Showing 66001 words to 69000 words out of 288773 words

Chapter 23 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1088

kwanaki biyu jikin khaleefa ba wani sauk'i, Dole Ahmad ya d'auko katifar shi da wasu cikin kayan sawar shi ya dawo nan yana kula dashi, jinya yake sosai kuma yana yin jiki, gashi ya rufe wayar shi Ahmad ma baisan inda ya wulla taba, yak'i yadda suje asibiti haka yak'i yadda y'an gidan su su sani, har cewa Ahmad yayi in ya fad'a musu bai yafe mishi ba, gashi cikin kwanakin sai damun shi Ayman da auntie suke a waya, tun yana d'agawa ya fad'a musu k'arya har k'aryar shi ta k'are ya daina d'agawa ma, gashi kullum ba sauk'i a ciwon nashi sai abinda ma yayi gaba, ko abinci baya iya ci sai ruwa da tea. Sosai Abubuwa suka taru suka yiwa Ahmad yawa, ya daina zuwa makaranta da clinic sai yini tare da majinyacin shi. Khaleed ya shigo sai biyu yana duba shi, shi kanshi ya tausaya da yaga halin da khaleefan yake ciki a lokacin, ya basu shawarar su tafi suga likita tunda su abun yafi k'arfin su. Ahmad yayi na'am da shawara hakan yasa ya kashe wayar shi gaba d'aya ya tattara nutsuwar shi wajen ganin ya zai shawo kan khaleefa har ya amince?


Saleema kuwa kwananta biyu tana jinya a tsaitsaye gashi bata da kowa da zai taimaka mata, ita da sauk'i bata kwanta kamar khaleefa ba amma fa ciwon kai kamar tayi hauka wanda yawan kuka ya haddasa mata, da kyar take iya jan jiki tayi wanka ta samu abinda zata ci ta sake komawa ta kwanta, tuni ta ajiye komai a gefe tana ji da kanta. Yadda take son khaleefa ya huce duk tunanin ta, ita kad'ai tasan daurewar da take wajen ganin ta k'arasa datse alak'ar su. Babu wanda take iya kulawa cikin y'an gidan su, haka wayar zata k'araci ring ta katse ba tayi picking ba. Tunda khaleefa yazo ranar da sukayi maganar nan bata sake ganin shi ko ji daga gare shiba, tasan dama mutum ne mai zuciya da komai, ba so ba tana ganin ko rayuwar shine zai iya sadaukarwa da dai ya wulak'anta. Tana cikin y'an tunane tunanen ta wayarta ta kad'a alamun shigowar sak'o, kamar ta share sai kuma ta d'auko tana dubawa, "nayi alfahari da samun ki matsayin matar aure na a farkon alak'ar mu, ashe mafarki nake. Na soki hadda hasashen irin yaran da zamu haifa ashe shifcin gizo ne, Sam ban d'auka ba zamuyi rayuwa tare dake k'ark'ashin inuwa guda ta aure ba, shin Saleema dama mutum na iya yin mafarki ido bud'e? Ashe masoyi zai iya rabuwa da masoyin shi akan dalilin da bai taka kara ya karya ba? Shin ni kike so dama ko asalina? Na kasa fahimtar ki har yanzu Saleema, don Allah ki wayar mun da kai na da yake cikin duhun rashin sani.......".
Murmushin takaici kawai tayi ta fara mishi refly kamar haka, "tabbas ka fad'i gaskiya, sai dai ba kai kad'ai ka shiga cikin duniyar mafarki ba hadda ni, na fara mafarki hadda yaudarar kaina akan abinda sam ban fahimce shi a dai dai ba, Abdallah duniya taci gaba, kan mutane ya waye, idan baka sani ba Ina son ka san cewa yanzu da uba ake ado, ko yau ka nemo asalinka Saleema a shirye take ta aure ka, babu shi kuma yana nufin babu kai ba Saleema da soyayyar ta har abada".
Tana sending massage d'in ta d'ora wayar saitin zuciyarta ta rintse idonta ta fashe da wani irin wahalallen kuka, she's suffering for all dis she's doing......


@@@@@@@@@


Kusan haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin tashin hankali da bak'in ciki, sun kasa fahimtar juna yayinda suke wahalar da kansu don ganin sun yak'i zuciyoyin su wajen ganin sun cire son juna daga ransu gaba d'aya, musamman ma Saleema da tafi shi shiga tashin hankali a al'amarin. A wata ranar asabar da yamma ta kasa jurewa ta lallab'a bayan tayi wanka ta futa da dafa bango taje apartment d'in Amna, tana zaune tana waya da y'an gidan su a lokacin, kamar a mafarki haka taga Saleema tsaye cikin halin ciwo, da sauri Saleema ta k'arasa jikinta ta rungume ta tana fad'in, "ki yafe ni Amna". Amna ma rungume ta tayi a jikinta tace, "me ya faru kuma Saleema?". Da kyar taja k'afarta ta zauna k'asa wanwar ta tattakura ta rushe da kuka mai ban tausayi da al'ajabi a gurin Amna. Sai duk ta gigice tana tambayar ta shin me yake faruwa dake? Me akayi miki. Kuka kawai takeyi ba amsa har Saida tayi mai isarta, tasa Amna ta bata ruwa tasha ta d'an samu nutsuwa.


@@@@@@@@


_Gida Nigeria_

Auntie ce zaune parlon sameera tayi shiru cike da damuwa tana nazarin maganganun k'awar tata, "yanzu kina ganin zuba ido zanci gaba dayi kusan sati banji daga khaleefa ba, shi kanshi abokin nashi ya daina d'aga wayata yanzu ko na kira ma bata tafiya, fisabilillah haka zan zuba ido yara su b'ace a wata k'asa?". Auntie ce meyin wannan maganar cikin damuwa.
Sameera da take sauraronta cikin tausayawa da kulawa tace, "ba haka nake nufi ba k'awata, Ina nufin ki nemi iyayen Ahmad kiji ko akwai wani abu da yake faruwa suka b'oye miki in yaso in kika ji wani abu da bai gamshe kiba sai ki ajiye komai kije har k'asar ki bincika". Gyad'a mata kai tayi cikin gamsuwa, sai yanzu ta gane abinda k'awar tata take nuna mata tun d'azun. Sameera taci gaba da kwantar mata da hankali har zuwa lokacin da taji d'an sanyi a ranta. Shaheeda ce ta shigo parlon da sallama, suka amsa suna kallonta, (doguwar budurwa ce kyakkyawa ba laifi suna d'aukar kamanni da Nur amma tafi Nur cikar jiki da dogon hanci sai hasken fata data k'ara da mai, sai dai budurwa ce ma'abociyar nutsuwa da aji, kallo d'aya mutum zai iya gane hakan, bata da yawan fara'a haka bata da d'aurarriyar fuska tsaka tsakiya, a rayuwarta ma ba wanda yafi ganin fara'ar ta kamar mamin su sai ko Auntie da tasu tazo d'aya da yayarta khadeeja, Cox shaheeda tana son mutum d'an gayu mai kyau, kamar dai auntien). Sanye take da riga har gwiwa da skirt mai tsaga a baya, tayi d'aurin ta simple mai kyau ta yafa siririn gyale da takalmi da jaka. Yadda take tafiya cike da yanga da yauk'i kad'ai ya isa yasa ta d'auki hankalin maza da yawa.
A k'asan k'afar Auntie ta zauna tana gaishe ta, auntie ta k'ara fad'ad'a fara'ar fuskarta ta amsa tana tambayar ta kwana biyu, tace, "kwana biyu naje gurin auntie suhaila ne zan mata hutu". Auntie tace, "Eh mammie ta fad'a mun". "Okay to Ina can ma tayi miscarriage shine ta k'arawa hutun nawa tsayi".
"Ayyah Allah ya maida alkhairy duk mammie ta fad'a mun har munyi waya da itama na mata sannu".
"Okay" ta k'ara fad'a. Har zata tashi sameera ta yiwa surayyah inkiya da ido tayi mata magana, sai tayi saurin kallonta tace, "Toh ni yanzu ko sai zuwa yaushe za'a zo ayi mun kwana biyu?". murmushi tayi tace, "insha Allah in mun samu hutu sai nazo miki auntie". "Kamar nan da yaushe kenan zaku samun hutun?". Shiru tayi tana nazari kafun tace, "nan da 3 months dai".
Zaro ido auntie tayi tace, "3 months sunyi yawa shaheeda ina laifin ma kizo mun end of this month, da kaina ma zanzo mu tafi". Wani murmushin ta sake yi tace, "Allah ya nuna mana auntie, Mamie Nur ta dawo kuwa?"
Sameera tace, "eh tana ciki kinsan ta da bacci". Auntie tace, "kamar dai Ayman kenan? Ko wane irin zama za'ayi ma ni surayyah". Sameera tace, "wallahi kuwa suje can su k'arata dai, in ma yini zasuyi bacci duk babu matsala". Sukayi dariya su duka. Hucewa shaheeda tayi ciki da salon tafiyarta.
Ajiyar zuciya sameera ta sauke tace, "kinga ta amince da yake tana sonki, shiyasa nake ji a jikina ke zaki iya shawo kanta ta amince cikin sauk'i tunda taku tazo d'aya, kinga da yadda taje gurin suhaila kuwa? Wallahi saida ta had'a da mijinta da yaran ma duka sannan".
Auntie tace, "ai ki kwantar da hankalin ki insha Allah duk zasu amince, shima khaleefan irinta yake yadda kika ga shaheeda haka yake, sai ya kwana biyu a d'aki lokacin da suna secondary, daga sallah sai cin abinci ke futo dashi, kuma shi ba kamar Ayman ba, baya bacci sai uban research akan duk wani abu da ya shafi physiotherapy, cikin irin binciken ne ya nemo wannan makarantar da suke yi ta Humboldt a Berlin, bai samu nutsuwa ba kuma saida ya tafi". Sameera tace, "Allah sarki khaleefa ai ankusa gamawa a tattara a dawo gida Nigeria a fara aiki kuma". Auntie tace, "aikuwa kam, har nayi magana da doctor salihu ya tabbatar mun ana yunwar masu irin kwalin su a k'asar nan, muddin wannan course d'in da suke yi yanzun sakamakon shi yayi kyau toh tabbas sun samu aiki sun gama, sai sun zab'i state d'in da zasuyi aikin ma".
Cikin jin dad'i sameera tace, "Masha Allah! Allah ya amince ya basu dukkan nasara".
Sun sake hira a tsaitsaye duk akan had'in auren da zasuyi tsakanin khaleefa da shaheeda, tuni sun gama tsara komai khaleefa kawai suke timming ya dawo k'asar asan wadda ake ciki. Shine dabarar auntie na janta gidanta end up month dai dai da lokacin da zai dawo, tasan bazai tab'a cewa shaheeda bata yi mishi ba, don ta futa irin wadda suke so a wannan zamanin.

_wannan kenan_


_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page 1️⃣9️⃣


*Germany*

Saleema kuwa saida ta nutsu bayan Amna ta kwantar mata da hankali da kalamai masu taushi sannan ta kwashe komai daya faru tsakanin ta da khaleefa ta fad'a mata, shiru Amna tayi lokaci d'aya kanta ya kulle ta rasa ta yadda zata kamo bakin zaren, "Ni na tab'a jin labari irin naku ma kuwa Saleema? Ya tashi ba dangin uwa, bai tab'a ganin mahaifin shiba, ke kuma kin rabu dashi saboda kina ganin shi shege ne? And you still love him, toh yanzu ke meye sunan ki a gurin shi, meye matsayin soyayyar ki, kinga a tak'aice kin nuna mishi origin d'inshi yafi soyayyar da kike mishi muhimmanci kenan". Dafe kai Saleema tayi tace, "Amna I don't know what come over me I just......". Sai ta dafe kanta da hannunta kurum. Zama Amna tayi kusa da ita tace, "babu wani abu da yazo kanki daman halin kine Saleema, haka kika yiwa ra'ees, bakya dogon tunani kafun aiwatar da abu".
Girgiza mata kai Saleema tayi tace, "ba zaki gane ba Amna, wannan matsalar ba irin ta ra'ees bace, sannan ba daga ni bane daga mahaifina ne, wallahi ko zan had'iyi zuciya na mutu ba zai yarda na auri wanda bashi da cikakken asali ba......".
"Tabdijan! Ni bansan ma ta yadda zan fasalta wannan al'amari naki ba, amma bari mu gani zuwa kwana biyu nayi tunani".
Da haka suka rufe wannan babi, Amna ta dinga d'auke mata hankali har Allah yasa ta saki ranta kad'an, ta komawa abinda ya kawo ta k'asar.

Ta b'angaren Khaleefa kuwa Ahmad ya samu nasarar kai shi asibiti gurin d'aya daga likitocin da suka koyi aiki a hannun su, Sun kwanta na a k'alla kwana hud'u kafun jikin shi ya dawo normal yaji sauk'i sosai. Ko da suka dawo ma Ahmad ci gaba da kula dashi yayi ya rage damuwa ba laifi amma Ahmad ya kula yana yawan duba wani sak'o a wayar shi wanda yake sake jefa shi a damuwa.
Sosai ya sake zama silent ba baki sai amsa da ido, har yanzu bai ce da Ahmad komai akan Saleema ba, shima ya zuba mishi ido kawai yana kallon shi, ya tabbatar yanzu in zasu shekara a haka bazai tab'a bud'e baki yace mishi ga damuwar shiba, sai kawai shi ya shirya tambayar shi da kanshi don yasan ta hanyar da yake ganin zai sama mishi maslaha.
Yana zaune sanye da 3 quarter da singlet, ya hard'e k'afafun shi biyu hannun shi rik'e da d'an k'aramin bowl yana cin farfesun kifin sannu sannu yana had'awa da romon me yaji sosai, waya ce kare a kunnen shi yana waya da auntie da take magana da harshen Arab cikin fad'a, "kasan yadda hankalina ya tashi kuwa? Cikin kwanakin nan bana iya baccin kirki komai nawa saida ya tsaya cak na kasa tsinana komai a office, k'iris ya rage na biyo flight nazo makarantar na ganka".
Madadin da da in sukayi waya da ita ko cikin damuwa yake yana jin sanyi yanzun sai ranshi ma ya sake bak'ik'irin, ji yake kamar ya rushe da kuka saboda jin muryarta da yayi. "kayi shiru baka ce komai ba khaleefa". Murmushi ya k'ak'alo idon shi ya kawo ruwan hawaye yace, "na d'an shiga busy ne auntie amma kuna raina keda Ayman shiyasa ina samun dama ku na fara kira, shi beyi picking bama maybe yana fushi dani ne". Auntie tace, "Anya kuwa? Sai dai ko yana da over work nima na kira shi bai d'aga ba".
Khaleefa yace, "toh Allah yasa".
Ta sake cewa "ameen" sun sake yin shiru kafun auntie tace dashi, "Wai yau saura kwana nawa ya rage ka dawo Nigeria?".
Ajiye bowl d'in hannun shi yayi ya tafi nazari kafun can ya nisa yace, "nan da cikakken sati biyu nake tunanin zamu kammala gaba d'aya".
Cikin jin dad'i tace, "Masha Allah ina ganin zaiyi dai dai da hutun Ayman sai muzo tare wannan karon". Khaleefa shiru yayi bai sake cewa komai ba, ganin haka sai auntie tayi sallama dashi. Yana ajiye wayar Ahmad ya dawo kusa dashi ya zauna. "Yeah man jikin naka da sauk'i sosai ko?". "Umm" kawai yace can k'asan mak'oshi, sake gyara zama Ahmad yayi yace, "khaleefa sai nake ganin kamar rashin lafiyarka yana da alaqa da sab'anin da kuka samu da Saleema cikin kwanakin nan". Kallon shi khaleefa yayi jim kafun yace, "me yasa ka fad'i haka? Ita tace maka mun samu matsala da ita ne?". "a'a ba ita bace, hasalima ni nafi sati biyu ban ganta ba, kawai lissafa ka nayi kamar yadda kake lissafa rayuwar mutane, toh ni dai banyi maka dole ba, idan kaso kaci gaba da b'oye damuwarka, nima bance dole sai naji ba, sai dai ina son ka riqe cewa alfarmar dana nema mana ta zaman jinyar ta k'are daga gobe, soo ko ka saki ranka ka manta da komai, ko kuma ka rushewa kanka shekarar k'arshen nan sai ka sake wata, Ni in na futa daga yau ba sake ganina zakayi ba har mubar k'asar, don banga amfanina a tare dakai ba tunda har zaka iya b'oye mun wani abu na daga rayuwarka baka son na sani". Ahmad yana gama maganarshi ya soma had'a kayanshi da duk wani abu da yasan nashi ne a d'akin, khaleefa yana zaune ko motsi baiyi ba bare ya bud'e baki da nufin dakatar dashi, abinda ya sake tunzura zuciyar Ahmad kenan ko gama had'a kayan baiyi ba ya nufi hanyar futa, sai lokacin khaleefa ya mik'e ya d'auki wayar shi dake bedside yace, "zaka tafi ka manta abu mafi muhimmanci naka Ahmad". Juyowa yayi ya kalli khaleefa da yake tsaye ta bayanshi yana mik'o mishi wayar shi, sai ya dawo da baya da nufin karb'a, sai da yazo gab khaleefa ya maida hannun shi baya yayi taku biyu zuwa tsakiyar d'akin sannan ya fara magana, "a wasu lokutan in kayi abu sai ka bani mamaki, Ahmad na d'auka kai zaka fara bada labarin khaleefa saboda sanin da kayi mishi babu wani mahaluki daya sanshi haka, sai gashi a aikace kana nuna kamar wannan maganar tawa hasashe ce, Ahmad na zab'i yin shiru ne saboda a wasu lokutan ba abinda yakai shiru dad'i da sanya zaman lafiya tsakanin al'umma". Sai ya dakata yaja dogon numfashi kafun yaci gaba, "abinda ya faru ko yake faruwa dani ban raina kaba amma abu ne da ba zaka iya yimun maganin shiba, Ahmad nayi Imani naji a jikina duk duniyar nan ba mai iya yimun maganin damuwata sai Allah, shiyasa shi kad'ai nake kaiwa kukana a yanzun........". Yana kai k'arshen maganar ya koma kan sofa inda ya tashi ya had'a kanshi da gwiwa yayi shiru yana nazari.
Ahmad jikin shi a sanyaye ya matso kusa dashi shima ya zauna ya dafa kafad'ar shi, "ko baka cemun komai ba naji sanyi a raina khaleefa, tabbas ka gama magana saboda Allah shine madogarar bawa, shi kad'ai zai yi mana maganin abinda yafi k'arfin mu, Ina taya ka da addu'ar Allah ya yaye maka damuwarka yayi maka maganinta, a k'arshe na fahimci ka dad'e da yakice komai daga ranka garkuwar jikin kace kawai bata dawo dai dai ba".
Khaleefa rik'e hannun Ahmad yayi gam ya rintse ido ya karanta addu'o'in kore damuwa sannan ya soma labarta mishi duk abinda ya faru tsakanin shi da Saleema daga ranar da taji tarihin rayuwarshi, abin ya girgiza Ahmad matuk'a, duk yadda yake tunanin abun sai gashi ya zarta tunanin shi, ehhh lallai ya yarda wannan matsala ta abokin shi maganinta sai dai Allah. Ya d'auki a k'alla wasu dak'ik'u shiru kafun yace, "wannan duk ba abinda zamu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login