzu bashi da tabbas akan waccen magana da Saleema ta jefa mishi, idan zai yiwa kanshi adalci bai kamata ya dinga huce fushin wani akan wani ba,,,,, sai ya matsa daga inda yake tsaye ya koma kan gadon shi ya jingina yana sake kawo gyara cikin mu'amulolin shi.
★★★★★
Tada sallar asubah da akayi a masallaci yasa khaleefa futowa da hanzarin shi. A jikin k'ofar shi ya tsaya yana tunanin abinda ya hana Ayman futowa, a k'a'ida duk lokacin daya futo zai tafi masallaci yana samun shi tsaye a k'ofar d'akin shi yana jiran shi, sai dai yau bai ganshi ba, sai yayi tunanin watak'ila ko ya tafi ne, don haka sai yayi hucewar shi shima. Ko bayan sun idar da sallah ma bai tafi ba ya tsaya yana duba masu futowa har suka k'are ya tabbatar baizo masallacin ba yau sannan ya kamo hanyar komawa gida yana tunanin abinda yasa har sallar asubah ta kwace mishi yau.
Kamar kullum yakan zauna a parlour yayi lazimummukan shi amma a yau sai yaji Sam bashi da nutsuwa, shin Ayman makara sallah yayi ko kuma wani abune daban yake faruwa dashi? Ganin tunanin shi yana rarrabuwa sai ya mik'e tsam yaje yayi knocking k'ofar shi, ya jima shiru kamar zai juya don ga zaton shi ko bacci yake, sai kuma wata zuciyar ta bashi shawarar ko bacci yake ai yana da kyau ya tashe shi yayi sallah ko shima ya rabauta da falalar da take cikin sallar asubah a lokacin ta, ya bud'e k'ofar ya shiga a hankali. Tun daga bakin k'ofa ya fara cin karo da pillows a k'asa duk an wurgo, gadon shi a hargitse shi kuma yana durk'ushe k'asan d'akin hannun shi a saitin cikin shi. Da sauri khaleefa ya k'arasa gare shi yana fad'in, "subhanallah Ayman, Ayman meya faru da kai kuma?". Ayman cikin tsananin azabar ciwo ya rik'e hannun khaleefa da hannun shi daya d'au zafi rau, khaleefa kuwa duk kid'imewa yayi ya rasa ta inda zai fara taimakon shi, kawai daga k'arshe sai ya rintse hannun shi da yake cikin nashi ya zuba mishi ido yana kallon shi cikin so da tausayi, ya fara tofa mishi duk addu'ar da tazo bakin shi, sun jima a haka kafun ciwon ya lafa mishi ya samu nutsuwa kad'an, har lokacin kanshi na cinyar khaleefa hannun su cikin na juna. Sai a sannan khaleefa ya tambaye shi abinda yake damun shi, da murya k'asa k'asa yace, "cikina k'irjina, bayana......". "dama kana fama da ciwon ciki tun kafun yanzu" da kyar ya ce, "Eh akwai magani na a drower zaka ganshi a farin kwali....". A hankali khaleefa ya janye shi daga jikin shi ya bud'e drower, shine a farko ma, gaba d'aya drower magunguna ne kamar za'a bud'e chemist lifdi lifdi, shi dai khaleefa ya d'auki iya wanda ya fad'a mishi ya tsaya yana dubawa, "wane likita ne ya rubuta maka wannan maganin". Ya tambaye shi da damuwa,,, Da kyar ya iya fad'a mishi "doctor Umar ne". Ajiye maganin khaleefa yayi ya d'auki mukullin motar shi ya tambayi Ayman, "akwai wani pharmacy kusa damu nan?". Girgiza mishi kai yayi ya yink'ura da kyar ya d'auko wayar shi dake yashe a k'asa ya lalubo wata no yai dialing, ringing uku ana hud'u ya d'aga, "ka futo pharmacy don Allah yanzu akwai maganin da yayana zai karb'a a gurin ka..... Ka bashi address zai taho da wayata". Daga can mutumin yace, "alright bashi wayar toh".
Sunyi magana da khaleefa ba me tsayi ba, kafun ya futa da sauri, shiya bud'e get ya cire mota waje, ya dawo ya rufe sannan ya tafi. Tunda yazo in aka d'auke masjid ba inda ya tab'a futa sai yau, da yake yasan garin kwana biyu da yayi baya nan ne anguwannin suka kwanta mishi baisha wani wahala wajen had'uwa da mutumin ba.
Bayan sun gaisa yake tambayar khaleefa shine abdallah da suka tab'a makaranta tare kafun ya futa waje karatu, khaleefa yace, "eh nine kayi hak'uri amma ni ban wani tuna ka ba fa", "ayyah ai shekarun da yawa shiyasa" nan ya mishi kwantace har ya tuno shi, aikuwa suka sake gaisawa, suna tafe a hanya suna hirar yaushe gamo har suka Isa shagon ya bud'e, khaleefa ya rubuta magungun da yake so ya shiga ya duba mishi. Koda ya bashi kud'i k'in karb'a yayi, haka nan sukayi exchange na phone number juna yace ayiwa Ayman sannu suka rabu kowa yayi nashi guri.
A gurguje ya dawo ya haura stairs, Ayman a haka har yayi alwala ya gabatar da sallar subh, _(kasancewar shi mutum ma'abocin addini)_ yana kan sallaya a lokacin da khaleefa ya shigo, ya ajiye ledar maganin a kusa dashi yace, "ya kake jin jikin naka?". Yace, "da sauk'i". "toh Allah ya k'ara sauk'i". Sake futa yayi ya lalubo kitchen d'in gidan ya shiga, tea ya tafasa mishi ya juye a d'an madaidaicin cup.
Saida ya bashi shayin ya tilasta shi ya shanye tass kafun ya b'alle mishi maganin ya sha". Bai zauna ba ya gyara mishi saman gadon ya hau ya kwanta shi kuma ya gyara d'akin fess.
Ba jimawa bacci me nauyi yayi gaba dashi shi kuma ya d'auko system yaci gaba da zama tare dashi yana aikin shi lokaci bayan lokaci yana kallon yadda yake baccin shi sadidan da alamu ciwon ya lafa.
Har gari yayi haske suna tare bai tafi ba, yana jin yarinyar nan me aikin su ta gama gyare parlon tazo tana knocking k'ofar Ayman, bai motsa ba bai Kuma ce mata kanzil ba, tana murd'a handle taga khaleefa dama taja jikinta baya da sauri ta b'ace a gurin.
Auntie kuwa ganin har raana babu Ayman bare khaleefa da yake zuwa su gaisa duk safiya ya d'auki break d'inshi ya tafi, sai ta kasa samun nutsuwa, Ayman baya tab'a kaiwa war haka ba tare da yazo ya ganta ba, in kuwa hakane lallai akwai abinda ke faruwa shirun nan ba lafiya ba.
Bayan ta shiga d'akin shaheeda da take ta zabga bacci lakadan ta tashe ta donta karya kumallo, part d'insu ta nufa direct, saida ta fara tsayawa d'akin khaleefa tayi knocking taji shiru, koda ta bud'e baya ciki, hakan yasa ta murd'a k'ofar d'akin Ayman. Yana zaune kan gadon Ayman d'in ya mik'e k'afafun shi laptop d'inshi akan pillow a cinyarshi, sai Ayman d'in a gefe yana bacci rabin jikin shi rufe da bargo.
Sai a lokacin ta sauke b'oyayyen ajiyar zuciya, khaleefa zare glass d'in idon shi yayi ya ajiye laptop d'in gefe ya sauke k'afar shi k'asa. Har hard'ewa k'afar ta take wajen saurin ta k'arasa ga Ayman da yake kwance, hannunta ta d'ora a gefen wuyan shi taji jikinshi sanyi k'alou, "naji jikin shi ba zazzab'i gashi alamu sun nuna bashi da lafiya me yake damun shi kenan?". Khaleefa saida ya fara