Showing 24001 words to 27000 words out of 288773 words

Chapter 9 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1040

haka basu sake ce da juna komai ba har Ayman ya tada motar suka fara tafiya, sun d'auki hanya bisa kwalta d'odar sannan Ayman yace mata, "nuriyyah fa bata da lafiya".
Da sauri raihana ta dube shi tace, "toh? me yake damunta kuma? Ai daka fad'a mun tun zuwana da naje naga jikin nata"
"Toh aranni muje biki sarkin zuwa dubiya, ai sai ki tsaya kiji tun yaushe ta fara ciwon ma tukun".
Lumshe idonta tayi ta bud'e tace, "tun yaushe kenan?".
"Jiya ne da safe ta tashi da zazzab'i da ciwon k'irji yanzun haka an bata gado a general hospital da auntie ke aiki, kuma alhamdulillah ina ganin zuwa gobe za'a iya sallamota yanzu don yanzu haka daga gurinta nayo nan, naga alhamdulillah jikin yayi sauk'i har munyi magana ma da ita".
Cikin jimantawa raihana tace, "ayyah Allah ya k'ara sauk'i".
Ya amsa da, "ameen". Sun sake yin shiru kowa da tunanin da yake a zuciyar shi kafun Ayman ya nisa yace, "wata nawa ya rage miki ki kammala karatun ki duka raihana".
Da mamakin shi tace, "yau kuma kake tambayata Yaya Ayman".
"Eh Ina sane so nake na tabbatar daga bakin ki kawai".
"Wata uku ne ya rage".
Ajiyar zuciya yayi yace, "zaki riga khaleefa gamawa kenan?".
Shiru raihana tayi tana maimaita sunan khaleefa a ranta, saura k'iris ta tambayi Ayman waye ma khaleefa a gurin shi sai kuma dai tayi shiru tana k'ok'arin tunowa da kanta, don ta fahimci tambayar zata iya sawa yaji haushi ko ba dad'i a ranshi tunda zaiga wato duk yadda yake k'ok'arin kyautata mata a y'an uwanta ba wanda bai sani ba a banza, ita ba ruwanta da nashi y'an uwan, shiyasa ma bata san waye khaleefa a tare dashi ba.
Kowa da abinda yake sak'awa tsakanin su har suka k'arasa harabar makarantar su.
Agogo ta duba a sanyaye kuma ta kalle shi, "Allah yasa kada kayi late gurin aiki".
"Noop kada ki damu na bada uzuri daga nan zuwa 3 hour masu zuwa idan naje ba matsala".
A tare suka bud'e murfin motar suka futo ya kewaya gidan baya ya d'auko mata jakar kayanta, sai daya had'a da wasu y'an canjin masu nauyi sannan ya mik'a mata, girgiza mishi kai tayi ta zame kud'in ta karb'i iya Jakarta ta kaya. Tamke fuskarshi yayi, "yaushe muka fara haka dake raihana". K'asa tayi da kanta tace, "kayi hak'uri Yaya Ayman bazan iya karb'a ba saboda hidimar da kakeyi dani tayi yawa, ummiena, khausar, Salma da sauran k'anne na kana hidimta musu ba tare dani kaina ka sanar dani ba, kana jinsu kamar naka familyn, ko iya wannan aka tsaya kayi mun abinda ban Isa na biya kaba a rayuwa". Tana gama maganarta ta d'auki hanyar hostel d'insu cikin sauri, bin bayanta yayi yana kiran sunanta sai dai ko saurarar shi batayi ba, haka ta dinga tafiya da matuk'ar sauri yana binta gudu gudu har Allah ya bashi ikon Shan gabanta, tana gab da shiga k'ofar hostel d'in. "Raihana wai me yake damunki haka?, duk abinda nakeyi ke kike sakani? Ko da kud'in ki nakeyi da zaki ce yayi yawa?, sannan idan bani dashi zanyi ne?".
"Amma Yaya Ayman......". Da sauri ya katse ta "bana son jin komai" ya karb'e jakar hannunta yasa kud'in a ciki, "gashi nan idan kinso ki kona su a bola ko ki zubar".
Yana gama maganar shi ko kallonta baiyi ba ya juya yabar mata gurin, bin bayanshi tayi da kallo yayi nisa sannan ta iya takawa sannu a hankali ta shiga arean hostel d'insu.
Su fateema da takwarar ta suna zaune kowa da abinda takeyi sai ganinta sukayi unexpected, aikuwa fateema ta daka tsalle ta rungume ta, "oyoyo sis u are highly welcome, wannan dawowar bazata".
Dariya tayi ta zame jikinta ta zauna gefen bed tana duban su duk sun wani tsare ta da ido, "toh kallon na meye haka kuma?".
Raheena tukur mai shigen sunanta tace, "ba dole mu kalle kiba keda kikace sai after one week zaki dawo kuma mun ganki yau da sassafe, hala Abba ne ya koro ki?"
Girgiza musu kai tayi, "ba d'aya abokin kwarai ne ya bani shawara ta kwarai".
"Aikuwa ya kyauta mana don a jiya kad'ai baki ji yadda mukayi kewar kiba, ko d'azu da muka makara sallar asubah ma saida raheenatu tace da kina nan wallahi ba zamu makara ba".
Dariya kawai tayi ita dai.
"To ya masu jego dasu ummie fatan kin baro su lafiya".
"Suna lafiya Lou alhamdulillah, yaeh me yake tafiya a makaranta"
Nan fa hira ta b'arke kowa na bata labarin abinda akayi cikin kwana d'aya da bata nan.

@@@@@@

Kwana biyu da dawowar ta da wani yammaci tana zaune a hostel tana goge kayanta data wanke, sanye take da body hug riga iya gwiwa kanta babu d'ankwali ta tsefe rabi, rabi kuma doguwar jelar shi na reto a saman kafad'ar ta.
Wayarta da take gefenta ta d'auki ringing. Ajiye ion d'in tayi gefe ta d'auki wayar tana dubawa da tunanin ko Ayman ne, sai dai sab'anin hasashen ta bak'uwar no ce. Shiru tayi tana sak'e sak'e a zuciyarta kafun ta d'aga wayar.
"Amincin Allah su tabbata ga kyakkyawar zinariyar mata". Sai ta jingina da jikin gadon tana tunanin waye wannan kuma?
"Yi hak'uri ban gabatar miki da kaina ba ko? Sunana abubakar Muhammad Imran, nine muka had'u dake kwanaki biyu da suka gabata har na takura miki kika bani no".
Tabe baki tayi kamar yana gabanta tace, "ohh kaine".
"Ashe baki manta niba?".
"Humm!" Kawai tace, shi kuma yaci gaba da maganar shi, "Ina ta tunanin kiranki cikin kwanaki biyun nan sai dai ina tsoro".
Nan ma bata ce komai ba, "kinyi shiru ko bakya son kiji tsoron meye?".
Yanzun kam hararar wayar raihana tayi tace, "taya zan tambaye ka kaida rayuwarka"
"Eh to hakane amma ai ya kamata kisan ko tsoron meye?".
"bari ayi yadda kake so to tsoron me?"
Murmushi yayi yace, "Tsoron kada nayi laifi a gurinki y'an mata, Ni kuma gani mutum da bana son takurawa rayuwar kowa".
"Da kyau ka taimaki rayuwarka kuwa?".
Murmushi ya sake yi donshi komai nata burge ta yake, "akwai abubuwa da yawa da nake son mu tattauna sai dai ban sani ba ko zan iya samun address d'inki, I mean addreshin gidan ku".
Sake yamutsa fuska raihana tayi tace, "gashi address d'in bazai samu ba Sam".
"Me yasa bazai samu ba gimbiyar mata". Ya tambayeta, "humm saboda bani da lokacin saurarar abinda za kazo dashi".
Murmushi ya k'ara yi, shi kad'ai yasan yadda yarinyar take d'aukar hankalin shi, "toh me kike tunanin zanzo dashi?".
"Tatsuniyar gizo dai ai bata huce ta kok'i, me zaka zo dashi wanda ya huce soyayyar yaudara irin wadda ku matasan zamani baku d'auke ta komai ba".
Wata y'ar k'aramar dariya yayi daga b'angaren shi yace, "Amma kin burge ni y'an mata, irin wannan fassara ta farat d'aya ba tare da dogon tunani ko nazari ba, sai dai ni har yanzu bakiyi laifi a gurina ba ko kad'an, saboda mutum baya tab'a fad'in sab'anin abinda yake zuciyarshi koda kuwa bai furta da baki ba za'a iya fahimtar hakan akan fuskarshi, sannan ruwan daya dake ka masu iya magana sukace shine ruwa......".
Shiru tayi ba tare da tace komai ba, "baiwar Allah kinyi shiru, ni ko sunan kima baki fad'a mun ba".
Da sanyin jiki dana gwiwa tace, "raihanatu".
"Raihanatu suna me dad'i". Ya fad'a yana fudda sautin murmushi kafun ya sake cewa, "raihanatu ina ganin kamar akwai wani abu a k'asan ranki dangane da soyayyah da maza! Am I right?".
Cikin katse hanzari tace, "babu komai a raina".
Wani murmushin ya sake yi, "akwai fushi a kwayar idon ki, sannan akwai zafi a kalaman ki, kina yin magana cikin fushin da yake tasowa daga k'asan zuciyarki, tun a ranar dana fara had'uwa dake, raihanatu dole akwai tabon wani a cikin zuciyar ki wanda yake assasa faruwar hakan".
Cikin b'acin rai yanzun raihana tace, "bani da tabo ko mikin soyayyah saboda ni ban bata muhimmanci ba bare ta wahalar dani Kota dameni the fact is Ina da wanda nake sone kawae".
"Ba haka bane raihana, idan da ace kina soyayyah da wani kuma kina tunanin auren shi to da tun a waccen ranar zanga soyayyar cikin kwayar idonki, kuma ba zaki dinga magana cikin fushi ba, kada ki manta ko yanzu kince baki ba soyayyah muhimmanci ba which is kin k'aryata kanki akan kalaman ki na k'arshe, dole komai a duniya bazai dinga saurin baki haushi ba, kina cikin soyayyah kowa zaki ganshi abun ban dariyarki da nishad'i coz you are deep love with someone else, sab'anin haka shine kike yin magana cikin fushi da fusata, wallahi ko kin k'i ko kinso hasashena a kanki gaskiya ne, ni yanzu mubar maganar jayayyah! Kina da Wanda kike so koma babu! Tunda ba matar aure bace ke, baki da engaged da wani zan fad'a miki abinda yake zuciyata daya sa na karb'i no ki waccen ranar, Ina son ki! Hak'ik'a ina k'aunar ki raihana, da gaske kuma auren ki zanyi shiyasa nake son ki bani dama, address d'in gidanku kad'ai ma ya wadatar".
Wani zazzafan numfashi ta fesar tace, "kayi hak'uri hakan bazai yiwu ba". Tana gama fad'in haka ta ajiye wayar jikinta a sanyaye, tana ganin ya kamata ta saurarawa rayuwarta da jefa kanta cikin matsala, a duk cikin samari biyar da akayi musu engage babu wanda ta tab'a jin tashin hankali wai don su rabu akan soyayyar shi, ita duk tashin hankalinta d'aya ne ya zatayi da kakarta da dangin mahaifinta da basa k'aunar ta ita da ummienta, ya ummienta zata ji idan mummunan labarin fasa auren ya risketa?
Abu na uku kuma Hasalima ita Saboda ta k'aryata matar Abba abubakar akan furucinta take amincewa da auren su, yanzu kuma lokaci yayi daya kamata ta farka daga rayuwar tatsuniyar da take ciki zuwa ta zahiriyyah, ta duba wanda ya dace ya cancanci ya aure ta, wanda yasan abinda yake yi, take son shi yake sonta, take son k'are rayuwarta dashi ba wanda ta futar don wani fushi da b'acin rai na k'addara ba.

_toh waye haka Raihana?_


_Comment and share_
24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page eight8️⃣


Ranar yini tayi sukuku kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, kasancewar basu da lectures sai ta yi kwanciyarta a gado ko abincin rana bata iya ciba, tariyar rayuwarta tayi tun daga lokacin da aka haifeta har zuwa yau.
Da yammaci Ayman ya kira ta ya had'a ta da nuriyyah tayi mata sannu da jiki.

Ranaku shida sun tashi kamar awanni shida cikin k'iftawa da Bismillah, kamar yadda Ayman ya mata alk'awari haka yauma ya bugo sammako yazo d'aukar ta, dama tun dare ta had'a kayanta, shiyasa yana fad'a mata yazo ba b'ata lokaci ta k'arasa had'a yanata yanata tayi sallama dasu raheena ta fuce.
As usual yana tsaye jikin motarshi ya hard'e duka hannuwan shi a k'irji, sanye yake da fararen suit, k'afar shi sakaye cikin bak'in cover shoe, gashin kanshi ma'abocin santsi sai d'aukar ido yake yasha gyara.
A nutse ta k'arasa har inda yake tsaye ta d'an russuna tace, "Yaya Ayman barka da safiya".
Idonshi a kanta yana nazarin ko akwai wani abu sabo a tare da ita ya amsa gaisuwarta har yana tambayarta ya karatu, ta amsa mishi da alhamdulillah.
Shiya bud'e mata front seat, ta shiga ya rufe, ya mayar mata da jakar kayanta baya sannan shima ya shiga mazaunin driver.
Suna tafe a hanya suna hira jefi jefi, rabin hirar duk hirar rikicin su da Auntie ne sai labarin iya da shaftarta.
Sunyi nisa a hanya ya k'ara satar kallonta kafun ya tambayeta, "kinsan kuwa kin rame sosai raihana?".
Jikinta a sanyaye tace, "na sani Yaya Ayman kuma ni ba komai nasa a raina ba yanzu".
"Anya kuwa raihanatu, na sanki da ajiye abu a rai ko ki zauna kita kukan kinnan mai d'aga hankali".
"Trust me Yaya Ayman duk babu d'aya cikin abinda kake zargi, Allah na saki raina akwai labari ma".
Kayataccen murmushi ya saki ya rage gudun motar kad'an yace, "Tom Ina ji Allah yasa na alkhairy ne".
Cikin jin nauyin shi tace, "na had'u da wani guy rannan fa".
Da sauri ya Kalleta itama shi take kallo tana so taji yadda zai karb'i zancen.
Sai ya maida hankalin shi kan titi yace, "wanene shi? Shin ya dace daki mallaka mishi soyayyar ki? Sannan kin tabbar yana da banbanci da wad'an can da kuka rabu ko shima irin sune?".
Murmushi ne ya kubuce mata tasa tafin hannunta ta rufe fuska. Dogayen yatsun hannunta yabi da kallo sunsha adon jan lalle, "ba don kar nayi k'arya ba da sai ince tunda kika kai shekaru goma a duniya ban tab'a ganin yatsun hannunki ko bayan hannunki ba lalle ba".
Bud'e fuskarta tayi tana kallon shi da mamaki tace, "ya kayi parking kuma muna tafiya, kada fa ka samu matsala gurin aiki ta sanadiyyata".
Idonshi cikin nata yace, "raihana bazan iya had'a abu biyu a lokaci guda ba, now am all ears".
"Toh ni ta ina Zan fara ma?".
"kada ki damu zaki iya farawa kota ina".
Rausayar da kai tayi ta soma labarta mishi komai tun daga had'uwar su da guyn har zuwa yanzu da wayar da suka sake yi jiya inda yake rok'on ta data bashi address d'inta.
Doguwar ajiyar zuciya Ayman ya sauke, "yanzu ya kike ganin za'ayi".
"Ai shiyasa na fad'a maka don ka bani shawara, in share shi ko in bashi dama naji da wadda yazo?".
"Indai har yayi miki ki bashi dama mana".
Murmushi ta sake yi tace, "toh ni dai bazance ba tunda har yanzu ta waya nayi magana dashi".
Ayman yace, "shikenan ki nazarce shi ki tabbatar da nagartar shi in yaso sai ki bashi dukkan damar da zai kasance mijinki, idan kuma shiriritane ya kawo shi... Toh dama nasan ke d'in ba layin shi bace ba b'ata lokaci ya kama gaban shi tunda wuri ma".
Kanta a k'asa tace, "toh Yaya Ayman nagode da kulawa da shawara mai kyau".
Ayman yace, "babu komai raihanatu Allah yayi mana jagora" tace, "ameen".
Daga nan suka ci gaba da tafiya suna hirar su jefi jefi har suka isa cikin gari.
Bai kyale taba saida ya kaita har bakin k'ofar gidan su, tayi mishi godiya ta shige gida. Ba k'aramin mamaki ummie tayi da ganinta ba, wankin gida takeyi har ta kusa gamawa ta ajiye tsintsiyar hannunta gefe tace, "raihana kece da sassafen nan?".
Tsugunna tayi gaban ummien tace, "eh nice ummie Ina kwana".
"Lafiya Lou amma ya kika samu mota da safen nan?".
Shiru tayi tana k'ila wa k'alan fad'a mata gaskiya.
"Ba amsa kenan?". Ummie ta fad'a tana d'aukar tsintsiyar ta.
Tana wasa da gefen gyalenta tace, "Yaya Ayman ne yaje ya d'auko ni?".
A wani irin fusace ummie ta juyo tana kallonta, "har yanzu kin kuwa San abinda kike a rayuwa raihana? Meyasa ba zaki zama mai taka tsantsan da mutane da rayuwa bane, kin fi kowa sanin halin da kike ciki a anguwar nan, su kansu Ayman d'in a idon mutane suke sannan daga ni harke mun kasa sanin abinda yake korar duk manema auren ki....."
"Kiyi hak'uri ummie insha Allah zan kiyaye gaba". Raihana ta fad'a cikin sanyi. Ummie bata kulata ba taci gaba da aikinta.
Sai taja k'afafu jikinta a sanyaye ta shige parlour ta kwanta kasan carpet tayi shiru tana nazarin abinda ummie take son nusar da ita game da huld'arta da Yaya Ayman wanda ita ta kasa fahimta, ita kuma fa komai ne yasa take sakin jikinta dashi ba sai ganin yadda yake d'aukarta kamar k'anwar shi ta jini, zata iya rantsewa tunda ta mallaki hankalin kanta Ayman ko hannunta bai tab'a rik'ewa ba, sannan duk abinda take so shima yana son abun da zuciyar shi duka, haka abinda ta tsana, yana jin bak'in ciki idan abu mara dad'i ya sameta, abu na k'arshe kuma na farko yana kyautata mata ita da familyn ta da jikinshi da aljihun shi, ita dai tana da yak'inin Ayman bazai tab'a cutar da ita ko yaci amanarta ba, sai dai maganar mutane da ba'a tab'a iya musu.
Tana wad'annan y'an sak'e sak'en ummie ta gama aikinta ta shigo da tea plask da cups ta dire mata, "ki tashi ki karya kumallo ko kinzo zaki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login