Showing 240001 words to 243000 words out of 288773 words
Chapter 81 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
me neman wani abu a ciki.
Sai da ta gama k'ullawa da kwance yadda zata tunkare shi da maganar cikin zuciyarta sannan tace,, "na gode fa! Allah ya k'ara rufa asiri ummie ma tace na maka godiya....".
Mik'ewa yayi zaune da kyau yana kallonta, kallon daya sauke mata kasala da sanya jikinta sanyi har ta gaza jurar ci gaba da kallon kwayar idon shi ta sauke nata k'asa.
"Godiyar me fa?". Ya tambaya don har ga Allah baisan ya mata wani abu da ya cancanci ta mishi godiya ba.
"Abun alkhairin daka aika masu al'ameen mana". Ta fad'a tana sake d'agowa ta kalle shi.
"Ohh wannan.....". Sai kuma yayi shiru. Kamar ba zai sake cewa komai ba sai kuma yace, "meye abun godiya don Yaya ya siya ma k'annen shi sweet?".
"Hakane! Amma sai Naga yana buk'atar a mishi addu'a ko?". Raihana ta fad'a.
"Toh na gode! Baki dafa komai ba yau a gidan ne?". Ya k'are wancen zancen.
"Sorry bari na kawo maka". Ta k'are fad'a tana nufar kitchen, khaleefa ya d'auke kanshi da sauri daga bin bayanta da kallo yana gargad'in kanshi.
Har ta kawo abincin ta had'a mishi baice komai ba, instead of ta tashi kamar yadda ta saba a duk lokacin data ajiye mishi abinci sai ta kunna kallo ta zuba ma rivi idanu, ya sani magana ce a bakinta take tunanin ta inda zata fara.
Bayan ya gama ta kwashe duk kayan sai tea plask k'arami da glass cups ta bari ko zai ci gaba da shan tea.
"Kamar akwai abinda kike son cewa raihana?".
Ta gyara zamanta, "Eh dama tambayarka nake son yi ko akwai abinda yake damun ka cikin kwanakin nan? Kamar na rashin lafiya haka ko....".
Murmushi yayi yasan yana daga abinda suka tattauna da likitan nan, "kinga nayi miki kama da marar lafiya?"
Ta girgiza kai, "a'a amma yanayin ka ya nuna kana cikin damuwa?".
Shiru yayi, hakan yasa ta sake cewa, "nasan har yanzu abun nan ne yake damun ka ko? Dama haka soyayyah take azabtar da zucuyoyi da kowanne k'aramin kuskure, sai dai ina ganin me zai hana kayi amfani da shawarar dana baka a farko, kayi jihadi ka auri Saleema ko ba komai zaka tsamo ta daga rayuwar rashin kamun kai da take zuwa nagartacciyar rayuwa, sanadiyyar haka sai kaga gaba an samu uwar da za'ayi alfahari da ita.....".
Tunda ta fara magana ya zuba mata idanu yana kallonta har ta kai k'arshe sannan yace, "kina ganin na dace da mace kamar Saleema? Shin ban cancanci na samu wadda bata da tabon namiji ko d'aya ba? Wadda ta killace kanta daga kowanne namiji take wa mijin aurenta tanadin kanta kad'ai? Haba raihana".
"Kayi hak'uri idan maganar da nayi bata maka dad'i ba, sai dai kaima fa a case d'in Saleema ka aikata babban kuskure, a k'a'ida laifin ka yafi nata, taya ma zaka yadda kana namiji da aka sani da hangen nesa kayi rayuwar da zuciyarka ta raya maka da macen ba halaliyar kaba? Idan kuma ya zamana kaine ka fara bud'e mata k'ofar data d'auka waccen soyayyar itace asalin soyayyar dako wanne budurwa da sauri sukeyi fa? Shin hak'k'in ta bazai kama kaba a yanzun da kake shirin juya mata baya?".
Khaleefa mik'ewa yayi tsaye yayi tattaki zuwa gabanta ya durk'usa ya rik'e duka hannuwanta biyu yace, "duk yadda zanyi miki bayani ba lallai ki gane gaskiyar abinda nake nufi ba, raihana Saleema fa ita ta bani dukkan dama a kanta ta dinga shige mun tana tura kanta gare ni...".
"Me yasa kai baka janye jikin ka daga gare taba?". Ta sake fad'a cikin jin zafin abun a ranta.
Khaleefa ya matse hannunta da yake cikin nashi ya sake cewa, "ba zaki gane ba raihana".
"Sai dai in baka yimun bayani yadda zan gane d'in ba, toh wane bayani ma ya rage kayi bayan ka....". Sai taji nauyin k'arasa ragowar maganar tayi k'asa da kanta.
Khaleefa ya sake rintse hannunta cikin nashi yayi k'asa da muryarshi kamar mai shirin mata rad'a, "kiyi hak'uri raihana amma tazo a lokacin da bazan iya cewa a'a gareta ba, kuma ko a hakan ma na rik'e kaina.....". Sai yayi shiru yanajin zafi da rad'ad'in abun har a cikin zuciyarshi, ta wani gefe kuma yana jin nauyin raihanan.
"Nayi nadama! hak'ik'a nayi nadama!! tun farkon dawowa ta gida hutu da mukayi wata magana da malam, na hana idanuna bacci darare da yawa ina neman yafiyar ubangijina....". Yaja dogon numfashi ya furzar da zazzafar iska daga bakin shi yace, "ban cika miki baki ba sam bana daga cikin mazan da suke bin son ransu,,,, nasan kuma insha Allah zan samu irin matar da nake so tunda ba duka aka taru aka zama d'aya ba.....".
Raihana ta janye hannunta a hankali ta mik'e tsaye ta d'an ja baya don rage kusancin da suka yi kafun tace, "tabbas Allah gafururrahim ne amma zai yafe iya laifin dake tsakanin ka dashi ne ba laifin daka aikata ga bawa d'an uwan ka ba har sai in bawan da kanshi yace ya yafe.... Kuma kalar matar daka fad'a akwai amma a cikin 100% basu huce 20% ba, taya zaka iya gano tsirarun nagartattun mutane 20 cikin milliyoyin gurb'atattu?".
Shima mik'ewa tsayen yayi yace, "tabbas zan gano kuma ko yanzun ina iya ganin d'aya daga cikin su......".
Tasan ita yake nufi, hakan yasa ta fara girgiza mishi kai, "ka daina d'auka na d'aya daga cikin su saboda nima ba tsallakewa nayi ba, sai dai ni nayi iya bakin k'ok'arina wajen ganin na kare mu daga fad'awa halaka.........".
Ai khaleefa bai bari ta kai k'arshe ba yayi wani irin taku sai gashi gabanta, ya rik'e k'afad'un ta da duka hannuwan shi ya fara girgiza ta, "me kike nufi raihana?".
Zuciyarta ta dake duk data tsorata da yanayin shi, "Eh saboda nima wani ya tab'a rungumata a bazata......". .
Wani mugun naushi ya kaiwa bangon gefenta cikin tsananin jin zafi har saida hannun shi ya fashe, idon shi ya sauya colour zuwa red bakin shi har wani turiri yake a lokacin da yake tambayarta fuskarshi gab da tata, "twin ne ko? Me yasa twin zai mun haka.....". Sai kuma ya koma baya yana girgiza kanshi.
"Bashi bane, tunda nake tare da Ayman bai tab'a attempting rik'e hannuna ba har kawo yanzu da nayi nesa dashi".
Safa da marwa kawai yake a parlon kamar zautacce saboda zafun rai k'irjin shi sai sama da k'asa yake. Abinda ya sake razana raihana har ta zab'i sulalewa ta gudu d'akinta don bata manta yadda ya huce fushin shi a kanta waccen ranar ba.
Sai dai tana fara tafiya ya dakatar da ita ta hanyar shan gabanta, "wane banzan ne ya samu zarrar tab'a ki ba kuma twin ba?".
K'asa tayi da kanta idonta ya ciko da ruwan hawaye.
Ya sake daka mata tsawa, "tambayarki nake RAIHANA!". Tuni hawayen daya cika idonta ya samu damar silalowa bisa kuncinta. Sai ya sassauta murya ya sake rik'e hannunta, "don Allah kice wani abu gare ni? Ki fad'a mun ina hannun shi ya tab'a a jikin ki tun kafun zuciyata ta gama tarwatsewa.....".
Cikin muryar kuka tace, "ni fa bance maka ya tab'a niba". Ta fad'a tana ja baya har ta samu majingina don masifar khaleefa tasa k'afafunta ma rawa suke kamar ba zasu iya d'aukar nauyin taba.
"Kar ki maidani bagidaje mana, an tab'a runguma ba'a tab'a jikin mutum ba?". Ya fad'a yana tokare hannun shi jikin ginin da take jingine, girgiza mishi kai tayi hawayenta suna ci gaba da sauka d'ayan bayan d'aya.
Sun jima a haka kafun yasa hannu a hankali ya fara share mata hawayen, abun yazo mata a bazata, ta d'auka yadda ya fusatan nan wanka mata mari zaiyi sai taji sab'anin haka.
Shi kuwa jikin shine yaji duk ya zama lakwas, kawai ganin hawayenta yasa yaji jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya sai naseehar auntie ta fara dawo mishi kamar lokacin take mishi hani da iya sarrafa kai yayin fushi.
A gurin ta durk'usa donta gaji da tsayuwa, shi kuma ya zauna gab da ita har gwiwar su na had'uwa.
Kallonta yake babu ko alamun zai k'ifta ido bare ya d'auke kanshi, kallon daya mata nauyi ta kasa jurewa har saida ta sunkuyar da kanta k'asa tana kallon tafin k'afar shi data ke shan gyara kamar baya taka k'asa.
Khaleefa kuwa a lokacin ji yake kamar ya shiga cikin zuciyarta yaga komai da yake ciki, sun jima shiru kafun yace, "na baki labarin soyayyata, amma ke baki tab'a bani labarin taki soyayyar ba.....".
Sai yanzun ta d'ago ta dube shi tace, "saboda babu wani abu mai kama da wanda kake sonji a labarina da abinda ya shafi soyayyata".
"Har rayuwar soyayyar ki da Ayman......?". Ya sake jefa mata wata tambayar.
Shiru tayi tana kallon shi irin yadda yake kallonta kafun tace, "Ni ban tab'a soyayyah da Yaya Ayman ba".
"Zai fi kyau muyi magana ta gaskiya don har alk'awarin da kika mishi na aure bayan deal d'in mu dake ya k'are na sani.......".
Wani irin sak tayi ta d'auke wuta ta zabga tagumi tana kallon shi a zuciyarta tana tunanin yadda akayi khaleefa da Auntie suka san maganar da ba'a tattauna ta gaban su ba? Toh kodai Ayman d'in ne ya fad'a musu da kanshi?.
_please ku k'ara hak'uri dani abubuwan ne da yawa_
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page sixty eight 6️⃣8️⃣
"Bari na sauk'ak'a miki tunani, har yanzu ni Ayman baice mun komai ba, amma naji komai da kunnena a lokacin da kuke tattaunawa dashi a parlon Auntie. Na taho da niyyar shiga sai na tsaya duba wani massage a wayata a dai dai lokacin da yake jaddada miki kalaman soyayyah, na zab'i dana ci gaba da tsaiwa ba don komai ba sai don kada na shiga hak'k'in ku duk da bani da wani tunani a kanki lokacin...... Tun a sannan na fara nadamar auren ki, don na fahimci da ace nayi jinkirin minti biyu a ranar da zan gabatar dake ga mamana! Toh da Ayman ne zai zamo mijin ki bani ba....
Raihana komai da kika sani a rayuwa yana da mafari...... Kina da nagartar da ko wanne namiji yake nema a tare da matar auren shi, daga soyayyar da Ayman yake miki na fara sanin haka, shiyasa tun a ranar na fara binciken halayyarki da tsarin rayuwarki, saboda Ayman ba irina bane.... Shi mutum ne mai tsinkaye da zuzzurfan tunani kafun aiwatar da komai, nasan ba zai tab'a zab'in abinda ba nagartacce ba.
Matakin farko dana fara d'auka shine yin nesa dake saboda Ayman ya same ki bayan auren mu ya k'are, sai dai baka Isa ka yiwa Allah wayo ba, hakazalika k'addara ta riga fata..... Ina tsakiyar sauraren hirarku auntie ta k'araso gurin, nayi yink'urin b'oye komai daga gareta amma ta hanani damar yin kowanne motsi, haka muka gama jin komai tare sannan muka shiga cikin parlon.
A lokacin tabi duk hanyar da tasan zata ji wani abu daga bakina game da irin auren mu ban yarda ba, har zuwanta Germany na kwanan nan tana son jin tabbaci akan irin auren da mukayi, shine a k'arshe da zata tafi ta k'are da bani k'aramin rubutu a takarda bayan mun rakata filin jirgi....... Na fara tunanin auntie tana zargin munyi contract marriage ne dake shiyasa tabar mun sharad'in ko bayan ranta na raba auren mu bata yafe mun ba.... Raihana duk tunanina a yanzun shine taya Ayman zai same ki idan har auren mu bai k'are ba? Shin d'an uwa d'aya tilo abokin tagwaitaka ya cancanci samun irin wannan tukuicin daga gare ni? Raihana wannan tunanin dashi nake kwana nake tashi har office in na fara aiki shi yake zuwa min kaina, ta d'aya b'angaren kuma wani b'arin na zuciyata daban yana tunzirani da azalzalata kan wani abu daban shima.....".
Shiru yayi kanshi a k'asa yana sake danne zuciyarshi da gudun aiwatar da abinda zai zamo kuskure ko nadama a gare shi, shiyasa baya son gaggawa..... kamar fudda sirrin dake cikin zuciyar shi yanzun.....
A hankali raihana ta gyara zamanta, hakan ya samar da tazara tsakanin su, bayan d'aukar wasu mintunan shiru ta fara magana da cewa, "kamar yadda na fad'a maka da farko, Yaya Ayman ba saurayina bane sai dai munyi rayuwa ta sabo dashi........".
Daga nan ta fara bashi takaitaccen tarihinta, tarihin daya tab'a zuciyar khaleefa ya sake tado mishi mikin da yake d'ankare a cikin zuciyarshi..... Musamman labarinta da imran, yaji kishin shi sosai fiye dana Ayman cox shine ya samu zarrar tab'a jikinta.
Shiru yaci gaba da wanzuwa tsakanin su yayinda raihana ta dinga k'ok'arin tsaida hawayen idonta.
A wannan yanayin khaleefa ya sake kallonta, muryarshi a tausashe kamar yadda jikin shi yake a sanyaye, "labarin soyayyarki tafe yake da rikita rikita da makirce makircen mutanen da baki sani ba, sai dai kin burge ni ta yadda kika kare mutumcin kanki baki yarda rud'in soyayyah yasa kin biyewa son ranki da zuciyarki ba kamar yadda mukayi.... Da ace Imrana ya samu dukkan dama a kanki raihana? Toh da bazan tab'a yafe mishi ba..... Har abada......".
Shiru yayi yana kallon hannun shi daya dame shi da rad'ad'i saboda naushin daya kaiwa bango d'azu ashe yaji ciwo.
A nutse ta share hawayen idonta ta kalli hannun tana kallon yadda yatsun suka kumbura. A firgice ta kai hannun ta gurin ciwon ta shafa tana yi mishi sannu, ya d'auke hannunta da sauri saboda wani zafi da yaji.
"Ya kamata mu tafi asibiti fa?". Ta fad'a cikin nuna kulawa.
"Zan iya dubawa". Ya fad'a bayan ya mik'e tsaye.
Itama mik'ewar tayi, ya d'auki hanyar d'akin shi ita kuma ta tsaya daga nan baya tana kallon shi.
Bayan mintuna k'alilan da shigarshi d'akin yazo bakin k'ofa ya kwankwasa, ta gane abinda yake nufi saita nufi d'akin ta shiga bakinta d'auke da sallama. Yana durk'ushe gaban first aid box daya ajiye a d'akin, itama saita k'arasa.
Ya nuna mata yadda zata mishi treatment yasa ta b'allo mishi magunguna yasha.
Saida ta tabbatar ya samu relief sannan ta futo a d'akin zuwa nata zuciyarta fal tunanin kalaman khaleefa masu kama dana wanda ya mutu a so....
***** Bayan ta kwanta bacci ta rasa gaba d'aya abinda yake damunta, sun fara magana da khaleefa basu gama ba, gashi ta kwanta bacci yak'i yiwuwa, tsabar fitina sai yanzu yunwa take tsikararta.
Tashi tayi zaune ta kunna glove haske ya cika d'akin gaba d'aya, ta dubi rigar jikinta da bata k'arasa sauka mata k'asa ba, ta zura zumbulelen hijab a samanta duk da bata tsammanin samun kowa a parlon.
Koda ta tura k'ofar ta futo yana zaune cikin parlon ya had'a kanshi da gwiwa, motsin tafiyarta ya sashi d'agowa sai kuwa cikin sa'a idanun su suka fad'a cikin na juna....
Ta sakar mishi tattausan murmushi ta huce zuwa kitchen, abinci ta zubo cikin plate ta dawo parlon daga nesa dashi ta zauna tace, "ya jikin?". Ba tare daya kalleta ba yace, "alhamdulillah".
"Amma ba jikin bane ko?"
"Um um". Ya sake fad'a ba tare daya yarda ya d'ago kanshi ba.
Har ta gama cin abincin ta maida plate d'in kitchen yana nan zaune a gurin.
"Ya kamata ka kwanta haka dare ya fara nisa".
"Bazan iya kwanciya ba".
Kamar ta tambayeshi dalili sai taga aiba hurumin ta bane, hakan yasa tayi hucewarta d'akinta ta barshi a gurin.
Sai dai ko bayan ta kwanta kasa nutsuwa tayi, sai taga kamar bai dace ta barshi a yanayin da yake ba...
Sai ta mik'e tsam ta futo parlon, yanzun kanshi ya kwantar jikin kujerar da yake zaune idon shi a rufe kamar mai bacci, tsabar nisan daya yi ko motsin zuwanta kusa baiji ba sai k'amshin turaren ta ne ya ankarar dashi wanzuwarta a gurin.
Ya mik'e zaune da kyau yana kallonta. Itama kallon shi take kamar me karantar wani abu cikin kwayar idon shi kafun nauyin shi ya cika ta tayi k'asa da nata idon.
"Shin har yanzu baka ji ka aminta dani ba?". Tayi tambayar kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta.
K'aramin murmushi yayi yace, "yardar cema tasa na bud'e miki sirrin daba wanda ya sanshi tare dani duk duniyaaaa.....". Shima ya bata amsa ba tare daya kalleta ba.
"Idan hakane meyasa kake son b'oye mun wani abu yanzu kuma?".
"Saboda fad'ar bata da wani amfani". Ya sake bata amsa.
Shiru tayi tana kallon shi kafun can ta nisa tace, "shikenan! Allah yayi maka maganin