Showing 282001 words to 285000 words out of 288773 words

Chapter 95 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1118

taya su murna sosai haka ma khaleefa.
Duk yadda khaleefa yaso d'auke kai ba tare da yaji daga raihana ba, kasawa yayi a wannan gab'ar, saboda yana son ji daga gareta a kullum dare da safiyar Allah sai ya saita mata sim card na k'asar. Su yini suna waya, su raba dare suna video call, y'an matan gidan kan zolayeta wani lokacin barin ma suhaana da take ganin asarar data ne kawai sukeyi tunda gasu kusa da juna.

****Amarya surayyah kuwa suraj bai tunkari inda take da kowacce magana ba saida ta kwana biyu a d'akinta, ta samu nutsuwar kintsa komai dai dai da yadda ya kamata ya kasance. A dare na uku ma saida ta gama shirin kwanciya bacci ya nufi sashen nata.
Sunyi magana ta kyakkyawar fahimta da maida komai daya faru a wancen shekarun matsayin k'addarar rayuwarsu, abinka da zuciyar dake cike da soyayyah, nan da nan komai ya huce tsohuwar zuma ta motsa.
A wannan rana surayyah ta sake tabbatar da soyayyah bata tsufa sai dai ta mutu in lokacin ta yayi, don Suraj ya sake tabbatar mata da hakan.
Kwanakin da suka biyo baya duk masu tsada ne a gurin wad'annan mutane da zuciyoyi ma'abota soyayyah, sun tattauna akan aikinta da yadda zatayi dashi, yadda Suraj ya fahimci tana son aikin sai yace a shawarce ko transfer zai nemo mata ne ita da Ayman, k'in amincewa tayi sam, a cewarta tunda saura watanni kad'an tayi retire tana son aje aikin a asibitin, dole ba yadda Suraj ya iya haka ya hak'ura amma bisa kyautata zaton shima rabin rayuwarshi ta koma can.

A kusa dasu ya bawa malam da iya kyautar gida mai d'an karen kyau da tsada, da ticket na tafiya saudiyyah umrahr sati hud'u. Hak'ik'a malam yaji dad'i yayi godiya ya nuna farin cikin shi, amma ya nuna sam bazai iya zama garin Abuja ba, da son samu ne ya k'arasa rayuwarshi a Kano.
Shiru Suraj yayi a wannan lokacin ya rasa abinda ya kamata yace ma, saida ya dawo gida sukayi shawara da surayyah sai ta bashi shawarar ya nema mishi wani aikin yi a nan garin inba haka ba bazai tab'a zama ba.
Da wannan shawarar yayi amfani ya d'anka mishi kula da masallacin gidan, (wato jan qamsussalawati).
Da kyar da sid'in goshi wannan karon aka samu ya zauna.

****Kwana ki sunyi ta hucewa har gashi hutun da andal ta d'aukar musu ita da khaleefa a gurin aiki ya k'are, ba don yaso ba zai tafi sai don gudun samun matsala.
Auntie kam taso tafiyar nan a yita tare da andal sai dai hakan bai zai yiwu ba, andal ta tabbatar mata koba don aikinta ba, ba zata k'asar a wannan lokacin ba. Dole a k'arshe tafiyar zata zam a rarrabe. Khaleefa da matarshi, sai suhaana da mamanta suka fara yin gaba. Bayan ansha kukan bak'in ciki da takaicin rabuwa da juna a k'arshe dai kowa ya koma bakin aikin shi.

A Abuja kuwa sauban da iyalan shi duka suka shirya tafiya sai Suraj da yayan shi, auntie da Ayman daya jingine aikin shi a gefe bama ya son tunowa bare batun komawa, ya kasa ya tsare so yake kawai suhaana ta zama tashi sai ayi wadda za'ayi.
Ranar da zasu tafi kamar maraya haka khaleefa ya dinga jin kanshi, sai yanzu yake ganin nisan dake tsakanin Nigeria da Germany.
Tafiyar wuri sukayi shiyasa sukayi sallama da kowa tunda wuri, Ayman da Abban su ne sukayi musu rakiya har airport da dingimemiyar kyautar da basu tab'a tsammani ba su duka hud'un. Khaleefa har sukayi nisa yana waigowa ya kalli wajen da yabar mahaifin shi da d'an uwanshi tsaye har ya b'ace musu.
Tun a cikin jirgi ya sak'alo hannun raihana cikin nashi, sai kaffa kaffa yake da ita da duk wani motsinta. Suhaana da take kallon su daga ta baya ba k'aramin burgeta suke ba, tana fatan itama ta samu kwatankwacin irin wannan kulawar daga Ayman bayan sunyi aure. (Nikam nace ba tsohon gwauro ba🤣🤣 zaki samu kuwa).
Suna sauka a airport suka raba hanya, kowa yayi nasa guri.

Lokacin da suka shiga gidan ba k'aramar k'ura suka tarar ta bud'e ko'ina ba, sallolin da suka hucesu kawai suka gabatar ta ajiye mayafinta gefe ta fara aikin gyaran gidan, khaleefa ma zame kayan jikin shi yayi ya rage daga shi sai three quatre da wata riga armless. Tun raihana na jin nauyin shi harta ware suna aikin tare.
Basu gama aikin ba sai nisan dare, lokacin gaba d'aya ta gaji ko hannunta da kyar take iya motsawa, ga yunwa tana sakad'ar cikinta. Ga khaleefa ma tuntuni ya bata shawaran da kitchen ta fara gyarawa ta musu girki suka ci don shi yunwa yake ji ta gaske, tak'i amincewa da tsoron in taci abinci jikinta zai mutu ta kasa aiwatar da komai. Tana kwance tana wannan tunanin taji motsin shi ya gama wankan zai futo, da hanzari tayi kitchen ta taya su aikin ta fara duba abinda zata dafa, gashi bata da ko kwallin kayan miya a gidan, albasar data bari ma duk sun bushe. Ruwa kawai ta d'ora taci gaba da dubo sauran abubuwan amfanin, tana aikin khaleefa ya shigo yaja sit ya zauna yana k'ok'arin saita layukan shi na k'asar, yana gamawa ya kira layin Ahmad ya fad'a mishi dawowar su, sun jima suna waya, saida ya warware mishi komai daya faru kafun suyi sallama. Shi ya karb'i girkin zai kula mata dashi yace ita taje tayi wanka.
Lokacin data futo har ya gama girkin ya zuba musu a plate, ya zuba mai da Maggi. A nan kitchen d'in suka ci tare da suka gama ta wanke plate d'in da sauran kayan, khaleefa nata mata fad'an ita wai bata gajiya da aiki ne? Murmushi kawai tayi ta k'arasa kammale komai a muhallin shi suka fuce. D'akinta taso sillewa wai zata had'a littattafanta, khaleefa komai baice mata ba ya d'aga ta cak ya nufi nashi d'akin shi da ita yana mitar ita bata gajiya ne da aiki, koda ya sauke ta akan gado addu'ar bacci ya karanto mata yaja musu duvet ya rungume ta sai bacci........

Komai yaci gaba da tafiyar musu dai dai, tuni ya koma aikin shi ita kuma ta koma makarantar ta, Yasmine da Ahmad sunzo musu tun washe garin dawowar su, inda suka sake nuna farin cikin su da abinda ya faru sosai.

Ta b'angaren soyayyarsu kuwa sai abinda yaci gaba, sosai khaleefa ya sabarwa raihana nau'in wata rayuwa..... Ya kulleta cikin duniyar da su biyu kad'ai ke rayuwa suna ganin junan su, khaleefa bai maida raihana cikakkiyar matar shiba sai data gama sakin jiki dashi sosai......
Komai ya tafi musu gentle and romantic cikin tausayawa da nuna kulawa da tattali, ta samu karb'ar dalleliyar kyauta daga khaleefa na samunta matsayin macen data killace kanta daga dukkan shirme da sakarci, ta mallaka mishi abu mafi tsada daga gurin kowacce mace budurwa, abun alfahari da tink'aho a gurin macen da tasan ciwon kanta ba ballagaza data gama bawa samarin banza a titi ba💁‍♀️😒. (Hak'ik'a da ina da wadataccen lokaci dana zayyane muku irin y'ar asalin kulawa da tattalin da raihana ta samu daga khaleefa).

*Sudan*
Matafiya sun isa lafiya, familyn surayyah ba k'aramin murna da jin dad'in ganinta sukayi ba, itama kuma ta nuna musu asalin yadda tayi kewar su, haka y'an uwa na nesa dana kusa suka dinga tururuwar zuwa suna gaisheta satin farko da tayi a garin.
Ayman daya k'agu yaga anyi maganar auren shi da suhaana amma yaga shiru, kasa jurewa yayi har ta kai damuwarshi ta futo sarari auntie na gani daga yanayin shi koda baiyi magana ba. Hakan yasa cikin sati na biyu Abban su ya shirya da yayan shi da dama saboda maganar ya biyo shi zasu je gurin dangin mahaifinta.
Da farko sunso su nuna kin amincewar su saboda wancen yaron ba wai ya hak'ura bane, amma daga baya da y'an uwan andal d'in suka ji labari suka shiga abun sai komai ya tafi dai dai aka tsaida magana kan zasu zo a saka rana nan da kwana ki biyu masu zuwa da ikon Allah.
Lokacin da auntie ta labartawa Ayman yadda akayi, tsoro ne ya kama shi, hakan yasa ya tubure kan lallai shi sai dai a d'aura auren in yaso ta gama karatun sai ayi biki, cox yana tsoron ya rasa ta yadda ya rasa wadda ya fara so a duniya. Da farko Auntie ba tayi na'am da rikicin Ayman d'in ba, sai dai daga baya k'anwar mamarta ta goyi da bayan hakan don inba haka aka yiba sai dai suji anayi bada suba. Koda ta tuntub'i andal da zancen cewa tayi hakan shine dai dai don ba k'ananun y'an iska bane wad'annan mutane.
haka kuwa akayi a ranar da za'a je batun saka rana aka k'are da d'aura aure. Auren daya jawo takaddama da rashin amincewar da yawa cikin familyn mahaifin suhaana da k'asa ta rufewa ido. Sati d'aya suka k'ara daga nan suka tattaro suka dawo Nigeria.
Sun sake hutawa kad'an kafun su fara Shirin komawa Kano saboda aikin Ayman da kuma na auntien. Don dai Suraj ba yadda ya iya da ita ne a wannan gab'ar amma da bazai tab'a amincewa taje wani guri da nisa ba, toh amma alfarmar y'an watanni ne zaiyi mata, da zarar tayi retire ba zai sake yarda ta zauna a garin ba, Ayman ma ya gama shirin shi tuni akan su, bata yadda za'ayi ya bar familyn su kowa da duniyar da yake. Ta tafi bisa rakiyar sauban da matarshi, sai Suraj da zai zauna tare da ita na sati biyu ya huce wata k'asa.....
Lokacin data dawo mutane da yawa sun shiga mamaki da dunbin al'ajabinta, masu mata kallon y'ar iska, da masu sheganta mata y'ay'a duka sun Raina kansu, hakan yasa da yawan su neman yafiyarta ciki hadda sameera data matuk'ar sake kama kanta, a nan ta sake tabbatar da surayyah tun asali ba ajinta bace, ba kuma tsarar k'awancen ta bace, ita d'in y'ar asali da gata ce gaba da baya, ta yarda abu d'aya ya had'a su shine k'addarar data raba ta da gida.
Duka wannan abun da yake surayyah mai kallon kowa da tsarkakakken zuciya ce bata sauya mata daga waccen matar ma'abociyar fara'a da son taimako ba, abu d'aya da ba zata iya ba shine sake aminta da ita ko bata damar shiga jikinta kamar da.

Suraj bai barta ta zauna a anguwar nan ba duk yadda take so kuwa, ya d'auke gaba d'aya ya maida ita d'aya cikin gidajen shi dake GRA.

*Germany*
Rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin tsari irin wanda khaleefa yake so da tsantsar soyayyah mara algus. Hak'ik'a khaleefa yayi nadama, yayi nadama irin wadda bazai tab'a dainawa ba har k'arshen numfashin shi. Da ace yana da damar da zai dawo da hannun agogo baya, daya dad'e da shafi tarihin soyayyar shi da Saleema a doron duniya. _wannan kenan_

Suhaana ta kammala had'a degree d'inta, alhmdllh za'a ce donta futo da result irin wanda ake so. A dai dai wannan lokacin mamarta ta d'auki hutu a gurin aiki suka tattara sukayi gida Sudan don gudanar da shagalin biki irin na al'ada.
Sunyi bikin su lafiyar Allah duk da raihana da khaleefa basu samu damar zuwa ba saboda dalilai masu nauyi da suka rik'e su.
Khaleefa ya tura mishi kud'i masu yawa matsayin gudunmawar su shida raihana.......

Alhamdulillah Yasmine ta haihu lafiya inda ta samu baby girl mai kama da ita da uban gaba ma. Bayan ansha rigima da rikici gurin yasmine akan lallai saita tafi gida tun cikin yana wata bakwai, a nufinta saita haihu gaban mamanta, shi kuma ya hana ta saboda wani family issue nasu can daya shafe su, a k'arshe dai sai k'anwar maman tace tazo da cikin ya shiga wata tara tana kula da ita har akayi haihuwar. Raihana kam ba k'aramin santin babyn tayi ba kamar ta gudu da ita lokacin data ganta, haka ta rik'e y'a gam gam tak'i ba kowa, ganin yadda take son yarinyar sai k'anwar maman yasmine da take tare da ita tace, "na fahimci dai kuna son yaara keda mijin ki, haka shima yayita santin yarinyar nan da yazo jiya, kuma ai bada jimawa ba zaku samu naku tunda naga bake d'aya bace.....".
Murmushi tayi ta d'ora hannunta a bakinta tana kallon yasmine, "kinji abinda aunty hafsa tace kuwa?". Murmushi auntie hapsa tayi tana barin gurin.
Yasmine tace, "naji nima dai kuma kusan kallon hakan nake miki tun kwana ki, yanayin da nake ciki ne yasa ban tab'a miki maganar ba".
"Au kema hakan zaki ce? Nifa Allah bani da komai kece tunanin ki yake baki hakan?".
"Humm wai kuwa anya kina kallon kanki a mirrow raihana? Gaba d'aya kin canja ga k'iba da kikayi kin zama big mama wallahi".
Harararta tayi sai kuma ta fara tunanin maganar yasmine d'in a zuciyarta, ita kanta tana jin sauyi a jikinta kad'an kad'an, sai dai abinda yasa tunaninta bai tab'a bata ciki bane saboda taga bata amaye amaye da irin laulayin da yasmine tasha.
Dariya yasmine tayi ganin ta tafi tunani sai tace, "gwara dai ki fara lissafi kada kiji haihuwa rana tsaka tunda Allah ya sauk'ak'k'a miki ba irin cikin mu bane".
Murmushi kawai tayi tace, "humm ba zaki gane ba yasmine nasan fa yadda masu ciki suke shan wahala ke kanki dubi yadda kika koma".
"Toh ai abinda nake so ki fahimta kowa da yadda abun yake zo mishi musamman haihuwar farko, amma a shawarce kije kiga likita, koda yake ke kanki zaki iya duba kanki tunda kinsan aikin.....". Raihana ta gyad'a mata kai cikin amincewa da batun yasmine d'in. Sun jima suna hira amma abun a ranta har ta dawo gida......
Har dare tana ta tunanin ta yadda zata tunkari khaleefa da zancen, sai tayi kamar ta fad'a mishi saita share, gashi shi sai tambayarta yake da son sanin damuwarta don wata sabuwar kulawa yake bata ta musamman, ga yawan fara'a a duk lokacin daya kalleta in taga dai dai har ajiyar zuciya yake saukewa wasu lokutan.
Da dare suna kwance tana ta mishi santin babyn su Ahmad yana sauraronta, tun yana taya ta har ya gaji da jin magana d'aya ya sake shigar da ita jikin shi ya d'ora hannunta a saitin cikinta, "Ina tunanin kema fa soon zaki samu naki babyn?".
Zaro ido tayi ta mik'e zaune tana kallon shi hadda k'ara haske a d'akin, "kar dai kaima abinda kake tunani kenan?".
Sai ya mik'e zaune da kyau yana kallonta, "tunanin me?". Sake waro ido tayi, "tunanin wai ciki ne dani".
Murmushi yayi har hak'oran bakin shi na bayyana yace, "waye ya fad'a miki haka?".
Shiru tayi cike da jin nauyin maganar data mishi, sai kuma ta rufe fuskarta da tafin hannunta.
Sake jawota yayi jikin shi ya fara jera mata tambayoyi, "kina jin ba dad'i a jikin ki? Ko tashin zuciya da son wani abu ko rashin son wani abu?". Duka ya jera mata tambayoyin a jere.
Girgiza mishi kai tayi, "Ni bana jin komai fa saboda bani da komai".
Wani murmushin ya sake yi, "Nima naga alamar hakan, bazan ce miki bakya d'auke da ajiyar babyna ba, iya gaskiyar dana sani ta wadatar cox ni bana son duk abinda zaki wahala nuru qalby Abdallah".
Saroro tayi tana k'ok'arin ajiye kowacce magana tashi a muhallinta, da yaga tana neman yima maganganun shi fashin bak'i sai ya maida wasan na manya, ya kuma shafe mata kowanne tunani da kwokwanto a ranta sai nashi.

Ranan suna yarinya taci sunan nafeesa mahaifiyar Ahmad. Y'an uwan su da yawa sunzo taya murna, haka y'an uwan Yasmine ma.
Raihana dai tana gidanta ranar tun safe ta kasa d'arawa ko nan da can, Cox ita ba wani son shiga hayaniyar mutane take sosai ba, bata futo ba har saida nadeeya matar Muhammad ta shigo mata, sun gaisa ta mata barka daga nan kuma suka shiga gidan yasmine d'in tare.

Ta samu yasmine da y'arta sunyi kyau Masha Allah, bayan ta gama sauraron mita da kumbure kumburen yasmine wai tayi fushi, har tayi ta gama ta hak'ura suka shiga hirar su kuma su ukun har nadeeya.
Suna tare har mazan suka taso office, yanzun ma kusan tare suka futo da nadeeya, daga inda ta samu Muhammad a waje sukayi sallama, raihana kuma ta bud'e musu gida suka shiga har Ahmad daya k'auracema gidan shi sai dare yake lallab'awa ya shige ya kwanta cikin kwanakin.
Ruwa ta kawo musu da abinci duk da basu ce mata suna jin yunwa ba, ta juya zata tafi taji an tab'a door bell, ta tafi don duba ko waye tunda jikinta har lokacin a suturce yake da gyale.....

Ja baya tayi tana kallon fuskokin y'an matan biyu gabanta yana tsananta fad'uwa, a cikin su fuskar da ba zata tab'a mantawa a rayuwar taba ta gane, macen data tab'a samun matsala da ita tunda uwarta ta haifo ta duniya...... Saaleema




_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA🧕*
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyaert lerwerl and doctor ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Storie


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login