Showing 27001 words to 30000 words out of 288773 words

Chapter 10 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1041

fara zaman yunwar taki ne saboda nayi miki magana akan babban abokin ki k'anin mahaifiyar ki?".
Mik'ewa tayi zaune ta k'ak'alo murmushin dole tace, "kiyi hak'uri ummie ni banga laifi a maganar kiba Sam, nasan gaskiya kika fad'a, a matsayin ki na mahaifiyar da tafi kowa sona nasan ba zaki so wani abu na cutarwa ya same ni ba, tabbas nayi kuskure na sake da yawa, gashi yanzu bansan ta yaya zan iya rage kusancin muba, bansan ma kota yaya ba, tunda ba komai ne ya kawo alaqar mu har zuwa yanzu ba sai kyautatawa da tarin halaccin shi gareni".
Nazarinta ummie ta k'ara yi kafun ta nisa tace, "Ni fa ba wai ina nufin ku rabu ko bana son alakar ki dasu bane, a'a Ina son ki dinga kiyayewa, babu laifi idan kunyi hira dashi a waya ko a k'ofar gidan ku ko gidan iya, muddin ba abinda ya keta shari'a zaku aiwatar ba, amma a dinga ganin shi yana yawo dake a motarshi za'a samu k'atuwar matsala, mutane da kike ganin su abune mai sauk'i su siyi sharri a kasuwa su lik'a wa mutum bare......."
"Insha Allahu zan kiyaye yadda kike so ummie duk da wasu lokutan karantar abinda nake ciki kawai yake ki ganshi, amma zan dinga kauce mishi".
Ummie tace, "Allah ya kyauta".
Had'a shayin tayi zata sha tace, "ummie ina khausar take tunda nazo ban ganta ba".
"Khausar ai tun zuwanki tana gidan Salma bata dawo ba".
"Tab su hajiya daru sai da aka samu wanda aka rik'e". Ummie tace, "aikuwa dai". Tana k'arasa fad'a ta mik'e ta nufi d'akinta.
Daga nan itama raihana breakfast tayi da daddad'an abincin ummienta data jima bata ci ba, bayan ta gama ummie tace ta shirya ta tafi can gidan masu jego watak'ila suna buk'atar ta wajen shawara da had'a abinda za'ayi.
Ko kayan jikinta bata sauya ba ta zunbula hijab da facemask ta huce.


*****************

5:30pm agogon k'asar jamus.
A farfajiyar baya ta babban apartment d'insu, zaune suke kan wasu kujeru na roba masu k'ayatarwa, duk da suna opposite juna amma dogon table ya raba tsakanin su, dukkan su sanye suke da kauraran kayan da zasu tare musu sanyin da ake bulbulawa a garin yau.
Kallon juna sukeyi tamkar kallon bankwana irin in sun had'u ba zasu sake had'uwa d'in nan ba. Khaleefa ne ya fara sauke ajiyar zuciya suka lumshe idon su a lokaci guda.
"Saleema". Ya kira sunanta a tausashe, "my future husband" ta amsa da wata kamilalliyar murya tana sake jifan shi da wani irin kallo na tsantsar so da k'auna.
Matsawa ya sake yi daf da ita ya hura mata iskar bakin shi mai d'umi a saman idanunta, "kin kuwa San yadda nake tsananin sonki Saleema?".
Girgiza mishi kai tayi tace, "sai ka fad'a".
Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi yace, "Ina sonki da yawa Saleema fiye da yadda kalmomin bakina zasu fad'a, ji nake kamar rayuwata ta fara ne daga lokacin dana fara ganin ki, ban tab'a soyayyah ba hakan yasa nasha wahala wajen iya bayyana soyayyata" murmushi yayi mai k'ayatarwa still yaci gaba da maganar shi, "kin kuwa san son wani baya buk'atar wani hujjah, idan har zaka iya kawo hujjar da tasa kake son wani to wannan shi ake kira da soyayyah, idan kuma ba zaka iya ba shine k'auna, Ina k'aunar ki Saleema".
A hankali ta mik'e cikin takunta na yauki da kissa ta kewayo gaban khaleefa ta zauna kan table d'in daya raba kujerun su, k'afarta na gugar tashi, numfashinta na sauka saman fuskarshi kamar zata shige jikin shi, ga wani azababben k'amshin turarenta da dama tuntuni yake barazanar kasssara jijiyoyin hancin shi na sake kai mishi farmaki na kusa. Cikin wata siririyar murya tace, "idan har zuciyarka lambu ce, bana son na kasance flower a cikinta, saboda flower k'aramin guri zai iya isarta, amma Ina son na zama kamar ciyawa, Ina buk'atar wadataccen guri, don Allah khaleefa kada ka rage wani gurbi da wata d'iya mace zata samu har ta shiga ta zama kwayar cutar da zata cinye dashen ciyawata....".
Tana gama fad'in haka ta dire k'asa kan k'afafunta.
Shima mik'ewa yayi suna kallon juna har kamar zai shigar da ita cikin faffad'an k'irjin shi ya b'oye ta.
"Every heart has love and pain! Only way of expression is different, ladies hide it in their gorgeous eyes, Saleema koda ba zaki ce komai ba Ina iya kallon komai ta cikin kwayar idon ki, soyayyar ki ta gaskiya ce ba algus a ciki, toh meyasa ni zan kasa baki cikakken guri kamar yadda kika yimun? Wallahi Saleema zan fad'a kamar yadda na saba fad'a, ban fara sonki don na daina ba, kin cike ko'ina na cikin zuciyata baki bar ko d'igon rata da wata zata miki kutse ba". Ya k'arasa fad'a yana zuba mata ido, eyeball to eyeball suke kallon juna.
Before they know sai ga goshin su ya had'e guri guda tsinin hancin su na had'uwa.
Saukar hannun Saleema da yaji gadon bayan shi shiya dawo dashi cikin hayyacinshi, ya janye jikinshi baya daga gareta, ya duba agogon dake d'aure a bayan hannun shi, "time for magrib prayer Saleema ya kamata muyi sallama".
Cikin jin nauyin shi kad'an tace, "okay byee....".
Kafun ta k'arasa khaleefa ya dakatar da ita ta hanyar fad'in, "shhhh! kada kice mun sai watarana saboda k'aramar kalma ce da take haddasa rad'ad'i da yawa, ga mutumin da yake sonka sosai kake sonshi kaima".
Cikin langwab'ar da kai tace, "toh me zance kenan futurehus".
Wani shegen murmushi ya mata yace, "koda yaushe kice sai mun sake had'uwa".
Itama murmushin tayi tace, "i will take note from now ma, meet u again".
Ta k'arasa fad'a had'e da blinking kiss to him, ya karb'a kamar zai manna a kumatu sai kuma ya wulla mata kayanta. Ta cafe tana dariya.
Shima ya juya yana murmushi, tunda ya fara tafiya ko sau d'aya bai waiwayo ba, saida ya kai k'arshen katangar dai dai inda zai shige d'akin shi ya waigo ya kalleta ya d'aga mata hannu da wannan murmushin.

Da daddare bayan ya baro apartment d'in Ahmad sai daya tsaya dai dai apartment d'inta yana kallon k'ofar kamar zai ganta a jiki, kafun yaja k'afafun shi jiki a sanyaye ya wuce nashi guri.
Ko daya kwanta kasa bacci yayi, moments d'insu na d'azu ya tsaya mashi a zuciya sai tuna kalamanta da sautin daddad'ar muryarta yake, baisan me yasa ba amma komai na Saleema yayi mishi, itace irin zab'in matar da yake so, mutane suna fad'in baka tab'a samun abinda kake so fully amma a had'uwar shi da Saleema ya k'aryata hakan, Allah yana iya mallaka maka komai dai dai yadda kake son shi.
Haka khaleefa ya kwana ba wadataccen bacci sama sama, a hakan kuma daya d'an runtsa zai fara mafarkin masoyiyar shi masu kama da zahiriyyah.

Tun a waccen ranar khaleefa da Saleema basu sake had'uwa ba, dama kuma shi mutum ne me tsari da yake yin koman shi a tsare, a yini sau biyu suke yin waya, daga safiya sai ko idan ya samu chance da rana, in babu kuma sai dare, a times ma text yake mata da daren kawai yayi kwanciyar shi, farkon soyayyar su Saleema tasha wahala kafun ta fahimce shi da inda yasa gaba, haka zatayi ta damuwa ta yini tana kiran wayarshi baya picking idan ta matsa mishi ma sai yayi switch up na wayar duka, amma daga baya data gane haka tsarin shi yake saita bishi a yadda yake suka zauna lafiya. Zasu had'u duk k'arshen sati, suyi waya duk safiyar duniya shikenan.
A wannan karon kam karatu ne yasha kanshi, tana ranshi sai dai bashi da lokacin kanshi bare ya ware nata, haka satin yazo ya huce basu had'u ba. Kullum yana cikin research da practice kai na burning, ko abincin kirki ya daina ci.
A wani dare bayan ya gama shirin kwanciya bacci wayarshi ya d'auko zai kirata sai yaga rututun missed call, raba dai dai akayi tsakanin Saleema da Ayman. Bayan kira hadda guzirin text massage.
D'aya ne daga Saleema, Amma hud'u daga Ayman ne, sai ya fara duba nata daya gani a farko, "masana sukace ka kusanci wani mutum wanda zai saka farin ciki, amma ka zama mafi kusanci ga mutumin da bazai iya farin ciki ba sai tare da kai, sai kaga banbancin, toh ni tun a yanzu na fara gane banbancin, sati biyu ba tare da ganinka ba, kwana uku babu wayarka na wujijjigu matuk'a har garkuwar jikina ta kasa jurewa na kwanta ciwon rashin ka a kusa future husband I miss you, I miss you more".
Murmushi yayi a lokacin daya karanta sak'on Saleema, sai ya duba na d'an uwan shi wanda duk complain ne "kwana biyu sai kiranka nake kak'i picking duk bakaji yadda zazzab'i ya lullub'e ni ba, gaskiya yau ka kirani naji muryarka in ba haka ba bazan iya bacci ba".
Murmushin dai ya sake yi yana tunanin wanda zai soma kira tsakanin su, yasan dukka kwantaccen rikici zai riska gurin kowannen su, amma babu wanda yafi tsoro kamar na Ayman, Saleema zai iya shawo kanta cikin sauk'i tunda suna tare a k'asa d'aya gini d'aya, amma Ayman ko abu ya huce ya dinga mita kenan.
Lokacin daya kira Ayman waya suke da Nur, amma yana ganin Kiran ya bata uzuri yayi picking, ko sallama bai tsaya yiba bare batun jin lafiyar juna, complain kawai yake, "yau kwana na nawa Ina kiranka fisabilillah? Wato sai yanzu kaga damar kirana, toh nima bani da lokacin ka yanzun lokacin masoyiyata ne......". Kit ya kashe wayar.
Shidai khaleefa dariya kawai yayi, ya sake kiran shi sau biyu amma busy. Sai kawai ya share shi ya kira tashi masoyiyar shima, sai dai me? yau bai tari lucky ba itama bata d'aga ba, ba dabi'ar shi bace kiran waya da yawa, shiyasa yana mata kira biyu ya ajiye wayar. Yana son yaji muryar auntie amma dare yayi ta iya yiwuwa ma tayi bacci yanzu haka.

Washe gari tunda yayi sallar asubah bai koma bacci ba, gyare gyaren daya kwana biyu baiyi a gidan ba yake, sai daya tabbatar ya gyara komai ya zubar da duk wasu shirgi na gidan sannan ya zauna yayi breakfast, wayar Saleema ya sake trying sai dai har ta katse bata d'aga ba, sai hankalin shi ya soma tashi kuma, lafiyar Allah bazai kira Saleema tak'i d'aga mishi waya ba, there must be something behind,
Bayan yayi sallar azahar tsaye yayi a gaban d'akin shi yana kallon d'akinta. Ya dad'e yana k'ila wa k'alan yaje d'akin yaji lafiyarta ko a'a, daga k'arshe sai kawai ya kasa jurewa ya nufi d'akin. Knocking yayi duk da yaji shiru kamar ba kowa a ciki.
A hankali Saleema da take kwance ta taso tazo ta bud'e k'ofar, sanye take da riga iya gwiwa Ash colour sai dogon wando bak'i daya saukar mata har k'asa kanta babu d'ankwali sai manyan kitson attached daya sauka har gadon bayanta. Kana ganin yanayinta zaka fahimci tana cikin halin ciwo har y'ar rama tayi. Fad'ad'a fara'ar fuskarta tayi tace, "au kaine? Ni na mayi fushi".
Shi kam khaleefa kasa cewa komai yayi sai kallonta yake kawai yana nazarin abubuwa da yawa a tare da ita, yadda ta rik'e k'ofa gam like her life defends on it kad'ai ya isa ya bayyana gab take da fad'uwa in taci gaba da tsayuwa.
Sai ya cire takalmin shi ya shiga cikin d'akin, aikuwa juyawar da zatayi wani irin juwa ya d'ebe ta, khaleefa ya tafi zai tarye ta da hanzari sai kuma Allah ya bata sa'a kafun ya kai hannun shi jikinta ta rik'e jikin window. "sannu Saleema, tun yaushe baki da lafiyar ne? Kinje asibiti ma?".
Rintse idonta tayi a lokacin da khaleefa ke jera mata wad'annan tambayoyi, hannunta guda dafe da kanta, a sannu tayi k'asa ta zauna sosai tana sauke ajiyar zuciya. Khaleefa ne yayi k'arfin halin rufe mata k'ofar yazo gabanta ya zauna yana Kiran sunanta, "Saleema! Saleema kina jina? Ko asibiti zamu tafi ne?".
Girgiza mishi kai tayi da kyar ta bud'e idonta tace, "naje tun kwana uku da suka gabata, don Allah khaleefa me nayi maka ka daina d'aga wayata ka daina kirana?".
"Saleema ni bakiyi mun komai ba, ban samu lokaci bane har a karan kaina ban samu lokacin kaina ba sai jiya, amma duk da haka kina cikin raina, ina jin Allah Allah na gama abinda nake nazo na ganki Saleema".
Cikin dauriya ta sakar mishi tattausan murmushi, "wane taimako zanyi miki Saleema, kinci abinci? Kinsha magani?".
Girgiza mishi kai ta sake yi cikin sanyi tace, "bazan iya cin komai ba my love, tunda na ganka nasan zan dawo normal ko babu abinci babu magani, dama rabin ciwon na rashin kane".
Murmushi khaleefa yayi mai k'ayatarwa shiyasa yake sake jin Saleema a ranshi da zuciyarshi sosai, kamo hannunta yayi duka cikin nashi yana kallonta eyeball to eyeball yace, "I love you, I love you Soo much Saleema, Tashi muje na taimaka miki kici wani abu kinji mie love".
Ja baya yayi ita kuma ta mik'e da kyar ta nufi hanyar bathroom, sai a lokacin na samu damar k'arewa d'akin nata kallo, komai dai dai dana khaleefa in aka d'auke banbancin kyale kyale da mata basa rabo dashi a d'aki sab'anin maza. Toilet tayi shi kuma ya fara gyara mata d'akin. Ko kafun ta futo ya share d'akin tass duk da ba datti sosai saboda Saleema ba dai tsabta ba, macece data tsani datti komai k'ank'antar shi, yanzu ma saboda rashin lafiyar data kwanta gashi sunyi fad'a da Amna da take taimakon ta.
A kitchen yaga duk abun buk'ata na had'a sauk'ak'k'en abinci da za'a iya ci cikin sauri, nan ya fara had'a mata abinda zata ci kafun tasha magani. Yana gab da gamawa ta biyo shi kitchen d'in, "sannu daga zuwa ziyara na had'a ka da aiki".
Murmushi ya mata yana k'are mata kallo cikin sabuwar shigar da tayi cikin wata doguwar riga fara sol mai had'e da vail ta nad'e kanta da vail d'in jikin rigar, alama tana son fararen Kaya.
"Gaskiya kinyi kyau Masha Allah kamar ba yanzu kika tashi daga ciwo ba".
K'arasa shigowa ciki tayi sosai ta jingina da carbinet tana kallon shi da sabon murmushi, "meka dafa mun?". Ta tambaye shi.
"Abu mai sauk'i da zaki iya ci, Ina fatan zaki lallab'a kici koba yawa".
"Ai ya zame mun dole ma cin wannan abincin naka koda in naci cikina zai fashe kuwa".
Lakace mata hanci yayi yace "in kika k'ara cewa komai ko? Sai kace wani ita kad'ai take sona".
Farrr tayi da idanunta tace, "Ai koba ni kad'ai nake sonka ba sonda nake maka yafi naka......".
Wani k'aton jug ya d'auka yayo inda take daf har tana jin hucin numfashin shi yace, "in kika sake cewa komai....."
Saleema tana guntse dariyarta ta kama bakinta da hannunta.
Ajiye jug d'in yayi yana dariya, itama dariyar tayi cikin shagwob'a tace, "sai wani zaren ido kakeyi nida bani da lafiya, kamata yayi ma fa ka lallab'ani".
Shafa sumar kanshi yayi ya koma ya k'arasa juye mata abincin a plate ya d'auko cokali d'aya da ruwa, yana gaba tana bayan shi suka futo, ya tambayeta magungunanta ta d'auko. Kusa dashi ta zauna, ya zaro wayar shi a aljihu yace, "oya kicinye mun abincin nan tass".
Shagwob'e fuska tayi tace, "Allah fa har yanzu ban gama warkewa ba ka k'arasa ladanka ka bani da hannayenka masu albarka sai nafi ci da yawa ma......".
Wani irin kallo da khaleefa ya jefa mata yasa ta kasa k'arasa abinda tayi niyyar fad'a sai k'asa k'asa.

_fatan Allah ya gafarta mana zunuban mu, marassa lafiya na gida dana asibiti Allah ya basu lafiya, mu kuma da muke da lafiya Allah ya qara mana lafiya, Wanda suka rigamu zuwa gidan gaskiya Allah ya jikan su yayi rahama a gare su, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani, barkan mu da ranar juma'ah_


_naji wasu sun rikice a lissafi, suna tambayar novel ranar laraba da weekend, ni kuma ranakun posting d'ina na fad'a muku, kwana hud'u a sati ne, Monday, Tuesday sai Thursday and Friday_

_Maryam sulaiman ummu elmustapha Ina godiya da jinjina ga ruwan comment d'inki, Ina yinki sosai kuma Ina jin dad'in comment dinkiπŸ˜πŸ‘πŸ‘ na dangwala miki wannan page ma na baki shi kyauta_


_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:01β€―pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*πŸ§•
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page nine9️⃣


Ganin ta tsorata dashi sai ya sassauta yanayin fuskarshi yace, "kici da kanki ba saina baki ba zaki fi k'oshi".
Marairaice mishi tayi kamar zata yi kuka tace, "kayi hak'uri amma don Allah muci tare".
Tsare ta yayi da ido kurum yana karantar yadda tayi maganar da iya gaskiyarta, sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login