Showing 225001 words to 228000 words out of 288773 words

Chapter 76 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1089

da son nemawa d'anshi aurena, sai sauban ya sauko har ya amince aka tsaida maganar auren mu amma fa ya gindaya mun tsauraran sharud'd'a, idan wani abu ya same ni ko nan da shekaru ashirin ne, kar na kuskura na taho gidan shi da sunan yaji, idan kuwa har hakan ta kasance toh lallai kada na tuna cewa ina dashi, idan kuwa har na yarda da dawowa gidan shi na zauna, toh bani ba Suraj ko y'ay'an da zamu haifa tare. A lokacin na makance kuma na kurumce Suraj da soyayyar shi kad'ai nake ji da gani cikin kwayar idona, bana kawo wata rana zata zo da har Suraj zai iya yanke hukuncin rabuwa dani.
Auren mu bai d'auki lokaci da tsawo ba akayi komai aka gama, na tare a wani sashe na cikin gidan su Suraj.
Mun shimfid'a rayuwa mai kyau da tsabta, a lokacin naga tsantsar soyayyah gurin Suraj har na sake gasgata lallai babu wata rana da zata zo har Suraj ya iya rabuwa dani.
Matsala ta farko dana fara samu dashi shine, shi ya kasance ma'abocin yawo k'ashashen duniya ni kuma ina shekara ta biyun k'arshe a karatuna, bazan iya barin komai in dinga gantalin binshi guri guri ba, sannan a lokacin sauban ya tattaro duk ribar kud'ad'ena na gado da yake juya mun ya dawo mun dasu hannuna har da uwar kud'in ma. Da taimakon Suraj daya k'ara mun wasu kud'ad'en na bunk'asa harkar kasuwancina.
Tsakanina da y'an gidan su Suraj muna huld'a amma baya baya bada yawa ko takura juna ba, na kanje sashen momy a kullum safiya mu gaisa da ita da alhaji, haka lokaci bayan lokaci har abinci nake dafawa mai kyau na kai musu, musamman alhaji dana lura yana son girki na sosai.
Muna zaune lafiya kowa da baya sona ya had'iye k'iyayyar shi in aka d'auke matar mukhtar! (Yayan su na biyu) data ke matuk'ar kishi dani kamar mijinta nake aure.
Tun dana fahimceta na sake jan jikina bana shiga harkarta, da yake ma wani lokacin tana bin mijinta Zaria gurin aikin shi sai nake mantawa da ita cikin jama'ar gidan.
Nayi aure da shekaru uku amma ko b'atan wata ban tab'a yiba, hakan yana damun Suraj don yana bala'in son yara sai dai ya shanye ko a fuska bai tab'a nuna mun ba, a lokacin na sake fad'ad'a harkokin kasuwancina har k'asashen waje nake futa nayi order kaya.
Tuni na gama karatunaa na ajiye kwalin a gefe.
Andal ma ta gama karatun ta har an saka ranar aurenta.
Lokacin bikin ya zo ban samu damar zuwa ba, saboda ya same ni cikin tashin hankalin rasuwar bango, jigo, k'ashin bayan wannan family wato tsohon ambassador Abdallah tofa, a sanadiyyar had'arin mota a hanyar shi ta dawowa daga Kano zuwa Abuja.
Mutuwar wannan bawan Allah ta gigitani matuk'a daga ni har Suraj haka muka gigice muka d'imaucewa.
Sannan mutuwarshi itace ta zamo matakin farko data fara bani matsala da mutanen gidan, saboda ganin idon shi ya kashe k'iyayya ta ga mutanen gidan wanda a bayan idon shi ta dawo.
Tun a gurin rasuwar k'anwar matar muktar ta had'u da Suraj ta mato a sonshi, musamman data fahimci yana da kud'i fiye da kaf y'ay'an gidan.
Sun had'a kai ita da yayarta inda suka fara kunno mun wuta ta gurin shi akan rashin haihuwa. A wannan gab'ar bansan ya suke so nayi ba saboda mutum bashi yake yiwa kanshi komai ba, haka Suraj ya b'ata ranshi yak'i bada goyon baya akan maganar auren da suke so mishi ya k'ara.
Haka dai naci gaba da rayuwata cikin nutsuwa da godiyar ubangiji. Ban fasa kyautatawa kowa da zuciya d'aya a gidan ba har wata matsalar ta sake tasowa akan gyaran jikin da nakeyi, nan ma Suraj da yayen shi suka dakatar da komai, a wannan gab'ar hatta momy da Fatima basu goyi baya ba.
Ban gama tserewa matsaloli a zamantakewata dasu ba har andal ta haihu muka tafi Sudan ganin ta ita da baby, haka mukayita santin baby boy kyakkyawa data samu. Bamu tafi ba saida Suraj ya cika ta da abun arzik'i, daga nan muka huce k'asashen da Suraj yafi harkokin kasuwancin shi muka sauke farali, muna sake tsananta addu'a akan samun rabo, bamu dawo ba sai bayan watanni.
A lokacin na dawo da sauye sauye jikina kuma naga sauyi a tare da mutanen gidan kansu, sai dai ban zargi komai a raina ba har Allah ya yiwa yaron da andal ta haifa rasuwa.
Suraj ya hana ni zuwa ban hanu ba saboda yadda mutuwar ta dake ni, haka na lallab'a shi na tafi bayan na yiwa mutanen gidan dana fahimci sun daina sake jiki dani ko abu na basu basa amfani dashi, kamar tsorona ma sukeyi sallama.
Sai dai abinda yakan bani mamaki bai huce ganin yadda matar mukhtar take nan nan dani ba ita da k'anwarta mai son Suraj haleema, komai zasuyi a sashena duk daba wani damuwa nake da shirgin su ko shiga ciki ba. Yawanci lokutan da haleema take zo mun gab da dawowar Suraj ne, zata ci kwalliya gwargwadon wadda tasan ni da nake matarshi zanyi, sai dai a tsarin Suraj shi mutum ne da yake rayuwarshi kai tsaye, tun farkon zuwan haleema ya nuna mun sam baya son ganinta a tare dani, saboda a lokacin har office ta bishi ta karb'i no shi duk ba sa'a bata samu fuska daga Suraj ba, shine ta sauya salo. Ni kuma wanzuwarta tare dani yakan yimun shamaki da kulawar dana saba bashi a duk lokacin daya taso office.
Wannan ya sake tunzura Suraj a ganin shi na zab'i mutanen waje a kanshi. A wannan rintsi da rashin fahimtar tafiya ta kama ni, har na tafi ba'a son Suraj ba, ko airport bai mun rakiya ba sai driver yasa ya kaini, ban damu ba saboda nasan koba komai zanyi abinda ya kamata a lokacin daya kamata ne, fushin shi kuma da zarar na dawo zai k'are komai ya huce.
Tunda na sauka a Sudan ban zauna lafiya ba, ba wai ciwo nake ji a jikina ba amma sauye sauyen da nake ji kullum k'ara ta'azzara sukeyi, koda na ba andal labari shawara ta bani kai tsaye akan naje naga likita, ita ta kaini har asibitin da take aiki. Naga likita yayi mun tambayoyi k'arshe ya dangane damun scanning.
Abun mamaki saiga sakamako ya futo da shaidar ciki na tsawon wata shidda a jikina kuma twins.
Wannan labari yayi mana dad'i sosai nida k'awata, haka mukaita farin ciki da nuna godiyar mu ga Allah, tun kafun na bar Sudan nake neman layin Suraj in sanar dashi kyakkyawan albishir bana samun shi, nayi mamaki don bai tab'a dogon fushi dani akan komai ba, naci gaba da sharewa saboda nasan da zarar yaji labarin samuwar cikin jikina farin cikin da zai riski kanshi ciki zai d'auke mishi hankali har ya manta da fushin.
Lokacin komawata gida yayi har da sati d'aya a kai ban koma ba, haka kurum nake jin kamar kar na tafi nayi ta zama tare da familyna da k'awata da aure ya sake nesanta mu da juna.
Ranar da zan tafi har a airport muna sake jaddadawa juna rik'o da alk'awarin da muka d'auka........ Haka na tafi muna kewar juna.
Lokacin dana dawo gidan Suraj baya nan, kuma koda naji dawowarshi na taho da nufin taryarshi k'in bani damar ganin shi yayi ya rufe kanshi a d'aki. Ina lissafe saida nayi kwana uku ban saka Suraj a idona ba bare na saka ran zai saurareni.
Ga mamakina na biyu haleema tunda na dawo bata zo part d'ina ba ko sau d'aya, haka yayarta ma, kowa a gidan sai wani irin bahagon kallo yake mun.
A rana ta hud'u Ina zaune cikin d'akin baccina na zabga tagumi na rasa me yake mun dad'i a duniya, hannuna rik'e da takardar sakamakon cikin dake jikina, naji an turo k'ofa an shigo da sauri na d'aga idona.
K'anwar Suraj ce fateema fuska sam ba fara'a take kallona. Banyi k'asa a gwiwa ba na tashi ina mata sannu da zuwa duk da ta shigo mun har k'arshen d'aki ba tare da neman izini ba.
Da sauri ta d'aga mun hannu tace nazo ana nema na a parlon momy na k'asa.
Na tashi jiki a sanyaye gwiwa a salub'e na tafi, kusan gaba d'aya familyn gidan sun taru a parlon banda yaran su, kowa fuskarshi a d'aure babu mai alamun walwala, akan mutum biyu idanuna suka fara sauka, haleema da take kwance kamar matacciya ba inda yake motsi a jikinta duk ta rame, sai Suraj da yake tsaye hannun shi hard'e a k'irjin shi, yatsun hannun rik'e da habarshi ya sakaye idanun shi cikin farin glass.
A nutse na k'arasa har gaban momy zan durk'usa a gabanta tayi saurin dakatar dani da fad'in, "dama kin daina wahalar da kanki wajen nuna mana ladabin banza da wofi kina cutar damu da hakan..... Abu d'aya kawai zan tambayeki shin da gaske kina da hannu a cikin ciwon haleema k'anwar Aysha?". Tambayar a bazata tazo mun, na kasa fahimtar takamaiman abinda suke nufi sai binsu da ido da kallo.
A haka wani mutumi ya shigo sanye da kayan fatun namun daji, shima yayi ta maganganun da ban fahimta ba har a k'arshe ya nuna ni yana fad'in lallai lallai saina rabu da haleema wai ni nayi mata tsafi ta kwanta ciwo.........
Haka Ina ji ina gani aka k'ulla mun sharrin abinda bansan ko meye ba, a k'arshe mutumin nan ya takura mun na karb'i wani ruwa a hannun shi na zubawa haleeema duk jikinta, sai gashi ta fara karkarwa tana yin wani irin abu har daga baya ta tashi zaune tana kuka tana tambayar a ina take. Kowa fuskarshi fal mamaki yake kallona in aka d'auke Suraj kad'ai daya kasa kallon kwayar idanuna.
Haka na durk'ushe a gurin na kasa ma kowa magana ina gunshek'an kuka da rantsuwa dede da raina Ina sanar dasu gaskiyar niba matsafiya bace.
Momy ce ta fara yin magana da cewa, "kin bani mamaki surayyah, a gidan nan mun yarda dake sai gashi a k'arshe kin ci amana, tunda muke a familyn mu bamu tab'a samun bara gurbi ba saboda duk munsan kanmu ke kad'ai ce bare.... Alhamdulillah da Allah yasa baki samu damar aiwatar da k'udurin kiba asirin ki ya tonu, kumaaa godiya ta biyu da bamu had'a zuri'a dake ba.... Suraj aiki ya rage naka ina fatan baka manta yadda mukayi da kai ba?".
Har lokacin Suraj bai d'ago daga yadda yake ba, a tunanina yana tunanin bazan tab'a aikata abinda suke zargina a kai bane, sai na nufe shi Ina ganin shi kad'ai ya rage mun, sai dai koda na durk'usa a gaban shi na dafa k'afar shi da sauri ya warce k'afar har yana had'awa da hankad'a ni nayi baya na fad'i a gurin, kafun na dawo nutsuwata zafafan kalamanshi masu kama da digar ruwan dalma sun fara ratsa dodon kunnena, "na dad'e banyi aure ba saboda tsoron kaidi da sharrin ku mata..... ke kad'ai naga haske irin wanda ban tab'a gani tare da kowacce mace ba, naga yarda nutsuwa da kwanciyar hankali ashe duk na jabu ne, a k'arshe keda nake ganin a duniya bazan samu kamar kiba kin watsa k'asa a idon wannan yardar da nayi miki, kina neman ruguza mana familyn da muka gina shi da aminci da kyakkyawar fahimta..... Hak'ik'a nayi nadamar sanin ki a rayuwataaaa, ki tafi kawai bana son sake ganin fuskarki abadaaannn....".
Lokaci d'aya tashin hankali ya diro mun wanda yasa na kasa gasgata shin da gaske ne duk miyagun maganganun nan suna futowa ne daga bakin sooraj? Na kasa yadda.
Ban sake tabbatarwa ba saida yaje part d'inshi ya d'auko duk wasu kadarorina da takardun makarantata da suke hannun shi ya d'anka mun cikin hannuna.
Jakar kayana dama tunda na dawo Sudan ban cire komai ciki ba itama ya d'auko mun ita a yadda take ya koreni daga gidan su yana sake tabbatar mun babu ni babu shi.
Cikin dauriya da k'arfin gwiwa na dubi Suraj a harabar gidan su y'an aikin sun taru suna kallon abinda yake faruwa, don sake tabbatar da abinda nake gani a karo na uku nace, "tabbas zan tafi kamar yadda ka buk'ata sooraj, sai dai ba zan tafi da dakon nauyin auren ka ba......".
A firgice raihana ta birkito zaune har littafin yana fad'uwa k'asa ta dafe kanta da hannunta tana fad'in, "aaaa'aaaaa auntieee". Yadda tayi d'in ya nuna kamar komai yana faruwa a kan idonta ne a lokacin.
Khaleefa da barci ya fara d'aukan shi sautin maganarta tasa shi mik'ewa zaune yana kallonta.......

*Kuyi hak'uri da jina shiru gaba d'aya kwana biyu ban samu zama ba sai yau, Ina godiya da jinjina gare ku masu bibiyar littattafan in-identical twins👍muna matuk'ar alfahari daku😍😍 k'auna mai tarin yawa*

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*

_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page sixty four6️⃣4️⃣


"Are you okay?" Ya tambayeta yana kallonta, bata bashi amsa ba ta damk'e littafin a hannunta ta shiga kitchen tasha ruwa ta tsaya tana maida numfashi.
Koda ta futo khaleefa yana zaune yana duba wayarshi, itama ta d'auki tata wayar ta duba time sai taga lokaci yaja da yawa, dab ake da kiran sallar subh.
Abin mamaki ashe raba dare tayi tana karatu?
Tattare yanata yanata tayi ta shige d'akinta, khaleefa ma d'akin nashi ya tafi.
***** zaune take gaban dressing mirrow d'aure da towel, powder ta shafa da wetlips ta zirara kwalli a idonta sannan ta shirya cikin dogon wando tight sai riga half bubu matching colour da wandon, ta sake gyara gashinta ta yafa madaidaicin gyale ta yane kanta zuwa kafad'un ta, tayi kyau na hak'ik'a cikin sauk'ak'k'en dressing d'inta.
Cikin takun da yake bayyana asalin wacece ita ta futo daga d'akin, yadda ta tsammata khaleefa bai futo ba, hakan yasa ta nufi d'akin shi ta kwankwasa.
Ya bata izini ta tura k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama, yana kwance ya k'udundune jikin shi gaba d'aya fuskarshi kad'ai ake gani. Tunda ta shigo ya kasa d'auke idon shi a kanta tamkar wadda ta shigo da sirrin magnet, ita kuwa kanta a k'asa ta k'arasa kusa dashi, nan ma saida ya lumshe ido yana shak'ar daddad'an k'amshin ta daya cika d'akin.
Gaishe shi ta fara da tambayar jikin shi, ya amsa still yana kallonta yama kasa d'auke idon shi, ganinta yake kamar mutum ta daban sabuwa ba raihanan daya saba rayuwa da ita gida d'aya ba.
"Na kawo maka breakfast d'inka nan?". Ta tambaye shi da murya mara amo.
Nan ma khaleefa saida ya lumshe ido yana jin farmakin da muryar take kai mishi all over his body, yasan muddin yaci gaba da kallonta da jinta very close to him zata iya rufto mishi da ko wanne tunani bahagon tunani kanshi.
"Ki taimaka mun da had'in ruwan wanka,,,, kada suyi zafi da yawa". Cikin amsar umarnin shi ta gyad'a mishi kai ta mik'e.
Yanzun ma saida tayi ta santin d'akin wankan kafun ta aiwatar da abinda ya kaita ta futo.
Yana kwance inda ta barshi ta futo ta fad'a mishi ta gama, ya gyad'a mata kai yana jiran ta k'arasa futa a d'akin saboda ba komai jikin shi sai boxer, wankan yake son shiga tun d'azu amma ya kasa tashi har Allah ya kawo ta.
Har ta murda handle zata futa ya kira sunanta, "Raihana". Bata amsa ba amma ta juyo, "ki jirani a dinning few minute zan futo".
Ta gyad'a mishi kai ta k'arasa fucewa.

Yadda ya fad'a..... tana zaune a dinning rik'e da wayarta tana tab'a chat ya futo cikin shadda milk sai zabga k'amshi yake, Koda ta kalle shi suka had'a ido cute smile ya sake mata, itama ta mayar mishi da raddin nata daya bayyana hak'oranta farare tass a waje.
Ya k'araso yaja kujerar da take fuskantarta ya zauna, ita tayi saving d'inshi sannan tayi saving kanta, suna karya kumallon amma ya kasa d'auke kanshi daga kanta, barin ma yatsun hannunta da sukayi maroon suka haska shiny skin hands d'inta,,,,,
Gaba d'aya abincin bai huce rabin plate yaci ba yaji ya futa a ranshi, kwalliyar raihana ta yau ta fara sauya mishi yanayi daga na khaleefa zuwa na matured Abdallah...... Duk yadda yake son d'auke kanshi a kanta kasawa yayi, haka ya dinga kallonta kamar zai cinyeta d'anye. A rayuwar khaleefa yana son shiga irin wadda tayi a jikin mace, shiyasa yake ganinta local a duk lokacin da ta kirma wannan uban hijabin ko ta saka atamfa, gani yake kamar rashin wayewa ne yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login