Showing 285001 words to 288000 words out of 288773 words
Chapter 96 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page eighty 8️⃣0️⃣
Final💃💃💃
Ja da baya raihana tayi ganin bak'in ba nata bane tace, "sannun ku" da kyar bayan ta danni zuciyarta, amna ce kad'ai ta iya amsata don Saleema kam kasa bud'e baki tayi sai zubawa raihana ido kawai tana kallonta, gabanta yana tsananta fad'uwa. Lokacin da suka gama shigowa cikin parlon raihana juyawa tayi zata shige d'akinta ta basu guri, yayinda a lokaci guda Amna ta kalli Ahmad dashi kanshi khaleefan da suke jifan su da kallon da me kuka zo?
"Kuyi.....hak'uri..... munzo magana da kai khaleefa". Amna ta fad'a tana yin k'asa da kanta.
Sai a lokacin khaleefa ya ankara da raihana da take k'ok'arin guduwa ya kira sunanta, bata iya amsawa ba, ta dai juyo ta kalle shi. Ya taso tsam daga inda yake yazo har inda take tsaye ya rik'o hannunta, ta narke mishi tana girgiza kai a lokaci guda ta bud'e baki don tayi mishi bayanin da zai fahimta, ya d'ora hannun shi saman lips d'inta yace, "shhh!". Da sauri ta had'iye ragowar maganarta tana kallon shi, har lokacin hannun shi yana kan lips d'inta, madadin ma ya d'auke hannun sai ya fara kewaya leb'en da babbar d'an yatsar shi.
Kusan a tare mutum biyu suka lumshe ido, Saleema da raihana, saleema kam a lokacin wasu muguyen harsasai ne suka soki zuciyarta suka raunana ta, a take idonta ya ciko da ruwan hawaye.
Shi kuwa murmushi yayi mai kyau, ya hura mata iska saman idonta, da murya mara amo yake fad'in, "kinsan me yasa nake k'ara sonki?". Ta bud'e idonta kad'an tana kallon shi ta girgiza kanta, ya sake matsa hannunta dake cikin nashi da salon soyayyah na musamman ya k'arasa cewa, "saboda ta ko'ina kinsan abinda kike yi a rayuwa, kina da sanin ya kamata irin wanda ba kowanne mutum keda shiba a wannan zamanin, sai dai a wannan gab'ar bazan iya sauraron wad'an can mutanen inba da alfarmar kiba kuma a gaban ki, tafiyarki tana nufin kowa cikin su ya kama gaban shi don bazan gansu ba".
D'aya hannun ta d'ora saman nashi ta kalli wajen da suke tsaye suna iya hango su tace, "let's go".
Kusan a tare suka tako har lokacin hannun su sark'afe cikin na juna. Daga d'an nesa dasu kad'an ya tsaya yayi magana da dakakkiyar murya, "me ya kawo ku". Saleema da jikinta ya gama yin sanyi ta fara magana da rawar murya, ya juya mata baya da sauri, ta durk'usa ita kuma ta fara neman yafiyar shi, yayi saurin d'aga mata hannu ba tare daya juyo ya kalleta ba yace, "Amna ki fad'awa k'awar ki komai ya faru ya k'are tsakanin mu, ita ya kamata ta yafe mun don ni na dad'e da yafe mata, nine nake neman azurfa sai kuma na samu zinare, kina ganin zanci gaba da yak'i?".
Ba Saleema ba hatta Amna saida maganar ta dake ta, a sanyaye ta girgiza mishi kai ta kamo hannun Saleema da tuni ta fara kuka durk'ushe cikin d'akin sukayi waje.
Raihana ta sauke ajiyar zuciya tabi bayan su da kallo cike da tausayawa.
Saleema kuwa bayan ta futa kuka sosai ta dingayi, Amna bata hana taba har saida ta tabbatar ta samu sassauci a zuciyarta, ta matso kusa da ita ta dafa kafad'arta zata fara magana tayi saurin d'aga mata hannu, "ba sai kin jaddada mun abinda na kusa haddacewa a kwakwalwar kaina saboda yawan ji daga gare kiba, Amna a yau na k'ara tabbatar da irin nisan da khaleefa ya mun, kina kallo Amna saboda k'iyayyah khaleefa ko iya kallon fuskana ba yayi,,,,,, Amna ina zan had'u da ra'ees? Da gaske har yanzu ra'ees yana sona kamar yadda kike fad'a? Indai yana sona ki taimaka ki fad'a mun inda zan same shi domin shine cikakken masoyina, da bai tab'a kyamata a kowanne irin yanayi na rayuwa ba".
"Alhamdulillah!! Nagode Allah da kika fahimci gaskiya har zaki fuskanceta, k'awata kamar yadda kika sani ra'ees yana nan da soyayyarki, bari in warware miki asalin gaskiyar da kika k'i tun farkon had'uwar ki da khaleefa, Saleema khaleefa bai zo da niyyar yaudarar kiba, hakazalika bai tab'a mafarkin rabuwa dake ba, kece kika damawa kanki lissafi, shiyasa na zab'i in tona miki asiri a farkon fara soyayyarki da taufeeq, domin yaron yana da matuk'ar had'ari, gashi duk hanyar da nabi don ganin na kawo miki gyara kin k'i yarda, shine dalilin da yasa na kai khaleefa garden waccen ranar, don already tun a lokacin ni nasan yayi aure, nazo miki da labarin farkon dawowarshi k'asar nan kika k'i saurarona, shiyasa a waccen lokacin daya ganki kina kissing taufeeq ya yanke hukuncin rabuwa dake, Saleema da ace kin yi dogon nazari kafun rabuwarki da khaleefa a ranar daya fara baki tarihin shi, da yanzu kece matar da yake aure ba waccen yarinyar ba, but alhamdulillah ta silar ki gashi yanzu ya nemo mahaifin shi, kowa ya fahimci su d'in halastattun yara ne da aka Haifa ta hanya mai kyau, and su sun futo daga babban family a Nigeria".
Sosai Saleema take kuka tana fad'in, "nayi nadama Amna, tabbas nasan ke d'in mai k'aunata ce, sannan kin kasance k'awa ta gari mai neman kawo gyara a rayuwata, tabbas hak'k'in ra'ees ne ya toshe mun kwakwalwa, ya kuma hana in samu khaleefa, don nayi butulci gare shi mummuna, ya rasa komai nashi saboda ni, ya dinga wahaltamun a k'asar da bani da uwa bare uba, Amna ki gaggauta kaini gurin shi don Allah ko yafiyar shi na nema.....".
Amna ta rik'o k'afad'unta tana k'arasa taya ta share hawayen fuskarta......
Fews months later
Abubuwa da yawa sun faru cikin watannin, ciki hardaa haihuwar raihana inda ta samu twins mace da namiji, bayan tasha tsananin wahala gurin haihuwa, da yake cikin familyn su ba wanda yasan cikin ya tsufa, da yawa dai sun d'ago kamar tana da ciki amma basu tabbatar ba sai labarin haihuwar kowa yaji. Aikuwa Auntie tace maza ya nemi ticket subi flight su taho gida a gyara yarinyar mutane inba so yake ranshi ya b'aci ba, ta dinga fad'a kamar zata ari baki don da gaske bai kyauta abinda yayi mata ba, don tace haihuwar fari saida bik'i da kula da gyara.
Da yake har lokacin raihana tana asibitin a can ake kula da ita da babyn don ba k'aramin wahala tasha ba, duk can su yasmine da sauran abokan khaleefa suka je ganin yaran suka mata sannu. Tsabar yadda khaleefa ke tausayinta ko futa baya yi yana tare da ita a kowanne motsinta ya dinga jera mata sannu ba iyaka.
Cikin satin yayi ciku ciku ya nema musu ticket suka taho Nigeria. Ya tambayeta inda zai kaita, tace ya fara kaita gurin Auntie, ta mishi alkunya ne kawai amma zuciyarta tana gurin ummienta, koda suka sauka a Abuja sukayi waya da ummie take fad'a mata zasu k'araso Kano nan da kwana ki biyu, sai tasa ta had'a ta da surayyahn ta waya sukayi magana, ta nuna mata itama uwace a gurin raihana kamar ita, duk abinda zata yiwa raihana ta riga tayi shi, don haka ta k'arasa zaman wankan jegon kurum a gurinta. Duk yadda auntie taso fahimtar da ita k'in sauraronta tayi don ita harga Allah bata ga abinda za'a kawo raihana ta mata wanda surayyan bata yiba.
Anyi taron suna lafiya, taron daya tara manyan mutane da dangi na nesa dana kusa, yayyen ummie da hajiya inna ma duk sunzo.
Yara suka ci sunan Abba da Auntie bisa shawara da amincewar miji da matar, saboda alkunya sai ake kiran namijin abie macen kuma anam, da yake raihana ba mai son hayaniya bace ranar sunan ma sashen momma ta gudu ta b'oye kanta sai tsiratun mutane suka san inda take.
Kulawa mai kyau auntie take bawa mai jego da yaranta cikin zallar soyayyah da k'auna. Dama khaleefa kwana shida yayi a garin ya koma bakin aiki.....
Amma kullum dare sai yayi video call da matarshi yaga yaran shi yadda suke k'ara murjewa da wani sihirtaccen kyau.
Gaba d'aya sai ya k'agu ta dawo cox gidan duk sai ya mishi faad'i, tunda sukayi aure basu tab'a rabuwa da juna ba sai yau, koda zasu rayu ba'a tare ba amma still suna a muhalli guda. Gashi ta b'angaren girki ya kasa jurar cin abincin gidajen cin abinci kamar yadda ya saba lokacin yana matashi, ta ko'ina raihana tayi karan tsaye wa rayuwarshi baya ganin iyawar kowa inba tata ba, k'arshe dai sai noodles ya dinga ci da shayi da burger.
Watanni uku sun shud'e amma auntie bata da niyyar dawo mishi da matarshi, hakan yasa ya d'auki hutu na sati d'aya a gurin doctor raazi don andal tuni tayi retire yanzu haka tana sudan cikin y'an uwanta. Washe gari kuwa yabi flight sai Nigeria.
A lokacin daya sauka raihana tana zaune cikin parlon auntie, sanye da wata doguwar riga ta material mara nauyi, gashinta nad'e a k'eyarta yaci gyara sai d'aukar ido yake da fudda sirrin k'amshi mai dad'i. Kanta a durk'ushe tana ta kiciniyar had'awa anam da take ta tsala ihu madara, gaba d'aya duk ta rikice sai b'arar da madarar da ruwan take har ta samu ta gama ta d'ago yarinyar ta rungumeta tana feeding d'inta. Khaleefa da yake daga bakin k'ofar shiga parlon yayi murmushi ya k'arasa karb'ar jakar kayan shi daga hannun d'aya cikin yaran security daya mishi rakiya har gurin. Sam raihana bata ji takun shiba sai saukar hannun shi kawai kan gwiwar k'afarta, ta d'ago idonta tana kallon shi, har razana tayi zata ja baya sai kuma yayi saurin rik'o ta, "calm down mana kada kisa anam ta kware, dama naga ojoro ake ganin bana kusa, yaushe mukayi dake za'a dinga basu Madara?".
Sosai ta shagwob'e fuskarta kamar zata mishi kuka tana kallon shi har lokacin, "Allah ba zaka gane ba amma dole saida madarar".
Baice mata komai ba ya mik'e daga gabanta ya zauna gefenta yana duban agogon wayarshi. Sai a lokacin ta russuna tana gaishe shi, yak'i amsata saima laluben wayarshi daya fara, a zuciyarta tace mai hali ai baya fasa halin shi. Saida ta gama da yarinyar ta juya zata ajiye ta ya kamo hannuwanta ya zare yarinyar a ciki ya sumbaci forehead d'inta.
Fridge ta nufa ta d'auko mishi drinks cikin taku na zallar aji da k'asaita, khaleefa yabi bayanta da wani jirkitaccen kallo har ta dawo gaban shi ta ajiye plate d'in, ya sauke ajiyar zuciya k'asa k'asa. Sake komawa tayi ta d'auko mishi dambun nama da kayan snacks, tazo ta ajiye zata sake komawa ya ajiye anam ya jawota jikin shi gaba d'aya ya rungume, cikin whisper yake tambayarta, "Wai abincin gidan gaba d'aya zaki kawo mun?".
Ta girgiza mishi kai tana son zillewa tace, "a'ah...ai snacks ne wannan..abinci zan kawo maka?".
"Nace miki Ina jin yunwa? Ko kina tunanin kayan snacks ya kawo ni".
K'asa tayi da idonta tace, "baka fad'a ba kam amma nasan kasha hanya, and kome kaci zuwa yanzu ya zazzage".
Ya sake matse ta cikin jikin shi yana k'ara kallon fuskarta yace, "it seems like bakiyi farin ciki da ganina ba ko?".
Tayi murmushi mara sauti da shagwob'abben murya tace, "nayi farin ciki mana".
"Toh aini ban gani a yanayin ki ko fuskar kiba, sannan ko kewata bakiyi gashi nan kin sake fresh hankalinki kwance sai walwali kike kamar diamond".
Ta kai mishi dukan wasa a k'irji tana fad'in, "Allah kaima baka kewana gashi nan kaima kayi fresh".
Yabi hannun da kiss yana sake jifanta da kallon zallar so da k'auna, "da banyi kewar kiba bazan datse aikina na taho ganin ki keda babies d'ina bayan ina da tarin abubuwan yi a office ba, kema kin sani".
Shiru ta mishi tana k'ok'arin zamewa a jikin shi,
"Na d'auka zan tarar kuna shirin komawa fa". Ya fad'a yana d'aukar glass cup.
Sai a lokacin tayi nasarar zamewa daga jikin shi tace, "Ina kuma?". Tayi tambayar tana k'ok'arin zuba mishi ruwa a cikin cupin daya rik'e a hannun shi,
Cup d'in ya sake mata ya mata alamar ta bashi, saita langwab'ar da kai tace, "Allah wani cikin Auntie ko mama zasu iya shigowa fa".
Had'e rai yayi a take yana kallonta ba wasa yace, "kika sake yimun maganar wani Allah zaki tunzurani nayi abinda banyi niyyah ba, ke bakisan dama na fara d'aukar zafi daku ba, duk wankan haihuwar duniya baya huce kwana arba'in amma ni har ana neman huce watanni uku baki da niyyar dawowa, and nazo kuma kina kawo mun shirmen wani wai zai ganmu, you better start your job from here don na daina zama kaman gwauro tunda kina kusa".
Shiru tayi kamar wadda ruwa ya cinye har ya gama maseefar yayi shiru, sai bata sake musu ba ta shiga bashi ruwan a cup, tsabar neman dalili kamar me shan tafasashshen tea haka ya dinga sipping.
Haka duk ta dinga bashi komai a baki har dambun naman, yana ci in romantic way gently har ya gama, tasa tissue ta goge mishi baki.
Mama haleema da tazo bakin k'ofa ba jimawa ta juya zata bar gurin tana murmushi.
Tana fara takawa taci karo da auntie, "a'a ya kika fasa shiga kuma ko bata parlon?".
Mama haleema tace, "a'a tana ciki naga ba ita kad'ai bane".
"Ita da waye kuma?". Ta tambayeta da mamaki.
"Bak'o daga nesa".
Auntie tana kallonta still tace, "khaleefa ne ya biyo bayan matarshi kenan".
"Eh ai yama yi k'ok'ari wata hud'u ake shirin tafiya fa".
"Toh bashi ake yiwa gata ba, wannan yaran inta tafi gida daga ita sai shi waye zai taimaka mata dasu, yama gama zaman shi ya tafi don raihana sai tayi wata biyar zata koma shima saboda karatunta ne".
Mama haleema tana dariya k'asa k'asa tace, "don mugunta! kyasan yadda zakiyi da rigimar shi ai dama kun saba".
Itama auntien dariya tayi tace, "yi musu knocking ina son shiga cikin bedroom na d'auko ma yaron nan magani".
Mama haleema ta koma da baya ta kwad'a sallama tun kafun ta k'arasa.
Raihana ta sauya direction da sauri tana amsawa, khaleefa ya d'an harareta kad'an, ta d'ora hannunta a baki tana mishi dariya k'asa k'asa.
Kusan a tare suka shigo ita da auntien, khaleefa ya russuna yana gaishe su, mama haleema ta amsa shi faram faram har tana zolayarshi, auntie kam sama sama ta amsa don kada ma yaga fuska yazo da wargi😎
Bai wuni a gidan ba yayi fucewarshi gidan twin d'inshi suka sha hirar su ta zumunci da suka jima basu yiba. Da dare ya dawo ya samu auntie tasa an shirya mishi masauki a can nesa da sashen da suke. Bai zauna ba nan ma tafiyarshi gurin Abba sukayi hirar su mai dad'i ta uba da d'a.
****A hankali kwanaki suka dinga shud'ewa, duk wata hanya da zaiga raihana ko su had'u zuwa yanzu ta toshe ta, tun yana zura ido yaga iya gudun ruwan su har ya fahimci ruwan ba mai k'arewa bane gashi yau kwana biyu ya rage komawarshi don baison ya samu matsala gurin aiki.
Hakan ya sashi fuskantar auntie a daren yake fad'a mata da kud'urin da yazo, Saida ta gama sauraron shi tass sannan ta nuna k'in amincewarta. A lokacin rasa inda zai saka ranshi yayi, gashi ya gama shirin komawa da ita amma ya fahimci auntie tana son mishi shinge da hakan. Sai ya mik'e yana tambayarta inda raihanan take wai zasuyi magana, daga inda take ta kirawota tazo tace ya fad'i abinda yake son fad'a matan a gabanta.
Ya sosa k'eya ba tare da yace komai ba ya futa a parlon.
Ba d'an k'aramin rikici ya musu a gidan ba sauran ranakun da suka biyo baya, kowa ya bashi hak'uri sai yace shifa saboda yunwa tana neman kama shi bazai koma ba saida matarshi, (ku kujifa sai kace kaf garin ba abinci sai k'asa🤣). Da anyi magana ya kafa hujja da yunwa kamar itace abincin. Dole Abban su ya shiga rigimar tasu wannan karon, shi ya tausasa Auntie ta hak'ura zata bashi matarshi su tafi amma tace bisa sharad'i. Tun baiji sharad'in ba yace ya amince.
Shima dai Suraj saida yayi dariya don ya gane rigima ce zalla irinta surayyah zata rik'e matar mutane ta maida mai aure gwauro.
Sharad'inta shine raihana zata je gurin familynta na Kano ta kwana musu biyu, sannan tare zasu tafi da mama haleema ta taya ta rainon.
Khaleefa ya sauƙe ajiyar zuciya don ya d'auka sharad'in yafi haka sai yaga abun duk irin wanda za'a iya jurewa ne, mama haleema kam ma dai su za'a yiwa gata.
Haka kuwa akayi raihana ta ziyarci Kano na kwana biyu sannan ta dawo aka fara shirin komawarta, wani sabon gyara auntie ta kaita akayi mata in an out. Ranar da zasu tafi kuwa mutane da yawa suka musu rakiya suka tafi Suka barsu cike da kewar twins.
Sosai aka bud'e sabon shafin soyayyah da nuna kulawa tsakanin raihana da khaleefa, har saceta yayi suka gudu saboda kunyar idon mama haleema, duk da tana basu rata sosai.
Sai a lokacin khaleefa yaga yadda suke kwanan zaune da anam