Showing 102001 words to 105000 words out of 288773 words

Chapter 35 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1107

merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page twenty nine2️⃣9️⃣


Saida ya jinjina girman alk'awari kafun yace, "toh insha Allah". Gyara zamanta tayi kafun ta fara mishi magana cikin nutsuwa, "shin wani abu ya faru da khaleefa gab da tahowarku Nigeria? Ina nufin meye musabbabin wannan sauyin nashi?". Ahmad d'auke wutaa yayi kafun ya nisa can yace, "eh to gaskiya a halin yanzu ba zance miki ga takamaiman damuwarshi ba, saboda kinsan dama shi ba mutum ne me yawan magana ba musamman akan damuwar shi, Auntie bazan b'oye miki ba ko a makaranta sai nayi futu futu na b'ata rai yake fad'a mun matsalar shi ko ciwon shi, shiyasa ni har muka dawo banga wani sauyi a tattare dashi ba gaskiya". Shiru tayi tana kallon Ahmad da sake nazarin shi, tana ganin kawai bazai fad'a mata bane saboda sirrin khaleefan ne da bai kamata kowa yaji cikin suba, koda yake akwai inda dole sai yayi bayani ai. Sai ta sake cewa, "hakane! Sai abu na biyu, rannan yana bacci da rana naga hoton wata kyakkyawar yarinya a wallpaper shi wacece ita?". Wayyoh Allah! Ahmad ya fad'a a ranshi a zahiri kuma yak'e yayi yace, "yarinya kuma? Ya kamanninta suke....". Shi kanshi baisan bakin shi ya furta hakan ba, sai tayi murmushi mai kyau tana sake tsare shi da ido, "kana nufin y'an matan da yawa kenan?". Da saurin shi yace, "a'a Auntie ba wai haka nake nufi ba, sai dai ni ban sanshi da wata mace ba gaskiya indai koba......". Sai yayi shiru ya saci kallonta, ta zuba mishi ido kuwa taji ta inda zai tsaro ta anan kuma. Sai yayi murmushin yak'e ya sake cewa, "eh yarinya d'aya nasan shi da ita gaskiya, kuma ba wata kwakkwarar alak'a a tsakanin su gaskiya in aka d'auke ta friendship da kasancewarta neighbor d'inshi a gidan da muke zaune". Sai ta murmusa.
"Ni kuma dawowar khaleefa yace mun akwai wata yarinya da yake so zai aura... Ita kuma wacece?". Ta sake jeho mishi wata tambayar, Ahmad saida yaji Kamar ya dafe k'eyar shi ya saita a guje da yaji wannan tambayar itama, don har ga Allah baisan cewa khaleefan ya yiwa auntie irin wannan maganar ba, sai dai ya daure da iya gaskiyar shi yace, "wallahi Allah ni bansan da wannan maganar ba, bansan akwai wadda zai yiwa maganar aure a kusa ba.....". "humm" kawai ta fad'a ta mik'e tsam ta shiga bedroom d'inta, ba jimawa ta futo da car key damk'e a hannunta ta zauna inda ta tashi, "sai abu na k'arshe cikin ku waye jami'in k'irk'iro maganar komawa Berlin aikin nan.... Shin me yasa ba zaku dawo gida Nigeria ku taimaki al'ummar mu da ilimin da kuka samu ba?".
Shiru yayi wannan karon har Saida ta sake mishi magana sannan yayi gyaran murya ya fara yi mata bayani da gundarin gaskiya, "a gaskiya bazan b'oye miki komai ba wannan aikin wani likitan Nigeria da yake aiki a k'asar ne ya bamu shi, saboda munyi practice da yawa a gurin shi ya Kuma yaba da jajircewar mu a lokacin, shine ya zab'e mu mu bakwai zamuyi aiki tare dashi na tsawon shekara biyar don mu sake gogewa a fannin aikin kula da duk abinda ya shafi k'ashin d'an Adam. Sunyi alk'awarin zasu bamu wadataccen kud'in da zamu tsira da abubuwa da yawa a k'asar mu, sannan idan mutum yaso zai zama parmanent doctor a gurin, idan baiso ba kuma sai yayi tafiyarshi k'asar shi bayan cikar wad'an can shekaru, sai dai mafi muhimmanci da Jan hankali gare mu duka shine, mun samu damar aikin nan bisa jajircewar khaleefa da kwazon shi, a yau idan kika nuna rashin amincewa kan komawarshi Germany toh yana nufin muma babu maganar aikin mu gaba d'aya, sannan shi khaleefa aikin nan ba wai sam ya d'ad'ara shi da k'asa neba, saboda indai matsalar kud'i ne bai kasance mutum mai handama da son abun duniya ba, yaji zai amince ne base on two main reasons, na farko yana da b'oyayyen burin shi da yake son cimma a Germany da bansan ko akan meye ba, na biyu cikin wad'an da mukayi karatu akwai wanda suka samu nasarar kaiwa wannan mataki k'ark'ashin scholarship, wannan damar itace kad'ai hanyar da zasu samu rufin asiri har su taimaki y'an uwan su su samu su tallafi wasu kafun lokacin da zasu bar k'asar ko suci gaba da zama, khaleefa yana ganin idan yak'i amincewa asibitin suka rushe upper da suka bamu kamar ya rugujewa su Muhammad kwarin gwiwa da burin da Suka ci na rayuwar su ne gaba d'aya......". Sai ya durk'usa k'asa gabanta kan gwiwowin shi yace, "don girman Allah auntie, kada ki hana khaleefa aikin nan munyi alk'awarin da zarar mun gama five years d'innan ba zamu sake zaman koda minti d'aya ne a k'asar Germany ba zamu tattara mu dawo gida, muma burin mu a amfana da abinda muka karanta bawai mu yita k'arawa mai k'arfi k'arfi ba".
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tace, "tashi zaune Ahmad ka daina durk'uso haka a k'asa". Sai ya mik'e ya koma mazaunin shi kanshi a k'asan d'akin yayi jigum yana jiran yaji hukuncin da zata yanke. Cikin taushi da sanyi yanzun ma take magana, "kamar yadda na fad'a mishi kaima Zan maimaita maka,,, wallahi babu inda khaleefa zai d'ara muddin bai futar da matar aure ba....". Shiru Ahmad yayi yana nazarin ta yanda khaleefa zai futa daga wannan d'aurin goron mai dabaibayi da auntie tayi mishi. Ita kuwa mik'ewa tsaye tayi ta ajiye mishi mukullin motar hannun ta gefen shi tace, "kyautar ka ta murnar gama karatu cikin nasara...". Bata jira jin abinda zaice ba ta shige d'akinta ta rufo, ta zauna gefen bed tana tunanin zurfin ciki irin na Suraj da khaleefa ya gado tass! Yanzu meye lefin bud'a baki yayi mata irin wannan bayanin da Ahmad ya mata, a wasu lokutan kalami masu dad'i kan sa mutum yaji zuciyarshi tayi sanyi har ya sauka daga k'adamin da ya hau na tsauri duk tsananin shi kuwa a lokacin.
Ahmad kuwa Mukullin data ajiye ya d'auka yana dubawa, sai ya mik'e tsaye fuskar shi washe da fara'a ya furta, "motar da ake yayi nake burin siya tunda daddy yak'i yarda ya siya mun". Sai ya futa daga parlon da sauri don ya nunawa khaleefa ya taya shi murna da godiyar da auntie tak'i bashi damar yayi mata.

_toh mubi hajji Ayman mana👉🏻_

Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya dinga jan motar shi a wannan yammaci yana bin kira'ar shuraim dake tashi cikin suratul Maryam har ya k'arasa gidan su nuriyyah, a k'ofar gida yayi parking yau ya kwankwasa k'ofa, wani da yake musu aikace aikace kamar yaron gida yazo ya bud'e mishi yana mishi sannu da zuwa, ya amsa da yauwa sannan ya k'arasa shiga cikin harabar gidan, inda suka saba zama ya tsaya ya kira wani matashi da yake durk'ushe gefe guda yana musu wanki, ya k'araso gaban shi ya russuna, "gani ranka shi dad'e". "Nur tana nan kuwa?". Ya tambaye shi, "eh tana nan". Ya bashi amsa a ladabce, "okay d'an yimun magana da ita". Ya bashi umarni. Ba musu ya d'auki hanyar cikin gidan. Bayan mintuna k'alilan ya dawo ya shaida mishi mammie tace Nur ba zata futo ba, Sam Ayman bai fahimci abinda aiken yake nufi ba don haka sai ya tambayi yaron, "ka fad'awa mammie injini kuma?". "eh yallabai na fad'a mata". Sai ya zaro 1k a aljihu ya bashi yace su raba shida d'an uwan shi, ya russuna yana godiya ya karb'a ya tafi.
Ayman kasa tafiya yayi ya kuma kasa shiga ciki, sai yaci gaba da tsayuwa a gurin yana ta tunane tunane har haeydar ya dawo, bayan ya daidaita parking ya futo hannu ya mik'awa Ayman suka gaisa yana mishi complain akan duk lokacin da yazo sai yayi ta tsayuwa a waje kamar wani bak'o, kanshi ya shafa ba tare daya ce komai ba, haeydar har zai huce sai ya tambaye shi, "to tasan kazo ma kuwa? Kwana biyu ban san meya samu wayoyin suba ko lalacewa sukayi ni ban sani ba dai amma in na kira su bana samun su, nasan kaima baka samun Nur a waya ko?". Gyad'a mishi kai Ayman yayi yace, "gaskiya kam, nima bana samun ta sam, yanzu kuma nazo ance mammie tace ba zata zoba, toh ina tunani ko bata fahimci nine nazo ba,,,,". Da mamaki haeydar ma yace, "a'a mammie da kanta kuma yau? Waya fad'a maka?". Ayman yace, "wancan da yake wanki". Kwala mishi kira haeydar yayi, ya taho da hanzarin shi, cikin b'acin rai haeydar ya fara mishi fad'a, "wato kaima ka fara k'arya irinta sahabi ko? Yaushe mammie tace maka Nur ba zata zoba kasan waye wannan kuwa?". Cikin tsoron haeydar d'in yace, "don Allah kayi hak'uri wallahi na fad'a mata ita da kanta tace a fad'a mishi Nur ba zata zoba...". Zai sake yin magana Ayman ya dakatar dashi, "kaga jeka abun ka nima bari nazo na tafi". Da sauri haeydar ya sake dakatar dashi, "a'a Ina ganin bata fahimta ba fa, kaima laifin ka da idan kazo kake cogewa a wajee, mu shiga ciki...". Ayman kamar yace a'a sai kuma ya fasa don yana son tabbatar da lallai mammie bata gane shi Ayman d'in ake nufi ba. Lokacin da suka shiga da sallama parlon da ita suka fara cin karo hakimce kan kujera tana kallo a tivi. A k'asa ya zauna ya fara gaisheta, ta amsa mishi kadaran kadahan, har lokacin bai kawo komai ba, haeydar ne yace, "tun d'azu fa yazo mammie yana tsaye a varender wai kince Nur d'in ba zata futo ba". Kallon haeydar tayi sannan ta dire k'afarta duka k'asa tace, "hakane da gaske nina hana Nur futowa.....". Cikin katse hanzari haeydar yace, "mammie why??". Saita galla mishi harara, "dakata mun malam" ta maida dubanta kacokan ga Ayman tace, "Kai mahaifiyar ka bata fad'a maka an tashi maganar aurenka da Nur a aiki ba....?". Saida gaban shi ya yanke ya fad'i, haeydar ya zaburo zaiyi magana ta daka mishi tsawa, Dole yaja bakin shi ya tsuke. Ganin kan Ayman d'in ya d'aure saita fara yi mishi Dalla dalla yadda zai gane, "Naga kana kallona a bai bai bari nayi maka gundarin bayani irin wanda surayyah ba zata tab'a zama tayi maka ba, shin tun tasowarka zaka iya kirga mun suwa da waye dangin ka? Sannan tsakanin ka da Allah ka tab'a ganin hoton mahaifin ku da tace ya mutu tun kafun kuzo duniyaaa ko a hoto? Ko kuwa ta tab'a baku labarin wani abu daya shafi mahaifin ku wanda ya shud'e lokaci mai tsawo a rayuwar auren su? Shin kuna ganin kunyi min adalci na d'auki Nur na baku babu cikakken asali ko tushe, ku haifi yara gaba su tashi a tantal batete.... Ya zamo dole a wannan karon idan har tana sonka da Nur ta futo da abinda take b'oyewa a kanku tsawon shekaru ciki kuwa harda rashin had'a dangantaka kota farce tsakanin ku da iya da kuke yiwa kallon kakarku......".
Tunda ta fara magana Ayman yaji Kamar an d'auki guduma an buga mishi a tsakiyar kanshi, wani abu mai girma da d'aci yana mishi yawo a kanshi zuwa gangar jikin shi, take kwakwalwar shi ta fara tariyo mishi abinda ya faru shekaru aru aru baya lokacin suna yara, yadda sukaita rigima da wani yaro d'an gidan su abulkhair daya fara kiransu da sunan shegu,,,,, ya tuno yadda auntie take shiga tsananin tashin hankali a duk lokacin da aka danganta su da wannan mummunar kalma, sun girma suna ganin kamar sun girmi waccen kalma komai ya huce sai gashi mutanen da basu tab'a zato ba suna neman dawo musu da ita cikin rayuwarsu rana tsaka,,,,, yoo meye banbancin ba'a san uban ka ba da shege, ai kawai don kar a futo a kira ka da shege ne direct aka sakaya da haka...... Lokacin daya mik'e ko gaban shi baya iya gani sosai ya futo daga cikin gidan yana tafiya har ya fuce, da kallon tausayi haeydar ya bishi, lallai ba don tsoron mamie ba daba abinda zai hana shi bin bayan shi, amma ya fahimci mamie yau tana sama ba sauk'i in ya takura da yi mata shishshigi komai ma zai iya faruwa.
A daddafe Ayman ya shiga cikin motarshi ya bata wutaa, tafiya yake ba don yasan inda zai nufa ba, a cikin ranshi babu abinda yake kai komo sai raihanatu, haka yayi ta bulayi a gari kafun caan yayi wani tunaniii, sai kawai ya d'auki hanyar zuwa gidan kaamil, wani abokin aikin shi da yayi aure ba jimawa, kamar a mafarki haka kaamil d'in ya ganshi bayan ya kira shi a waya yace mishi yana k'ofar gida, murmushin yak'e kawai yake mishi a lokacin da yake mishi tayin shiga cikin gidan bayan ya gama yaba k'ok'arin shi na iya gane gidan bayan sau d'aya ya tab'a zuwa tun ana aikin gidan. "Kaga a gurguje nake ka shigo nan muyi magana ni bazan shiga ciki ba...". Ayman ya fad'a mishi kawai, sai ya bud'e front seat ya shiga, a gurguje suka gaisa kaamil na tambayar shi ko lafiyar shi, yamutsa fuska yayi kad'an yace, "kawai headache! Yauwa kwanaki mun fara magana dakai a office akan friendship da love relationship, shine nazo yanzu ka k'arasa warware mun yadda abun yake". Galala kaamil ya saki baki yana kallon shi, Shi tuni har ya manta sun fara wata magana irin haka banda yanzu daya tuna mishi, don a lokacin katse shi yayi bai saurare shiba Sam. Sai ya tambaye shi, "ko zaka sake dawomun da farkon bayanin, nan Ayman ya dawo mishi da bayanin daki daki kamar yadda ya fara mishi bayani a wancen lokacin, saida ya dire Aya sannan kaamil yace, "na gane komai, amma akwai y'an tambayoyi da zanyi maka, wacce kafi kishi tsakanin k'awar ka da budurwarka?". Shiru yayi kafun can yace, "toh aini bansan kishin ba saboda Nur bata tab'a yin wani saurayi bayan niba". Kamil yace, "okay ita waccen k'awar fa?". Da sauri yace, "kai ita aure ma zatayi". Sai kaamil d'in yace, "yawwa ya kake ji a duk lokacin daka ganta da saurayinta....?". Saida ya rintse ido saboda tuno da abinda yake ji d'in, Cox abinda yake jin bamai dad'i bane, nan ya fad'a mishi dallah dallah har kawo yanzu ma daya daina kulata baki d'aya, Saida kaamil ya gama jin bayanan shi gaba d'aya sannan yayi murmushi yace, "abu mai sauk'i Sam ba budurwarka kake soba, wannan k'awar taka kake Soo tunda dad'ewa kai kanka bakasan da haka ba,,, exchange d'in matsayi ka musu ita da budurwarka da babu komai a ranka game da ita sai shak'uwa da zumunci na y'an uwan taka, Amma fa ba makawa daga dukkan alamomin da suka bayyana wannan k'awar taka da kakewa text kullum safiya kake so, gwara kaje ka shaida mata tun da wuri kafun lokaci ya k'ure maka Ayman, a k'arshe ka k'are da auren matar da baka da wani buri ko fata a kanta gaba d'aya". Cikin tausayin kanshi da tunanin yadda zaiyi babun bad'ilahu ya kife kanshi a sitiyeri yace, "lokaci ya jima da gama k'ure mun kaamil, da naasani tun farko na saurare ka a lokacin daka fara yimun wannan bayanin, watak'ila da yanzu ni zata aura nan da kwanaki k'alilan,,,,, koda yake itama ba lallai ta iya aurena ba......". Ya k'arasa fad'a yana jujjuya kanshi jikin sitiyerin motar. Kaamil ga zaton shi Ayman yana cikin damuwar rashin raihana ne shiyasa yake duk wannan sambatun, sai ya dafa kafad'ar shi da son ganin ya K'arfafa mishi gwiwa yace, "kayi hak'uri abokina indai ba'a d'aura auren ba har yanzu kana da sauran dama, za'a iya zuwa wajen d'aurin aure ma a fasa indai rabon kace ita d'in, Soo kada kaji komai abokina kada kayi saurin sarewa". Gyad'a mishi kai yayi kamar gaske duk dashi yaji a jikin shi ma sam hakan ba mai yiwuwa bane.
Sai ya k'ak'alo murmushi kamar gaske yace da kaamil d'in zai k'arasa gida, nan sukayi sallama yana k'ara kwantar mishi da hankali suka rabu. Koda Ayman yayi gaba kamar gaske kasa ci gaba da tukin yayi saboda nauyi da duk wata gab'a ta jikin shi tayi, sai ya Parker gefen hanya ya fashe da wani kukan zallar bak'in ciki da tashin hankali, da gaske mammie ce yau take jifan shi da mummunar kalmar rashin asali da bakinta, itace ta hana mishi auren Nur, a k'arshe gashi y'ar tata ma ba ita yake soba raihanatu yake so, raihanatun data jima dayi mishi nisa sai dai ya d'aga kai ya hangi k'urar ta bayan ta huce. Sai ya fara dukan sitiyerin da hannun shi yana kuka had'e da girgiza kai.
Saida ya kwashe a k'alla wasu dak'ik'u masu yawa a gurin yana kuka sannan ya samu sassaucin yanayin da yake ciki, yaja motar a hankali yabar gurin.
Lokacin daya koma gida auntie bata nan sai bai bi takan kowa ba ya shige d'akin shi ya rufo k'ofa.
Shi kuwa Ahmad koda ya futo a parlon d'akin su ya samu Khaleefa zaune yana jiran shi, mukullin mota ya d'ora mishi kan cinya, "kyautar da auntie ta bani". Sai ya d'auka gami da taya shi farin ciki.
Nan sukaita hirar su, yawan cima akan abinda ya faru suna makaranta ne na dariya ko ban haushi suke tattaunawa, duk don ya d'aukewa khaleefa hankali akan abinda suka tattauna da auntie, baisan bama shi ko a jikin shi bai damu ba ko kad'an, tunda yasan dole akwai abinda zasu tattauna da bata son yaji shiyasa tace ya basu guri.

Ta b'angaren auntie kuwa tana shiga d'akinta sauya kaya tayi daga na zaman gida marassa nauyi zuwa nad'in lafaya, yau ko jaka bata d'auka ba sai mukullin mota da ATM card.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login