Showing 243001 words to 246000 words out of 288773 words
Chapter 82 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
abinda yake damun ka, am yauwa gobe in na tashi makaranta akwai inda zani idan ba damuwa".
"Bakisan gari bafa?". Ya fad'a yana kallonta.
"Insha Allah ba zan b'ata ba". Ta bashi amsa kanta s k'asa.
"Toh Allah ya kaimu". Ta amsa da "ameen".
Sunci gaba da zama har dare ya sake nisa sosai bacci yaci k'arfin idon su suka yi sallama kowa ya tafi makwancin shi.
*****Washe garin ranar raihana tayi shirinta cikin doguwar rigar material mai multi color, yau bata samu damar tashi da wuri ba shiyasa ko lokacin data futo bata samu khaleefa ba tuni yabar gidan.
Bata futa makaranta ba saida ta gama gyara abinda ta lalata a gidan.
Ko a makarantar ma Allah Allah ta dingayi a tashi taje gurin doctor andal taji abinda ta shirya mata. Aikuwa suna futowa lectures ta kira likitan, sukayi maganar da bata huce mintuna biyu ba ta k'arasa titi don tarar abun hawa bayan ta rufe fuskarta da mask gudun had'uwa da khaleefa.
A gaban harabar asibitin ta tsaya ta kira likitan ta fad'a mata ta iso, ba jimawa wata nurse tazo ta tafi da ita.
Lokacin data isa offishin likitar tana tsaye jikin wawakeken windown daya kewaya ta gefen titi.
"Sannun ki da zuwa raihanaaa". Ta fad'a da hausa da kyar kamar me koyon magana, murmushi tayi ta k'arasa cikin kujerun da suka bada round kamar gurin lunching haka da hutawa ta zauna, "sannu doctor ya aiki?". Ta tambayeta da harshen jamus da take koyo yanzun.
"Alhamdulillah" ta fad'a tana gabatar mata drinks.
Ruwa kawai tasha kad'an ta sake maida hankalinta ga likitan.
"Muna magana jiya bamu k'arasa ba gashi yanzu yamma tayi kada ya riga ki komawa gida yasa hankalin shi a kanki ko".
"Ehhh toh amma maganar da kika ce zamuyi fa".
"Zamu k'arasa ta waya amma kafun ki tafi zamu je dake ki duba wani patient".
Ba musu raihana ta amsa mata, Suka mik'e kusan a tare zasu futa, har sunkai k'ofa andal ta tuna mata ta sake rufe fuskarta.
A nutse suka dinga hucewa andal tana gaisawa da mutane tsilli tsilli har suka Isa wasu private rooms, Saida ta tsaya ta fara neman izini aka bata kafun ta tura k'ofar ta shiga da sallama raihana na biye da ita.
Mutumin yana zaune hannun shi d'aya sak'ale d'ayan kuma rik'e da cup yana shan wani abu, yayinda wasu ma'aikata mata har biyu suke goge goge duk daba wani datti cikin d'akin.
Ajiye kofun hannun shi yayi ya zare farin tabaran idon shi yana yiwa andal maraba, su kuma ma'aikatan suka fara fucewa bayan sun gaishe da likitan.
Raihana zuciyarta saida tayi darrr kamar ta faso k'irjinta ta futo lokacin da tayi arba da mutumin, kama take gani ta zahiri tsakanin mutumin dasu khaleefa.....
Har andal ta samu guri ta zauna saman wasu kujeru tana tsaye bata motsa ba har saida tayi mata magana sannan ta sauke ajiyar zuciya ta k'arasa kusa da ita ta zauna.
Saida suka fara gaisawa da andal tayi mishi sannu sannan raihana ma ta gaishe shi ta mishi sannun. Ya amsa yana kallon bak'uwar fuskar bai daice komai ba.
Doctor andal ta mishi tambayoyi game da lafiyarshi sannan suka mishi sallama suka futo, daga nan kai tsaye inda zata futa a asibitin sukayi, ta rakata har inda zata hau mota sannan tayi mata magana, "wannan mutumin dana kaiki kika duba shi yanzun, yana da alak'a ta kusa da mahaifin khaleefa amma shi kanshi khaleefan bai sani ba...... Nasan ba saina jaddada miki wannan maganar ta zamo sirri tsakanin muba?". Raihana ta gyad'a mata kai, sai taci gaba da cewa, "yazo an mishi aiki ba tare da kowa cikin ahalin shiba sai escort d'inshi da nurses da suke kula dashi, ba don kuma bashi da family ba sai don ya tsame hannun shi daga duk wani abu daya shafe su, a tak'aice ina son ki d'auki nauyin abincin da zaici daga yanzu har zuwa sati biyun da zai gama jinya ya koma k'asar shi, Ina fatan hakan zai samu ba tare da khaleefa yasani ba......".
A wannan karon saida tayi nazarin abubuwa da yawa cikin zuciyarta sannan ta amsa mata da tabbacin duk yadda sukayi dashi zata fad'a mata in ma zai hana.
Suka k'arasa sallama ta tafi gida zuciyarta fal tunane tunane, da tambaye tambayen da ba mai bata amsa.
Ranar khaleefa bai dawo da wuri ba sai dare, Koda yaci abinci bai tashi a parlon ba har ta futo rik'e da littafinta da waya, ta zauna k'asan carpet nesa dashi tace, "am yau.. ma...ina son k'arin bayani akan wani abu da ban fahimta ba".
Ya d'ago idonshi a nutse ya kalleta, zuciyarshi na raya mishi abubuwa da yawa game da ita, "let's see" ya fad'a tare da mik'a mata hannu ta bashi littafin.
Ba musu ta mik'a mishi ya ajiye k'asa yana dubawa, Koda ya fara mata bayani tattare gaba d'aya hankalinta da nutsuwarta tayi kanshi har ya gama ta mishi nata bayanin gwargwadon fahimtarta. Ya jinjina mata sosai kamar waccen ranar.
Har ta tashi zata tafi ya tambayeta, "kin fara aiki da computer ki kuwa?".
Ta juyo tana kallon shi tace, "a'a".
"Meyasa?". Ya sake tambayar ta just enjoying how she's starring at him cike da kunya data kalle shi sai ta waske ta hau wasa da yatsun ta.
"Ban iya aiki da ita sosai ba".
"D'auko tawa muga".
"A ina kenan,".
"Shiga d'akina zaki ganta". D'akin ta nufa ta d'auko bayan ta ajiye littattafanta a gurin, yana zaune inda ta barshi ko sanyin parlon baya ji.
Koda ta bashi system d'in kusa dashi ya nuna mata ta zauna, ya fara operating gently yana nuna mata komai da bayanin amfanin shi yadda ya kamata.
Saida ya tabbatar duk bayanin da yayi sun shiga kanta sannan ya d'ora mata computer kan cinyarta bayan ya d'ora pillow a k'asa.
"I'm all eyes".
Murmushin daya k'ara mata kyau tayi ta fara bin komai daki daki tana satar kallon shi duk. Idon shi a kanta har tazo shiga wani folder da yayi creating yana ajiye sirrikan da baya son wani yasani sai ya durk'uso kanta ya kewaya hannun shi na dama ta d'aya gefen ya d'ora saman nata hannun.
Abinda ya assasa mata ja baya da sauri saboda wani yarrr da tsigar jikinta tayi, cikin sa'a kuwa sai gata a jikin shi gaba d'aya. Wani irin yanayi khaleefa ya riski kanshi a ciki musamman da k'amshin jikinta ya shige shi sosai, koda ta motsa da niyyar guduwa ture laptop d'in yayi daga jikinta gaba d'aya ya kewaye hannayen shi ta saman cikinta ya cusa fuskarshi cikin gashinta yana shak'ar wani ni'imtaccen dawwamammen k'amshi da yake tashi a gurin.
Tsabar rik'on tsaurin daya mata yasa duk jikinta ya d'auki rawa, idonta ya firfito waje, musamman da taji ya tuje gashin kanta yana yamutsawa.
Kwata kwata khaleefa baisan abinda yake aikatawa a lokacin ba har saida wayar shi tayi ringing..... Da sauri ya raba jikin su kamar wanda ya aikata wani mummunan laifi haka ya dafe kanshi yana jin haushin kanshi da kanshi.
Ita kuwa a gurguje ta tattara komai nata ta bar mishi gurin.
Tana shiga d'akinta Ahmad ya kira wayar khaleefa yace ayi mata godiya.
"Godiyar me?". Khaleefa ya tambaye shi.
"Kasan maganar da mukayi da kai jiya a office?".
Khaleefa yace, "rigimarku da madame?".
"Exactly! Toh jiya Ina zuwa na tarar an gyara komai hadda tarya ta musamman daga Yasmine, abinda aka jima ba'a yi mun ba, tun a lokacin nasan ta had'u da nagartacciyar data bata shawara ta kwarai, yau da safe kuwa sai take fad'a mun raihana ce tayi mata nasiha shine jikinta yayi sanyi ta k'uduri aniyar gyarawa, har da bani hak'uri..... Gsky man ba zance maka komai ba sai ka k'ara rik'e matarka da kyau, Cox yarinyar tasan abinda takeyi a rayuwa, idan har ka sake ka rabu da ita zakayi babbar asara don yarinyar nan d'aya ce tamkar da million".
"Nagode!". Shine kad'ai abinda khaleefa ya fad'a ya ajiye wayarshi gefe yana nazarin maganganun Ahmad, ya fahimci a kullum Ahmad baya jin dad'i idan bai yabi raihanan ba.
******** Kamar kullum, Amna ta futo cikin shirin futa makaranta, kamar koda yaushe ta tsaya tana knocking k'ofar Saleema duk da tasan ba bud'e mata zatayi ba, ta d'auki adadin wasu lokuta a gurin har daga k'arshe ta hak'ura ta fidda rai ta juya da nufin tafiya.
Har ta juya zata tafi sai kuma dai tayi wata shawara, ta koma da baya ta buga apartment d'in da yake kusa da ita, wani matashi d'an asalin k'asar yazo ya bud'e, Suka gaisa Amna ta tambaye shi ko yana jin motsi a part d'in da yake mak'otaka da nashi? Yayi Jim kafun yace, "eh amma ba wai sosai ba".
Godiya ta mishi da sallama ta juya taci gaba da tafiya har ta futa daga cikin gidan gaba d'aya.
Yau har a makarantar damuwarta ga k'awarta Saleema tafi ta kullum, har Allah Allah ta dingayi su tashi lectures tayi abinda ya kamata don ceto rayuwar k'awa d'aya tilo da bata da kamarta kaf fad'in Germany........
Kuyi hakurinn dai gaashi nan ba editing
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page sixty nine6️⃣9️⃣
Wayarta ta ciro a jakarta ta fara laluben layin Ahmad, har zata kira shi saita tuna indai bai tashi office ba bazai picking call d'inta ba, sai kawai ta rubuta mishi gajeren sak'o kamar haka, "Assalam! Kayi hak'uri na sake dawowa gare ka da k'ok'on barana, ka taimaka kasa abokin ka yayi wani abu akan case d'in k'awata cox kullum abun gaba yake sakeyi..... Nagode".
Lokacin da sak'on ya riski Ahmad ya futo sallar la'asar ne, jimm yayi yana nazari kafun ya sauƙe ajiyar zuciya, gaba d'aya komai ya hargitse musu baisan taya zai fara b'ullowa al'amuran gaban shiba, ga case d'in Saleema! Ga wani babban case daya tattara gaba d'aya hankalin shi yanzu akai, ga khaleefan kwana biyu abubuwa sun mishi yawa, ya tabbata ko za'a samu taimakon khaleefa ba yanzu da gaggawa ba.
*Nigeria*
Kamar koda yaushe yauma ta tashi tun kafun gari yayi haska ta had'a breakfast irin wanda tasan Ayman yafi so, ita kuma ta fara shirin futa office, zuwa lokacin da Ayman ya gama shirin shi ya futo da niyyar karya kumallo tuni ta ratayo Jakarta da duk abinda tasan zata buk'ata ta futo.
Mik'ewa yayi tsaye yana kallonta yace, "dama ba kin daina zuwa office ba?".
"Yaushe na fad'a maka haka? Ni hutu na d'auka kuma tun last week ya k'are"
Nan take ya had'e fuska, "gaskiya ni bana son aikin nan Auntie, tun muna yara fa haba.... Kinyi abinda kikayi Allah ya bada lada yanzu kuma lokacin hutawarkine.....".
Fuskarta sam ba alamun wasa itama tace, "Toh ubana mai cikakken iko dani ai saika hana ni zuwa ko?".
Ta fad'i haka tana nufar k'ofar futa daga d'akin kai tsaye, da sauri ya riga ta Isa gurin k'ofar ya tura da bayan k'afar shi ya marairaice mata, "please mum aikin nan ya k'are haka in dai baso kike......".
"Indai baso nake raina ya b'aci ba? Ayman zan sassab'a maka fa idan baka futa a hanyata ba wallahi kaji na fad'a maka".
K'asa yayi da kanshi kamar baiji abinda ta fad'a ba.
"Nace ka bani hanya na huce!". Ta fad'a a tsawace cikin fushi.
Wayarshi kawai ya ciro ya fara neman layin khaleefa saboda wannan yak'ine da bazai iya shi shi kad'ai ba saida taimakon d'an uwa d'aya tilo.
A lokacin khaleefa yana zaune a dinning zaiyi breakfast, sai satar kallon k'ofar raihana yake ko zai ganta, don tunda wannan abun ya faru suka shiga wasan b'uya da ita, kwata kwata bata yarda su had'u.
Yayi mamakin ganin kiran Ayman da sanyin safiyar nan, ba zai iya tuna when last sukayi waya da safe ba.... Koda yayi picking yaji dalilin kiran mamakin shi gushewa yayi take kuma yanayin shi ya nuna zallar b'acin rai. Daga ta cikin wayar yanajin maganar da auntie take cikin zafi zafi, "Ayman abinda baka tab'a yi dani ba zamu fara yau? Saboda ubanka khaleefa yana zuga ka dama shi baya ganin girmana kaima yake son kabi layin shi ku juya mun baya gaba d'aya ba?". Khaleefa ya dafe kanshi saboda furucinta yayi mishi girma a zuciya da kwakwalwa.
"Bata wayar". ya fad'a cikin bada umarni.
Koda Ayman ya mik'a mata wayar k'in amsa tayi sai sababin fad'a kawai take kamar zata ari baki, sai ya mayar da wayar kunnen shi, "tak'i karb'a fa".
"Naji maida wayar handsfree".
yayi kamar yadda khaleefa ya bashi umarni.
"Please ki saurari abinda zan fad'a, don Allah ki zauna muyi magana ta fahimta ba don niba ba don halina ba Auntie please am begging you....".
"Khaleefa! Ya kamata ku shiga taitayin ku.... Tun kafun kusan kanku nake aikina kuma, saboda ku ba fasawa zanyi ba tunda bada k'afar kowa cikin ku nake tafiya ba....".
Shiru duk sukayi suna ci gaba da sauraron fad'an da takeyi tuk'uru rai b'ace, sukan manta rabon da suga b'acin ranta bare fad'an ta irin haka.
"Ayman bud'e mata k'ofar ta tafi zamuyi magana anjima". Abinda kad'ai khaleefa ya fad'a ya katse kiran ya kife wayar saman table da yake gaban shi.
Shima Ayman kaucewa yayi daga hanya ya hard'e hannun shi a k'irji jikin shi a sanyaye, ko fuskarta ya rasa zarrar kallo.
Har ta bud'e k'ofar zata futa sai kuma ta koma da baya cikin parlon ta zauna ta rabka uban tagumi.....
Ayman ya nufi inda take a sanyaye zai durk'usa gabanta tayi saurin dakatar dashi ta hanyar daka mata tsawa, "tafi ka bani guri".
"Auntie am.....".
"Ka tafi nace!!!!". Ta sake fad'a tana nuna mishi hanya.
Wannan karon har saida ya razana saboda yadda tayi maganar. Sukuku ya fuce a parlon don in yaci gaba da takurata zata iya mishi komai yadda ta d'au zafin nan.....
Ko breakfast bai yiba ya d'auki jakar shi da mukullin motarshi ya futa a gidan.
Khaleefa kam ci gaba da zama yayi wayarshi nata ringing ya kasa d'agawa har aka fara danna k'ararrawar k'ofa ba k'auk'autawa. Abinda ya sashi mik'ewa ba tare daya shirya ba ya d'auki duk abinda yasan zai buk'ata ya futo zai futa daga gidan, yanzun ma saida ya sake satar kallon k'ofar raihana, kafun ya d'auki k'aramar papper yayi rubutu gajere ya ajiye mata k'ofar d'akinta.
Yana murd'a k'ofa ya fara da sauraron mitar Ahmad, "kaifa wani lokacin baka yiba wallahi, gaka ga wayar ka kasa picking Allah ka sauya hali".
Shafo sumar kanshi yayi bisa al'adarshi yace, "sorry nayi hakane da nufin zaka iya tafiyarka".
"Au haka ma zaka ce?".
"A'a nifa don kada kayi late nace haka, but am really sorry".
Sai a lokacin suka gaisa suka fara takawa har inda motar Ahmad take.
Ko a hanya suna tafe Ahmad na mishi mitar motar da yak'i mallaka, shi dai sam bai kula shiba cox inda sabo yaci ace ya saba da jin magana d'aya a gurin Ahmad d'in, shi kuwa sam bai damu ba yana ganin k'asar daba dawwama zaiyi cikin taba, baya ga haka ma motar haya a garin bata da banbanci da motar gida, and shi yanzu matsalolin gaban shi sun take komai da bashi da muhimmanci da bai zama mishi dole ba.
Raihana ta futo cikin shirin doguwar riga maroon colour, tayi rolling kanta da wadataccen gyale, tana d'ora k'afarta taci karo da takardar da khaleefa ya ajiye, saita durk'usa ta d'auka ta fara dubawa, "here's my no, call me".
Guri d'aya ta samu ta zauna tana tunanin mai yiwuwa har tayi k'undunbala bala ta danna mishi kira, tayi rashin sa'a lokacin wayar bata kusa dashi, saita rubuta mishi gajeren sak'o, "kamar yadda kaso, na kira baka yi picking ba....".
Bayan ta gama aikinta kamar kullum yau ma ta shirya tray guda na shayi da lunch ta d'auki wayarta da jakarta ta futo a nutse daga gidan bayan ta sakaye rabin fuskarta a zuciyarta tana addu'ar Allah yasa ta dawo kafun dawowar khaleefa don yau taso yin late.
Direct ta d'auki hanyarta, yau ko ta offishin likitar bata biya ba ta nufi d'akin majinyatan, tayi knocking, bayan jimawarta a tsaye aka bata izinin shiga, ta murd'a k'ofar a nutse bakinta d'auke da sallama.
Yana kwance yana duba magazine ta