Showing 198001 words to 201000 words out of 288773 words

Chapter 67 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1114

a hankali ya dinga matsawa bayan ya sake ta tana maida numfashi har ya koma inda wayarshi ta fad'i ya d'auka ya juya a zafafe ya futa daga gurin, don tabbas yaci gaba da tsayuwa zai iya illata Amna ta yadda ba zata iya morar kanta ba. Da k'afa ya dinga takawa da mugun sauri har yayi tafiya mai nisan gaske sannan ya samu mota ya hau, komai yana yinshi ne da k'arfin zuciya don jikin shi babu sauran kuzari, duk gabban shima jinsu yake kamar ba'a jikin shiba.

***Tun kafun passengers su fara futowa Ahmad yake tsaye a cikin airport d'in yana dakon futowar auntien, ya d'an jima yana jira kafun ya hangota tana tahowa rik'e da jakar kayan ta.
Kafun ta k'araso ya tafi da hanzari yana mata maraba, dafa kanshi tayi tana jin dad'in ganin shi cikin k'oshin lafiya.
Shiya karb'i jakar kayanta har zuwa inda yayi parking motarshi, ya zura kayan a baya ya bud'e mata gefen driver ta shiga, ya maida murfin ya rufe shima ya zagaya d'aya side d'in ya shiga ya fara tuk'a motar a nutse yana k'ok'arin barin gurin.
Suna tafe a hanya suna hira har suka d'auki hanyar shiga anguwar su. A zuciyar Ahmad kawai tunanin irin farin cikin da khaleefa da raihana zasuyi idan suka ganta yake, a lokacin da motar su ta shiga farkon layin.

***Raihana tana zaune tana chat ta tuna da lallenta da zata tisa kafun ta kwanta bacci anjima, sai ta ajiye wayar ta d'auko plastic bowl ta zuba kayan kallen a ciki da ruwa ta fara kwab'awa, nan da nan parlon ya cika da k'amshin muhallabiyyah da kayan lalle. Tana cikin kwab'awa taji ana murza mukulli a parlon yak'i shiga, tasan khaleefa ne don shi kad'ai zai zura mata key yace zai bud'e mata gida, kasancewar akwai key a jiki bata cire ba sai k'ofar tak'i bud'ewa, abinda ya sake b'atawa khaleefa rai kenan ya fara yiwa k'ofar wani kalar duka had'e da danna bell har saida raihana ta d'an tsorata don komai beyi kama dana lafiya ba.
Tana murza key ko gama bud'ewa k'ofar bata yiba ya turo ya shigo yayi cilli da wayarshi gefe guda, ya dafe kanshi da hannun shi yana shak'ar mummunan warin lalle abu na k'arshe daya tsana a rayuwarshi. Raihana data gama karantar a yanayin daya shigo d'auke wayarta tayi da bowl d'in lallenta da nufin gudu ta bashi guri, sai dai tana zuwa zata gifta ta gaban shi yaji warin kusa dashi, aikuwa a harzuk'e ya fincike bowl d'in garin hanzari har yana had'awa da wayarta da yatsun hannunta yayi wulli dasu duka kan tiles suka tarwatse a tare, sai ya dawo da duban shi gare ta ya fara nuna ta da yatsa yana takawa inda take tana ja baya har suka kai k'arshen bangon d'akin, tuni raihana ta gama tsorata banda zare ido ba abinda take yi, shi kuwa cikin d'aga murya yace, "wannan ya zamo na farko na k'arshe da zaki had'a wannan abun a inda kikasan idona zai gani......".
Tsabar tsorata duk jikin raihana ba inda baya rawa har bakinta, kallon shi kawai takeyi da auntie da take bayan su ta tabbatar baisan da shigowarta ba, don sun shigo ne ita da Ahmad a dai dai lokacinta da yayi wancakali da kwanon lallenta.
Daga ta bayan shi Auntie ta tafa hannayenta biyu tace, "da kyau! Da idanuna naga yadda kake tafiyar da amanar da kasa na karb'o a gurin masu k'aunarta iyayenta na baka kaima Amana don ka kula da ita,,,,,".
Raihana da gudu ta shige d'akinta don ba zata iya yin kuka a gabanta ta k'ara mishi laifi ba.
Shima k'afar shi yaja don zuwa yanzu ya fara daina gane mutanen da suke gurin, zai iya aikata komai ga kowa cikin rufewar ido.

Daga auntie har Ahmad da kallo suka bisu kowa zuciyarshi fal tunane tunane.
Gaba d'aya jikin auntie yayi sanyi da ganin irin wannan mummunar zamantakewar da take wakana tsakanin mutanen da tazo da kyakkyawan yak'inin samun su sun fara rayuwa cikin farin ciki da k'aunar juna , amma sai gashi a ranarta ta farko taci karo da abinda ya shallake tunaninta bare guntun mafarkin ta da take yi a can gida Nigeria ido rufe ko bud'e.

_shike nan yau mutanen raihana sun samu abun fad'a🙆‍♀️🙆‍♀️_

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*


_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page fifty six 5️⃣6️⃣


Ahmad ne daya ga duk jikin auntie a sanyaye tama kasa zama ya ajiye mata jakar kayanta cikin parlon yace, "ki zauna auntie wannan abune da.....". Da sauri ta katse shi ta hanyar d'aga mishi hannu. Shiru yayi yana kallon yadda gaba d'aya jikinta ya gama zama lakwas. Ta jima a tsaye kafun ta zauna cikin d'aya daga kujerun parlon.
Kusan mintuna da yawa kafun ta bud'e bakinta ta tambayi Ahmad, "dama haka khaleefa yake treating Raihana kamar ya siyo baiwa a kasuwa, ka fad'a mun gaskiya".
"Wallahi! Wallahi auntie kwatankwacin abu irin wannan bai tab'a faruwa tsakanin suba, yau d'in ma akasi aka samu ya huce fushin daba nata ba a kanta".
Saida ta nisa sannan ta sake tambayar, "fushin wa kenan?".
Cikin inda inda Ahmad yace, "ehh.. a'a....ina.... ina ganin ko a gurin aikine wani abu ya had'a shi da wani? Ban sani ba nima tunda gaskiya na riga shi futowa office".
"Kenan a can ka barshi?" Ta sake tambayar Ahmad.
"Eh na barshi yana aiki ma don har ta office d'inshi na biya kafun na tafi d'auko ki".
"Kenan yana da wanda suke rigima a office d'in?". Ta sake jeho mishi wata tambayar.
Zuwa yanzun Ahmad ya fara tsorata da tambayoyin na auntie, don yana ganin idan yaci gaba da amsata zata kaishi har inda baya son aje.
"Toh ai shi ba harkar kowa yake shiga ba, bare har akai ga samun sab'ani tsakanin shi da sauran ma'aikata aboksn aiki".
"Toh kaga ashe b'acin ran nashi ba daga office ya futo dashi ba kamar yadda ka fad'a da farko, lallai yaje gurin wani da ya b'ata mishi rai kafun ya k'araso gidan shi, ko kuma rigimar dama ta fara tsakanin su tun kafun ya futa daya dawo ta d'ora". Shiru Ahmad yayi cox anje inda bashi da amsar da zai bayar wajen ganin ya kare khaleefa.
Ita kanta ta fahimci haka daga yanayin Ahmad d'in shiyasa taja bakinta ta tsuke amma ba don tambayoyinta sun k'are ba. So take tasan musabbabin abinda ya tashi zafun zuciyar khaleefa, don tabbas k'aramin abu baya tab'a shi har yayi irin abinda yayi akan idonta d'azu. Kuma yadda tasan raihana duk da ba'a shedar mutum tasan zaiyi wahala in daga itane matsalar ta fara.
Sun d'auki adadin wasu mintuna a zaune kafun raihana ta futo yafe da gyale madaidaici, duk data wanke fuskarta amma har yanzu idanunta sun nuna alamun tayi kuka. Kusa da auntien ta k'arasa ta durk'usa kan k'afarta ta fara gaisheta. Auntie ta amsa cike da tausayin yarinyar, saida suka gama gaisawa taji lafiyar kowa daga mutanen Nigeria sannan ta gaishe da Ahmad ma.
Shima dai cike da tausayawa yake dubanta har suka gama, bayan sun gama gaisawa ta maida kanta k'asa shi kuma Ahmad ya futa daga gidan bayan yayi musu sallama.

Itama sai a lokacin ta tuna ko ruwa bata kawowa auntien ba, hakan yasa ta tashi da sauri taje kitchen ta had'o mata tray guda na ruwa da tea, bata zauna ba saida ta had'a da zubo mata abincin da ta ajiye zata kaiwa yasmine.
Ko ruwa auntie kasa sha tayi sai bin yarinyar da kallo duk inda tayi, ita kanta har yanzu jikinta a sanyaye yake burinta kawai auntien taci wani abu ko ba da yawa ba.

***Ahmad yana zaune a gidan shi ya tasa abincin da yasmine ta ajiye tsakiyarsu ido yana ta faman juya cokali a ciki. Kallon shi Yasmine tayi da kyau kafun tace, "Anya baka b'oye mun wani abu ba? Tun d'azu daka shigo na fahimci yanayin ka duk ya sauya, na tambayeka kace lafiya ni kuma banga alamun lafiyar ba,,,,, don Allah hubby kada ka fara shigo mun da dabi'ar b'oye b'oye tun yanzu".
Ajiyar zuciya yaja ya ajiye cokalin gefe yana kallonta ya bata amsa da, "Yasmin damuwar ba tawa bace ta khaleefa ce, kuma kona fad'a miki baki da maganinta tunda nima da nake tare dashi tsawon lokaci na kasa samun mishi magani,,,, gashi auntie tazo d'azu da yamma".
Da sauri Yasmine tace, "what! Auntie maman su khaleefa? What a very big surprise".
Ganin ta tafi wata jahar sai yaci gaba da tayata "yea! ita fa yanzu haka ma tana gidan sai gobe insha Allah zamu shiga ki gaisheta". Had'e fuska tayi tace, "kana nufin baza muje yanzu ba".
"Haba Yasmine wane irin yanzu kuma kalli lokaci dare fa ya fara yi".
"Toh ai ba wani dare ne yayi sosai ba, Ni dai don Allah Ina son na gantaaaaa" ta k'are zancen kamar zatayi kuka.
Had'e kai da gwiwa Ahmad yayi yana ci gaba da sauraron yasmine da magiyar da take mishi kan ya kaita taga auntien, shi kuma ba daren ne damuwar shiba kawai baya son taje gidan a yanzu da yake a hargitse, koda safen ma sai ya shiga in yaga komai ya daidaita sannan zai kaita su gaisa d'in,,,, don wannan family issue ne daya shafe su bai kamata kowa cikin shi ko ita suyi musu shishshigi a ciki ba.
Sai ya k'ara sauke ajiyar zuciya ya matsa kusa da ita ya jawota jikin shi don kawo k'arshen wannan rigimar tata.

***Khaleefa kam tun bayan shigarshi d'akin shi yake kaiwa da komowa ya kasa samun nutsuwa ko guda, gaba d'aya ya rasa inda zai jefa rayuwarshi yaji sanyi, ko idon shi ya rufe hoton fuskar Saleema yake gani data fara zama bak'ik'irin a zuciyarshi daga yammacin yau zuwa yanzu, ya zauna ya tashi ya dinga kaiwa ginin d'akin duka har saida duk ya jiwa hannun shi ciwo.
Lallai kuka ma rahama ne, a yau yaso ace ya kasance kamar Ayman d'an uwan shi da yake da saurin hawaye, da yaji dad'i don koba komai zai rage rad'ad'in dake cikin zuciyar shi.
A k'arshe sai bathroom ya shiga ya tara ruwa me yawa cikin bathtub ya shige gaba d'ayan shi da kayan jikin shi, tsananin sanyin ruwan ya dinga tab'a jikin shi yana bin kowacce kafar gashi yana shigewa, tun yana jin sanyin ruwan har ya gama bin jikin shi duka ya daina jin shi.
Ya jima zaune a ciki yana hasaso abubuwa da yawa kafun ya iya futowa bayan ya d'auro alwala, ya sauya kayan jikin shi zuwa wasu riga da wando milk ya tada kabbarar sallah, bai bar kan dardumar ba saida ya jira aka kira sallar isha'i ya gabatar da sallar, still bai tashi ba yaci gaba da zama yana lazimi da tunanin da yake neman zama sashe na rayuwarshi ta yau.
Baya jin yunwa, baya jin k'ishin ruwa bare har ya tuna wani abu daya cancanci ace yayi shi a lokacin, burin shi d'aya ya daina ganin hoton Saleema a majigin kwakwalwar shi gashi abun ya faskara. Adadin ganinta da yake, adadin tashi da hankalin shi yake k'ara yi.

***Auntie kuwa da kyar ta iya tsakurar abincin da raihana ta dafa mata sabo don kada ta zauna da yunwa, tasha tea me d'an yawa saboda kada raihana ta d'auka ko akwai wani abun a ranta,,,,,, a yau duk jikin su yayi sanyi babu wata hira ko dogon zance tsakanin su har lokacin kwanciya bacci yayi, raihana ta shiga d'akinta ta gyarawa Auntie kayanta a ma'ajiyar data ba kayan, ta sake gyara mata saman bed inda zata kwanta, ta dawo ta risketa a parlon inda take ci gaba da zaune har yanzu. Ta durk'usa cikin ladabi tace, "Auntie ya kamata ki huta haka nasan kinsha tafiya ga zaman jirgi me wahala, shiyasa har na gyara miki gurin da zaki kwanta ma".
Shiru tayi tana nazari kafun can ta nisa ta mik'e zuwa cikin d'akin raihana na take mata baya. Saida ta shiga bathroom ta d'auro alwalar kwanciya bacci kafun ta shirya cikin kayan bacci masu kauri, bata hau saman gadon ba ta had'a barguna uku a k'asa masu laushi ta fara k'ok'arin kwanciya, raihana data sake shigowa taga abinda take k'ok'arin aikatawa hana ta tayi ta hanyar cewa, "a'a auntie don Allah kada ki kwanta a k'asan nan bayan ga kan gado na gyara miki". Murmushi tayi irin nasu na manya tana kallon raihana da take magana cike da wauta ta k'uruciya tace, "ba komai nan d'in ma yayi".
Ba don taso ba ta kyaleta, amma fa abun sai taji ya mata wani iri ace auntien tana k'asa ita kuma ta hau kan bed tayi d'erere.
Zama tayi a gefen gadon tayi shiru tana nazarin abubuwa da yawa, itama auntien shirun da tayi tunanin khaleefa kawai take, tana son taji halin da yake ciki saboda tunda ya shiga d'akin ya rufo kwakkwaran motsi baiyi ba har ta baro parlon, ga raihana tana shirin kwanciya muhalli d'aya da ita saboda kunya.
Tashi tayi zaune da kyau tace, "shi wancen haka zai kwana ba tare da yaci komai ba kenan?". Shiru raihana tayi kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, "kiyi hak'uri raihanatu amma ba don halin shiba don hak'k'in aure da kasancewarki matar shi dafa mishi coppee ki kai mishi, sannan koda wasa kada kice don kunyi fad'a da mijin ki zaki raba makwanci dashi wannan kuskurene me girma, so daga nan kiyi zaman ki Allah ya bamu alkhairy".
Da kyar ta iya mik'ewa saboda dabaibayin da auntie ta mata, haka a kunyace jiki a sanyaye ta mik'e don cika umarnin auntien.
Duk da kayan jikinta ba marassa kauri bane amma saida ta d'ora hijab iya gwiwar k'afarta fari sannan ta k'ara ma auntien sallama ta tafi.
Raihana tasan khaleefa ko ruwan hannunta basha yake ba bare wani coppee saboda kyankyami watak'ila, rana d'aya da yaci abincinta shine ranar da yaji zai mutu da yunwa cikin dare.
Ta jima tsaye a kitchen bayan ta had'a mishi kofi d'aya na coppee da abinda zaici iya zallar cikinshi shi kad'ai sai tea daya sha kayan k'amshi, ci gaba da tsayuwa tayi tana sak'e sak'enta da k'ulle k'ulle har ta gaji sannan ta d'auki tray d'in tayi k'undunbala zata nufi d'akin.
Saida ta tsaya ta kwankwasa mishi, a lokacin yana zaune kan resting chair ya had'a kai da gwiwa, bai d'ago ba ya bata izinin shiga daga inda yake, ta turo k'ofar ta shigo bakinta d'auke da sallamar da amsawarta ta gagara a gurin shi.
Har gaban shi ta ajiye tray d'in ta matsa can nesa kan drower gefen gado ta zauna tana sake k'arewa d'akin kallo da yabawa mamallakin d'akin musamman yadda ya tsara komai. Gashi very neat bako d'igon datti kamar ba d'akin namiji ba.
Ya jima a durk'ushe kafun ya d'ago ya sake zubawa trayn data shigo dashi ido. A hankali kuma ya karkata akalar ganin shi har inda take zaune tana wasa da cumb data samu a inda ta zauna.
Baisan dalilin zamanta a d'akin ba don shap ya manta da auntie ma tazo gidan a yau. Sake kallon trayn yayi, kafun ya tsiyaya tea a k'aramin glass cup ya kai bakin shi da sauri ya shanye, sake zuba wani yayi ya sake shanyewa ya k'ara a haka har saida yasha 5 cups of tea ya hak'ura yana sauke ajiyar zuciya. Ya mik'e ya shiga bathroom bayan tsawon lokaci ya sake futowa ya ganta inda ya barta, sai yaja tsaki a k'asan ranshi yana tunanin abinda zaisa ta shigo mishi d'aki a irin lokacin da yafi buk'atar kad'aici.
Cikin sake had'e rai ya fara tambayarta, "akwai abinda kike buk'ata ne".
Ta fahimci inda tambayar tashi ta dosa shiyasa ta mayar mishi da amsar, "auntie ce....." Sai kuma ta kasa k'arasawa sai kanta data mayar k'asa.
Khaleefa dafe kanshi yayi da yake tsananin sara mishi yana tuna zuwan auntien, gaba d'aya ya manta tazo don komai ba tunawa yake ba. Agogon bangon d'akin ya kalla yaga dare ya fara nisa watak'ila ma tayi bacci yanzu.
Sai baice komai ba ya koma inda ya tashi yaci gaba da zama. Ta d'auke trayn ta mayar gefe ta sake komawa taci gaba da zama kan drower.
Anta kiran wayarshi baya picking yayinda suke ci gaba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login