Showing 231001 words to 234000 words out of 288773 words
Chapter 78 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
a waje, misali kamar Laila da khaiz, Romeo da Juliet....... Kowacce soyayyah akwai k'alubale mai girma a cikinta, amma wadda ta girmi kowacce yanke alak'ar masoya take💓💓💓)
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page sixty five 6️⃣5️⃣
Koda raihana ta gama karantawa shiru tayi tana tunanin komai daki daki cikin kwakwalwarta, bata tashi a gurin ba taji shigowar khaleefa gidan, ta duba lokaci da sauri gab ake da sallar magrib inda Allah ya taimaketa ma tana da sauran lokaci tasan bai fiya cin abinci a farkon dare ba, kamar yadda ba yaci tsakiyar dare, a tsarin rayuwar khaleefa komai nashi a tsare yake.
Bathroom ta shige ta d'aura alwala ta futo ta shimfid'a darduma ta tada kabbarar sallah.
Tana cikin sallar taji ana knocking k'ofarta, tasan khaleefa ne tunda dashi kad'ai take rayuwa a gidan, bai shigo ba har saida ta idar da sallah ta bud'e k'ofarta, sanye yake da jallabiyyah fara sol saboda tsabar yunwar da yake jima ya kasa tsayawa da k'afafun shi sai jingina yayi, tana bud'e k'ofar bai jira umarninta ba ya shige d'akin, (dama ya tsaya ne gudun kada ya shiga baisan a yanayin da zai same taba...)
Raihana ta bashi hanya tana kallon yanayin shi, direct kan gadonta ya zauna ya had'a kanshi da gwiwa, ta k'arasa kusa tana tambayar, "kana lafiya kuwa?".
"Abinci... Kawo mun abinci raihana yunwa nake ji kamar naci babu...".
Shiru tayi tana kallon shi a ranta tace, "Toh kawai kaci babun mana....". Ta fad'a k'asa k'asa ba tare da tasan maganar zucin da take ta futo fili ba, ya d'ago da mamaki ya kalleta sai tace, "Babu abinci a gidan yau sai dai na dafa maka mafi sauk'i yanzu....".
"Yaaa Salam! Meyasa yau? Ko shiryawa zaki shirya muje Eve Eno?".
"Har na dafa fa, it will not take much time bari nazo....". Ta k'arasa fad'a tana juyawa da nufin futa... Batasan lokacin daya mik'e ba sai ji tayi kawai ya rik'o hannunta ta baya.
Ta juyo tana kallon shi, ya marairaice mata fuska kamar zaiyi kuka, "put down your hijab kawai, cox I can't wait har sai kin dafa wani abu....".
Cikin kwaikwayon salon da yayi magana raihana tace, "Ni bana jin zuwa ko'ina zaka iya tafiyarka kai kad'ai".
Muryarshi k'asa k'asa yace, "kina d'aukan komai wasa, am serious wllh ji nake kamar zan fad'i".
"Nafa ce kayi tafiyarka, me yasa ma sai dani". Ta fad'a cikin shagwob'a shagwob'a.
"Saboda jikina babu k'arfi, in muka tafi tare zaki iya taro ni idan na tafi zan fad'i".
Ya k'arasa fad'a yana sake hannunta hango hijab d'in nata can k'arshen bed.
Da kanshi ya warware shi ya zura mata fuskar sama a k'asa (irin yadda tsofaffi sukeyi🤪)
"Muje mana please Allah in na kasa tafiya zaki san yadda zakiyi dani".
"Toh a haka zan tafi kuma.... kalli yadda kasa mun hijabin fa?". Ta sake fad'a cikin shagwob'a.
Khaleefa jingina yayi da bango yana kallonta da lumsassun idanun shi, yama kasa bud'e bakin shi yace wani abu saboda tsabar yadda yake jinshi. Gaba d'aya ya sakankance zai dawo ya tarar ta gama abinci as usual, shiyasa ko lunch baiyi ba dama breakfast yau a gurguje yayi shi.
Ganin da gaske zai iya kaiwa k'asan sai itama ta zama serious ta gyara hijab d'in suka futa.
Inda Allah ya taimake su a farkon layin suka samu motar haya suka shiga.
Ko a motar ma sai jujjuya kai yake har suka k'arasa inda zasu ya biya kud'in motar da katin shi suka futo.
Bai zauna ba saida yayi order abincin da zasu ci. Suna zama aka gabatar musu da komai, aikuwa Bismillah kawai yayi ya fara cin abincin sauri sauri..
Bai lura da raihana bata ci komai ba saida ya kusa cinye rabin plate d'in gaban shi, ya kalleta sannan yace, "sorry ban tambaye ki abinda zaki ciba nayi order, me zaki ci".
Girgiza mishi kai tayi, "Ni yunwata bata kai taka ba, zan iya jira har sai na dafa da kaina in mun koma gida".
Shiru yayi yana nazarinta kafun ya k'arasa cin adadin wadda zai tsaida mishi yunwar da yake ji a lokacin, duk yadda yake matuk'ar jin dad'in abincin su yau yaci ne kad'ai alallalurati, sam jin abincin nasu yayi a wani bai bai, ba taste kamar ba'a yi shi da maggi ba. Banda yana matuk'ar jin yunwa ba abinda zai sashi cin abincin.
Bayan ya gama sun futo suna tafiya ya fahimci raihana tana mishi dariya ciki ciki, kamar ya shareta sai kuma ya kasa had'iyewa ya dakata da tafiya ya tsare ta da idanu yace, "mahaukaci na zama kike mun dariya kuma?".
Had'iye dariyarta tayi tana kallon shi kamar za tayi dariyan tace, "Man tunowa nayi fa d'azu kace wai in kazo fad'uwa na tare ka? Koda wane k'arfin.....". Ta k'arasa fad'a tana sakin sabuwar dariya.
Shi kanshi dariyar yake yi saboda a lokacin yayi maganar ne bilhak'k'i da iya gaskiyar shi.
Haka suka taru suna dariya mara sauti a gurin kafun khaleefa ya fara tsagaitawa yana kallonta da yadda dariyar ta bala'in sake futo da sirrin kyawunta.
Ba tare daya ankara da abinda ya keyi ba cikin shagala a kallonta ya fara matsawa kusa har saida yaje daf sai saukar hannun shi kawai sukaji yana shafa siraran lab'b'an ta.
Take ta had'iye dariyarta ta maida fuskarta guri d'aya tana kallon shi da jin yadda yake kewaya d'an yatsar shi saman lips d'inta, lokaci guda kuma tsigar jikinta ta fara zubewa.
Shima sai lokacin ya lura da abinda yake yi ya koma baya cikin matuk'ar jin nauyinta yaci gaba da takawa, itama tabi bayan shi har inda zasu samu motar da zasu koma gida.
Daga nan tafiyarsu taci gaba da kasancewa silently har suka k'arasa gida.
****Bayan ta gama shirinta na kwanciya bacci, addu'o'in ta tayi ta tofe duka kusurwowin d'akin, taja bargo ta rufe har kanta, hannunta ta kai ta shafa lips d'inta kamar yadda khaleefa yayi d'azu, take kuma murmushi ya sub'uce saman lab'b'an nata, ta sake k'udundune kanta a ciki.
*****Shi kuwa khaleefa yana zaune yana operating system d'inshi moment d'insu na d'azu ya shiga dawo mishi, ya tuna saura k'iris ya aikata mummunan kuskuren da bazai tab'a iya yafewa kanshi ba.... Mtss! Yaja tsaki a fili yace, "Wai me yake k'ok'arin sauya kane? Man ya kamata ka kama kanka sam ba haka ya kamata ka mu'amulanceta ba".
Ya k'arasa fad'a yana sake jan wani tsakin, ya rufe laptop d'in duka ya k'arasa hawa kan gadon ya kwanta ya rufe idon shi......
*Nigeria*
Ayman ya futo cikin shirin futa office, kitchen ya shiga ya samu mama haleema tana ta k'ok'arin had'a mishi karin kumallo, tana ganin shi ta fad'ad'a fara'ar fuskarta tace, "ba dai har ka futo ba, yau na makara kaga shayin kawai na dafa abincin bai kammalu ba, gashi kai baka iya cin bread ba bare ka had'a da tea, in kuma kana da sauran lokaci mintuna k'alilan ya rage na gama".
Fuskarshi fad'ad'e da fara'a yace, "kada ki damu mama zan sha iya tea d'in ma in naje office saina samu wani abu naci insha Allah".
Mama haleema tace, "aini bana son naji kace zaka karya a office d'in nan Ayman, saboda ba karyawan kake yiba saika kawo uzurin aiki yasha kanka, da dai ka bari na k'arasa ko tafiya dashi ma sai kayi, indai baso kake kuma doctor surayyah taci tara taba in ta samu d'an amanarta ciki fal yunwa".
Dariya ya sake yi yace, "kada ki damu had'a mun shayin kawai, ko gaisawa ma ba muyi ba". Ya fad'a yana durk'usawa har k'asa ya fara gaisheta, ta amsa tana kiciniyar had'a mishi shayin sauri sauri tana sake jaddada "Allah daka jira kaga Amanar ka auntie ta bani, in ta same ka da yunwa naci Amana kenan....". Dariya ya sake yi ya karb'a shayin yana sake cewa, "ba zata gani ba sai dai ma taga nayi k'iba da kumatu".
Duka sukayi dariya, Ayman dai yana daurewa ne kawai amma cike yake da kewar mahaifiyarshi, ba zaice mama haleema bata k'ok'ari ba, itama tana iya nata banda rauni na shekaru daya tab'a ta, amma lallai auntie bata tab'a bari ya futa war haka bai karya ba har ranar aiki kuwa.
Haka dai ya gama lallab'awa ya fuce a gidan.
Da yamma ya taso office yana driving yana bin wak'ar balaraben mawak'in nan maheer Zayn, Yana son zuwa duba su iya yau ko don ya rage zaman kad'aici da tunani a gida. Sai dai ba zai tafi musu haka ba, hakan yasa ya tsaya a store d'in da yake kan hanyarshi ya musu shopping na kayan ciye ciye dai dai gwargwado.
Ya shiga anguwar yana tafe a hankali yana gaisawa da mutane har ya k'arasa k'ofar gidan.
Da malam ya fara cin karo a k'ofar gidan tare da bak'i, bayan yayi parking ya futo ya k'arasa suka gaisa da malam da bak'in shi sannan ya shiga gidan.
Iya tana zaune a k'ofar d'akinta tana aikin tuk'a tuwo, baki kawai ta saki tana kallon shi har ya k'araso kusa da ita ya zauna, "wannan kallon fa kamar kin fara rasa idanun ki?". Ya fad'a da sigar zolaya.
"Kaci gidan ku kaida rasa idanun, yo ba dole na kalle kaba kaida kayi mana yajin aiki kamar mun yi maka kashi a gado".
Murmushi yayi yace, "yajin aiki sai kace wasu gwamnati? Hutu naje yanzu kuma na dawo, gashi nazo ma a dai dai". Ya fad'a yana nuna tukunyar tuwon gabanta.
"Aifa gashi na gani". Ta fad'a tana dariya, shima dariyar yayi suka gaisa yaji lafiyarsu ita da malam sannan ya bata kayan daya taho musu dashi.
Ta karb'a tana mishi godiya da sanya albarka.
Sunci gaba da hirar su har aka kira sallar magrib malam ya shigo suka d'aura alwala tare suka huce masallaci.
Basu dawo gidan ba saida sukayi sallar isha'i.
A parlon iya suka zauna suna tab'a hirar su shida malam inda yake tambayar yaushe zaiyi aure, yayi murmushi yace, "mai ran k'arfe da sauran lokaci".
"Kullum haka kake cewa toh Allah yasa muna da rabon gani".
"Insha Allah da ranku da lafiyarku malam, to su waye ma mad'aura auren?".
"Wanda Allah ya d'orawa duk wani hak'k'i a kanku mana, ko baka fatan ganin su a rayuwarka....?".
Ayman ya gyara zama yace, "malam su waye hakan kenan? Dama muna da wasu a hak'k'u bayan ku".
Malam yace, "kwarai kuwa, wanda suke da hak'k'i fiye damu ma, in lokaci yayi kuma zaka gansu".
Ayman yayi shiru yana nazari kafun ya sake cewa, "toh Allah ya bamu ikon gani".
Malam yace, "ameen".
A haka iya ta same su ta kawo musu tuwon data tuk'a miyar zogale suka fara ci Ayman na zuba mata santi.
Yaci da yawa kuwa don saida yaji kamar wanda yake ci zai dawo mishi ta hanci sannan ya hak'ura.
Ranar bai bar gidan ba sai wajen goma na daree, yana zuwa gida shirin kwanciya bacci kawai yayi ya kwanta,sai dai bacci yak'i yiwuwa sai tunane tunanen duniya.
Mik'ewa yayi zaune ya kunna hasken d'akin ya d'auko wayarshi ya fara neman layin auntie don ita kad'ai yake rab'a yaji farin ciki a rayuwarshi......
Tana fara ringing ta d'auka, kamar yana gabanta ya fara da cewa, "I miss you mom, yaushe zaki dawo neee".
Daga ta cikin wayar tace, "Sai ranar daka girma ka daina shagwob'a".
"Haba don Allah ni wace shagwob'a kuma nayi? Mom please idan baki dawo cikin satin nan ba zan ajiye komai na biyo ki...".
Murmushi tayi tace, "Ayman so kake na taho ban gama rok'ar maka abinda nake son ka samu a rayuwarka ba".
"Auntie tunda kika haife mu kike mana addu'a baki tab'a gajiyawa ba, hakan yasa rayuwarmu ta tashi cikin godiyar Allah, toh meye bamu samu ba da kike mana rok'on shi a saudiyyah har wannan lokacin?".
"Cewa zakayi meye baka samu ba don shi d'an uwan ka ya samu! Matar aure ta gari wadda zata soka ta kyautata maka gwargwadon iyawarta...".
Shiru yayi ya kasa cewa komai har auntien ta k'ara cewa, "yanzu dai insha Allah Ina tafe cikin kwanaki biyu masu zuwa....".
Da sauri yace, "da gaske!".
"Da gaske insha Allah".
Cikin farin ciki yace, "I love you Mom! Sai yanzu zan iya bacci da naji wannan daddad'an albishir d'in, Allah ya kawo ki lafiya.....".
"Daina saurin murna Ina dawowa a fai fai zan kasa ka ko za'a samu wadda zata d'auka tunda kai har yanzu ka kasa tsaida ranka guri d'aya, so be ready...." Ta k'arasa fad'a tana d'an dariya k'asa k'asa.
Cikin zallar sangarta yace, "kema haka zaki ce ko? Haka fa malam ma d'azu ya takura mun..... Shikenan tunda kun daina sona....".
"Ohhh! Kaina bisa wuyana, nasan kai d'in mai farin jini ne kona kasa ka a fai fai ma ba mai d'auka".
"Anya kuwa yabo na kikayi Auntie.....".
Dariya suka sanya kusan a tare.
Sun jima suna hirar su kafun suyi sallama ya ajiye wayar yana murmushi, a haka bacci b'arawo ya sad'ad'd'afo ya sace shi.
Cikin kwana ki biyun kuwa doctor surayyah ta dawo, lokacin Ayman yana office kiran wayarta ya same shi.
Da matuk'ar farin ciki ya d'aga yana fad'in, "welcome back lovely Auntiena".
"Thank you son! Mintuna goma na baka".
"Gani nan zuwa insha Allah". Ya fad'a tare da ajiye wayar.
Uzuri ya bayar a rubuce ya futa daga companyn gaba d'aya.
Cikin mintuna k'alilan ya Isa airport ya taryo ta.
****Suna tafe a mota yana ta bata labarin yadda yayi kewarta har suka k'arasa gida, mama haleema tayi mamakin ganin auntien a bazata ta kuma ji dad'i kwarai.
Nan da nan ta shiga shirya mata abinci da abun sha iri iri a gabanta, saboda tsabar gajiya doctor surayyah kasa cin komai tayi, don ta taho da tarin bacci a idonta. Koda da dare yayi ta samu tasha yoghurt mai sanyi da dambun naman da Ayman ya siyo mata, bata tsaya sallama da kowa ba ta shige d'akinta sai bacci.
Washe gari abokan business da aikinta suka dinga zuwa mata sannu da zuwa, haka sauran mutanen gari ma da take mak'otaka dasu duk sun turo mata da sak'on barka da zuwa wasu kuma sunzo da kansu.
Da daren ranar su malam ma suka zo, suka jima suna hira har malam ya samu damar mata tuni akan maganar daya tab'a yi mata game da y'an uwan mahaifin su khaleefa, ya had'a da mata nasihar da baya gajiyawa a kullum idan ya samu zama da ita, a wannan karon sosai naseehar ta shige ta har da hawaye, a lokacin ta fad'awa malam ita tuni tayi nadama ta hak'ura, ta fahimci abinda ya dinga nusarshe da ita tsawon shekaru, sai dai ta d'anka aikin fallasa gaskiya a hannun mafi hikima da k'uruciyar da zata iya fuskantar k'uruciya y'ar uwarta ta bayyana mata komai yadda zata fahimta.
Malam yaji dad'i ya dinga sanya mata albarka da mata fatan gamawa da duniya lahira, da zasu tafi ta had'a musu tsarabar duk data siyo da sunan su da kuma sak'on khaleefa da raihana gare su.
Washe garin ranar data dawo da safe Ayman zai futa office ta bashi dabino dasu bagaruwa da sauran kayan chocolate tace ya biya ta gidan su raihana ya kaiwa su hibba.
Baiyi mata musu ba ya karb'a zai cika umarninta, a zuciyarshi yana ayyana in ba don ita data Isa dashi ba, baya jin wani zai sashi yaje k'ofar gidan su raihana a halin da yake ciki yanzun.
Tsaye yayi a k'ofar gidan yana tuna abubuwa masu girma da nauyi gami da rad'ad'i a cikin zuciya,,,,, cikin irin tunanin ya tuna had'uwar shi ta k'arshe da raihana, ranar da taje k'unshi Zahra saloon har ma ta soya mishi wainar fulawa