Showing 48001 words to 51000 words out of 288773 words

Chapter 17 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1083

Aikuwa lallai zata ja baya a huld'arta dashi da sannu zai gane kuren shi.
Daga nan sai raihana ta sauya salon mu'amular ta dashi a hankali, sun shirya amma bata sake mishi irin yadda take mishi da farko, haka takan dad'e kafun ta yarda yazo gidan su, ranar da zaizo kuma bayan tsawon lokaci toh zata tabbatar ba makaranta ta shirya muhibba ko jidderh taje dasu sitting room d'in. In yaso sai su zauna daga nesa dasu.
Duk wannan abun Imran ya gane don shi takeyi, a tunaninta ai bazai tab'a ta a gaban yaran ba, shi kuma abinda bata fahimta dashi ba shine, yana yin komai nashi Kai tsaye, zai iya yin abinda yafi runguma a public tunda ai matar shi ce nan da watanni kad'an, toh shi baiga wani abun aibu a ciki ba.

Sannu sannu kwanaki suna ta dad'a mik'awa, har gashi yanzu khausar tayi wata biyu a gidan mijinta, wanda yake nufin bikin raihana saura wata biyu ciff itama. Ranar wata juma'ah Salma tayi musu sammakon zuwa k'arfe takwas na safe ko karyawa ba suyi ba. A d'aki ta samu raihana ta futo daga wanka tana shirin saka kaya, da matuk'ar mamaki ta nufe ta tana fad'in, "Masha Allah kune da asubanci haka?". Ta k'arasa fad'a tana karb'ar samha a hannunta, Salma jakar hannunta ta ajiye ta zaune gefen katifa tana fad'in, "wash daga mota zuwa nan dana d'auko ta duk na gaji". Raihana harararta tayi ta zauna itama tana kallon yadda yarinyar tayi girma Masha Allah.
Sun gaisa kamar koda yaushe in sun had'u Salma sai complain take raihana tak'i je mata sai dai a waya kullum tace zata zata.
Raihana tace, "shine ke kika buga uban sammako haka kika zo, to ai kin kyauta". B'ata fuska Salma tayi tace, "nima ba zuwan ku bane takanas, gidan waccen matar da baki tab'a zuwa ba nazo na d'auke ki mu tafi tun kafun lokacin bikin yazo ki shiga uzuri".
Dariya raihana tayi bayan gama jin abinda Salma ta fad'a tace, "lallai ma Salma da wannen safen zamu je musu gida kamar wasu korarru".
Baki Salma ta saki tana kallonta kafun tace, "a'a kamar dai wasu y'an iska, nifa ba wai yanzu yanzu nake nufi ba, sai anjima rana ta d'aga sosai".
Sai a lokacin raihana tayi dariya. Suna hirar su da salma ta k'arasa shiryawa suka d'auko baby samha suka dawo parlor. Duk yaran sun tafi makaranta tun 7:30 tare suka karya kumallo suna yi suna hira har suka kammala.
Ummie da take bacci a d'aki hayaniyar suce ta futo da ita, ita kanta tayi mamakin ganin Salma da wannan safiyar, koda yake wannan ma ba shine karo na farko da take zuwan sassafe ba.
Sun gaisa da ummie har tana d'aukar samha tana k'ara kallon yadda tayi wayo sosai.

Ranar yini suka yi suna hirar su ta y'an uwantaka, sai k'arfe uku ma suka shirya tafiya gidan khausar d'in. Kamar koda yaushe raihana bata yi wata uwar kwalliya mai yawa a fuskarta ba, ta shirya cikin riga da skirt na material masu shegen kyau da tsari. Ta yane kanta da gyalenta wadatacce ta rufe rabin fuskarta da face mask.

Gidan khausar ma Masha Allah, madaidaicin gida mai d'auke da wadatattun d'akuna da aka cika fal da kaya, kujeru ma set biyu akayi mata kamar yadda akayiwa Salma, haka kayan gado, babbah da k'arami, farin cikin da khausar tayi na ganin su yana da yawa, ta rasa inda zata ajiye su don murna, data fara d'ebo musu lemuka a fridge kuwa saida raihana tace, "muda waye zamu Sha duk wannan". Sannan ta dakata tana dariya. "Auntie ai ku d'inne kuka rikitani da zuwan bazatar ku, sai dai waye ya bada shawarar ayi zuwan yamma?". Raihana kallon Salma tayi, aikuwa khausar ta marairaice mata, "Kai don Allah auntie Salma ya zaki ce a bari sai yamma".
Salma mik'ewa tsaye tayi ta rik'e k'ugu tace, "kin ji had'in borm ko? Toh wallahi wannan ta zaune a gaban ki badon niba da ita da gidan ki sai bayan aurenta, bazata tab'a zuwa ba tab yauma kinsan daya na d'ebo ta muka zo, abban samha fa na biyo k'arfe takwas ma a gidan su tayi mun a can na karya".
Khausar dake kallonta had'e fuska tayi, "hakane auntie raihana? Zuwa tayi tun asuba ta d'ebo ki?".
Murmushi raihana tayi tace, "eh mana tunda ni d'in ruwa ce ko kaya ba".
Duk dariya sukayi. Kafun su fara hirar yaushe gamo, nan khausar ke basu labarin hajiya Inna (kakarsu) tazo mata tun bayan sati biyu da auren, tayi ta basu labarin yadda sukayi hadda had'o mata su yajin daddawa su tukud'i, da sauran abubuwan buk'ata na gargajiya".
Raihana tace, "Ina ruwan hajiya innah baiwar Allah,kwana biyu ta d'aga mun k'afa har na manta rabon da mu had'u ma".
Salma tace, "eh ta d'aga miki k'afa kam amma ai basu fasa k'aramar maganar suba, don ko rannan da na kai samha asibiti na biya ta gidan don mu gaisa, kinsan kana kwana biyu baka jeba zata hau complain ta ce ummie ce ta hana ka, toh shine fa da naje suke ta fad'in wai bakya son zuwa aike kin fi k'arfin kizo takanas gaishe da kowa a cikin su, ko sabga akeyi bakya zuwa, maganganu dai iri iri hadda wanda umma salaha take kaiwa". Tabe baki raihana tayi tace, "oho musu dai su suka sani suda kullum cikin yi musu laifi nake".
Khausar tace, "kuma dai ya kamata auntie raihana ki daure kije ki gaisheta, ai ba zaki daka ta halinta ba don Allah zaki yi don Abban mu kuma data haifa".
"Zanyi k'ok'ari" shine kawai abinda raihana ta fad'a.
Salma tace, "ai dakin bar wahalar da bakin kima indai auntie raihana ce, wanda suke son ganin tama mutanen kirki bata je musu ba sai gidan hajiya Inna da take jiran k'iris da ita, ni kaina bana goyon bayan taje ma wallahi saboda a karon banza za su b'ata mata rai ta dawo tayi ta kukan nan nata mara jin ban hak'uri".
Raihana da take jinsu tana nazarin maganganun su d'aya bayan d'aya mik'ewa tayi don amsa kiran da Ayman yake yi mata a lokacin. Bayan sun gaisa dashi shima complain ya fara mata na kwana biyu ko neman shi bata yi, har zazzab'i ya kwanta kwana uku baya futa office bata sani ba saboda yanzu ta watsar dashi ba ruwanta da neman shi ta mijinta kawai take da aurenta, hak'uri kawai ta bashi saboda ita har ga Allah rikita rikitar data shiga ta Imran ce ta maida kwakwalwarta busy har ta manta da wasu abubuwan ma, amma fa duk da haka shi yana ranta. Sun d'an tab'a hira har tayi mishi alk'awarin zata zo gidan iya tayi mishi waina cikin weekend saboda ya mata k'orafin ya rasa appetite, baya iya cin komai sai tea tsura, aikuwa cikin jin dad'i ya fara mata godiya da fad'in data kyauta mishi kam, raihana dai dariya tayi ta mishi kafun suyi sallama ta ajiye waya.
Dawowa tayi gurin su Salma da khausar da suke ta hirarrakin su, tunda suke maganar su bata ce musu kanzil ba, in ka ganta cikin su saika d'auka itace k'anwa sune yayyen saboda sauk'in kanta, dama ita Sam ba mutum ce mai fad'a da shiga shirgin mutane ba, koda yaushe tana yin rayuwarta ne ita kad'ai khausar ma kusan yanayin su d'aya, amma Salma kamar ba umkiem su ta haifeta ba, Sam bata d'aukar raini yanzun nan za'ayi wacce wacce kowa ya kama gaban shi.

Basu suka bar gidan ba sai bayan sunyi sallar magrib, suna shirin tafiya gida khausar nata k'orafin wannan ziyara bata Isa ba sai sun k'ara zo mata zuwa na musamman, suka samu suka lallab'ata akan lallai zasu tsaida rana su dawo kafun bikin raihana, da haka dai sukayi sallama ta rako su har bakin get bayan ta had'a musu kayan snacks da biscuit a kaiwa su jidderh, da kyar suka karb'i kud'in data basu su hau mota, raihana ma gaba tayi sai Salma ta rik'e ta mak'alawa, a napep raihana take fad'a ma Salma ita fa so tayi sai kud'in ta sun had'u ta siyawa khausar gift na abu mai kyau da zata ji dad'in shi sannan tazo, Salma tace, "don takurawa kai ba? Koda yake kada na hana ki yi mata bayan nima kinyi mun na zama mai hana alkhairy, amma gani nayi bafa wani abu kike siyarwa ba, sannan har yanzu baki fara aiki ba abinda yake hannun ki ga biki yana ta k'aratowa, a k'a'ida kin shiga lokacin da ko kika fi kowa buk'atar kud'i a hannu saboda hidindimu".
Murmushi raihana tayi tace, "noop akwai abinda yake hannuna da zanyi mata hidima dashi, kuma kinga ni bani da wata hidima a gabana, komai ummie ta gama siya tun a wancen lokacin ma, in baki manta ba lokacin da aka fasa aurena na k'arshen nan komai abbah ya sauya mun sababbi iri d'aya dana khausar, ni kuwa me zanyi da kud'i".
Salma cikin jinjinawa tace, "haka ne kuma tabbas, toh amma dai kada ki yiwa hannun ki kakaf, kuma muna nan muna addu'a insha Allah an gama fasa auren ki, in Allah ya yarda wannan sai anyi dashi.....". Murmushin takaici raihana tayi tana tuna abinda yake tsakaninta da Imran d'in ma a yanzu tace, "Ni na dad'e da fudda tsammani Salma, na barwa Allah dukkan lamuran rayuwata, shi kad'ai yasan abinda yake bad'ini, kuma shi yasan abinda yake mafi dacewa ga rayuwar bayin sa".
Salma tace, "wannan haka yake, toh Allah ya tabbatar miki da alkhairin shi".
Ta amsa da "ameen". Sai wajen isha'i suka Isa gidan su, aikuwa ummie taita musu fad'an kaiwa daren da suka yi, dama raihana tayi tsammanin za'ayi haka, kuma duk sun haddace wannan dokar gidan suce tun ta k'uruciya, basa futa bada izinin Abban suba, sannan basa kai magrib a waje ko gidan wa suka je, idan kuwa har suka kai dare to tare da abban su zasu dawo. Salma tana zama don tayi sallah ta huta mijin ta yazo d'aukarta, aikuwa ummie ta fatattakata tace sallar ma tayi a d'akinta in taje sai tafi lada.
Raihana dai tana tsaye sai dariya take mata ciki ciki.

***********

Washe gari ya kama asabar, tun da wuri raihana ta gama aikinta na gidan ta had'a musu abincin karin kumallo, ko data je gaishe da abban su da safe sai ta tambaye shi tana son zata je ayi mata lalle nan kan titi gurin Zahra, Abba da yake tankwashe da k'afa kan sallaya yana yin lazimi ajiye carbin yayi a gefe ya fuskanceta da kyau kafun yace, "toh ba damuwa nawa ne ake yin lallen?" raihana tace, "bak'i ne kad'ai ma za'ayi mun dubu d'aya da d'ari biyar ne". Dubu biyu ya bata yace sauran tayi wani abun dashi, bata karb'a ba tace, "Abba ai akwai kud'i ma a gurina da ka barshi kawai". Had'e fuska yayi yace, "rok'on Imrana kud'i kikeyi?". Ta girgiza kanta da yake k'asa tace, "a'a Abba". "toh kenan Ina kika samu kud'i bayan bakya juya komai a hannun ki". Sai tayi tsuru tsuru cikin rashin sanin abinda zatace, "ke nake tambaya kinyi shiru?". Cikin tsoro tace, "Abba akwai ragowar kud'in da ummie ta bamu na gyaran gashi da lalle dasu kwalliya a lokacin banyi amfani dasu duka ba". Sai lokacin ya d'an sassauta yace, "toh da sauk'i amma ki karb'a ko wani abun ba sai kiyi dasu ba tunda hidindimun ku kullum basa k'arewa". Cike da jin dad'in yadda ya fahimce ta ta amshi kud'in tare da yin godiya. Shiyasa har yanzu bata nuna kud'in da Imran ya dinga zuba mata a account ba saboda tasan fad'a za'ayi mata bana wasa ba.

Har ta tashi zata tafi sai abban ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, "raihanatu dama Ina son yin wata magana dake". Raihana Saida gabanta ya yanke ya fad'i ta dawo jiki a sanyaye ta sake durk'usawa gaban shi, dai dai lokacin ummie ta shigo rik'e da tray na abincin karin shi.

Dubun godiya da goyon baya my fans, Ina yinku fiye da yadda kuke yinaπŸ‘πŸ‘πŸ˜


_Comment and share_
24/03/23, 2:02β€―pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*πŸ§•
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page fourteen1️⃣4️⃣


"Ina fatan komai yana tafiya dai dai babu wata matsala tsakanin ku dashi Imrana d'in ko?" Saida gabanta ya fad'i sannan jiki a salub'e tace, "babu wata matsala Abba".
"Toh Masha Allah ki ci gaba da yawaita addu'a insha Allah, Allah zai zab'a miki abinda zaifi zama alkhairy ga rayuwarki". Gyad'a mishi kai tayi "insha Allah Abba zan dage sosai" ta mik'e ta fuce daga d'akin.
Misalin k'arfe sha d'aya da rabi tayi sallama da ummie ta d'auki kud'i da wayarta ta fuce daga gidan.
Wani shago dake kusa dasu na kwalliya, gyaran jiki da lalle ta nufa direct, bayan sun gaisa da ma'aikatan gurin, zama tayi jiran me lallen ta gamawa wadda akewa a lokacin itama tayi mata.

Allah ya taimake aka gama da wuri suna d'an hirarrakin su da mutanen gurin lokaci bayan lokaci. Tun ba'a dad'e da gama mata ba sukayi waya da Ayman yake shaida mata yana gidan iya, ta fad'a mishi ita kuma tana zahra's saloon in ta gama zata zo, yaso biyota tun a lokacin ta hana shi saboda zai dad'e yana jiranta a k'ofar shagon kafun lallen ya kama jikinta ta wanke.
Tana shirin sallama dasu aunty Zahra bayan an gama kiran shi ya sake shigowa, bata d'aga ba ta futo da sauri tasan ya gaji da jira ne, sai ta tsaya da mamaki tana kallon shi tsaye hard'e da hannu a k'ofar shagon, sanye yake da JC black and white dai dai jikinshi, sai kanshi rufe da hula ta sak'a fara sol. A hankali ta k'araso gaban shi bata dai ce komai ba. Ayman ne cikin shagwob'ewa sosai yace, "raihanatu lallen nan ya dad'e almost 2 hours fa ina jiran ki".
Cikin had'e rai itama tace, "toh ba dama na fad'a maka lalle ana dad'ewa ba, ka had'a komai da komai ne?". Murmushi Ayman yayi yana kallon k'afarta da hannunta yace, "gaskiya ne lallen ya miki kyau sosai, gashi ba don ni akayi ba amma kuma nina fara gani". Ya k'arasa fad'a da neman magana.
Raihana fuskarta a had'e har lokacin tace, "toh wa yace daka gani ka yaba?".
"Saboda idanuna ba zasu iya ganin abu komai k'ank'antar shi a tare dake bakina bai magantu ba".
D'an hararar gefen shi tayi tace, "toh anan zamuyi wainar ne naga muna ta tsayuwa lokaci na tafiya".
"Toh ai kece kika tsayar damu a nan d'in, ni kuwa yana iya yadda kike so haka za'ayi gimbiyar mata".
Murmushi kawai tayi ta fara yin gaba yabi bayanta da sauri suka jera, suna tafe suna hira kai inka gansu saika d'auka wasu shahararrun masoya ne na k'arshe d'in nan.
Saida ta saci kallon k'ofar gidansu da zata huce, gidan a rufe yake ruff!
Iya nata aikace aikacen ta suka shigo da sallama kusan a tare. Cikin farin ciki tace, "haba ai tunda naga Ayman yana duba agogo tun d'azu nasan ke yake jira, Ina shiga d'aki in futo na nemi mutum na rasa, nace toh ya tafi ya taho dake".
Ita dai raihana bata ce komai ba sai gefen iya data samu ta zauna tana gaishe ta da tambayar malam.
"Malam yau ya tafi kasuwa zai had'o wasu turaruka".
"Ayyah Allah ya dawo dashi lafiya" Suka amsa da "ameen".
Saida suka fara yin sallah sannan ta duba duk abubuwan da zasu buk'ata na waina a kitchen d'in iya, kusan tare suka had'a ko tace Ayman ya barshi baya bari sai yayi a cewarshi wai yunwa yake ji yau sosai.
Iya dai inta kallesu murmushi kawai take taci gaba da ayyukan ta.
Haka aka soma soya wainar fulawa ta mutum biyu, in ya zuba ta gasu raihana ta juya ta kwashe a plate, saida suka tara da yawa suka ba iya, ta karb'a bayan tayi godiya ta zauna ta fara ci, wata suka k'ara tarawa, raihana ta d'auki plate d'in takai kusa da iya tace da Ayman, "Ka zauna kaci don Allah ni na gode da tayin aikin wanda kayi ma Allah ya bada lada".
Mak'e mata kafad'a yayi kamar k'aramin yaro, "bakya son kici tare dani ko raihana?".
"A'a Yaya Ayman saboda kace kana jin yunwa ne idan ba yanzu ba sai yaushe zakaci kenan?". "toh ni bazan iya ci ba tare dake ba yau ko yunwar zata kashe ni kuwa sai an kafa tarihi".
Saita dafe kanta oohh Yaya Ayman rigima, "Ni dai Allah kaci abincin ka nima zanci ai in na gama".
"A'a fa" ya fad'a yana yin kicin kicin da face, Dole raihana ta hak'ura a k'arshe Suka gama wainar tare suka zuba wadda zasu iya ci sauran ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login