Showing 171001 words to 174000 words out of 288773 words

Chapter 58 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1080

inda makusarta take kenan, ko daya cika kallonta sai ya fara ganin wasu sirrikan kyau da a baya bai tab'a sanin su a tare da ita ba. Gashi kwana ki biyu da bai ganta ba har wani haske ta k'ara a idon shi da sihirtaccen kyau.
Fulawa take ta kwab'awa zata yi doughnut da zata dinga breakfast dashi na kwana biyu. Kamar me koyon girki haka ya dinga bin komai da take yi daki daki, a nan ya sake tabbatar da tsabtar ta ganin yadda take komai tsaf tsaf ga nutsuwa.
Raihana bata ganshi ba sai daf da zata gama k'arasa had'a komai. Cikin sa'a ta kama shi yana kallonta.
Binshi tayi da kallo a kaikaice, kamar koda yaushe yauma sanye yake da k'ananun kaya, riga bak'a wando fari da ratsin bak'i, hannun shi rik'e da wayar shi ya hard'e su a k'irji, da alamu ba daga office yake ba, ya jima da dawowa ko kuma bai futa bama.... Kamar marar gaskiya haka ta hau duru duru kafun tace, "in... Ina.... Ina kwana".
K'arasa shiga kitchen d'in yayi ya d'auki cupi a kusa da ita ya tsiyaya ruwa yasha sannan yayi mata magana da murya can k'asa, "hala yanzu kika tashi bacci?".
Girgiza mishi kai tayi kamar me tsoron wani abu, yatsun hannunta da suka sake futo da zanen lallenta maroon da kullum cikin tisashi take kamar yadda auntie ta koyar da ita ta kuma bata shawara yabi da kallo. Tab'e baki yayi take yaji haushin kanshi ya kama shi har ya fara tuhumar kanshi uban me ya shigo dashi ma har idon shi yaga abinda baya sooo, gashi ranshi ya kwad'aitu da k'amshin girkinta da yaji ya gani a lokaci guda kuma lallenta zai mishi shamaki da abincin.
Har ya juya zai futa sai ya tuna ashe fa magana yazo suyi da ita, daga inda yake tsaye ya juyo ya kalleta yace, "ranar laraba zamu Nigeria saboda Friday za'a d'aura auren Ahmad, sai ki zama ready".
Wani irin farin cikine ya kamata har batasan lokacin da ta d'ago ta kalleshi hak'oranta duka a bud'e ba.
Haka kurun Khaleefa sai yaji kyashin yadda zata b'ata mishi rai ita tayi farin ciki, yasan tunaninta shine a Kano ne ta yadda zata ga familynta, sai yayi murmushin mugunta yace, "dama kin daina murna... Iya Abuja kad'ai zamu".
Take kuwa farin cikinta ya koma ciki, amma duk da haka sai taci gaba da yak'e, koba komai in taje Abuja zata ji k'amshin Kano ba kamar yanzu da take nan ba.

Ko daya futa tuhumar kanshi ya dinga yi akan abinda yayi mata yanzu, shin ya kyauta kenan daya kawo mata labarin da zatayi farin ciki ya lalata shi da b'acin rai? Ko kuma ita laifin tane da kullum take labta lalle a hannunta ta dinga cika mishi hanci da k'amshin girki? Shin ya tab'a fad'a mata baya son lallenta shida karan kanshi yaga taci gaba dayi?
Sai ya samu kanshi da zama a parlour abinda yakan jima baiyi ba, tar tar hoton fuskarta ya fara dawowa kwanyarshi da yadda tayi dariyar data bayyana duka hak'oranta waje, ba k'aramin kyau tayi a lokacin ba, lallai yayi missing daya lalata mata farin ciki bai gama k'irga hak'oran taba.

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*

Comment and share
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page forty eight4️⃣8️⃣


Haushin kanshi yaji akan yadda ya zauna yana ta tunaninta da lissafo jadawalin b'oyayyen kyawunta kamar wani marar abinyi.
Tsaki yayi kafun tsam ya tashi ya shige d'akin shi ya rufo.
Ko daya zauna a gefen gadon shi kasa nutsuwa yayi, idanun shi nata hasko mishi zara zaran yatsun hannunta da suka ci adon jan lalle, sai k'amshin turaren jikinta da yasha banban da sauran duk wasu turaruka daya sani a duniya, ga kayan snacks da take soyawa sunyi ja a cikin mai suna fudda k'amshin su, a gaba d'aya duniyar khaleefa ba abinda yafi so kamar snacks, ko yanzu a Germany kullum cikin yawon cin burger yake. Dafe kanshi yayi da duka hannuwan shi ya runtse ido amma still hoton fuskarta tana wannan murmushin sai gilma mishi yake a majigin kwakwalwar shi.
Mik'ewa yayi tsaye ya kaiwa katifar gadon shi naushi wai ko zai ji ya daina tunanin ta, amma bai daina ba, ya zauna ya tashi, ya k'aro gudun AC dake aiki a d'akin amma duk ba sauk'i saima tsigar jikin shi data fara zuba saboda sanyi daya k'ara bayan wanda akeyi a garin.
Daga k'arshe sai ya d'auki wayarshi ya futo daga d'akin ya bar mata gidan gaba d'aya.
A harabar gaban gidan ya tsaya, yana k'arewa anguwar da shuke shuken harabar gaban gidan kallo, Saleema ce ta fad'o mishi ranshi, take yaji matsananciyar kewarta kamar yayi tsuntsu ya ganshi a gabanta yanzu, yana son ganin kyakkyawar fuskarta yayi kissing wannan cute lips d'in nata, yayi hugging d'inta da wannan plat tummy nata da yake wa ritsawa d'aya da hannun shi. Lokaci d'aya yanayin rayuwar da sukayi a baya ya fara dawo mishi daki daki. Abinda ya taimaka matuk'a wajen sauya mishi yanayin shi gaba d'aya cikin lokaci k'alilan.
Gaba d'aya kanshi ya d'aure ya fara sarawa da d'aukar sabon ciwo har jijiyoyin kan na tashi rud'u rud'u. A haka Ahmad ya futo gidan shi ya hange shi, saiya taho zai k'araso inda yake saboda dama gurin shi zaije, fuskantar haka da khaleefa yayi ya fara juyawa zai koma inda ya futo ba tare daya nuna ya ganshi ba koda wasa, saboda a yanayin da yake baya son magana da kowa. Shi kuwa Ahmad zama dashi yau da gobe yasan kafatanin halayen shi, tabbas yasan ya ganshi ya nuna bai ganshi ba, me yiwuwa hakan baya rasa nasaba da yana buk'atar kad'aici, shima dama akwai abinda yake so ya same shi suyi shawara a kai, kuma yanzu muddin ya takura zasu iya samun matsala dashi, don haka sai shima salin alin ya shige gidan shi.

*Bayan kwana ki biyu*

Tun kafun ranar da zasu tafi raihana ta had'a kayanta a jaka guda, duk da kayan da zata tafi dashi bai huce kala biyu ba, sai undies da kayan bacci da dogon hijab da gyale d'aya.
Yau kuwa data kasance ranar da zasu tafi da wuri ta shirya gudun samun matsala da man, tayi kyau cikin shigarta ta doguwar rigar lace A shape data zauna mata das a jiki ta bada shape me kyau wa surar jikinta. Yau bata saka hijab ba sai wadataccen gyalen data d'ora har saman kanta ya lullub'e ta ruf. Kusan a tare duk suka futo ita dashi kowa rik'e da jakar kayan shi, cikin ladab raihana ta gaishe shi, ya amsa ta kadaran kadahan.
Yadda tayi kyau haka shima yayi kyau da shigar manyan kaya hula ce kad'ai babu. Ko raihana a ranta saida ta yaba kyawun da yayi, don ita a kaf dressing na maza ba wanda tafi k'imantawa kamar na manyan kaya.
A kan d'aya daga kujerun parlon ta zauna ta barshi nan tsaye yana danna waya.
Shi kuwa direct Ahmad ya kira ya tambaye shi ko yana sane da zasuyi late in bai futo ba yanzu? "Gani nan nima ai". Abinda Ahmad ya fad'a kenan k'it ya katse kiran. Raihana yabi da kallo duk da yadda ya dinga kwab'ar kanshi da k'ok'arin d'auke kwayar idonshi amma ya kasa, ba k'aramin kyau ta mishi cikin shigarta ta yau ba, gashi abinda yafi mishi dad'i yadda yau bata zuba wannan uban hijabin tasa in sun fita a dinga kallon su a k'asar daba tasu ba, abu na biyu yadda take da matuk'ar taka tsan tsan, tunda sukayi aure ba zaice ga abu d'aya da tayi mishi na laifi ba, duk abinda ya bata umarni karb'a d'aya take yi mishi, ko yanzu tafiyar nan da zasuyi ko lokacin tashin jirgin bai fad'a mata ba amma ta futo a ready kamar ta sani, kuma ko ranar daya sanar mata tafiyar bai b'ata bakin shi wajen yi mata dogon sharhi ba.
Knocking k'ofa da akayi ya ankarar dashi Ahmad ya k'araso, sai ya d'auki jakar kayan shi yayi gaba itama ta biyo bayan shi, saida ya tsaya ta futo ya rufe gidan sannan suka nufi inda Ahmad yake tsaye da motar haya da zata kaisu filin jirgi yana jiran su. Duk suka gaisa da angon kamar kullum yauma har yana tsokanar raihana ya taji yau da zata Nigeria bayan kwashe watanni a Germany? Kamar kullum ba tace komai ba sai murmushi da tayi.
Ko a cikin mota raihana da khaleefa kusa da juna suka zauna amma baiji wannan tashin k'amshin turaren ba, ba k'amshin ne babu kwata kwata ba, akwai amma mastad'a'a banda sunyi kusa ma ba zaiji ba.


Misalin k'arfe uku da rabi na rana suka sauka a Nnamdi Azikiwe international Airport dake Abuja. Ba b'ata lokaci kuwa Ahmad ya d'auki waya zai kira y'an gidan su a turo driver ya tafi dasu, khaleefa ya hana, "haba man! Ga motocin haya nan da yawa ba sai mu tafi a su ba".
Haka kuwa sukayi khaleefa ya samo motar haya ya fad'a mishi anguwar da zai kaisu.

Sun samu tarba ta mutumci daga maman Ahmad da y'an uwan shi, barin ma raihana, da yake akwai k'annen Ahmad biyu da sukayi aure sunzo gidan suma biki sai suka yi ala ragab da ita.
Khaleefa dama yana b'angaren Ahmad, zaman mintuna k'alilan sukayi, shima saboda sallah da cin abinci, suka sake futa basu dawo ba sai dare. Gaba d'ayan su a gajiye suke burin su d'aya da sunci abinci su kwanta, sun samu gidan da k'arin wasu cousins d'in Ahmad guda biyu suma da suka zo biki daga nesa.
khaleefa koda Ahmad ya kawo musu abinci kasa ci yayi ya koma gefe yana danna wayarshi. Ahmad yasan sarai ko yana jin yunwa zai iya kwana a haka, saboda kasancewar shi d'an matuk'ar takura kai da yin abinda zai cuci gangar jikin shi. Ko shawara baiyi dashi ba ya nemi k'anwarshi khadija ya fad'a mata tasa raihana ta shirya mishi tea da wani abu mara nauyi da bazai d'auki lokaci ba.

Ta kam da wuri ta gama shirin baccinta tayi kwanciyarta kan gadon d'akin da suke ita dasu ummu aphnan, da mamaki ummu aphu tace, "bacci da wuri kuma raihana? Don Allah ki tashi kada kanki ya shiga duhu nan ba gidan da zakiyi bak'unta bane"
Mik'ewa tayi zaune ta kalli ummu aphnan data k'araso kusa da ita ta zauna ta dafa kafad'arta "Raihana mijin ki yana da kawaici da kara kamar yadda kike, a shekarun baya ban tab'a zaton Khaleefa zai auri mace sak da sak irin shiba, saboda masana tarihin soyayyah sunyi ittifakin ba'a zaman lafiya a gidan da aka had'a hali sak da sak, sai dai yanzu na k'aryata kaina ganin yadda kuke da mijin ki kuma kuke zaune lafiya,,,,, sai dai don Allah raihana kada idon mutane yasa ki cutar da khaleefa, tunda kuka zo ba ruwanki da bibiyar lamuran shi bare kiji ko yaci abinci ko yana buk'atar wani abun haka....".
Gaba d'aya tunda ta fara maganarta har ta gama raihana bata fahimci abinda take nufi ba, tunda dai tasan khaleefa ba k'aramin yaro bane bare ace komai sai anyi mishi. Kamo hannunta ummu aphnan tayi tace, "yanzu ki taso muje na had'a miki komai Ahmad yace kin iya dafa Sudan tea irin na k'asar ku". Murmushi raihana tayi don tunda tazo suke ta kallonta y'ar k'asar su Auntie, hijabinta wadatacce ta d'ora saman riga da wandon baccin dake jikinta.
Ummu aphu da kanta ta rakata har kitchen tana taya ta da hira har ta had'a tea d'in ta juye a plask, ta had'a faten doya da kwai da wadataccen kifi, kafun wani lokaci kitchen ya cika da k'amshi, khadija kam kasa hak'uri tayi saida ta zuba kad'an taci, tana ci tana ta yabawa raihana wai komai ta iya kamar rainon auntien su Khaleefa, raihana tana dariya a ranta tace ai d'alibarta ce.
Duk yadda khadija taso hanata raihana k'in hanuwa tayi saida ta tsabtace duk inda tayi aiki ta had'a komai a tray, ta d'auki d'aya ummu aphnan ma ta d'au d'aya suka tafi.
Suna zaune su kusan hud'u a lafiyayyen parlon, kusan duk sanye suke da kayan bacci, hira suke me kama da musu duk sun cika parlon da manyan muryoyin su ko sallamar da su raihana sukayi ba suji ba. Daga gefe ummu aphnan ta tsaya tana kallon su kawai, yayinda raihana take daga bayanta tana kallon khaleefa tana ganin yadda yake ta mayar musu da zance cikin nutsuwa da tattausan lafazi, tunda take dashi bata tab'a ganin yana magana da k'arfi kamar haka ba sai yau, kuma lallai akan abu me matuk'ar muhimmanci yake magana. Shima sanye yake da fararen kayan bacci sol a zaune kan k'aramin table dake tsakiyar parlon.
Ahmad ne ya fara lura da shigowarsu ita da khadija, sai yayi gyaran murya ya mik'e yace, "guys ya Isa haka! Nima na yarda da gaskiyar khaleefa,,,, mu ajiye wannan maganar a gefe,,,,, Bismillah ku k'araso raihana".
Sai a lokacin khaleefa ya d'ago ya fara laluben inda zai ganta a parlon, tafiya take amma kanta a k'asa har suka k'araso tsakiyar d'akin suka ajiye trayn a gurin.
"Sorry Madame, mun saki aiki cikin dare.... Kinsan man ne iyayi gare shi kamar me laulayi, ba komai yake ciba". Ita dai ba tace komai ba sai murmushi da tayi.
Kallon gargad'i khaleefa yayi ma Ahmad ba wasa yace, "ka dinga sanin me zaka fad'a a kaina". Ahmad yana y'ar dariya yace, "toh", khadija da take dariya itama tace, "aikuwa ta mishi girki me dad'in gaske".
D'aya daga cousin sis na Ahmad mai suna jafar kallon raihana yayi yace, "toh Madame ai sai ki saving d'in mu ki k'arasa ladan ki ko". Aikuwa baiwar Allah sai ta fara k'ok'arin bin umarnin shi, sai dai Ahmad da khadija har rige rigen hanata sukeyi, "wane irin lada kuma a bawa k'aton banza abinci, raihana yi tafiyarki Allah ya bamu alkhairy". Saiya kalli khadija data rik'e mata hannu yace, "idan muna buk'atar wani abu zamuyi miki magana". Kai ta gyad'a taja hannun raihana suka tafi.
Ita kuwa dama duk a takure take tunda suka zo ta kasa sakewa, da zata gaishe suma kamar marar gaskiya haka ta bud'e baki, yanzu kuwa da aka sallame su har ajiyar zuciya ta sauke.
Jafar dama tana futa ya kalli khaleefa, "yae! Wannan yarinyar fa". Khaleefa da yasan za'a rina duba da irin kallon da yaga jafar yana yi mata, murmushi yayi yace, "jafar da magana ne?". Da sauri jafar yace, "me kyau ma kuwa, yarinyar ta burgeni sosai ga nutsuwa ga aji".
Wani miskilin murmushi khaleefa ya sake yi lallai raihana tana da farin jini yana sane da duk inda suka je sai tayi saurayi, sai dai duk cikin tarin samarin nan har yanzu bai ga wanda zai iya bawa dama ya sameta ba, saboda har ga Allah nutsuwarta da hankalinta sun zarta na duka mazan, yana son raihana ta samu miji nagartacce na gasken gaske, yana son ta samu mijin da zai sota kwatankwacin yadda yake son Saleema yasan shi kad'ai zai iya rik'e ta amana. Shiyasa yanzu ya fara yiwa wani mutum mai matuk'ar daraja da k'ima tanadin ta, toh amma bari yaba jafar dama yaga ko zaisha.......
"Kayi shiru khaleefa so nake ka huce mun gaba tunda y'ar uwar kace yadda bazan sha wahala ba". Wani murmushin khaleefa ya kuma yi yace, "kada ka damu zan mata maganar, duk da yanzu bata da lokacin soyayya".
Zaro ido jafar yayi, a lokacin da Ahmad da takaici ya cika sa har takai ya kasa sa musu baki a zancen su ya mik'o mishi shayi. "bar shayin nan Ahmad hankalina bazai kwanta ba har sai mun gama magana da khaleefa".
Khaleefa kuwa har ya karb'i shayin ya tuna da yatsun hannunta daya gani waccen ranar, saiya maida kan tray ya ajiye, da mamaki Ahmad ya kalle shi, "Wai kana nufin har yanzu jikinta da lallen".
Da sauri mukhtar da shima bai sa musu baki a zancen suba saboda wasu abubuwa da yake tunani tsakanin raihana da khaleefan yace, "kamar ya fa".
Saida Ahmad ya zauna sannan yace, "zancen mune nida shi duk ba zaku gane ba okay....".
Zai sake cewa wani abu khaleefa ya katse mishi hanzari, "mubar maganar nan Ahmad please".
Shiru duk sukayi kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarshi kafun jafar ya katse shirun nasu da cewa, "Ni dai don Allah khaleefa kayi mun magana d'aya". Wannan karon Ahmad ne yayi magana, "wannan fa jafar ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login