Showing 42001 words to 45000 words out of 288773 words

Chapter 15 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1090

kyaji sanyi a ranki, kin d'an yi kyau ba laifi".
Kan kujera raihana ta zauna sosai tana dariya tace, "ka hutar da bakin ka, ba sai naji wani abu daga gare kaba".
Dariya yayi ganin ta ramfo shi.
Ya bud'e baki zaice wani abu hapser ta shigo da sallama, saida ta tsaya suka gaisa da Ayman sannan tace, "raihana ummie tana neman ki fa".
Mik'ewa tayi tace, "okay kice mata Ina zuwa".
Tare suka futa bayan ta tsaya tayi sallama da Ayman don ba lallai lokacin da zata dawo yana nan ba, taji yana fad'awa Nur a waya d'azu yana hanya. Su raheela ta kira suka huce gidan su direct, anguwar ta cika taf da mutane Masha Allah, haka cikin gidan nasu ma. A parlour ta ajiye su suka tafi nemo ummie.
Ameena ce ta nemo mata ummie ta had'a su sannan ta tafi, ummien kanta tayi kyau cikin shadda irin ta jikin raihana har d'inkin, ba make-up a fuskarta ko wetlips da kwalli bata saba amma duk da haka tayi kyau sosai.
"Wane irin bacci kika yi yau har aka d'aura aure baki tashi ba? Ina fatan dai ba wai baki da lafiya bane kika b'oye don nasan halinki sarai".
Girgiza mata kai tayi tace, "a'a ummie lafiyata Lou kawai gajiya ce".
Ummie tace, "Toh Allah yasa, dama su yuseep ne suke ta tambayata ina kike?".
Cikin mamaki tace, "laaah ummie Yaya yuseep yazo? Suna Ina?".
"Suna sitting room". Ai ummie na gama fad'a mata tayi waje da hanzari, da Salma taci karo a hanyarta, "yauwa ai nemanki nake, har gidan iya inda muka kwana naje tace mun yanzun kika futa da friends d'inki, saurayinki sunzo d'aurin aure shida mahaifin shi da wasu samari dai haka ko k'annen shine".
"Imran ko? Toh ni me zanyi musu, da yayi tafiyar shima".
Salma tace, "ai bai nemi had'uwa dake ba shi kanshi, kawai cewa yayi in ya kira no ki baya samu, na fad'a mishi kin kashe wayar ne, shine yace a fad'a miki don Allah ki kunna zakuyi magana".
Samha ta karb'a a hannun Salma dake ta b'angale mata baki ta tace, "aikuwa bazan kunna wayata yanzu ba, dame zanji? Hayaniyar mutane ko d'aga wayar shi".
Ko k'ara sauraron Salma batayi ba ta huce zuwa sitting room abinta, ita ko Salma da mugun mamaki tabi bayan y'ar uwar tata da kallo, Ashe har yanzu tana nan da halinta bata sauya ba? Ta d'auka tsawon 2 years da sukayi ba tare ba ta bar halayen ta na ko in kula, ko ada tana tunanin anya ba biris d'in da takeyi da masoyan ta ne ke korar su har su fasa aurenta ba? Iya sanin ta mutum d'aya raihana take saurara har taba lokacin ta fiye dako wane namiji, shine wani kwayar mutum guda da basu da wata kwakkwaran alak'a ta soyayyah, hasalima shi sama da shekaru uku yana da wadda yake so zai iya aure a ko wanne lokaci daga yanzu.

A ranar data kasa hak'uri zama tayi kurum ta rabka uban tagumi tana nazarin matsalar raihana, kallo d'aya data yiwa Imran yau taji ya kwanta mata a ranta, sai taga duk cikin samarin da raihana tayi babu mutum kamarshi, ko don duk babu saurayi a wad'an can?.

Raihana kuwa da hanzarinta ta k'arasa sitting room d'in bakinta d'auke da sallama, duk suka amsa mata cikin sakin fuska, a k'asan carpet ta zauna suka fara gaisawa dasu d'aya bayan d'aya, yuseep ne da matarshi sai sauran y'an uwan ummie. Ta jima rabonta dasu musamman yuseep don ba a garin yake ba, sai in abu ya faru irin haka yazo.
Ta jima suna d'an hira jefi jefi kafun ta futo daga d'akin.
Gurin su raheela taje ta kaisu Suka gaisa da ummie da amarya sukai musu Allah ya sanya alkhairy, saboda cikowar mutane a gidan sai kawai ta mayar dasu gidan iya, nan Suka baje kolin hirar yaushe gamo, itama Fatima ansa ranar aurenta da wani cousin d'inta, nan da eight month biki. Sosai raihana ta taya ta murna da fatan alkhairy, sai yamma suka tafi da alk'awarin sai bikin raihana suda dawowa.

Wannan karon dangin abban su a gidan Abba abubakar suka yi nasu yinin shiyasa akayi lafiya aka gama lafiya, ba d'auki ba dad'i irin Wanda Suka fara jiya, aka tafi da amarya gidanta lafiya bayan tasha ruwan naseeha daga dangi da abokan arzik'i, iya ce da umma suka kamo hannunta kamar yadda suka yiwa Salma haka itama suka yi mata a wannan karon har gidan mijinta.
Sai gidan nasu ya zama shiru saboda yawancin mutane sun tafi gidan amarya da yake ba nisa tsakanin su dashi.
Ita dai raihana bata jeba, tana sallar isha'i ma kwanciyarta tayi can k'uryar d'aki. Sai k'arfe d'aya da y'an mintuna na dare ta farka, su kuma lokacin y'an kai amarya sun dawo har sun kwanta bacci.
Wayarta ta d'auko cikin Jakarta ta kunna, nan massage suka fara ribdigun shigowa, biyu ne daga Ayman, amma kusan hud'u daga Imran ne.
Sak'on farko, "Na kira ki wayar ki a kashe Ina fatan kina cikin k'oshin lafiya". Na biyu "me yasa kika kashe wayar ki?, raihana ganin ki a yau yasa da nazo gida na kasa bacci bansan me yake shirin faruwa dani ba, amma daga na rufe idona fuskarki nake gani tana mun gizo cikin kwalliyar ki kamar kece amaryar da ake biki, ba komai nake tunani ba raihana sai nan da watanni biyu masu zuwa alak'a ta dake zata zo k'arshe, wani zai raba mu bayan duk tsawon shekarun da muka kasance tare, tun baki mallaki hankalin kanki ba, raihana na taya ki murna Ina kuma miki fatan Allah yasa wannan guy dashi za'ayi a wannan karon, amma Ina tausayin kaina da zanyi rashin da har abada bazan tab'a maye gurbin shiba, don Allah raihana da kinga text massage d'ina ki kirani ko zanji sanyi a raina".
Shiru raihana tayi bayan gama karanta sak'onnin biyu da suka zo daga d'an uwa kuma aboki na gari wato Ayman.
Tayi yink'urin kiran shi yafi sau uku tana fasawa saboda tunanin yana tsakiyar bacci a lokacin, daga k'arshe sai kawai ta share ta fara duba sak'onnin Imran, duk na fatan alkhairy ne sai d'aya na complain me yasa zata rufe wayarta, ya shiga damuwa sosai gashi yazo d'aurin aure har ya tafi basu had'u ba. Raihana ranta da zuciyarta cinkushewa sukayi da abubuwa da yawa, daga k'arshe sai kawai ta kife kanta jikin gwiwarta tana zubda hawaye, soyayyar Imran tana so tayi tasiri a zuciyarta, lallai taga alamun karyewar lagonta a wannan karon duk da yak'i da take da zuciyarta, tsoronta d'aya har yanzu bata sa a ranta za'ayi auren ta dashi ba, Cox ita ta dad'e da sarewa, tana ganin a k'addararta har yanzu mijinta bai zoba tukun, tana ji a jikinta shima tafiya zaiyi ya barta kamar wad'an can samarin da tayi.
Ta wani gefen kuma ga Ayman, ita kanta ba k'aramin tashi hankalinta yake ba idan ta tuna da k'aratowar rabuwarsu a kullum dare da safiyar Allah, tasan ba abune mai sauk'i rabuwarta dashi bayan kwashe tsayin shekaru goma da d'oriya tare.
Tana wannan y'an tunane tunanen wayarta ta fara ruri,,,,,, Ayman ne, saita saisaita yanayinta ta share hawayenta sannan ta d'aga a nutse, "assalamu alaika". Ya amsa da "Ameen wa'alaikumussalam" ya fad'a shima a d'aya b'angaren. Raihana cikin sanyin jiki tace, "Yaya Ayman kaine kira da daren nan". Cikin muryar bacci yace, "ya zanyi raihana na kasa samun nutsuwa, bacci na fara amma baccin ma ba dad'i, ban d'auka zan samu wayarki bud'e ba ma yanzun".
"Ayyah nima yanzu na bud'e dana farka, toh amma Yaya Ayman me yake damunka da zai hana maka bacci? Duk yadda kake da son bacci?". Jinginar da kanshi yayi jikin fuskar gadon da yake kwance yace,
"Ni kaina bansan me yake damuna ba raihanatu, the only thing I know is jina nake cikin tashin hankali, wanda yake k'ara hauhauwa a kowacce safiyar Allah".
Ajiyar zuciya raihana ta sauke tace, "kuma kana yawaita addu'o'inka? Duk da nasan baka da wasa da addu'ah amma ka dage sosai, yanzu bari muyi sallah raka'a biyu mu kaiwa Allah kukan mu, dama shi yafi sanin damuwarmu kuma shi zaiyi mana maganinta". Cikin jin dad'in kalamanta da nutsuwar ta Ayman yace, "toh shikenan raihanatu, insha Allah zan dage da ninka addu'ah akan wadda nake yi".
Daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye waya. Alwala ta d'auro bayan ajiye wayar ta kabbara sallarta inda tayi ta kai kukanta ga Allah subhanahu wata'ala daya yi mata zab'in abinda yafi alkhairy a rayuwarta. Shima Ayman hakan ya aikata.
Duk mutanen d'akin suna bacci har ta gama ta koma tayi kwanciyarta sak'on gud night ta gani daga Ayman, tayi mishi reply ta ajiye wayar gefenta.
Da safe ragowar bak'i suka had'a ya nasu ya nasu suka huce, zuwa yamma gidan su ya dawo daga ummie sai su sai kuma Salma wadda zata huce a daren ranar itama, sai a lokacin ummie ke nuna mata kyautar da Imran da mahaifin shi suka kawo, drinks ne kusan katon goma sha biyar, abun har mamaki yaba raihana. Saita tafi d'akin su da sauri ta nemo wayarta inda ta ajiye ta dawo d'akin, Ashe ma ya kirata, sai dai kiran bana yau bane tun daren jiya dai dai lokacin da suna wayar nan da Ayman. "Ya Salam to yaushe kuma Imran ya kirani ban gani ba?" ta fad'a tana zama saman kujera, no shi tayi dialing kamar kullum har ta gama bai picking ba, a tunaninta zai biyo baya sai ta ajiye wayar taci gaba da harkokinta, sai dai me? Har yuseep yazo ya tafi da Salma da dare bai kira ta ba. Hakan ya d'an d'agawa raihana hankali kad'an har ta shiga damuwa, lallai akwai wani abu saboda lafiyar Allah baya iya yini ba tare daya kirata ba, sai dai ko in ita tak'i d'agawa saboda dakushe k'arfin alak'ar su.
Har dare su muhibba suna gugar uniform d'insu na makaranta don Abba yace dole su koma gobe ai an gama biki, ita kuma tana zaune jigum rik'e da waya, ta kirashi yafi sau hud'u a iya zamanta anan ma amma baya d'agawa, al'ameen ne ganin suna ta magana bata jiba yazo ya dafa k'afarta, sai ta d'ago ta kalle shi, "ga kayan kinan iya ta bayar a kawo miki". Karb'ar kayan tayi ta shige d'akin su da a yanzun ya zama nata ita d'aya.
Ranta cinkushe da d'ar d'ar da kewar y'ar uwarta ta nemi guri ta kwanta tana karanta addu'o'in bacci, tana ji ummie na tambayar su muhibba a parlour ina take, jidderh tace ta kwanta bacci. Da mamaki ummie tace, "tunda wuri yau kuma? Kodai waya take?".
"Wallahi ummie ta kwanta na shiga fa na ganta" jidderh ce meyin wannan maganar".
Rufe ido tayi da tunanin ko ummie zata shigo duba ta sai kuma taji ta huce.

@@@@@@

Kamar da wasa saiga raihana ta d'auki cikakkun kwana biyu babu Imran bare wayar shi, tun tana mishi text na tambayar ba'asin shirun shi har ta fudda rai ma gaba d'aya. A kullum safiya sai sunyi waya da Ayman yaji lafiyarta wannan alk'awari ne, haka ta wattsapp indai taci nasarar samun shi online zasu yi chat, shine ma dasu raheela ke d'ebe mata kewa wani lokacin.

Yau da yammaci tana zaune k'ofar kitchen ta gama had'awa ummie miyar tuwon dare kenan tana hutawa d'an aiken iya yazo kiranta, ummie da take zaune gefenta ta kalla sai taga tace da yaron tana zuwa, ajiyar zuciya ta sauke a hankali saboda yadda taga ummie bata son alak'ar ta da Ayman bata d'auka zata yarda taje kiran da bata raba d'ayan biyu shine ummul'a'ba'isin shi. Doguwar rigar material ce a jikinta wrapper, d'inkin ya mata cas cas, d'an madaidaicin gyalen kayan ta d'auko a d'aki ta yafa don b'oye gashin kanta da batasa d'an kwali ba. "Ummie saina dawo".
Ummie tana kallon rawar k'afarta tace, "ki tafi ma malam da tuwon sannan ki tabbatar kin dawo kafun abbanku ya dawo".
Cikin jin dad'i tace, "insha Allah ummie". Daga nan kitchen tayi ta d'auko plask ta zuba miya ta d'auki tuwon malmala biyu tasan maybe Ayman yaci tasa a leda ta futa.
Da sallama ta shiga gidan iya, babu kowa a tsakar gidan, daga parlor iya ta amsa mata, saita k'arasa ta shiga parlon, tana ta aikace aikacen ta, Ayman kuma na zaune kan kujera yana operating system idon shi sakaye cikin farin glass. Sanye yake da t shirt sai dogon wando Ash.
Ajiye tuwon tayi kan table k'arami dake gaban shi, "yanzu haka akeyi raihana sai ki b'ace b'at bake ba labarin ki kamar ke muka kai d'akin mijin". Iya ce ta fad'i haka, Had'a ido sukayi da Ayman, lokaci guda gaban su ya bada rass! Iya kam ko lura da yanayin da suka shiga batayi ba ta ci gaba da maganarta, "koda yake kamar yau ne kema zamu mik'a ki naki d'akin da shekara ta kewayo muje mu d'auki y'an uku".
Ayman kwantar da kanshi baya yayi had'e da lumshe idanun shi da sauri yana imagining ga raihana tayi aure har da ciki.
Yayinda ita kuma tayi k'asa da kanta ba tare da tace komai ba, "me aka kawo mun yau kuma? Kayan ki suna cikin d'akina na wanke na ajiye miki ban samu wanda zai kawo miki ba, yanzu wannan yaron ma da Adam ya tura kiran ki da kyar ya je Saida na had'a da bashi k'arin gyad'a".
Jiki a mace ta kai tuwon gabanta tace, "ai suna da kyuya ummie ce tace a kawowa malam tuwo".
"Ita dai ruqayyah bata gajiya duk lokacin da tayi tuwon nan, a tak'aice ma dai yau ba malam aka kawowa ba Ayman kika kawowa don tunda yana nan sai yaci gashi dama har malmala biyu".
Shi dai Ayman Murmushi kawai yayi ya gyara zaman shi, idon shi na kallon raihana da kullum take k'ara sauyawa mishi.
Ita kuwa gaisawa tayi da iya sannan shima ta gaishe shi, ta tafi d'akin iya da suka kwana wancen ranar ta d'auko kayanta a gefen gado. Kusa da Ayman ta zauna tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren shi, "Yaya Ayman wai baka da lafiya ne yau?".
"A'a raihana amma me kika gani". Ya fad'a yana tsare ta da ido. Sai ta juya kanta gefe tace, "babu komai". "ai koda komai ma ba zaki fad'a ba indai kece".
Ita dai murmushi kawai take, iya da kanta taje kitchen ta d'auko plate ta zuba mishi tuwon, ta zuba mishi miyar daban a wani d'an bowl. .
Har gaban shi ta ajiye tayi hucewarta harkokinta na k'ulle k'ulle a tsakar gida, bai wani ci na kirki ba duk da irin yunwar da yake ji kuwa ya rufe duka tuwon da miya.
Raihana shiru tayi tana nazarin shi kafun ta nisa tace, "Allah Yaya Ayman baka da lafiya kawai baka son naji ne".
K'ak'alo murmushi yayi ya d'auke mata hankali ta hanyar kawo wata hirar ta daban, sun jima suna hirarsu kafun ta dai daici lokacin dawowar abbanta tayi mishi sallama ta tafi gida, Allah ya taimake ta bai dawo ba sai dai tana shiga ba jimawa ya dawo, hira da Ayman ta d'auke mata hankali da yawa, taji dad'in futar don ta d'ebe mata kewa ba kad'an ba. Takan jima kafun suyi hira taga dariyar shi irin ta yau, lallai yau ya tuna mata da abinda ta jima da mantawa dashi, hirarraki dai iri iri.

Shima Ayman ta b'angaren shi abinda ya faru kenan, a lokaci guda ya tsinci kanshi cikin farin cikin daya shafe mishi dukkan wani k'unci daya shiga lokaci guda a yammacin.
Bai bar gidan iya ba saida yayi sallar isha'i tare da malam a masallaci.
Lokacin daya shiga gida ummie tana tare da bak'i abokan kasuwancin ta a sitting room, sai bai nemi ganinta ba ya huce kawai bayan sun gaisa da halima mai aikin su, bathroom ya fad'a yayi wanka ya shirya cikin kayan bacci milk masu taushi, zama yayi gefen bed sannan yayi dialling no nuriyyah, tana zaune ta duk'ufa kan laptop d'inta ko me takeyi dai da alamu ta bashi muhimmanci, ko ring d'in bataji ba sai da k'anwarta heedaya ta d'auko wayar har zata kai mata sai taga sunan mine da emoji na love a jiki, ta fahimci no yaya Ayman kad'ai tayi saving da haka, sai tayi sauri ta d'aga sannan ta kara a kunnenta, Ayman tacan b'angaren cewa yayi cikin kwantar da murya, "baby yau ko nema na bakya yi".
Dariya heedaya ta sakar mishi a kunne cikin k'iriniyarta da rashin ji tace, "ba babyn bace Yaya Ayman nice da ka yiwa fake promise, yanzu fad'a mun Ina chocolate d'ina". Dafe kai Ayman yayi a ranshi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login