Showing 186001 words to 189000 words out of 288773 words

Chapter 63 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1124

yammaci wani lokacin inya gaji da zaman gidan kuma ya futa k'ofar gida yasa kujera ya zauna yana shan iska, wani lokacin idan Ahmad ya lek'o ya ganshi yakan zo suyi y'ar hirar su, idan kuma y'an futar basa kanshi yayi zaman shi a gida tare da matarshi, don yanzu an samu banbanci tsakanin shi da khaleefa.
Yasmine ma takan zowa raihana lokaci bayan lokaci don ma raihanan ba mazauniya bace, yayinda har yau Allah bai ba raihana ikon je mata ba kamar yadda ta fad'a, ba k'aramin mamakin yadda raihana take iya duk ayyukan gidanta dama na kanta ba tare da gazawa ko nuna gajiyawa ba Yasmine take, duk sammakon da zatayi na futa lecture bata barin gidanta da d'igon tsinke bare aga datti, haka data dawo zata wanke k'urar data kwaso ta sauya kayan jikinta zuwa na zaman gida ta sake k'alk'ale gidan, lallen k'afarta kuwa tunda yasmine tasan ta tasan k'afarta dashi bata tab'a ganin k'afar fari ba. A d'an zuwan da take yi gidan ta fahimci kamar kowa harkar shi yake tsakanin miji da matar, (don a tsarin su basa pretend na nuna alak'a mai kyau ta k'arya a idon mutane alhali ba haka suke zaune a zahiri ba, sukan yi komai kansu tsaye musamman ma khaleefa) da farko tayi tunanin ko fad'a sukayi, amma bayan ganin irin bahaguwar zamantakewar kusan sau ba adadi sai kanta ya d'aure, sunsha zuwa gidan da dare suci abinci ita da Ahmad amma khaleefa yayi order.
Abun ya d'aure mata kai da yawa har takai ta kasa hak'uri saida ta yiwa Ahmad maganar, sai dai Ahmad ya nuna mata tsabar miskilanci ne na miji da matar, haka suke rayuwarsu tun kafun yanzu, da haka ya toshe mata tunaninta gaba d'aya daga kan abinda taso fahimta wai ko zata iya kawo gyara wa lamarin.
(An samu banbanci tsakanin Yasmine da raihana, don kuwa Yasmine tana da wayewa ta ilimin boko fiye data addini, amma tana iya k'ok'arinta wajen ganin ta kiyaye dokokin addininta, tayi karatu tun daga matakin secondry har zuwa University, sannan ita ba tayi rayuwar Nigeria ba sai in tazo hutu lokaci bayan lokaci, a gidansu su hud'u maman su ta haifa, akwai yayyenta biyu maza sai k'anwarta da take bi mata, iyayen su suna da matuk'ar rik'on al'ada, wanda hakan yasa suka raine su da yaren hausa, amma in bacin haka da ba zasu san komai a hausa ba, tana da kirki da sauk'in kai amma bata da hak'uri, ta iya girki irin na mutanen k'asar data rayu tare dasu gwargwadon iko, hakama na k'asar Nigeria, bata son aiki da yawa saboda garkuwar jikinta bai saba da wahala da yawa ba, shi kanshi Ahmad a abubuwa da yawa hak'uri yake da ita. Ta b'angare d'aya kuma akwai kyakkyawar alak'a ta soyayyah tsakaninta da mijinta wadda ta k'aru da 70% bayan auren su)
A iya d'an zaman raihana da yasmine ta k'aru da abubuwa da yawa da ba zasu k'irgu ba, ta fannin kula da jiki da girke girken k'asar Africa, ranar data bata turarukan ta na shafawa kuwa washe gari Ahmad suna futa aiki ta taho mata, sai dai ta daki gurbi don raihana a yau ta riga su ma futa zuwa makaranta, kuma bata dawo ba har yamma, lokacin da raihana ta dawo ita kuma ta shiga harkokin girki hakan yasa basu had'u ba.
Da daddare tana zaune cikin d'akin barcinta har tayi shirin kwanciya barci don tana da futa gobe da wuri ma aka mata knocking k'ofa. Kwan! Kwan!! saita mik'e zaune ta kunna fitilar gefen gado tana kallon k'ofar, ci gaba da bugun akayi abinda ya assasa mata saukowa ta d'auki hijab d'inta dogo ta saka.
Khaleefa ne tsaye ya juyawa k'ofar baya hannun shi duka biyu hard'e a bayan shi, ganin baisan da futowarta ba sai tace, "yauwa".
Ba tare daya juyo ba yace, "Bismillah k'araso". Ya gama fad'a yana yin gaba, itama bayan shi tabi tana kallon Ahmad da yake zaune cikin kujerun parlon.
Daga gefe ta tsaya ta d'ora hannunta jikin kujerar suka gaisa.
"Sorry Madame mun taso ki kina baccin ki ko?".
D'an murmushi tayi, "ai ban ma fara baccin ba".
"Alright dama mutuniyar ce jiya ta rikita mana gida da wani kalar turare na gargajiya mai sanyin k'amshi, koda na tambayeta sai take cemun ai ke kika bata, kuma tabbas ina jin irin k'amshin shi a gidan nan,,, Soo shine nazo naji ko zamu iya samun shi a k'asar nan?".
Satar kallon inda khaleefa yake tsaye tayi, ya fuske kamar baiji abinda abokin shi ya fad'a ba, ita kam shiru tayi kafun can tace, "minti biyu Ina zuwa?".
Komawa tayi cikin d'akinta ta d'ebo da yawa fiye ma da wanda ta bata da farko ta dawo parlon ta mik'awa Ahmad. "Ka k'ara kai mata wannan".
B'ata fuska Ahmad yayi, "bama son haka! Inda zamu samu kawai muke son sani".
"Ai ba zaku samu a k'asar nan bane, nima auntie ce ta had'a mun shi".
Kallon khaleefa Ahmad yayi yace, "man kace sirrin daga gare kune ma".
Sai a lokacin ya d'ago da kanshi ya dubi Ahmad ba tare da yace komai ba ya mayar da kanshi bisa wayarshi.
Godiya mai yawa Ahmad ya mata ya d'auki kwalaben turaren, komawa tayi d'akinta shi kuma yayi sallama da khaleefa ya tafi.

Koda Ahmad ya fad'awa Yasmine yadda sukayi da raihana ba k'aramin mamaki tayi ba, "mahaifiyar mijinta ce auntie dama?".
Ahmad yace, "kwarai kuwa!". .
"Toh aini na d'auka maman tace data haife ta".
Ahmad yana kallon Yasmine yace, "ai matar ce k'arshe ce, ke a duniya babu wani mutum mai mutumci da zan baki kwatancenta dashi suyi dai dai, ita d'in ta kasance k'arshe a cikin masu mutumcin mutumci, soon zata zo k'asar nan zaki ganta ai".
Ita kam Yasmine abun ya bata mamaki, kenan duk wasu sirrikan matan Sudan ita taba raihana? She can't believe za'a iya samun irin wad'annan iyayen mijin, ganin kirkin maman Ahmad yasa ta d'auka a duniya ba wadda ta kaita sa'ar suruka, sai gashi taga wadda ta ninka ta kirki sau trillion.

@@@@@@@@@


*NIGERIA*

Yanayin da take jin jikinta cikin watannin ya tabbatar mata lallai bata da cikakkiyar lafiya, k'arfin hali kawai take da kwarara kanta don bata son gazawarta ta futo ko abinda zai nuna rauninta. Hakan yasa bata fasa futa office ba a kullum safiyar Allah.
Yauma tunda safe ta shirya cikin wadatacciyar suturar da take suturta jikinta a koda yaushe, ta d'ora rigar likitoci a sama. Tana futowa engineer ma yana futowa. Har k'asa ya durk'usa ya gaisheta cike da ladabi kamar koda yaushe, ta amsa shi da murmushi a fuskarta, ita ta fara shiga motarta shi kuma ya tsaya amsa waya.
Harta yiwa motar key tana k'ok'arin fara murza steery ta kasa, hakan yasa ta d'ora kanta jikin steering tana jin yadda zuciyarta ke tsananta bugu, "allahumma la sahala illah ma ja'altahu sahala, wa anta taja'alul hazni iza shi'ita sahala,,,,". Abinda take faman maimaitawa kenan a cikin zuciyarta.
Ayman da yake waya daga inda yake yana kallon yadda tayi ta gaban farin gilashin motarta katse wayar yayi ya taho inda take.
Knocking glass d'in yayi, ta d'ago a nutse tana k'ok'arin daidaita yanayinta, ta sauke glass d'in tana kallon shi.
"Kina lafiya kuwa auntie". Ya tambayeta da larabci.
Gyad'a mishi kai tayi tana k'irk'iro murmushin da iyakacin shi kan lab'b'anta.
Sanin lallai ba zata iya driving da kanta ba saita futo bayan ta zare keyn motar.
"Muje ka sauke ni". Ta fad'a tana nufar inda motar shi take.
Shima bayanta yabi yana girgiza kanshi don yasan lallai ba lafiya ba tunda har ta kasa driving, bazai iya tuna karo na k'arshe data tab'a shiga motarshi don ya rage mata hanya ba kasancewarta mace mai dakakkiyar zuciya, tuna wannan ya sake tabbatar wa Ayman lallai bata da lafiya sai dai kuma zurfin cikinta bazai tab'a barinta tace komai ba yanzu ko ya tambayeta.
Har suka k'arasa asibitin ba tace dashi ba shima baice mata ba. Yana gama parking ta d'auki jakarta ta futa tare da mishi addu'ar, "Allah ya kiyaye" ya amsa da "ameen". Yana d'aga mata hannu.
K'in barin gurin yayi har saida yaga shigarta ward d'in da office d'inta yake, sannan ya sauƙe boyayyiyar ajiyar zuciya yayi reverse ya futa hospital d'in.

Da doctor seera kawai suka gaisa ta shiga office d'inta ta fara aikin duba tulin patients da suke zaman jiranta.

____________★ Da yamma sauri sauri Ayman ya futo daga office saboda kada tace zata hau motar haya a yanayin da take, lokacin daya shiga clinic da yawa daga cikin ma'aikatan asibitin sun fara watsewa don yamma tayi sosai. Kai tsaye ofishinta ya nufa a ranshi yana addu'ar Allah yasa bata tafi ba.

Doctor surayyah tana kwance kan kujerar hutu doguwa da take a gefen office d'in, ba bacci take ba amma ta lula cikin duniyar tunani, tana a haka aka turo office d'in aka shigo, bata tashi ba sai bud'e idonta da tayi tana kallon k'ofar, doctor seera ce tsaye da shirin tafiya gida.
"Na d'auka ma kin tafi, amma lafiyarki kuwa?". Ta tambaya da tarin kulawa bayan ta maida k'ofar ta rufe.
Mik'ewa tayi da kyar ta zauna tace, "ban tafi ba kin ganni gaba d'aya na tashi yau bana jin dad'in jikina, kuma bansan me yake damuna ba".
"Subhanallah! Amma kika k'i zuwa kiga doctor Saleh".
Girgiza kanta tayi, "seera ba matsalar Saleh bace, wannan matsala ce da take buk'atar addu'a ki tayani da addu'a kurum".
Da kulawa seera tace, "toh Allah yayi miki maganin abinda yake damun ki,,, Naga kamar yau baki zo da mota ba ko zaki taho muje saina sauke ki".
Jakarta da wayarta ta d'auka "ina tunanin Ayman zai dawo d'auka ta saboda d'azu shiya ajiye ni, toh kada na tafi kuma yazo bai same niba ba zaiji dad'i ba". Tana rufe bakinta ana knocking k'ofa, "come in" Suka fad'a kusan a tare ita da doctor seera, da sallama a bakin shi ya turo k'ofar ya shigo.
"D'an halak yak'i ambato". Doctor saira ta fad'a tana kallon shi. Murmushi yayi ya k'arasa shiga office d'in ya durk'usa yana gaishe da doctor k'awar auntie.
Sallama ta musu don har ta kusa huce lokacin tafiyarta.
Itama surayyah bata zauna ba ta d'auki wayarta da keyn office d'in suka futo Ayman rik'e da Jakarta.
Koda suka Isa inda ya parker motarshi, shiya bud'e mata front seat ta shiga sannan ya kewaya mazaunin driver.
Suna tafe suna hira jefi jefi har suka k'arasa gida, Ayman bai rabu da ita ba saida ya rakata har part d'inta ya tabbatar ta zauna mama haleema ta kawo mata ruwa mai sauk'in sanyi tasha, har ya tafi zuciyarshi bata gama aminta da auntien tana lafiya ba, cox yasan halinta ciwo inba yaci k'arfinta ya kwantar da ita ba bata tab'a yarda ta nuna ma kowa bata da lafiya, duk a gudun kada ta d'aga musu hankali.
Kamar yadda yake lura da yanayinta haka mama haleema ma take ankare da duk wani motsinta cikin kwanakin, shiyasa a yau data gama aikinta ta zab'i kwana a gidan tare da ita, don taga yau abun Kamar yafi na kullum.
Da daddare tana kwance don yau tunda wuri ta shige bedroom ko abinci bata ci na kirki ba saboda zazzab'i daya fara taso mata.
Tana kwance taji ringing d'in wayarta, da kyar ta mik'e zaune ta jingina da fuskar gadon ta d'aga kiran.
Raihana ce ta kira ta don su gaisa, kwana biyu basu gaisa ba saboda yawon makaranta da yake cinye mata rabin lokacin aiwatar da komai.
Har suka gama wayar bata yarda raihana ta fahimci wani abu a cikin muryarta ba.

________★★★ washe gari duk inda doctor surayyah ta kaiga nuna ita d'in *JARUMA* ce saida abun yaci tura, gaba d'aya bayan tayi sallar asubah kasa tashi tayi ko daga kan sallaya zazzab'i mai zafi ya rufe ta, saboda zafin zazzab'i hak'oranta har kad'uwa suke suna dukan junan su.
Ayman da bai gama samun gamsuwa da yanayinta na jiya ba, k'arfe bakwai yana futowa wanka kayan shi kawai ya zura ko mai da turare bai sakawa jikin shi ba ya futo ya nufin sashenta.
Tun daga parlour yake sallama shiru har ya nufi jikin d'akin barcinta. Yayi bugun yayi sallama amma shiru kake ji babu alamun akwai mutum mai motsi ma a d'akin. A gigice ya tura k'ofar gaban shi yana tsananta fad'uwa.
Tana kwance magashiyan ko hannunta bata iya d'agawa. Aikuwa ya nufe ta yana kiran sunanta da gudu. Kanta ya d'ago yana faman jera kiran sunanta "Auntie! Auntie!! Auntie!!!"
Da kyar ta bud'e kwayar idonta data canja launi ta kira sunan shi, "Aaaayyyymannn".
"Na'am! Auntie me yake damun ki? Tun jiya nace baki da lafiya kika k'i fad'a mun kika ce lafiyarki lou,,,,,,".
Girgiza mishi kai tayi tana k'ok'arin mik'ewa ta zauna amma ta kasa, abinda ya sake gigita Ayman kenan har ya futa da gudu ya d'auko mukullin motarshi. Da yake mama haleema a gidan ta kwana, tana futowa don kama ayyukan gida taga giftawar Ayman da gudu, saita bishi da kallo kafun ta nufi d'akin auntien don tasan lallai daga can ya futo.
Da taimakon ta auntie ta tashi suka sauko k'asa inda Ayman ya futo da mota. Direct wani private hospital na abokin shi ya nufa da ita bayan ya kira shi a hanya ya sanar dashi zuwan su.
Suna zuwa emergency aka karb'e su hannu bibbiyu aka shigar da ita don ceton rayuwarta. Zuwa lokacin ita kad'ai tasan yadda take ta fafutuka da rayuwarta.

An d'auki awowi da yawa kafun a futo da ita a gadon marassa lafiya tana bacci. D'aki aka bata duk hankalin su Ayman a tashe sai tambayar nurses abinda yake damunta suke, har suka futa d'akin basu ce dashi komai ba abinda ya sake dagula mishi lissafi, saida wata nurse ta dawo tace yazo doctor farouk yana son magana dashi.
A hargitse ya nufi ofishin likitan ko zama baiyi ba bare a kaiga maganar gaisuwa ko jin lafiyar juna yadda aka dad'e ba'a had'u ba ya fara da tambayar, "likita me yake damunta mamana?".
Seat ya nuna mishi, "ka zauna Ayman sai muyi magana".
Dafe kanshi yayi ya d'aga kai sama cikin danne hawayen daya cika idon shi yace, "ka fara fad'a mun abinda yake damunta farouk!".
Duk yadda likita farouk yaso shawo kanshi suyi magana a nutse k'i yayi. Daga k'arshe ma sai kawai ya fara hawaye, dafa kafad'ar shi doctor farouk yayi cikin son kwantar mishi da hankali yace, "ba wani mummunan abu bane yake damunta, zazzab'ine da stress sai jininta daya hau da d'an yawa".
Cikin son tabbatar da abinda yake fad'a Ayman yace, "don Allah kada kayi kun k'arya don ka kwantar mun da hankali na rok'e ka ka fad'a mun gaskiya farouk,,,,,".
"Kaima kasan bazan fara aikata abinda kake nufi ba, wallahi zazzab'i da hawan jini shine kad'ai matsalar mahaifiyarka da bincike na ya gani".
Ajiyar zuciya ya sauke kad'an yana share hawayen fuskarshi da hankie.
Sai a lokacin ya zauna suka gaisa da farouk ya k'arasa mishi bayani.
Ranar gaba d'aya a asibitin suka wuni tare da ita ba tare da sun fad'awa kowa ba har dare.
Ko abinci babu wanda ya iya ci a cikin su tun safe har daren, basu iya samun kwanciyar hankali ba saida suka ga ta motsa ta bud'e idanunta, har rige rigen yi mata sannu suke shida mama haleema.
Bata iya amsa suba ta sake komawa wani baccin, sai a lokacin mama haleema ta d'anji kwarin gwiwa ta futa don samo musu abinda zasu ci har mara lafiyar idan ta tashi.
Ayman kasawa yayi ya tsare ko gud'a yak'i yarda ya tab'a jikin wannan baiwar Allah mai tarin sadaukarwa a gare su fiye da wadda Allah ya d'orawa duk wata uwa a duniya.
Koda mama haleema ta dawo kasa cin abincin yayi duk yadda taso ya daure ya lallab'a yaci wani abun kasawa yayi.
A daren ranar yana kallon kiran khaleefa na shigowa wayarshi akai akai amma ya kasa d'agawa.

Haka ya kwana sur bai runtsa ba kamar me gadi. Auntie bata farka ba saida iskar sanyin asuba ta kad'a.
Ayman ta fara gani gefenta ya zuba mata ido ko k'iftawa babu yana kallonta, yayin da hawayen idon shi ya fara sauka kad'an kad'an.
Hannunta ta mik'a ta kamo hannun shi cikin nata ta rintse tana girgiza mishi kai, "ka.. kwantar da hankalin ka.....".
Girgiza mata kai shima yayi ya kai hannun ta bakin shi ya sumbata tare da rik'e hannun gam gam yana zubar da hawaye.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login