Showing 192001 words to 195000 words out of 288773 words

Chapter 65 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1117

dangane da gadon barcinta ta kwanta, ko kayan jikinta bata iya tsayawa cirewa ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.


*******

Kamar kowanne hutun k'arshen mako, tun safe khaleefa bai futa ko'ina ba yana aikin gyaran d'akin shi, yana aikin maganar da sukayi da Ahmad na dawo mishi daki daki.

Da yamma bayan yayi wanka ya shirya cikin shigar da tafi amsar jikin shi wato k'ananun kaya riga da wando farare k'al, gashin kanshi yasha gyara duk inda ya gifta sassanyan k'amshin turaren shi ke tashi.
Key da mukullin motarshi kawai ya d'auka ya futa daga gidan ba tare da raihana ta sani ba.

*****Rabon shi da apartment d'in tun ranar da suka bar Germany zuwa Nigeria hutun kammala karatun su, rabon shi da ita kuma tun ranar da yaje gareta ya mayar mata da zobenta.

_in few hours na muku shi sai hak'uri zaku ganshi ba edit_

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*


_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page fifty four 5️⃣4️⃣


Tsayuwa yaci gaba da yi kamar get man ya tsurawa gaban part d'inta ido, ya jima yana k'ullawa da kwancewa saboda har ga Allah baya son ya koma gareta a yanzun ba tare da ya samu cikakken hujja da zaiyi yak'i da abinda ya raba su da farko ba kamar yadda yayi alk'awari.
A nutse ya fara juyawa zai bar gurin, har ya fara tafiya sai yaga giftawar wata kamar Amna, sai ya juya da sauri ashe itama bayan ta gifta ta ankara dashi, hakan yasa suka juyo kusan a tare.
Amna ta fad'ad'a fara'ar fuskarta ta k'araso inda yake, shima sakin fuskarshi yayi suka gaisa da ita kafun ta tambaye shi, "sai yau ka tuna damu?".
Baice mata komai ba, dama tasan ba zaice d'in ba. Sake d'auko wani zancen tayi, "kun had'u da ita ne?".
"Ba zuwa nayi don ta ganni ba". Ya bata amsa kai tsaye ya fara k'ok'arin barin gurin.
Dakatar dashi Amna tayi ta hanyar sake cewa, "shin ka hak'ura da Saleema ne?".
Juyowa yayi ya kalleta da kyau, fahimtar kamar akwai magana a bakinta sai yace, "har abada bazan tab'a iya hak'ura da Saleema ba kema kin sani, itace kacal macen dana fara so zanci gaba kuma da so har k'arshen numfashina.......".
Murmushi itama tayi a wannan karon, "shin wannan alk'awarine da kuke rik'e dashi kaida ita ko ita kad'ai take rik'e dashi?".
Bai bata amsa ba saida ya gama juya maganganun ta, "Ina ganin kamar akwai magana a bakin ki Amna! Well ni yanzu bani da lokacin jaddada magana akan abinda na neesa damu ma sun sanshi bare ke,,, Soo ina ganin sai anjima ko?".
"Ka fad'i gaskiya sai dai kak'i bani damar da zan fad'i gaskiyar dana sani nima,,,, shin kana tsoron kada ka jima a waje matarka ta rufe maka k'ofa ne".
Cak ya tsaya daga tafiyar daya fara yi, tsabar yadda maganar ta shige shi saiya kasa juyowa ya kalleta sai itace ta k'araso gaban shi, "waya fad'a miki nayi aure" ya tambayeta fuskarshi babu alamun wasa.
"Ah abun duniya yana b'uya ne? Musamman yanzu da mutane suka zama y'an jarida! Ina ganin yadda wayoyin hannun mu suke saurin isar da sak'o ko y'an jaridar albarka". Ta k'are zancen tana murmushi.
Khaleefa dafe kanshi yayi da hannun shi, wannan yana daga dalilin da yasa ya dinga hana Ahmad yayatawa mutane auren shi, yanzu ga irinta nan zai jik'a mishi ruwa a guri mai wuyar bushewa. Yasan tunda Amna ta sani lallai Saleema ma ta sani.
Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi ya tambayeta, "yanzu Ina saleeman take?".
"Ban sani ba don kaga nima shigowata kenan! Ga lokaci ya fara ja har na fara gajiya da tsayuwa,,,,, Ina ganin sai anjima ko?".
Ya fahimci Amna duk magana take yab'a mishi a kaikaice.... Har ta fara tafiya khaleefa bai iya barin gurin ba saida ta bud'e k'ofarta ta shiga sannan yaja k'afafun shi ya fara barin gurin shima.
Murmushi Amna da take kallon shi ta window tayi, a zahiri kuma saita ce, "yanzune za'a fara wasan! nasan duk inda zanyi a garin nan sai ka nemo ni ko don tunanin ta yadda zaka gyara alak'ar ka da Saleema! Alak'ar data dad'e da yankewaaa".
Wani murmushin ta sakeyi tana girgiza kanta kurum, zuciyarta cinkushe da abubuwa da yawa.

Gaba d'aya khaleefa ya kasa samun sukuni, yafi hour d'aya a gaban gidan bai shiga ba yana tunanin yadda zasu kwashe da Saleema idan tayi ido hud'u dashi. Baisan me zaice mata akan auren raihana da zai wadatar har ya kare kanshi ita kuma ta fahimce shiba. "Wayyoh Allah". Ya fad'a yana sake jingina kanshi da bangon gidan.
Ko bayan ya shiga gidan ma tunanin daya d'ora kenan, lallai Ahmad ya kwanto mishi kura, a tsarin rayuwarshi mace d'aya ce zab'in shi, shiyasa bai auri raihana don ya zauna da ita ba, ya aureta ne don ya rabu da ita da zarar deal ya cika kowa ya gama samun abinda yake so cikin su, tun yana under 20 years ya tsara rayuwarshi mijin mace d'aya cal da y'ay'an su, kuma koda suna soyayyah da Saleema ya fad'a mata shiba mijin mata da yawa bane, ita kad'ai ta ishe shi rayuwa da yaranta uku da zata haifa mishi, (don saleema bata son haihuwa da yawa a tsarinta, khaleefa kuma yaji ya amince a lokacin). Toh taya kenan zaice mata auren yarjejeniya sukayi da raihana don cikar burin shi na samunta? Shin ko zai shekara mata bayani zata gane kuwa?

Da wad'an nan tunane tunanen bacci b'arawo ya sad'ad'd'afo yayi wuff dashi.

Washe garin ranar raihana ta tashi da zazzafan ciwon kai, komai kasa yi tayi tun safe sai kwanciya daga farkon gado zuwa k'arshe.
Bata ji dama dama ba saida rana ta futo sosai Yasmine suka zo gidan ita da Ahmad.
Har bedroom ta biyo ta ta sameta nannad'e cikin bargo gashin kanta a hargitse k'arewa ma ko kayan bacci bata sauya ba.
Koda ta tambayeta lafiyarta kuwa? Bata fad'a mata abinda yake damunta ba ta tashi ta fad'a bathroom a gurguje tayo wanka ta futo d'aure da towel, gaban dressing mirrow ta zauna tana shafa mai yasmine na mata fad'an ya kamata ta shirya suje saloon a k'ara gyara kan nan, murmushi tayi tace "to ba komai hajiya kisa mana lokaci".
"Aini ko yanzu ma".
Zaro ido raihana tayi tace, "inke kin shirya ni ban shirya ba".
B'ata fuska Yasmine tayi, "aikuwa indai kece ba samun lokaci zakibyi ba haka zaki ta cewa sai kin samu lokaci har na gaji da jiran ki na hak'ura.... Gaskiya bari ma na fad'awa hubby ya kamata muje saloon d'in nan yau".
Ko jin ta bakin raihana bata yiba ta fuce zuwa parlon inda suke zaune shida khaleefa zaman kurame, don ba hira suke yiba kowa aikin gaban shi yake cikin su.
A kusa dashi ta zauna ta shige jikinshi kamar ta tsaga jikin shi su zama abu d'aya, ta kanainaye hannayen shi ta kwantar da kanta gefen wuyan shi tana magana da zallar shagwob'a, "hubby don Allah ka kaimu saloon nida raihana ayi mana gyaran kai yanzu".
Khaleefa da ya kalle su tab'e bakin shi yayi a ranshi yana ayyana, "wannan marar kunyar matar Ahmad d'in tazo za taita nanik'e shi ko kunya bata ji". Tashi yayi kamar koda yaushe ya basu guri.
"Yaushe aka tashi zuwa saloon d'in? Waye jami'in shirya tafiyar? Indai kece ma ba zaku ba".
Sake shagwob'ewa tayi tace, "hubbyyy pleaseeee".
"Na fad'a miki ba inda zaku duk salon kar kibar mutum ya huta, yau weekend d'in ma sai kinje yawo".
Fushi tayi ta mik'e zata bar gurin tana jejjefa k'afa kamar yarinyar goye ya rik'o hannunta, "Ni ka rabu dani".
"Nifa da Wasa nake miki, taya ma zan hana ki bayan ni za'a yiwa gayu". Murmushi tayi ta dawo ta rungume shi tare da sake mishi kiss😘 a kumatu tana godiya.
Da kallo ya bita har ta koma ta shaidawa raihana data gama saka kaya cewar ta futo Ahmad ya amince.
Tsayawa da dube duben neman abunda take tayi ta tambaye ta, "har khaleefa kika tambaya?".
"Kai! Wane ni! wannan mijin naki me d'aure fuska ko hak'orin shi ba'a ganiiii ta Ina ma zan iya tambayar shi,,," sai kuma tayi k'asa da murya taci gaba da zancenta, "Allah bazan iya tunkarar shi na tambaye shiba, yana gani nama ya bar gurin".
K'aramar dariya raihana tayi tace, "aike d'in ce kin kasa fahimtar abinda yasa da kinje gurin mijin ki yake baku guri".
"Na sani yadda kuke yine ke dashi bazan iya ba, haka kurum kaida mijin ka saika dinga wani d'auke mishi fuska kamar auren dole,,,, Wai bakya ganin yadda kuke yine a gaban mutane kamar wasu marassa gaskiya,,,, feel free kiyi rayuwarki babu kallon kowa bare idon wani yayi miki shamaki".
Murmushi raihana tayi ta girgiza kai tana jinjina maganar Yasmine d'in, toh in banda yasmine ita daba irin auren su sukayi ba ina zata ga fuska a gurin khaleefa, kuma koda auren soyayyar sukayi ma ita ba zata iya irin rashin kunyar nan ta yasmine ba, tana ganin ita kanta yasmine d'in donta rayu a k'asar data sha banban da wadda suka rayu a cikine shiyasa.
Mayafinta ta yafa saboda Yasmine da take ta azalazalarta, tama k'i barinta ta d'auko magani tasha saboda ciwon kanta daya lafa kada ya sake dawo mata idan aka tab'a kan. Riga da skirt ne a jikinta daya zauna mata cif, har zata yafa gyale saita fasa ta d'ora hijab bayan ta tubke gashinta, ta d'auki wayarta suka futo yasmine nata mitar tayi dressing me kyau ta maka hijab ta rufe.
Lokacin da suka futo parlon khaleefa ya dawo yana ci gaba da operating system d'inshi.
Daga gefe d'aya ta zauna ta fara gaishe da Ahmad cikin nutsuwarta, tunda ta futo bai d'aga ido don ya kalleta ba, saida Ahmad yace, "khaleefa na fad'a maka fa zamu yi musu rakiya saloon kayi banza ba kace komai ba".
"Sorry! Kuje kawai ni bazan iya zuwaa ba". Ya bashi amsa hankalin shi akan aikin da yake yi.
"Har raihana fa zamu". Ahmad ya sake jaddada mishi.
"Ahmad kuje mana" ya fad'a cikin k'osawa da zancen.

Ahmad ne ya fara yin gaba Yasmine mak'ale dashi, sai raihana da take take musu baya, har ta giftashi sai ya kira sunanta, "Raihana!". Ta amsa da "na'am" tana dawowa baya. Master card d'inshi ya mik'a mata, "kiyi amfani da wannan". Ba tayi mishi musu ba ta russuna ta karb'a ta mishi godiya tabi bayan su.
A motar Ahmad sukayi tafiyar, Yasmine kamar y'ar gari ita ta kaisu har gurin.
Koda suka shiga Ahmad ne yayi magana dasu ya biya su kud'in ya tafi anjima zai dawo ya d'auke su, rigima sosai yasmine tasa akan abinda yasa bazai jira suba yake son tafiya ya barsu su d'aya. Haka nan ya hak'ura ya zauna cikin mota zai jira a gama musu.
Ita aka fara yiwa da yake bata da cikar gashi nan da nan aka gama, sannan aka yiwa raihana ma.
Tun a gurin Yasmine take yaba yadda suka gyara musu me kyau har suka k'arasa gida zancenta kenan. Yana nan inda suka barshi sai dai ya kwantar da kanshi kamar me bacci saboda nisa daya fara yi a duniyar tunani ko sallamar su bai jiba. Ahmad ne ya zauna a parlon yana kiran sunan shi su kuma suka shiga cikin d'akin gadonta, ta adana mishi catin shi a guri me kyau suka yi alwalar sallar azahar data kwace musu.

Raihana ta riga Yasmine idarwa tana idarwa ta shiga kitchen ta had'a musu abinda zasu ci a sauk'ak'e ta jera musu a dinning ita kuma ta d'au nata ta shige d'akin barcinta.

Ranar ma basu bar gidan ba sai dare bayan sunci abincin dare, gaba d'aya har suka gama hirar suka tafi Ahmad bai fahimci kan khaleefa ba, ya fahimci a wani irin ruguje yake baya iya gane komai da kowanne zance sai wanda ya ajiye a ranshi yake cin ranshi.

Da dare raihana harta kwanta ta tuna da catin shi, saita diro kan gadon ta d'auki card d'in a inda ta adana shi ta nufi d'akin shi direct, yana kwance ya tsurawa rufin d'akin ido, Koda ta buga bashi da wani sauran k'arfi ko kuzari na mik'ewa, hakan yasa ya bata izinin shiga ba tare daya motsa daga yadda yake ba. Ta tura k'ofar ta shiga da sallama, karon farko data tab'a shiga d'akin shi tundaa take a gidan, wani sassanyan k'amshi da d'umi me dad'i ya dake ta, daga jikin k'ofa ta tsaya tace, "card d'inka dama na kawo maka". Ba tare daya kalleta ba yace, "me yasa bakiyi amfani dashi ba".
"Ahmad ne ya biya duka".
Baice mata komai ba ya barta tana ci gaba da tsayuwa har ta fara gajiya da kanta ta sake ce mishi "ga catin". Sai a lokacin ya mik'e zaune ya jingina da fuskar bed ya mik'a mata hannun shi still ba tare daya kalleta ba, ta k'araso a nutse cikin taku mai bayyana hakan ta d'ora mishi catin a hannun shi.
Yabi lallen hannunta da kallo, k'amshin turaren ta na barazanar ruguza mishi kafofin jinshi saboda shigar da sukayi mishi ta sauri. Ya lumshe ido ya bi bayanta da kallo har ta fuce.

******

Kwana kin da suka biyo baya duk ya jera sune cikin rashin walwala har a office ma, so yake ya nemo Amna ya warware mata zancen auren shi cikin fahimta yadda zata gane, yasan zata iya fahimtar da Saleema cikin sauk'i fiye dashi.
Da yamma koda ya tashi office kiran doctor andal ya tafi amsawa, tana tsaye ita da wani kyakkyawan matashi ga dukkan alamu fad'a take yi mishi cikin harshen larabci, Koda khaleefa ya lek'o yaga hakan juyawa yayi nufin yi sai ta dakatar dashi ta hanyar kiran sunan shi. Dawowa yayi cikin office d'in, ta bashi seat ya zauna ita kuma taci gaba da kallon matashin tana nuna shi da yatsa cikin harshen Arab tace, "wannan ya zamo karo na k'arshe da zaka zo mun da shirmen zantuttukan ka har k'asar da nake aiki irin wannan, in su da suke zuga ka basu da hankali kai ai me hankali ne, sannan kamar yadda na fad'a muku da farko suhana tana shekarar k'arshe a karatun ta, ni kuma saboda ku bazan hana ta k'arasawa ba, you better wait for her ko ka hak'ura wannan duk ya rage naka".
Tana gama zancen ta bar gaban shi ta koma cikin office d'in taja seat ta zauna ta had'e kanta da table dake gaban kujerarta tana k'ok'arin shanye b'acin ranta, sam batason abinda zai b'ata mata rai akan auren nan har suja ta fasa abinda tayi niyyah. Saboda wani shirmen zancen su can suke nufin ta katse karatun y'ar ta a watannin da zata kammala ta basu aurenta, bayan ba barta zasuyi ta kammala ba in anyi auren. Mtsss! Ta sake jan tsaki tare da tashi zaune da kyau tana duban sashen da khaleefa yake.
"Yi hak'uri na barka kana jirana ko?".
"A'a ba komai". Ya mayar mata da amsa.
Tsabar yadda ta shiga rud'ani ta manta da yaren Arab ta mishi magana saida taji ya mayar mata amsa da yaren. Da mamaki ta kalleshi, "kana jin larabci dama?".
Gyad'a mata kai yayi, saita sake cewa, "toh amma kana Nigerian me ya had'a ka da labarci?".
"Yaren mamata ne".
Tana son sake tambayarshi maman shi sudaniyya ce? Don larabci daya mata zam na Sudan ne, amma tana tsoron kada yaga ta dame shi da tambayoyin bin kwakkwafi, hakan yasa ta hak'ura amma abun yana zuciyarta.
Sun tattauna akan abinda ya shafi surgery da suka yiwa wani d'an wasa a k'afar shi, a k'arshe ta dire da tambayar lafiya ta ga yanayin shi ya sauya kwana biyu, "bana jin dad'in jikina ne" amsar daya bata bata wani gamsar da ita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login