Showing 51001 words to 54000 words out of 288773 words

Chapter 18 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1062

rufewa iya a cooler. Gefen iya suka zauna kan tabarma suna cin wainar. Ayman kam sai zuba loma yake saboda wainar tayi mishi dad'i ba kad'an ba, a duniya baya jin za'a samu wadda ta iya wainar fulawa irin raihana, yana ganin har degree tayi indai ta fannin iya sarrafa kowanne kalar abinci ne. Ita kuwa raihana dake d'osane tana d'an yafuta da kad'an kad'an wani tunanin take yi daban, tun tana iya cin wainar har ta daina ta zabga tagumi ta lula duniyar tunani, maganar Ayman ce ta farkar da ita ta juyo tana kallon shi, "bakya cin wainar nan fa Ina lura dake raihanatu, ni kuma nafi son kici sosai saboda daga yau ba lallai na sake samun damar ganinki irin haka ba, abincin ma nasan zai zama sau d'aya a tarihi". Sai kuma ya sake yin kalar tausayi ya tsame hannun shi daga abincin yaci gaba da maganar shi, "yanzu fa shikenan kin kusa zama matar wani raihanatu, zakiyi auren ki ki tafi ki barni bayan lokaci k'alilan ki manta dani ......".
Raihana tana kallon kwayar idanun shi itama cike da tausayin yadda zatayi kewarshi tace, "har abada bazan tab'a iya mantawa dakai ba Yaya Ayman, ka zamo mun d'an uwa garkuwa jigo da zan iya bugar k'irji nayi alfahari dashi a ko'ina, wallahi yaya Ayman da zan haifa d'an da nake da ikon bashi suna saina saka sunan ka, tabbacin zan dinga tunawa dakai all the times".
Shiru Ayman yayi wani abu abu mai wuyar fassaruwa shimfid'e saman fuskarshi, duk sunyi shiru kamar wanda aka aikowa da sak'on zagi, iya da take gefen su har lokacin sun ma manta da ita, gyaran murya tayi tace, "toh waye zai cinye muku abincin?". Kallonta kawai Ayman yayi ya maida hannun shi cikin abincin, raihana ma ci gaba da cin abincin tayi jiki a sanyaye, ba wanda yake iya cewa komai sai kallon kallo da Murmushin yak'e. Iya dai girgiza kai take inta kalle su tana k'ara karatun kowanne motsin su.
A dai dai wannan lokacin surayyah tayi sallama, duk suka d'aga ido suna kallonta. Sanye take da doguwar rigar super Holland ta yafa gyalen ta wadatacce, fuskarta washe da fara'a ta k'arasa shigowa, yara nabin bayan ta da kayan lemukan gidan da taga sun k'are da kayan shayi. A hankali raihana ta cire hannunta a abincin ta koma gefe.
Surayyah kam zama tayi kan tabarmar, yaran suka ajiye kayan a gabanta ta sallamesu da y'an kud'ad'e da kayan snacks cikin wanda ta kawowa iya.
Shima Ayman dena cin abincin yayi ya zaro wayarshi ya bada attention d'inshi a can. "Ina yini Auntie?". Raihana ta fad'a kanta a k'asa, da fara'ar ta sosai tace, "a'a raihanatu yakike ya maman naki". "Tana lafiya qalou". Auntie tace, "Toh Masha Allah ki gaisheta". Ta amsa da "zataji insha Allah".
Suna gama gaisawa ta mik'e ta yi musu sallama zata tafi, iya tace, "au har zaki tafi raihana?". Tace, "eh iya a gaishe da malam". Iya tace, "tom ki gaida gida da ummien taki na gode kinji Allah yayi miki albarka".
Mik'ewa Ayman da yake zaune yayi yabi bayanta, har takai k'ofar gida ya cimmata, "kin yiwa kowa sallama amma banda ni, meyasa?".
Juyowa tayi ta kalle shi, "Tom kaima sai anjima Yaya Ayman".
Murmushi ya k'ak'alo yace, "bari na taka miki". Sunci gaba da tafiya shiru kowa da abinda yake tunani har suka Isa k'ofar gidan su, har sunyi sallama zasu rabu raihana tace, "ooh Yaya Ayman dama Ina son in mun had'u mu k'arasa maganar nan, sai naga kud'i wancen watan? Ni kuma sai naga yanzu tunda na gama karatun.......". Da sauri tayi shiru tana kallon yadda ya d'aga mata hannu rai a had'e, "Ina ce mun riga mun gama wannan maganar dake tun a waccen ranar? Toh Ina ruwan ki don nayi miki abinda ba dole kika yi mun ba? Koda yake har yanzu baki gama fahimtar irin matsayin da kike dashi a gurina ba ko?".
Ita dai raihana shiru tayi ba tace komai ba, "Ina magana kinyi shiru raihanatu". Girgiza mishi kai tayi slowly tace, "kayi hak'uri Yaya Ayman".
"Good ki gaida ummie dasu jidderh".
Da gyad'a kai ta amsa ya d'aga mata hannu ya juya, itama shigewa gida tayi.

#########


Auntie ce zaune ta tattara nutsuwarta tas tana sauraron iya da take magana a lokacin, "abinda nake so na tambaye ki shine, "shin yaran nan haka zaki zuba musu ido ba maganar aure?". Murmushi auntie tayi tace, "iya akwai maganar auren su mana, Ayman akwai y'ar k'awata sameera nuriyya da suke soyayyah, khaleefa zai dawo nan da watanni biyu masu zuwa, idan yana da zab'in matar da yake so ba dole, amma idan babu toh akwai yayar Nur shaheeda har tafi Nur kyau da aji tana karatu yanzun haka a maitama sule, nasan bazai k'ita ba don ta futa son kowa k'in wanda ya rasa, saina had'a duka na aurar dasu hakan yayi ko iya".
Iya girgiza kai tayi tace, "idan har kin yaba da tarbiyyar yaran babu laifi, kuma idan sun amince suda kansu hakan yayi, Allah ya tabbatar mana da alkhairin shi". Iya ta fad'a tare da had'iye abinda tayi niyyar fad'a game da raihana da Ayman a lokacin.

@@@@@

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, bikin raihana sai dad'a k'aratowa yake, gidan su Imran sun kawo kayan lefe akwati mai daraja saiti takwas, sunyi komai dai dai k'arfin su har an tsaida lokacin biki nan da sati uku masu zuwa, duk wani shirye shiryen biki ya kammala saboda suna jin k'amshin da gaske wannan karon za'ayi da Imrana. Saboda a duk samarin da take yi babu wanda maganar shi ta tab'a kaiwa tsawon wannan lokacin har a karb'i lefe. Ranar da aka kawo wannan Kaya umma salaha kwana tayi bata yi bacci ba saboda tashin hankali, yaron ya cika taurin kai duk wasu sharud'd'a sai daya shallake su, bata manta karo na k'arshe da tasa akayi mishi magana a kan yarinyar y'ar iska ce yawon bariki take, cewa yayi ko a gidan karuwai take haka yake sonta, zai aure ta domin Allah. Na farko dama da aka fad'a sam baiyi tasiri ba, hakan yasa ta fara shirya bita da k'ulli da zagon k'asa, ranar da taje saloon da k'unshi suka tafi tare da Ayman har hoto tasa aka d'auke su a k'ofar gidan, aka tura mishi hadda doguwar wasik'a kamar wani abun arzik'i har shagon kasuwar da yake, kuma a dai dai inda zai gani ya karanta, ba komai aka fad'a ba sai Ayman shine wanda suke soyayyah da raihana sama da shekara takwas suke tare, ya gama lalata rayuwar yarinyar gaba d'aya, shiyasa sau biyar ana sa ranar aurenta duk wanda yayi bincike ya gano saiya barta, kaima kana tare da itane saboda bakasan ainahin wacece ita ba.
Maganar ta shige shi sosai ya Kuma ji haushi kwarai musamman duba da yanda suke ta fafatawa akan Ayman d'in tak'i rabuwa dashi, koda yake bari yaba kanshi maslaha Allah ne ya d'ora mishi masifar son raihana, kuma yau ko kanjamau ce a tare da ita ba abinda ya Isa yasa shi fasa aurenta, sannan matsalar Ayman ya riga ya dad'e da gamawa da ita, jira kawai yake a d'aura auren su, ko gaisuwa bazai k'ara yarda ta had'a ta dashi ba, dole wannan dangartakar ta k'are tunda dai shi d'in aiba Muharramin ta bane bare ace. Da wannan tunanin yaji sanyi a ranshi da k'arfin gwiwa.
Da hoton da takardar yayi musu kyakkyawan adani.
Na biyu munir aka sa yayi mishi magana face to face, still dai abu d'aya aka k'ara fad'a, nan ma yayi watsi, sun d'auka abun ya shige shi sai gashi da kwana biyar an kawo lefe, tashin hankali yasa ta kasa katab'us tunda abubakar ya fad'a mata, musamman da taji akwati har takwas, ko su Salma basu samu irin wannan lefen ba bare y'arta data aurar a wahale, k'arshe mijin bashi da komai duk k'arya ce ya dinga tsula musu, yanzun kusan su suke taimaka mata, don kar auren ya mutu nema asirin su ya tonu aji halin da suke ciki amma ita tuni ta gaji da wannan jeka na yikar aure. shine yanzu hankali tashe take neman yadda zata b'ullowa wannan aure na raihana.
( _Ku kuji fa, madadin ta kula da abinda yake gabanta ta kashe wutar gabanta, ta k'are da neman lalata auren wata don ta cusa bak'in ciki ga rayuwar iyayenta, toh hassada dai ga mai rabo_........)

Gidan su raihana kuwa y'an uwan ummie na kusa dana nesa duk sunzo sunga kaya sun yaba kwarai, ta b'angaren Abban suma mom ziyada tazo tare da babbar y'arta, kakar sukam tace sai biki ita ba zata iya gantalin zuwa ganin abinda ba tabbas ba, ai ba girin girin ba dai tayi mai, ta kuma hana kaf y'ay'anta zuwa da y'an majalisar ta, matar Abba abubakar kam a wannan karon bata hanu ba saboda tana son gani da idonta donta tabbatar da abinda y'an anguwa suke ta rad'e rad'in fad'a.
Saboda tsabar bak'in ciki da hassada kasa b'oye bak'in cikin ta tayi, gashi zane k'iri k'iri fuskarta ta nuna, haka ta dinga kyab'e baki da fuska tana yatsine yatsine. Har dai ta tafi ko ala sanya alkhairy ba tace ba.

Soyayyar raihana da Imrana kuwa sai abinda ya dad'a k'aruwa ma, yadda ta fahimci yana sonta sosai sai itama ta bada hankalinta a kanshi, tun waccen ranar bata k'ara had'uwa da Ayman ba sai dai waya, itama ba sosai ba yaja baya da ita sosai a hankali saboda ya ragewa kanshi rad'ad'in ranar da zasu rabu, ta bayan fage yana ta tunanin abinda zai siya mata as a wedding gift da zai burgeta sosai. Iya ma nata had'a mata magunguna irin na gargajiya da ake yiwa kowacce yarinya idan zatayi aure tun zamanin da. Da kanta takai mata da taje ganin kayan lefe, ta zaunar da ita ta karanta mata yadda zata yi amfani da kowanne a ciki. Ita dai ta karb'a tana dariya ta shige d'aki cike da kunya.

★★★★★★

Raihana tana zaune a d'aya daga kujerun parlon gidan su, sanye da doguwar rigar kinomo ta ciki kuma riga ce body hug da straight skirt da yabi lafiyar shape d'in jikinta ya zauna, tayi rolling kanta da k'aramin gyalen rigar blue, kayan ciki kuma black. Fuskarta akwai light make up data k'ara mata kyau matuk'a, gaisawa tayi da k'awayen ummie da Suka zo ganin kaya, suka amsa suna zolayarta wai ta saka su ummie a ranta duk ta rame, ita dai dariya kawai tayi don har ga Allah bata ga ramar da suke fad'a ba, d'aya cikin su da ummie take kira suwaeba tace da ita, "ya maganar ci gaba da karatu ko aiki? Da fatan ya amince zaku d'ora bayan auren ko". Girgiza mata kai tayi idonta na kallon k'asa, ummie ce ta yi musu bayanin yace shi bai yarda ba, baban ta kuma bai matsa ba, tunda gasu Salma da khausar nan ko y'ar higher institution d'in da tayi ma babu wadda tayi a ciki.
Suwaeba tace, "kuma dai don d'an kasuwa ne da ma'aikaci ne Ina tunanin zai iya barinta", ummie tace, "anya kuwa? Abun fa ra'ayi ne wani ko shine ya haifi boko bazai yarda matar shi taci gaba da karatu ko ta futa aiki ba".
D'aya cikin su tace, "haka ne kam kema haka akayi miki gashi raihana ta gaje ki". Dariya duk sukayi, mik'ewa raihana tayi ta nufi d'akin ummie, bin bayanta ummien tayi tana shirin kwanciya gefen bed tace, "ba tun d'azu al'ameen yace miki ya kaishi sitting room ba?".
Saita mik'e zaune kurum, ummie tace "bana son shashanci kin fi son sai ya gaji ya fara kiran ki a waya wato". Tace, "a'a ummie yanzu zan tafi ai". "Ya daifi" tana fad'a tayi hucewarta waje.
Ita kam raihana tunanin abunda zai je yazo kawai take, tafi son ace su muhibba suna nan ta tafi tare dasu, don tun wancen ranar bata k'ara yadda sun had'u ba y'an rakiya ba sai kwana kwanan nan, ummie tayi fad'a harta gaji ta kyale ta kawai don ba fad'ar dalilinta zatayi ba in abun zai kashe ta kuwa.
A sanyaye ta futo ta zura plat shoe a k'afarta ta nufi sitting room d'in. Yana tsaye a tsakiyar parlon hannun shi duka biyu goye a bayan shi ya zuba ma saman d'akin ido fuskarshi na fudda wani annurin farin ciki. Jingina tayi itama jikin k'ofar tana kallon shi kamar wadda aka turo, sauke idon shi yayi a kanta a nutse yana binta da tsantsar kallon so da k'auna.
"Mrs Imrana Muhammad Abubakar" sai data lumshe idonta ta d'ora hannunta a k'irjinta tana murmushi mai kama da dariya. Slowly ya tako gabanta sai bud'e ido tayi ta ganshi daf da ita har numfashin shi na sauka saman fuskarta, "alhamdulillah burina ya kusa cika raihana, Zan mallake ki a matsayin matata". Juyar da fuskarta tayi yanayin ta na sauyawa kad'an daga na tsantsar farin ciki zuwa na d'aure fuska ta soma tunanin yadda zata kauce mishi, Imran kam hannun shi yasa ya tokare gefe da gefenta ya k'ara kusantar da fuskarshi gare ta, cikin b'ata fuska sosai ta kalle shi idonta ba wasa a ciki tace, "me kake yine haka don Allah ka matsa.....". Ai bai bari ta k'arasa ba ya d'ora yatsar shi guda akan lips d'inta yace, "shhhhh! Yau dai d'aya raihana, yau d'aya ki barni naji d'umin jikin ki, na sumbaci wannan lausasan lips d'in. Only light romance baby". Ya kai k'arshen maganar yana shirin had'e bakinta da nashi.

_raihana kina ruwa tsilli tsilli🙆‍♀️_


_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page 1️⃣5️⃣


Da wani irin sauri raihana ta ingije shi ta matsa gefe can nesa tana sauke ajiyar zuciya kwayar idonta na tara ruwan hawaye, Imran dafe kanshi yayi ya juyo yana kallonta, yadda take jifan shi da wani irin kallon takaici kad'ai ya isa ya nuna mishi ta Kai mak'ura wajen fushi da jin haushin shi, k'ara matsawa yayi amma bai k'arasa har gabanta ba ya tsaya daga baya baya ya soma fad'in, "kiyi hak'uri my love ni ban d'auki kiss and hug as something different ba, ina tunanin in babu so da k'auna ba abinda zai shigo dasu cikin alak'ar mu, naga kina kallona wani iri, amma kiyi hak'uri na fahimci baki so shiyasa tun waccen ranar ban sake kwatanta aikata hakan ba, duk da yadda ni nake da ra'ayin hakan ga matar dana tabbatar zan aura, a yauma na kasa control yadda nake ji a kanki ne shiyasa, ji nake kamar har mun riga mun zama d'aya, bawai nayi da nufin b'ata miki rai ba". Sai ya durk'usa a gabanta bisa gwiwowin shi, "amma don Allah kiyi hak'uri ki gafarceni".
Duk yadda raihana taji zafin shi saida zuciyarta ta d'an sassauto taji sanyi da nutsuwa kad'an. "ka tashi kada wani ya shigo ya ganka a d'auka wani abun ne".
Girgiza mata kai yayi "sai zuciyar ki tayi sanyi kince kin hak'ura sannan".
Fuskarta babu yabo babu fallasa tace, "toh nace ya huce shikenan?".
Sake girgiza mata kai yayi yace, "umm umm ki fad'a har ranki da gaske bada sigar na takura miki ba".
"Toh na hak'ura don Allah ka tashi". Mik'ewa tsaye yayi ya samu guri ya zauna, itama zaman tayi.
Shiru babu wanda yace da d'an uwanshi kanzil har na tsawon wasu mintuna kafun raihana ta fara maganarta cikin sanyi da fad'in, "kayi hak'uri duk da na yadda dakai, na yarda abunda ya faru yanzu ya huce har abada bazai sake faruwa ba, Cox we have no much time da irin hakan zata sake faruwa ma, toh sai dai duk da haka ni bazan fasa yi maka magana ba akai, farko daka tab'a hugging d'ina kwanakin baya na d'auki fushi dakai sosai nasan baka manta hakan ba ae?". Gyad'a mata kai yayi, tace, "good toh bazan b'oye maka ba babu irin tunanin da banyi ba a lokacin, ciki harda na yanke alak'a ta dakai saboda na kalle ka a matsayin gama garin mayaudaran maza dake amfani da kud'in auren su dake gidan su yarinya su lalata mata rayuwa daga k'arshe su tsallake su gudu su barta. Sai dai a hankali d'abi'un ka suka dinga fad'a mun gaskiya a kanka da yadda ka d'auki alak'ar mu har na gane baka daga cikin jerin irin wad'an can da nake maka kallo a lokacin, sai dai kana da ra'ayin soyayyar zamani da y'an mata da samari kan gudanar a matsayin ba komai ba duk cikin so da k'auna ne which is totally wrong, da farko dai haramun ne ka sani har a addinan ce ka tab'a jikin matar daba muharramar kaba, na biyu shin duk munsan abinda zai faru damu gobe? Toh taya kenan zamu tabbatar da cewa mu mullakin juna ne? Ba fata nake ba amma cikin second ubangiji zai iya juya dukkan al'amuran shi ta fuskar da bamu tab'a zato bare tsammani ba, shin wane suna zamu kira kanmu dashi kenan? Mun yaudari kanmu ko kuma mun yiwa kan mu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login