Showing 270001 words to 273000 words out of 288773 words

Chapter 91 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1035

ka bani, tayi idda in aureta".
Komawa yayi kurum ya zauna ya dafe kanshi da hannun shi ba tare da yace komai ba. Kusa dashi ya zauna yana fuskantarshi da kyau kafun ya fara da cewa, "Khaleefa kana son wahalar da kanka a rayuwa. Da farko waccen yarinyar Saleema, yanzu kuma Raihana, duk da soyayyarta tayi maka kamun kazar kuku amma har yanzu ka kasa amincewa da hakan, kana ta yaudarar kanka wai zaka iya sakinta ni na aureta, ya kamata zuwa yanzun ace ka manta da waccen tatsuniyar ka shiga cikin tunani na zahiri, da farkon farawa kayi duba na tsanaki kan irin al'ummar da muke rayuwa tare dasu, koda ace wani abu bai tab'a shiga tsakanin ka da raihana ba, babu ta yadda za'ayi ma ka saketa na aureta mutane suja bakin su suyi gum suna kallon mu basu tanka ba, sannan ni a karan kaina da nake d'an Adam ba dutse mara zuciya a jiki ba ina jin kishin yadda wani zai rayu da mace koda bai tab'a mu'amulantar taba ni in aureta.... Duk sonda nake wa mace zan iya hak'ura da ita muddin ya zamana ta auri wani na, sannan ni ko lokacin dana furtawa raihana kalmar so bisa shawara ta wani abokin aikina ne, ba kuma nayi donta barka ta dawo gare nine watarana ba, a'a sai don na sauke nauyin soyayyarta a kaina, kuma alhamdulillah a lokacin na samu salama da nutsuwar ruhi, sannan a lokacin na fahimci auren ku gaba d'aya set-up ne duk da bata fad'a mun kai tsaye ba, shiyasa har na amince da abinda raihana ta fad'a mun....". Sai yaja gwauron numfashi kafun yaci gaba da cewa, "khaleefa soyayyar raihana ta shiga zuciyarka ko kak'i ko kaso, saboda raihana mutum ce da muddin ka zauna da ita zaiyi wahala ka yarda ka rabu da ita, bare kuma ace zama ya had'a ku k'ark'ashin igiyar aure, nasan ka fini sanin komai dazan fad'a a kanta yanzun.... Khaleefa tunda naji labarin zaku tafi wata uwa duniya daga kai sai ita ku kwana muhalli d'aya na fudda rai da ita gaba d'aya kaima kuma shirin ka ya rushe, shiyasa na turo mata sak'o mai nuni da hukuncin dana yanke na k'arshe a kanta ranar da zaku tafi,,,,,,,". Sai yaja ajiyar zuciya, "komai na rayuwa yana da iyakarshi, Allah bai tsara zan auri raihana ba tun farko shiyasa duk sonda nake mata ban tab'a bud'e baki na furta mata ba, alhamdulillah finally Allah zai maye mun gurbin ta da wadda zata fi zama alkhairy a rayuwata, bada jimawa ba zanyi yak'i in nemo soyayya kamar kowanne saurayi mai irin shekaruna, sannan a shawarce kaima ka ajiye komai ka nemi soyayyar matarka, don mun fara gajiya da ganin ka tuzuru, nasan auntie zasu so ganin jinin ka zuwa yanzu.....".
Dariya khaleefa da yake kallon shi yayi ya mik'a mishi hannu suka dunk'ule hannuwan guri d'aya a tare da d'aya hannun kuma suka sauke ma juna naushi a gefen kafad'a suna dariya.
"No one like you". Khaleefa ya fad'a cikin jinjinawa ga Ayman.
"Ka fad'i gaskiya kam, auren mu tun farko shiri ne, sai dai tun kafun mubar k'asar nan jikina ya fara sanyi, na fara jin shakkun sakinta don nasan mugun abun fad'a zan bar mata, sai dai dana ji dangantakarku sai naji sanyi a zuciyata, har na fara maka tanadinta don a ganina ka fini cancantarta........". Nan ya k'arasa bashi labarin zaman su in briefly tare da sake jinjinawa Ayman bisa ga kyakkyawar fahimta da sadaukarwa daya mishi.

Sunci gaba da hirar su duka Ayman zolayarshi yake, da yaga dai da gaske ba zai kyale shiba ya huta sai ya mik'e yana mishi sallama. "a'ah ya zaka gudu kuma muna hirar mu?".
"Na gaji da hira da k'aton tuzuru tunda muka zo gidan nan ban zauna da matata ba". Khaleefa ya fad'a yana kallon shi.
Dariya Ayman yayi sosai yace, "har ka samu bakin gori kaida matar ma suna ta tara a gurin ka".
"Humm! Haka ma zaka ce bayan saboda kai na takure kaina nayi komai ko".
"Toh ni saka nayi malam! A hakan ma kuma dai nasan duk an rage hanya shine za'a lallab'a ace an barmun, wato ruwa tasha ana so ana kaiwa kasuwa".
Harararshi kawai khaleefa yayi ya fuce don in ya biye mishi ba zai tafi ba.
Yaso shiga parlon k'asa sai dai bazai so ganin fad'uwa ba, yana tsoron yadda auntie take kallon komai har yanzun ta fuskarta. Lokacin daya shiga side d'in raihana ta kauce a parlon tuni don ta gama abinda take yi har abincin shi da mama haleema ta kawo ta adana mishi inda ya kamata.
Bai taba komai ciki ba don yaci abinci gidan iya, yadda yake a gajiyen nan kwanciya kawai yake son yi ya huta.
Koda ya shiga d'akin shi raihana ta tsabtace shi tas kamar ba d'akin daya futa ya bari da uwar k'ura ba.
Yayi shirin shi na kwanciya bacci tsab cikin fararen kayan bacci sol da suka futo da annurin shi, littafin addu'o'in shi da yake bedside ya fara dubawa kafun wani lokaci bacci ya silalo ya kwashe shi.


****Washe garin ranar tunda sassafe ya samu kira daga Abban su, sai ya zura jallabiyyah kurum ya futa don amsa kiran shi, ya same su tare da uncle d'inshi, ya durk'usa a gaban su yana gaishe su duka, suka amsa mishi kusan a tare.
Mukullin guest house d'inshi da suka baro jiya ya bashi yace ya d'auko musu kayan su idan ba damuwa, cikin sauri ya karb'i mukullin ya futa daga parlon. Yana futowa kuma ya had'u da Ayman zaije gurin su su gaisa, mik'a mishi hannu khaleefa yayi suka gaisa ya mishi side hug yana tambayarshi gajiyar tafiya, yana y'ar dariya yace, "ai tabi makwanci, ina zuwa kuma da farar safiyar nan na ganka da key".
"Abbane ya aike ni d'auko mishi kayan shi a guest house d'inshi da muka sauka jiya".
"Bari na shiga mu gaisa dasu saina raka ka muje". Khaleefa yace, "tom zanfi jin dad'i ma kuwa, amma kada ka zauna dogon zance".
Ayman yayi gaba yana fad'in, "yadda kake so". Yayi murmushi yana nufar parking lot na gidan.
Bai jima ba kuwa ya futo ya same shi, Da motarshi yayi amfani suka je ya d'auko musu kayan su gaba d'aya suka futo Ayman yana yaba kyan tsarin gidan.
Suna tafe suna hirar su har suka k'arasa gidan, bayan sun kai mishi kayan ma basu rabu ba don khaleefa jawo shi yayi b'angaren su. Suka zauna a parlour zuciyar khaleefa da tunanin raihana ko bacci take shiyasa ba motsinta kwata kwata.

~~~ ita kuwa bayan futar khaleefa ba jimawa ta futo ta nufi b'angaren auntien don su gaisa, ta shiga bakinta d'auke da sallama, sai tayi turus tana kallon suhaana data ke zaune kusa da momma da wata k'atuwar rigar bacci tayi rolling saman kanta da gyale hannunta rik'e da mug tana shan tea mai zafi. Ajiye mug d'in tayi ta nufe ta da gudu suka rungume juna tana fad'in, "tun jiya nake tambayar auntie ke...". Raihana tace, "ayyah ai bansan kun iso ba....". Saita zame jikinta ta durk'usa cikin parlon ta fara gaishe dasu momma da ammie, suka amsa suna tambayar ina ta shige suke ta nemanta tun jiya, Auntie data futo daga d'akin baccinta tace, "ai raihana ganinta yayi wahala". Momma tace, "ai na fahimci kamar bata son hayaniyar mutane tun a can". Auntie ta k'arasa futowa tana fad'in, "Ina ruwan Raihanatu bata son kwarabniya dama sam".
Ita dai da take jinsu murmushi tayi kanta a k'asa tana gaishe da auntien, bayan sun gama gaisawa take tambayar Ina mama haleema, auntie tace, "tana kitchen". Saita mik'e tama suhaana alamun ta biyo ta, aikuwa ba musu tabi bayanta suka futa zuwa kitchen d'in.
Stool taja mata ta zauna, ita kuma ta k'arasa kusa da inda mama haleeman take had'a abincin tana fad'in, "Ina kwana mama haleema".
"Lafiya lou fatan kin tashi lafiya me b'oye kanta daga cikin mutane". Y'ar dariya tayi tace, "kema haka zaki ce mamaa". Tana dariya itama tace, "eh mana ai gaskiya ne". Sai sukayi dariya, raihana ta tambayi dame zasu iya taimaka mata, mama haleema tasan kota hana su ba zasu bari ba, saita basu ayyukan da zasu rage mata. Raihana ta yarawa suhaana da yaren da take fahimta, ta matso kusa cikin jin dad'i tana taya su aikin. In zata yiwa mama haleema magana saita fad'awa raihana, ita kuma ta juyawa mama haleema hausa, in mama haleema ta bata amsa da hausa kuma sai raihana ta juya mata harshe ta fad'a mata. Haka dai sukayi tayi har suka gama aikin. Mama haleema ta zuzzubawa kowa ta basu suka kai musu. Raihana ce ta kaiwa su Abba nasu abincin daga nan suka gaisa, ita kuma suhaana ta kaiwa matan tunda bata shirya ba. Bayan duk sun kai musu abincin karin kumallon k'arshe ta ba raihana nasu khaleefa tunda ance mata suna tare shida Ayman, ta tambayeta kota had'a musu ita da suhaana. Tace, "eh ba damuwa tare zamu tafi da ita idan ta dawo daga sauyo kayan da taje".
Lokacin da suka shiga khaleefa ne kad'ai tare da Ayman, suhaana ta tsaya daga baya raihana kuma ta k'arasa ciki tana sake wata sallamar. Khaleefa ya amsa k'asa k'asa yana binta da kallo, Ayman kuma ya amsa yana d'orawa da fad'in, "Masha Allah sannu da k'ok'ari matar big Yaya". Tayi murmushi bayan ta ajiye trayn tana gaishe da Ayman d'in, ya amsa cikin faram faram. Taso gaishe da khaleefa don basu had'u ba tun jiya ma ita rabon data ganshi, sai dai taji kunyar aikata hakan gaban Ayman. Saita mik'e kawai ta karb'i trayn hannun suhaana data cake a bakin k'ofa sukayi ciki. Khaleefa har ya mik'e da nufin bin bayanta ya fasa don yaga ba ita kad'ai bace, shi kuwa Ayman suhaana yabi da kallo yana murmushi, yaso ace ta shigo ko gaisawa sunyi kamar yadda suka saba a duk sanda suka had'u, sai dai ba damuwa tunda tana tare da matar twin d'inshi komai zai zo mishi da sauk'i.
Khaleefa ne yayi saving d'insu suka ci abincin tare suna hirar da tun lokacin da suke rayuwa tare gidan iya.
Suna hirar amma rabin hankalin su ya kasu kashi kashi, shi khaleefa kacokan tunanin shi yana kan raihana, yayinda Ayman yake son ganin suhaana, yana ta tsarawa da kwance yadda zai tunkareta da zancen soyayyah don bazai yadda yayi wasa da damar shiba.

Su kuwa bayan sun gama karyawa wanka raihana ta shiga, ta futo suhaanan ma ta shiga, lokacin da zata futo tuni raihana ta shirya cikin riga da skirt na atamfarta mai kyau, ta futowa suhaana wata doguwar rigarta da take zaton zatayi mata tunda kusan size d'insu zai zo d'aya. Rigar kuwa ta mata cif cif kamar dama tun asali tata ce bata raihana ba.
Suna ta hirar su tana taya raihana k'arasa gyara inda bata gama gyarawa ba jiya, da yawa in tayi abu sai taga kamar yasmine, ohh ita tunda tazo ma ba suyi waya da yasmine d'in ba ko sau d'aya.
Sai ta tsaya da aikin da takeyi ta lalubi wayarta tayi dialling no yasmine d'in, sai dai layin yak'i tafiya, hakan yasa ta ajiye wayar gefe suka k'arasa zura ragowar kayan a wardrobe suka rufe, hanyar futa suhaana tayi, raihana ta dakatar da ita ta hanyar tambayarta, "tafiya zakiyi kuma muna hirar mu?".
Sai ta juyo tana kallonta, "akwai abinda zanyi yanzun nan zan dawo".
Raihana tana kallonta tace, "nasan ba dawowa ma zakiyi ba".
Tace, "insha Allah zan dawo". Ta fad'a tana fucewa ita kuma ta zauna gefen gado.
Futowarta yayi dai dai da futowar khaleefa zai futa, ganinta yasa shi dakatawa har ta k'araso suka gaisa ta fuce shi kuma ya juya akalar shi zuwa d'akin da raihanan take.........

****Doctor surayyah ce durk'ushe gaban momma tana jujjuya kud'in data bata a hannunta, ta d'ago da niyyar tambayar na meye momman ta riga ta da cewa, "kiyi hak'uri mun sake aikata wani laifin gare ki surayyah, wannan kud'in sadakin kine na auren ki da muka mayar da mijin ki uban yaran ki Suraj..... Ina fatan bamu kasance ma'abota son kan mu da yawa ba?".
Shiru surayyah da take durk'ushe tayi ta d'auke wuta..........

*Barka da babbar ranar juma'ah ga d'aukacin y'an uwa musulmi na duniya*.



_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy seven7️⃣7️⃣


Kwakkwaran numfashi ma ta kasa yi bare ta iya amsawa momma, ba zata ce taji farin ciki ba haka ba zata ce bata yi farin ciki ba, tana ganin duk abinda malam zaiyi a duniya ba zai tab'a cutar da ita ba, haka itama wannan baiwar Allah data nuna nadamarta gareta a fili.
"Kiyi hak'uri surayyah". Momma ta sake bata hak'uri.
Tana girgiza kai tace, "ba kuyi kuskure ba, haka duk hukuncin da kuka yanke dai dai ne".
"A'a surayyah bafa za'a ce babu kuskure cikin abinda muka aikata ba, sai dai kiyi hak'uri kawai, zaki fi fahimtar komai idan kika samu zama da Suraj ko wani cikin iyalan gidan late Abdallah ya warware miki komai game da auren sa da kuma yadda muka fahimci gaskiyar sharrin dasu haleema da Aysha suka had'a don haleeman ta aure shi".
"Insha Allah momma". Ta fad'a jikinta a sanyaye.
"Allah yashi miki albarka". Momma ta fad'a ita dai ko amsawa bata iya yiba ta huce abinta.
Tana shiga d'akinta ta watsa kud'in saman bed ta kwanta tare da dafe kanta da hannunta, andal da take zaune gefen gadon ta juyo tana kallonta sai dai bata ce da ita komai ba a wannan gab'ar tana buk'atar a barta taji da kanta kafun k'ara mata haske ko bata shawara. Ita kuwa kasa nutsuwa tayi, tunda taji ance auren Suraj taji tana son jin labarin abinda ya faru bayan tafiyarta. Sake futowa tayi ta zauna kusa da k'afar momma tace, "mommy ki bani labarin abinda ya faru bayan tafiyata don Allah".
Gyara zama momma tayi dama saboda kada ta hau bata labari bata nemi ji bane.
"Wato surayyah bayan tafiyar ki abubuwa da yawa sun faru, Suraj ya shiga matsananciyar damuwa har da kwanciya doguwar jinya, daga nan bai sake samun nutsuwa ba, yayi neman ki duk Inda yasan zai same ki amma bai same kiba, har k'ara yayanki ya shigar dashi court yana tuhumar shi da laifin b'atan ki, anyi shari'a babu wanda yayi winning akan wani saboda rashin kwakkwarar hujja, bayan lokaci mai tsayi saina fara mishi maganar futo da mata yayi aure tunda naga abun nashi bana k'are bane, amma fafur yak'i, kullum akayi magana sai yace kin tafi da soyayyar shi da tarihin auren shi a rayuwa, tun muna ganin abun wasa har ya fara bamu tsoro, a nan muka fahimci lallai abun nashi ba mai k'arewa bane, ta gefe d'aya ga haleema data mato a sonshi da k'aunar shi sai bin kanshi take yana Shashshare ta. Bisa shawara da shige da fucen Aysha muka lik'a mishi haleema aka d'aura musu aure, a wannan lokacin saida yayi zama na musamman dani game da auren, ya sake tabbatar mana bashi da gurbin da wata mace zata samu matsuguni a gidan shi da zuciyarshi, haka dai muka yo mishi rubdugu da fad'a sai bai sake ce damu komai ba, ya koma gurin yarinyar itama ya zaunar da ita ya mata bayanin irin abinda ya mana bayani, amma soyayyah ta rufe idonta har tasa take d'aukan abun kamar mai sauk'i ta furjanye idanuwanta ta shigo gidan suraj. An d'aura aure haleema ta tare a part na kusa da naki tana zaune, tunda taje bata ga k'eyar suraj ba hasalima an kawo ta da kwana uku tafiya ta kama shi wata k'asa cikin k'asashen African nan, haka ya tsallake ta yayi tafiyarshi ya shafe kusan wata hud'u sannan ya dawo bisa tursasawar su mukhtar, sai dai koda ya dawo suna muhalli d'aya bata sauya zani ba, haleema tayi duk kissa da kisisinar da tasan zata iya abun baiyi aiki ba, inta takura ma ranta ne yake b'aci a banza. Duk da haka ba tayi zuciya ba don a gidan Suraj bata rasa ci sha ko suttura mai kyau ba, abu d'aya ta rasa miji da kulawar shi da soyayyarshi. Toh haleema ta jure zaman shekara biyu da rabi a gidan suraj kafun ta gaji ta nemi saki da kanta ba tare da neman shawarar kowa ba, ya d'anka mata takardar sakinta uku bayan ya titsiyeta da tuhumar gaskiyar abinda ya faru game da matarshi, don ya kama su kwana ki suna hirar ita da matar wanshi Aysha, a lokacin ya nuna kamar bai ji suba ashe abun yana ranshi sai da akazo wannan gab'ar, da farko k'in amsa laifinta tayi, har saida ya had'a abun da hukuma, a can ta warware yadda komai ya faru, daga ita har Aysha bai saurara musu ba saida ya hukunta su da hukunci mafi tsanani, sannan mijinta ya k'ara da turo mata sak'on sakinta har gidan iyayenta.
Rayuwa fa tayi tsanani wa wad'annan mutane biyu da Suraj don tuni ya sallama komai sai harkakokin kasuwancin shi yasa gaba, yayinda a kullum dare yake mana kukan yana da y'ay'an shi a wata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login