Showing 75001 words to 78000 words out of 288773 words

Chapter 26 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1101

ya shigar da motar ciki ya daidaita parking a parking lot.
Shiya fara futa direct ya haura stairs ya shige d'akin shi ya kwanta rigingine idonshi na kallon sama, ganin yanayin shi duka sai auntie ta bishi da text massage, "zamu bi jirgin k'arfe takwas gobe". Ko daya duba baice komai ba ya ajiye wayar, yana ajiyewa kuma kiran khaleefa na shigowa, a yanayin da yake baya son magana kowa, sai kawai yayi switch up d'in wayar duka.

★★★★★

K'arfe takwas da mintuna suna tsaye a filing tashi da saukar jirage na AMINU Kano international airport, babu b'ata lokaci suka hau kan screening akayi duk abinda ya kamata suka shiga cikin jirgi suka lula gajimare.

*Brandenburg airport, Berlin*

Khaleefa na hango da Ahmad a wannan filin tashi da saukar jirage tsaye da yammacin wannan raana, sunyi kyau cikin shigar shadda sky blue da mahaifin Ahmad ya d'inka musu cikin jerin kyaututtukan shi gare su, d'inkin manyan kayan baya rasa nasaba da ganin most of their pics da k'ananun kaya suke yi, kawai sai yayi hasashen maybe basu da manyan kaya ko guda d'aya, shine ya d'inka musu su kusan kala biyar biyar, irin d'inkin da matasa suke yayi a lokacin, ya kuma zauna musu dass a jikin su kamar anyi measuring da tip. A nutse Auntie da Ayman suke k'arasowa har suka zo inda suke, wani irin bak'in ciki ne ya lullub'e khaleefa from no where lokacin da yayi tozali da fuskar mahaifiyar shi, sai ya kasa k'arasawa ya tarye su har saida Ayman yazo ya rungume su shida Ahmad yana musu congrats. Da kyar ya iya k'irk'iro murmushi ya wanzar saman fuskarshi yana kallon Ayman cike da tausayi, "ta samar damu ta hanyar da bata dace ba, ta had'a mu yak'i da k'addarorin mu! Mutane har sun fara kyamatar mu a k'asar daba ruwan wani da wani ma Ina ga mun koma Nigeria kuma?". Khaleefa shi kad'ai yake wannan maganar a cikin zuciyarshi yana kallon fuskar Auntien. Ahmad ne ya fara k'arasawa gabanta ya russuna yana yi mata sannu da zuwa, shi kam khaleefa yana daga inda yake tsaye yana kallonta da wannan murmushin dai har lokacin. Cikin farin ciki surayyah tasa musu albarka idonta cike taff da hawaye tana kallon su, basu yi wata doguwar magana ba suka hau taxi suka kaisu Hotel d'in da suka yi musu booking d'aki. Har suka sauke su khaleefa baiyi wata doguwar magana da kowa ba, yanayin shi ba k'aramin fargaba da zullumi ya wurgawa Ayman ba, ya dad'e da fahimtar khaleefa ya sauya wata d'aya kafun kammala karatun shi, ya yiwa Auntie maganar tace yayi busy ne, yanzu kuma gasu sunzo gurin shi babu wani d'okin ganin su ko murna, sai Ahmad ne yake haba haba dasu.
Ni kam tsayawa kawai nayi ina kallon tsananin kamar da take tsakanin wad'annan twins da har yanzu bata sauya ba, sai banbancin haske da khaleefa yafi Ayman kad'an da d'aurarriyar fuska, da wasu sauye sauyen na tsarin aiwatar da abu ga wanda ya samu kusanci na kusa dasu kad'ai zai iya gani.
Room and parlour ne, suna shiga auntie ta shige bedroom d'in da k'aramar jakarta, shi kuma Ayman ya zauna a parlon, khaleefa basu zauna ba shida Ahmad suka tafi nemo musu abinci.
Kafun su dawo sun yi uzurirrikan su sun sauke faralin dake kansu tuni. Auntie bata ci wani abincin kirki ba Ayman d'in ma haka, ita kanta ta fara ankara da yadda khaleefa ya koma gefe kamar wani bak'on mutum sai Ahmad ne yake musu kamar shine jinin su.
Sun yi mata bayanin abubuwa da yawa, Ahmad hadda labarin no yabo da aka bawa khaleefa a jiya yake bata. Ta sake jin dad'i ta musu addu'o'i sosai. Basu bar gurinta ba har dare, Ahmad yaso su tafi da Ayman ya kwana apartment d'in wani a cikin su sai dai yak'i sam, dole suka hak'ura suka barshi zai kwana tare da Auntie.

Toh Tafiyarsu gida Nigeria ta banbanta data Ahmad, saboda shi ba gida ya nufa ba kai tsaye k'asar turkey yayi inda zaiga wata y'ar wan mahaifin shi da yake zaune din din din a can. Sun gama shirya komai dama tun kafun ya gama karatun shi, har sun daidaita da yarinyar a waya ganin juna kawai zai je suyi ayi maganar aure.
A daren ranar kusan raba dare sukayi yana taya khaleefa had'a abubuwan shi muhimmai suna kuma hirar su akan k'udururrukan su, shi Ahmad yaso su fara gabatarwa da Auntie maganar aikin tun kafun subar k'asar, sai dai khaleefa yace a bari abi komai sannu a hankali, In sun nutsu sai su had'u su tunkareta da maganar su biyu, maganar binciken su akan familyn mahaifin khaleefa kuwa tuni sun gama shirya yadda komai zai kasance da zarar khaleefa ya koma gida.
Koda zasu rabu ba k'aramin sanyi jikin su yayi ba, ji suke kamar in sun koma Nigeria ba zasu ci gaba da kasancewa tare kamar yadda suke a nan ba. Dama masu iya magana suka ce sabo........


@@@@@@@


A yau da misalin k'arfe shida da rabi jirgin su khaleefa ya sauka a Nigeria, bayan shafe adadin shekaru tara cip yana karatu a Germany bai tab'a zuwa hutu k'asar shiba ko sau d'aya tunda ya tafi.
Koda khaleefa ya shak'i iskar k'asar shi saida yaja gwauron numfashi yayi hamdala ga Allah subhanahu wata'ala daya dawo dashi lafiya kamar yadda ya tafi, A yau ga khaleefa ya dawo da tarin ilmummuka da nasara akan abinda yaci burin karanta don ya taimakawa al'ummar k'asar shi dama na wasu k'asar baki d'aya. Auntie suna sauka a jirgi ta ware gefe ta kira sameera a waya saboda da ita ne suka shirya agender zata turo shaheeda ta d'auke su a motar ta, khaleefa da Ayman na tsaye gefe guda ba wanda yake iya cewa da d'an uwanshi kanzil k'ark'ari dai in sun had'a idanu su yiwa juna murmushi. Sun d'anyi jira na a k'alla adadin wasu mintuna kafun shaheeda ta k'araso, ko kafun tazo khaleefa har ya k'osa sai faman duba agogon hannun shi yake. Auntie ce da take rataye da jakarta ta kira su suka taho Ayman rik'e da babbar jakar kayan khaleefa shi kuma khaleefa rik'e da wata y'ar k'arama suka zo gaban motar suka tsaya.
A idanun khaleefa wata kyakkyawar budurwa ce fara sol ta bayyana, kallo d'aya yayi mata ya fad'a kogin tunanin inda ya santa? Ganin bai tuna ba saiya watsar da tunanin a gefe, ita kuwa rungume Auntien tayi tana mata sannu da zuwa, auntie cikin farin ciki tace, "sannun ki da k'ok'ari kema". Ayman ma k'arasawa yayi yace, "big Auntie sannun ki fa". Fuskarta da fara'a har lokacin tace, "Kai za'a yiwa sannu Yaya...." Sai kuma tayi shiru ta saci kallon khaleefa daya d'auke kai tamkar ma baisan da wanzuwarta a gurin ba, a ranta tace wannan sarkin jin kan shine khaleefan kenan, sai kuma ta tab'e baki ta bud'ewa auntie front seat zata karb'i Jakarta ta zura mata, "a'a barshi shaheeda zan zauna a baya nida Ayman". Tana fad'in haka ta shiga gidan baya Ayman ma haka, ko kanzil khaleefa baice musu ba ya shige mazaunin driver, kallon shi shaheeda ta kuma yi a karo na biyu, ganin Sam ba fuska a tare dashi har yanzu sai ta kalli Auntie, "feel free dear ya hutar dake ma". Murmushi kawai tayi ta shiga gefen shi ta zauna kurum.
Slowly yake tafiya da motar suna nuna mishi hanya har suka Isa anguwar malam kuma tsohuwar anguwarsu ta da. Nan ma khaleefa bin komai yake da kallo tamkar bak'o a garin.
Yana tsaye a k'ofar gidan ya zuba mishi ido kamar wanda yake karantar wani abu, ganin haka sai Ayman ya k'arasa gaban shi ya dafa mishi kafad'a, "welcome back home bro". Murmushi ya tattaro da kyar ya yiwa d'an uwan shi sannan ya tsallaka yabi bayan su auntie da har sun shige gidan.

Iya tana zaune tsakar gida ta shimfud'a k'atuwar tabarma ta shirya cikin atamfarta mai kyau kamar wadda zata futa wani kwarya kwaryan biki. Tana ganin su ta k'ara fad'ad'a fara'ar ta ta fara yi musu lale marhabin. Kusan a tare khaleefa da Ayman suka k'arasa suka durk'usa a gabanta, dafa kansu tayi d'aya bayan d'aya tana tuno da lokacin suna yara. Shaheeda kam gefe guda ta zauna ta ciro wayarta a jaka tana daddannawa.
Malam ma da yake sitting room jin motsin su ya futo dashi, yazo suka rungume juna cikin farin ciki da tsantsar murnar ganin su cikin k'oshin lafiya, musamman khaleefa da suka d'au shekaruuu basu ganshi ba, sai dai gashi nan sun ganshi kamar Ayman. Cikin girmamawa su duka suka gaisa da malam, ya amsa su da fuskar dake nuni da farin cikin ganin su.
Abinci iya ta soma d'ebowa tana ajiye musu a gaban su kala kala da lemukan da tayi musu duk na gargajiya. Abun har dariya yaba khaleefa a ranshi yake tuna iya nanan da kirkinta in mutum yazo saita k'arar da abincin gidanta kaf a kanshi. Ayman ne ya magantu, "iya wa kike tarya da wannan tarin abinciccikan, mu ko khaleefa?". Harararshi iya tayi tace, "a'ah! Kaji ka kai kuma da wani batu, kuda kullum muna tare duka tafiyar taku ta jiya ce fa, toh magaji na shiryawa duk wannan sai in yaso ya san muku".
Dariya auntie da malam sukayi suna kallon khaleefa daya ke bin kwanukan abincin da kallo kamar me nazarin wani abu, cikin sigar zolaya Ayman ya sake cewa, "toh ai sai kiyi mishi bayanin duk abinciccikan don ya manta su fa da alama". "Da gaske magaji ka manta cimar ka ta gado sai irin abincin masu jajayen kunnuwa?". Fuska a had'e khaleefa yake kallonta, duk gurin babu wanda baiyi dariya ba har shaheeda da take zaune tana kallon su a gefe saida ta murmusa. "Kinsan fa duk duniya khaleefa ya tsani a kira shi da sunan nan". Ayman ya fad'a yana sake dariya k'asa k'asa. Iya ce tace, "au toh meye khaleefa meye magajin? Duk abu d'aya ake nufi dai in baka sani bama yau in fad'a maka ga uwar ka nan tana ji ai ta fad'a maka da bakinta kaji".
K'ara tamke fuska yayi ya kalli malam da yake kallonsu kurum yace, "me ran k'arfe Allah zan bar gidan nan".
Malam yace, "a'a kunga ku kyale shi don Allah, yaci abincin shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali". Duk guntse dariyar su sukayi, khaleefa kam hankalin shi kacokan ya mik'awa iya da take mishi bayanin sunan kowanne abinci na gurin dalla dalla, a ciki biyu kawai zai iya ci itama iya donta manta waye khaleefa, Sam bai iya cin d'an wake ba tun yana yaro, sai yasa ta zuba mishi dambun shinkafa daya ji zogale da gyad'a.
Ai koda ya koma gefe sai kawai ya fara mik'a loma baji bare gani, suma sun zuba wanda suke ganin zasu iya ci a gurin, auntie ta tambayi shaheeda, "wanne zaki ci cikin girkin iya, gasu nan dai sai ki zab'a". Murmushi tayi tace, "Ni ko dambun ma kika bani". Aikuwa auntie ta zubo mata dambun fal plate ta had'a mata da zob'o drinks don wannan kam tasan favorite d'inta ne ko bata tambaya ba.
Shikam oga khaleefa ginger and lemon yasha, babu laifi yaci abincin da yawa kuma yaji dad'in shi, rabon daya ci wani abinci mai yawan haka har ya manta ma shi. Auntie da iya nata hirar su tana basu labarin irin nasarar da khaleefa da abokin shi Ahmad suka samu, malam sun yaba shida iya sunata addu'o'i. Khaleefa ne ya soma mik'ewa ya wanke hannun shi ya d'aura alwala ganin ana gab da kiran sallar magrib, malam ma tashi yayi yaje yayi tashi alawalar sannan ya futa masallaci, khaleefa da yake tsaye daga gefe bin bayan shi yayi, sai dai bai k'arasa masjid d'in ba ya tsaya jiran a kira sallah a nan k'ofar gidan, ko kad'an baiyi mamakin ganin yadda mutane suke tayi mishi magana ba, don yasan zuwa yanzu sun manta dashi sai dai ko in suna yi mishi kallon Ayman ne. A haka Ayman d'in ma ya futo ya same shi bayan an kira sallah har an tayar.
Suka bi jam'i suka yi sallah, ko da aka sallame su kam basu futa ba suka ci gaba da zama tare da malam da masu zuwa yana yi musu k'ari har lokacin da mukhtarin isha'i ya shiga.
Sai da sukayi sallar isha'i cikin jam'i sannan suka jero su uku suka nufo gidan. Malam ya shige sitting room su kuma suka shiga parlon iya inda duk suke, suma da alamu idar da sallar su kenan.
Basu yi wata doguwar hira ba yanzun kam sukayi sallama da iya, malam ma suka je sukayi sallama dashi sannan suka tafi khaleefa da alk'awarin sai ya dawo zuwa na musamman gurin malam.
Yanzun kam auntie ce take driving, Ayman a gefenta, shi kuma da shaheeda a baya, ya rasa dalilin da yasa ake ta cusa mishi zama guri d'aya da yarinyar nan shi kam.
Babu jimawa suka k'araso gidan su, Ayman ne yayi amfani da key na gurin shi ya bud'e get, auntie ta cusa hancin motar ta ciki, bayan ta daidaita parking duk futowa sukayi, khaleefa da yake bak'o ya tsaya yana kallon gidan, kamar ba shine gidan da suke zuwa ganin aiki shida Auntie kafun ya tafi Germany ba, sannan kamar ba shine gidan da sukayi video call da Ayman ba ranar da suka tare a ciki.
Auntie direct taja hannun shaheeda suka yi part d'in su, Ayman kuma ya tsaya a parlon k'asa yana nunawa khaleefa gidan ciki da waje, main parlour mai d'auke da d'akuna hud'u da sitting room a k'asa, sai k'ofar stairs guda biyu d'aya a bud'e inda zaka bi zuwa saman dasu Auntie suka bi, sai d'ayar da take rufe ruff da key. A jikin spare key Ayman ya duba ya bud'e k'ofar, nan stairs na hawa sama ya bayyana, ta wata k'ofar daban kuma parlour, khaleefa ya haska torch ta wayar shi saboda duhu ko'ina, shima parlour ne wadatacce hadda dinning area, sai bedrooms guda uku sai sitting room a ciki, da kitchen wadatacce mai k'ofa biyu, d'aya tabi ta cikin parlon, d'aya kuma ta futa ta bayan vantilation d'in gidan, gurin akwai k'aramin corridor.
Khaleefa tunda suka shiga yake kallon part d'in, har dai ya kasa shiru ya tambayi Ayman da yake ta aikin mishi k'arin bayani "yanzu wannan part d'in sama da k'asa zaman me Auntie take dashi ba kowa? Ai gidan nan ya muku girma indai ku kad'ai zaku rayu cikin shi". Murmushi Ayman yayi ya dafa kafad'ar shi yace, "wannan b'angaren da zamu zauna ne ni dakai bayan munyi aure, amma fa batayi mana Dole ba duk wanda yake da kud'in yin ginin shi daban zai iya gina nashi ya zauna koya kama haya ita vata da damuwa".
Wata irin fad'uwa gaban khaleefa yayi dum! dum! Sai yaji duk k'afafun shi sun sage mishi kamar ba zasu iya d'aukar gangar jikin shi ba, ba shiri ya samu gefen wani d'an tudu ya zauna tare da dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu, a yau gaba d'aya sai yanzu ya samu sa'idar tuno ta, tuni ranshi ya koma bak'ik'irin ya manta da tunanin komai sai kalmar da take mishi yawo aka, """koba kasan kowanne mutum da uba yake ado ba..... A zuciyar shi yaci gaba da tambayar kanshi, toh mu kuma da muke shegu dawa zamuyi ado kenan?""". Ayman ganin ya shiga damuwa sai ya zauna gefen shi ko la'akari da k'urar gurin baiyi ba yace, "kayi hak'uri khaleefa dama ita Auntie bata tsawwala ba tace mutum zai iya kama haya a duk inda yaga yayi mishi". D'ago da kanshi yayi ya girgiza mishi kai yace, "noop ko kad'an ni bani da dogon buri a rayuwa tun da can kai ka sani bare yanzun". Ayman cikin aminta da zancen shi hundred percent yace, "na sani kam, toh amma tunda ka dawo na fahimci wasu tarin sauye sauye a tare dakai, don Allah d'an uwana ka fad'a mun me yake damun ka? Kasan fa a duniya bamu da kamar juna......". Yanzun ma sake girgiza mishi kai yayi ya mik'e tsaye, "Babu wani sauyi a tare dani Ina nan yadda ka sanni rashin samun cikakken nutsuwa ne maybe yasa kaga hakan yanzu ma". Sai ya kalli b'angaren saman yace, "saman ma kamar k'asa yake kenan?". Ayman babu yabo babu fallasa don yasan ya b'oye mishi ne, kuma dama a yadda yasan khaleefa indai har ba sauya hali yayi ba, sai abu ya kusan kashe shi yake bud'e baki ya fad'a ko damuwa ce kuwa, sai yace, "eh iri d'aya ne muje ka gani mana".
"A'a ka barshi kawai, ya kamata ace by now munyi wanka mun huta gajiyar tafiya kuma". Cikin gamsuwa duk suka futo daga b'angaren, saida Ayman ya rufe sannan Suka bi hanyar da Auntie tayi. Parlour ne suka tarar zagaye da komai blue, sai dinning me d'auke da kujeru k'alilan. Tsayawa khaleefa yayi turus yana jira yaji inda zasuyi, shima Ayman baiyi magana ba ya nufi nasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login