Showing 216001 words to 219000 words out of 288773 words

Chapter 73 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1065

zama na har abada tare da juna ba.... Amma a shawarar raihana gwara ya shawo kan Saleema su daidaita su maida soyayyar su ko don ya kawo gyara wa rayuwarta, shi kuma hakan ne bazai iya ba, da ace bai ganta da kanshi ita da wani a wancen lokacin ba da sai ya iya karb'arta bayan yaji labari, amma yanzu koya aureta bazai iya sake had'a jikin shi da ita ba kyankyamin tama yake ji, wanda yayi a baya ma bisa kuskurene da rufewar ido cikin soyayyah, kuma da ace Saleema ta kama kanta ta dakatar dashi tun a farkon fara tafiyar kafun suyi nisa da basu je inda suka jeba......
Koda khaleefa yaje dai dai nan a tunanin shi saiya dunk'ule hannu ya kaiwa bango naushi zuciyarshi tana matuk'ar yi mishi rad'ad'i da k'una had'e da zallar nadama.

Raihana ma ta b'angarenta irin tunanin da takeyi kenan,,,,, Sam bata fatan wani abu mai kama da k'addara yazo ya had'e ta da khaleefa ta zama matarshi ta har abada,,,,,, ba zata iya ba sam ba zata iya had'a jikinta da wanda ya kasa killace kanshi ga mata marassa kamun kai ire iren saleema ba. Tana da matuk'ar hak'uri amma tana da mugun kishi musamman ta b'angaren y'an mata marassa kamun kai,,,,,shiyasa Ayman yake burgeta a rayuwa, ada tana kallon tsarin rayuwarsu iri d'aya ne da khaleefa, sai dai a yanzun ta fahimci yayi ma khaleefa fintinkau a nutsuwa hankali da kame kai daga aikata kowanne irin mummunan aiki..... Ba k'aramin asara zatayi ba inta yadda ta rasa Ayman........asara irin wanda ba zata tab'a maye gurbinta bama kuwa......

_not edited_


_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page sixty one 6️⃣1️⃣


Daga khaleefa har raihana kowa d'auke wuta yayi, haka suka ci gaba da zama sai kallo da ido, yayinda ako wacce rana suke samun kusanci da juna.
Ana gobe Auntie zata tafi suka futa su duka gidan khaleefa ya jibgo mata uwar siyayyah tamkar bada kud'i ya biya ba, jaka guda ya had'awa twin bro d'inshi ta abin duk da yasan yana so, duk da Ayman d'in fushi yake dasu a cewarshi sun rik'e mishi auntien shi,,,, baya kiran no kowa a cikin su.
Daren ranar da zata tafi ta damk'awa raihana wani madaidaicin diary data rubuta shi a d'an zaman da tayi dasu a k'asar Germany......
Koda raihana ta kalleta da neman k'arin bayani murmushi tayi tace, "wannan kundin tarihin rayuwata da k'addara tane, raihana ban tab'a yarda wani yaji sirrina ba amma ke na amince dake bisa sharad'i......".
Raihana shiru tayi tana sauraronta bugun zuciyarta na k'aruwa.
"Na k'are gaba d'aya rayuwata kan y'ay'ana y'an biyu na,,,,,, Alhamdulillah cikin su babu wanda bana so ko nafi so sai dai wanda zuciyata tafi karkata gare shi,, wanda nafi tausayin shi wato mijin ki khaleefa, a zahiri mutane da yawa suna ganin kamar Ayman yafi sona akan shi wanda sam ba haka bane,,,, Ayman yafi nuna kulawarshi a fili amma khaleefa yakan ajiye komai a ranshi, a lokacin da suke under 15 going to 16 year's na tab'a kwanciya wani ciwo a gidan iya, kullum Ayman yana zaune a gefena baya iya matsawa ko'ina, yayinda khaleefa ya sake nisantata sai dai shima ya kwanta jinyar kanshi, yayi ciwo mai tsanani kamar ba zai tashi ba abinda ya rabawa Ayman hankali gida biyu ya rasa wanda zaiyi jinya a tsakanin mu. Bayan naji sauk'i khaleefa ma yaji sauk'i, sai iya take tambayarshi wata rana cewa ya akayi shida ba kullum yake wuni a gurina ba amma ya kwanta jinya har ya kusa mutuwa? A lokacin murmushi ya mata kamar ba zai bata amsa ba sai kuma yace, saboda naji ciwonta ata jinin jikina... Naji tsoro kada wani mummunar abu ya sameta, da ace auntie ta mutu a wannan lokacin la shakka da nine na biyu dazan bi bayanta.
Tun daga wannan ranar na dinga auna komai da yake nufi, tabbas yana da matuk'ar k'awazuci fiye da zato sai dai yana da dakakkiyar zuciyar da take iya d'aukar komai har ya iya b'oye shi a ciki, ba komai khaleefa yake yiwa kuka ba, daga tashin shi zuwa yanzu saina k'irga miki adadin lokacin da naga hawayen shi". Sai taja dogon numfashi sannan taci gaba, "raihana abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwar khaleefa a k'asar jamus, wanda a baya suka sa ya fara juyawa zuwa wani mutum mara son hayaniya, mutane da fassara kowa a yadda yaga dama,,,,,, sai dai zaman ki dashi yasa naga sauyi mai yawa a tare dashi, so nake kiyi iya k'ok'arin ki wajen ganin kin k'arasa aikin da kika fara,,,,,, so nake kimun wata sadaukarwa ki rayu da khaleefa domin yafi buk'atar ki fiye da Ayman...... Ta hakane kad'ai zai samu nutsuwar zuciya irin wadda ya rasa a silar fad'awa soyayyar wannan yarinyar......".
Da mugun sauri raihana ta kalli auntien tana tambayar kanta a zuciyarta shin dama auntie tasan da maganar su da Ayman ne ko kuwa Ayman d'in ne ya fad'a mata da kanshi?
Murmushi tayi ta sake damk'a mata diaryn cikin hannunta tace, "kada ki damu kanki da tunanin yadda akayi naji sirrin ku keda Ayman,,, sai dai wannan sak'on dana baki kiyi iya yinki ki tabbatar khaleefa baisan abinda yake ciki ba".
Shiru tayi ta sake tafiya nazari tabbas suna tsaka da hira ita da Ayman a waccen ranar sunji motsin mutum ata jikin k'ofa daga baya kuma auntie ta shigo, sannan kallon da tayi musu a ranar ya tabbatar mata taji komai sai dai ba tayi tunanin haka ba sai yanzu.
Da haka sukayi sallama raihana tayi shirin barci ta wuce d'akin khaleefa bayan ta yiwa diaryn kwakkyawan b'oyo cikin ma'ajiyar kayanta.

Washe gari suka tayata ta shirya kaya sun futo su rakata airport suka had'u dasu Ahmad sun futo suma da nasu sinkin tsarabar, sai suka rankaya su duka zuwa filin tashi da saukar jiragen......
Sai a lokacin taba khaleefa k'aramar takarda tace kada ya duba sai k'arshen watan da ake ciki.

Tafe suke su hud'u, shi yana gaba sanye da farar shadda sol riga da wando da malum malum ya rufe fuskarshi da facemask, mutum uku na take mishi baya sanye da suit black.
Auntie ta taho tare da raihana itama fuskarta rufe da rabin gyalenta, suna tafe tana jaddadawa raihana kada tayi wasa da duk wani sirri data bata, Shi kuma mutumin yana magana dana bayan shi. Sam hankalin su baya kan hanya shiyasa basu ankara da juna ba saida sukayi karo wayar hannun shi ta fad'i, da sauri auntie ta kauce raihana kuma ta durk'usa da nufin d'auko mishi wayarshi, har ta kai hannu saita kasa d'auka saboda wani hoto data gani kan fuskar wayar,,,,,, inba gizo idanunta suke mata ba kamar tasan ta cikin hoton.
Ganin yadda tayi sai escort d'inshi suka ce mata, "excuse me madame". Ja baya tayi suka d'auki wayar suka ba mutumin suna sake bashi hak'uri, "sorry boss".
Da hannu ya amsa su ya huce gaba suka mara mishi baya,,,,, auntie da take tsaye a gefe tabi bayan shi da kallo gabanta yana tsananta fad'uwa.
A gurin ta dakatar dasu suka k'arasa sallama.
Kuka sosai Yasmine da raihana suka sanya a lokacin da take rungume dasu.
Bayan ta gama saka musu albarka da fatan alkhairy juyawa tayi ta fara tafiya.... Duk suka bita da kallo suna d'agawa bayanta hannu har ta b'acewa idaniyar su.
Juyawa sukayi Ahmad rik'e da yasmine yayinda raihana da khaleefa suke tafe cikin sanyin jiki.
Har suka k'arasa gida babu wanda yace ma d'an uwan shi kanzil kowa da abinda yake tunani cikin zuciyarshi, lokaci bayan lokaci kuma raihana tana share hawaye.

Tana zaune a parlonta shiru don gidan yayi mata ba dad'i, gani take kamar zata ga auntie ta kawo mata tea, ko ta futo da trayn abincinta mai dad'i tana mata barka da zuwa.
Sai kawai ta fara kuka, dai dai lokacin da khaleefa ya rabu da Ahmad ya shigo gidan, jikin kujerar da take zaune ya k'araso yasa hannu biyu ya dafa kujerar cikin taushin murya yace, "kiyi hak'uri".
Juyowa tayi gaba d'aya tana kallon shi da murya me laushi tace, "I'm missing her....".
K'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya sauke yace, "meee tooo".

Yinin ranar haka suka k'arasa shi sukuku kamar kajin da kwai ya fashewa a ciki. Da dare bayan sunci abinci ta gyara gurin d'akinta tayi shigewarta ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta.
Dama khaleefa bai saka ran ganinta a d'akin shiba, koba komai yau shima zaiyi bacci cikin nutsuwa yayi birgima a gadon shi yayi juyi irin wanda ya jima baiyi ba.

***Saleema tana can cikin damuwa da tashin hankalin ramuwar gayyar da khaleefa zaiyi mata donta tabbatar ba kyaleta zaiyi ba yadda taga ranshin nan ya b'aci, ga tawagarta tun a waccen ranar suka kwaye mata baya, a cewarsu tasan yarinyar tana da wanda zai tsaya mata ta yaudare su tace bata da gata bata da kowa saida suka je suka ga ashe tana da aure, kuma mijinta yana da dukkan dama da ikon d'aukar mataki a hukumance tunda aiki yake wa k'asar, yanzu su in taja yakai report a makarantar su ya zasuyi kenan..... Duk yadda taso fahimtar dasu wani abu kin sauraronta sukayi, suka dinga aman rashin mutumci basu tafi ba saida suka mata tatas suka goranta mata mai son maso wani.
Wannan abu daya faru yasa ta sake zama tamkar mahaukaciya sabon kamu, ta daina zuwa schl ta daina d'aga wayar y'an gidan su, ta rufe kanta a b'angarenta bata da wani aiki sai kuka.
Tausayi sosai take ba da yawa cikin wad'an da suke makotaka da ita, sai dai basu da hanyar taimakon ta.
Amna ta futo lectures a wani yammaci wayarta ta d'auki ringing koda ta duba mahaifin Saleema ne yake kiranta, bata d'aga ba don batasan k'aryar da zata mishi yau ba kuma, (da yake duk fad'an da zasuyi basa yarda su fad'awa y'an gidan su). Haka taita kallon wayar tana ringing da katsewa har aka gaji aka daina jera kiran.
Shiru tayi a gefe d'aya tana tunanin ta yadda zata iya shawo kan Saleema har ta fahimci gaskiya, hanya d'aya ce dai ta rage yanzu wato ta inda aka hau,,, khaleefa kenan wanda batasan ta inda zata fara tunkarar shi da maganar taimakon saleeman ba...... Shin zaima saurare ta?

****Har ya shirya futa office bai ga alamun taba, ya daiga breakfast shirye a dinning, yana sane tun ranar da Saleema ta mata tozarcin nan bata sake zuwa makaranta ba, ko nufinta ta daina zuwa?

Yana d'aura agogon shi a hannu ta futo rik'e da cup, kaikaitaccen kallo ya mata tun daga sama har k'asa, tayi maseefar kyau cikin straight skirt da riga mai tsagu gefe da gefe, kanta ba d'ankwali sai gashin da yasha nad'i kamar doughnut, ta d'auka ya futa a gidan shiyasa ta futo kanta tsaye.
D'auke wuta khaleefa yayi sai kallon yadda d'inkin ya zauna a jikinta atamfar kuma ta haska ta, bai tab'a zaton haka atamfa take mata kyau ba sai yau da yaganta ba gyale ba hijab.
"Masha Allah lak'uwwata illah billah....". Ya fad'a kan harshen shi k'asa k'asa.
Kanta a k'asa tace mishi, "Ina kwana".
"Laafiyaa" ya amsa still idon shi a kanta.
"Me yasa kwana biyu bakya zuwa makaranta?".
Shiru tayi bata ce mishi komai ba, hakan yasa ya sake maimaita tambayarshi da d'an k'arfi.
Sai a lokacin ta d'ago ta dube shi, k'arara yake ganin tsoro a kwayar idonta, sake taku biyu yayi har gabanta ya tsaya dab da ita k'amshin turaren ta na isar da sak'o ta hanyar amfani da kafofin jinshi. Ya lumshe idon shi ya bud'e a kanta sannan ya fara magana da wani keb'antaccen sauti, "Banda yau! Amma gobe ki tabbatar kin koma makaranta,,,,, ki saka ranki a inuwa indai Saleema ce tana can cikin tsoro ba zata sake yink'urin fara tab'a kiba, idan kuwa har ta sake wannan gangancin!...... Hummm".
Yana gama zancen ya huce kai tsaye dinning, ganin taci gaba da tsayuwa a gurin sai yayi mata magana, "yau ba za'ayi saving d'ina ba?".
Saida tayi kamar ta juya d'akinta ta d'auko gyale, sai kuma dai ta fasa ganin yadda yake ta kallonta.
Da takun nutsuwa ta Isa dinning ta had'a mishi abincin, koda ta kai plate in gaban shi yatsun hannunta yabi da kallo zata d'auke yayi caraf da hannun yana kallon yadda hatta farcenta yayi maroon. "lallen nan dai da nace bana so ba za'a daina shiba?". Yadda yayi maganar da sanyi ya bata kwarin gwiwar mayar mishi martani, "kayi hak'uri Auntie ce ta shard'anta mun yinshi akai akai".
Murmushi yayi ya saki mata yatsun ya fara juya abincin gaban shi, "wato auntie dai so take ta ganki kamar ita, ni kuma na dinga yawo gidajen cin abinci?".
Bata ce komai ba sai murmushi da tayi kawai ta juya a nutse ta fara barin gurin.
Bai iya hak'uri ba saida yabi bayanta da kallo, musamman k'afafunta da take wata irin tafiya dasu tamkar bata so. Ya sauƙe k'ak'k'arfar ajiyar zuciya sannan yaci gaba da cin abincin shi.

*Bayan wasu kwana ki*
Raihana ta koma makaranta har ma ta maida hankali akan karatun ta, shi kuma yaci gaba da concentrating kan aikin shi, daga ita harshi sukan yi waya da auntie lokaci bayan lokaci haka y'an gidan su raihana, bata sanin lokacin da khaleefa yake kiran ummie ko Abba sai in tayi waya dasu suce mata ai khaleefa ya kira su jiya ko d'azu, su al'ameen kuwa dama sun zama kamar abokan shi, wani k'arin mamakin raihana ma har no ummaa kakarta yasa aka bashi suke waya, Ayman dai da gaske fushi yake dasu don yak'i magana da kowa a cikin su, koda khaleefa ya tambayi su iya sai suke fad'a mishi suma kwana biyu yayi musu yaji baya zo musu, tun khaleefa na ganin abun wasa sai gashi abun ya fara damun shi ganin da gaske d'an uwan nashi yake.

Cikin lokacin daga khaleefa har raihana sun kasa bud'e sak'on auntie, ga zaman shirun da suke ya fara damun kowa a cikin su musamman ma khaleefa don yaji dad'in hirarrakin da sukayi da ita a lokacin da suke kwana tare muhalli d'aya.

Yauma har ya kwanta kamar wanda aka tsikara da allura saiya tashi, ya k'ara haske a d'akin ya futa a ciki.
Harta kashe glove d'in d'akinta sai dim light data bari hannunta rik'e da diaryn da auntie ta bata tana nazarin yadda zata fara karanta shi.
Babu zato taji bugun shi, saita k'ara haske a d'akin da sauri ta bashi izinin shiga ba tare data motsa daga yadda take ba
Ya tura k'ofar ya shiga idon shi ya fara hasko mishi littafin da take rik'e dashi, kamar wanda aka ja da magnet ko rufe k'ofar baiyi ba ya shiga kai tsaye da nufin karb'ar littafin ganin handwriting ta baya kamar na auntie, da sauri ta damk'e littafin tana tuna gargad'in da auntie ta mata a kanshi.
Kai tsaye khaleefa ya mik'a hannu da nufin zare littafin, tayi saurin zura shi cikin duvet tana girgiza mishi kai, sai ya kama hab'a yana mata kallon mamaki kafun yace, "hadda saurin ki hajiya? Handwriting na gani kamar na auntie shiyasa..... Bani na gani".
Had'e fuska tayi tam ta turo k'aramin bakinta gaba, "gaskiya ni bana son irin haka, meya kawo ka d'akin mutane da daren nan?....".
"Wani abu daban sai kuma naga wani daban... A sauk'ak'e ki bani littafin nan na duba abinda nake son gani in dawo miki dashi simple and fine".
Cikin shagwob'a tayi magana wannan karon wai ko zai barta, "don Allah kayi hak'uri ba irin littafin ka bane?".
"Toh irin na waye?". Ya kwaikwayi salon yadda tayi magana, kife kanta tayi jikin cinyoyinta tana tsoron kada ya dage lallai fa sai ya gani. Da sauri ta d'ago jin k'amshin turaren shi kusa da ita, ta zaro ido tana kallon shi ganin ya zura hannu ta k'asan bargon da take ciki, kafun ta tantance me yake shirin aikatawa ya d'aga ta cak daga ciki ya sauke ta kan k'afafun ta.
Bata yarda ya kalle taba tayi saurin rungume shi donta b'oye jikinta saboda wata shegiyar sexy nightie ce a jikinta, cikin kayan daya siya mata ta ganta, daga gwaji sai bata cire ba tunda tasan ba shigo mata yake ba, koda ya buga ma bata d'auka zai shigo ciki ba.
Shi kuwa tunanin shine ya tsaya cak, notikan kanshi suka fara juyawa zasu kwance, yana kallon littafin amma ya kasa mik'a hannu ya d'auka.... Da kyar ya iya k'arfin halin fara janye jikin shi, sai dai yana motsawa take sake shige mishi, zuwa yanzu ya fahimci bada gangan take aikata hakan ba, Koda ya fahimci rigar jikinta kamar take son b'oyewa, hannun shi ya kai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login