Showing 201001 words to 204000 words out of 288773 words
Chapter 68 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
da zama jigum daga shi har ita data ke matuk'ar jin bacci, ga d'akin shi bata ga komai da zata kwanta a kai ba sai gado falle d'aya shima ba wani kato irin wanda zasu buk'ata ba. Ko data ga zata rikito kan drower tashi tayi ba tare data kalle shiba tace, "Ina jin bacci, Ina son zan kwanta". .
Sake kallonta yayi kamar yace mata to ni na kawo ki, sai kuma dai ya basar, ya k'ara shafe adadin wasu mintuna har ta fudda ran samun amsa daga gare shi sannan yace, "zaki iya kwanciya a gadon".
Kamar abinda take jira kenan ta nufi gadon ta kwanta daga can gefe ta karanta addu'o'inta ta shafa, sai dai fa tana kwanciya bacci ya gagara yiwuwa, na farko ta fara tunanin abinda yake damun khaleefa don tasan lallai ba haka yake ba, na biyu ga haske ita bata iya bacci inda haske.
One hour! Two hours!! Three hours!!! Tana kwance amma ba bacci take yi ba duk data rufe har kanta ba inda ake gani amma barci ya gagareta, saita yanke hukuncin d'aura alwala tayi sallolin nafilarta zasu fi akan tunane tunanen banza da wofi. Sai dai ga mamakinta koda ta tashi zaune khaleefa yana nan inda ta barshi kamar an dasa shi ko kwakkwaran motsi baya yi. Zuwa yanzu ta fara tsinkewa da lamarin na khaleefa, toh shi kuwa me ya same shi haka zai raba dare a zaune cikin tashin hankali haka?".
Fasa aiwatar da abinda tayi niyyar aiwatarwa da farko tayi, taci gaba da zama tana nazarin shi kafun can tayi magana yadda zaiji cikin murya mara amo, "komai yayi zafi maganin shi Allah! Abun duk daba zamu iya magance shi da kanmu ba sai mubar mishi shi yasan yadda zai tafi da komai......". Har tayi zancen ta gama bai nuna alamun ya jita ba, har raihana ta fara tsoron khaleefa kuwa anya da numfashi? (Toh wa ya sani ma koya had'iyi zuciya ya huta da rayuwar๐).
Sai zuwa can sannan ya d'ago saboda tsabar damuwar da yasa a zuciyarshi idon shi yayi wani irin jaa. Duk daba kyakkyawar mu'amula a tsakanin su amma yaji dad'in maganar da tayi mishi, koba komai an samu wanda zai kwantar mishi da hankali.
(Dama shi a zuciyarshi Kashi uku nau'in fushin shi ya rarrabu, Allah yayi khaleefa wani irin mutum mai zafin zuciya barin ma idan ranshi a b'ace yake, yana iya yankewa mutum kowanne irin hukunci kowaye shi a lokacin da yake cikin fushi, shiyasa yafi buk'atar kad'aici a irin wannan lokacin, yanki na biyu kuma da zarar ya gama tunani da irin hukuncin da zai yankewa mutum toh yana buk'atar kafad'ar da zaiyi kuka tunda shima mutum ne kamar kowa, yana kuma buk'atar rarrashi da shawarar yadda zai fuskanci koma meye ya tunkaro shi, na uku kuma shine baya rik'o amma yabar abu ya barshi har abada kamar Ayman, wannan kuma zuciya ce da bamusan gurin gwanin da suka samo ta ba uwa ko uba).
So ko a lokacin da raihana tayi magana ya gama kaiwa limit na tsakiya.
Hakan yasa ya tashi yaje ya wanke fuskarshi ya futo ya kashe glove d'in d'akin saina bedside kawai ya bari ya k'arasa kan gadon ya zauna daga k'arshen gadon kamar yadda tayi, ya zura rabin jikin shi cikin duvet ya jingina kanshi da fuskar gadon idon shi bisa rufin d'akin ya tsura mishi ido..... A zuciyarshi yake tunanin ko ya amince da ita yau taji wani yanki na sirrin shi kamar yadda ta yadda dashi ta fad'a mishi nata a ranar data fara ganin shi, don ajiye zance a rai kamar yadda ya fad'a ba abinda yake sai sake assasawa mutum damuwa da jefa shi cikin tashin hankali.
Ya jima yana nazari kafun can ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya kalli sashen da take zaune. Itama a dai dai lokacin ta juyo da nufin satar kallon shi saboda ajiyar zuciyar shi ta d'au hankalinta sosai, sai kuwa cikin sa'a idanun su suka fad'a cikin na juna. Kowa a cikin su kasa d'auke idonshi yayi saima son karantar sak'on da yake cikin idon kowannen su day suka fara, hakan yasa suka lula duniya mai nisan da saida raihana tayi da gaske ta iya futowa a ciki, saita lumshe idonta a hankali tare da juyar da kanta gefe.
Shima ta b'angaren shi hakan ce ta kasance, shiru ya sake biyo baya kafun yayi gyaran murya ya fara magana da disashshiyar murya irinta wanda yaci kuka ya godewa Allah. "kiyi hak'uri d'azu na huce fushi na a kanki alhalin ba kiyi mun laifin komai ba".
Har lokacin kanta a k'asa tace, "na fahimci hakan, kuma duk da haka nayi maka laifi sai dai a rashin sani ne tunda baka tab'a fad'a mun baka son warin lalle ba".
Juyowa yayi ya fuskanceta, ya akayi ta fahimci haka? koda yake dole zata gane yadda yayi mata fancakali da kwano.
"Hakane! Duk da ba wai bana son lallen bane kwata kwata, a'a ina kyamatar shi ne a zuciyata, amma nasan lalle yana daga alamar mace y'ar gayu ta gasken gaske ma'abociyar tsabta da ado kamar dai mamana". Murmushi ne ya sub'ucewa raihana har hak'oran bakinta na bayyana, "ai ita Auntie ta kasance ta musamman ko a cikin mata dubu samun irinta sai an tona".
Shima murmushin gefen baki yayi duk da ba wai ya futo sosai ba ya sake cewa, "me yasa kika ce haka!".
"Saboda dalilai da dama". Ta fad'a cikin shagala da manta da wanda take tare.
"Toh ko zan iya sanin wasu daga ciki".
Sake jan bargo tayi ta k'arasa rufe fiye da rabin jikinta sannan taci gaba da maganarta, "sai dai na fad'a maka muhimmai daga ciki duk da nasan ma ka sani".
"Ehem go ahead!".
"Shin a rayuwarka ka tab'a ganin auntie da datti koda tana aikin gida irin aiki yasha kanta d'in nan?". Abun dariya yaba khaleefa don ya d'auka wani k'atoton dalili zata d'auko mishi, amma dai ya dake baiyi ba, madadin haka ma sai ya bata amsa da, "a'a ban tab'a gani ba".
"Yauwa sai na biyu, ka tab'a ganin ta cika fuskarta da kyale kyale ko aji gidanta ba da ita kanta ba k'amshin turare?".
"A'a" ya sake bata amsa idon shi a kanta, so yake kawai takai k'arshe yaji dalilin nata.
"Abu na uku daya kasance ba akan ado ba shin ka tab'a zuwa mata da kukan ka ta barka bata share maka hawayen ka ba?".
Tsam yayi da ranshi ya tafi tariyar rayuwarsu tun daga yarinta har kawo yanzu da suka mallaki hankalin kansu, tabbas itace mai share musu hawayen su kuma bata tab'a gajiyawa da hidimta musu ba,
Jin yayi shiru sai taci gaba da cewa, "Toh kaga ashe ta kai nagartacciyar uwa k'arshe fiye da duk wata uwa da muka sani a duniya".
"Hakane uwar alfahari ce Auntie, duk da ba wai bata da wani laifi ko kuskure ba a rayuwarta ba".
Jim raihana tayi kafun ta sake cewa, "shin ka manta a rayuwa alkhairin mutum yana dannar sharrin shi, ai duk d'an Adam baya rabo da sharri amma abun so da alfaharin shine ace alkhairin mutum ya danni sharrin shi kamar dai ita". Sake jinjina maganarta khaleefa yayi, da yake jin tana wannan maganar akan auntien sai yake ga kamar ita ta haifa ba shiba, "idan na fahimce ki dai dai kina nufin iyaye mata sunfi iyaye maza muhimmanci a rayuwar y'ay'an su?". Ya k'arasa fad'a yana tsura mata ido da son jin amsar da zata bashi.
"Kowanne da nashi sashen, idan ana maganar jigon iyali uba kenan, amma fa in akazo maganar uwa toh ita rufe k'ofa ce, don tana taka muhimmiyar rawa a tarbiyyar yara dama rayuwarsu baki d'aya. Komai kaga tayi tana da nata dalilin babu wani abu na kuskure da zata ma yaranta da gangan tana sani". Ta kai k'arshen zancen tana satar kallon shi, shima kallonta yake babu ko cikakken k'ifta ido a zuciyarshi yana rairaye kowanne zance d'aya da take fad'a da iya gaskiyarta.
Jinjina kai yayi kafun ya sake ce mata, "koda ace ta aikata tabkeken laifi ga yaran? Taya ma kike tunanin uwa zata iya tafiyar da iyali ita kad'ai babu jigo (wato uba) kamar yadda kika fad'a?". Wannan tambayar khaleefa yayi ta ba don yasan ta futo daga bakin shiba.
Itama kanta saida taji tambayar kamar da gangan ya yita, shiru tayi kanta a k'asa kafun can ya nisa ta bashi amsa, "Ina tunanin wannan tambayar ba don neman amsa kayi ba, tunda ga misalin irin iyayen nan a tare daku, Ina ganin mahaifiya ko haihuwar d'a tayi ta barshi haka nan a duniya ba tallafinta bare sa hannunta har ya girma ya zama wani abu toh ta gama yi mishi komai, idan zai tara duk abinda yake cikin duniya ya bata bazai tab'a biyanta ba.... Balle ku da kuka tashi cikin asalin gata, ko masu uba a anguwar nan ba zasu fad'a muku komai ba, auntie ba iya matsayin uwa ta d'auka a rayuwar kuba, ta d'auki matsayin uwa! Uba! Bango! Jigo kai matsayin komai ma a rayuwarku gaba d'aya, ita ta kasance d'aya tamkar da dubu, da ace wanda ya mutu yana dawowa, toh da tabbas mahaifin ku zai dawo don kawai ya jinjina mata bisa ga sadaukarwar da tayi". Raihana tana kaiwa nan tayi shiru tare da jan dogon numfashi kafun ta k'ara kallon shi ta saki k'aramin murmushi tace, "yi hak'uri zaka ga kamar Ina ta magana akan iyaye mata kamar saboda ni mace ce, a'a Ina fad'in abinda yake gundarin gaskiya ne, kuma zan iya tsayawa a gaban kowa nayi irin wannan bayanin musamman ma wad'an da suke k'ok'arin kushe mana iyayen mu mata kan k'ok'arin da sukeyi damu, a nan kam zan iya cewa sai inda k'arfina ya k'are".
Sai a lokacin khaleefa daya zuba mata ido kamar robbot ya motsa tare da janye kwayar idon shi daga kanta.
Wane irin sani da so wannan yarinyar take yiwa auntien su haka? Koshi data haifa bai tab'a magana a kanta irin haka ba, haka tunda sukayi maganar can da Saleema ya daina yabawa duk wani k'ok'arinta da jajircewa kamar yadda take yi a baya, ba gaira ba sabab ya fara zarginta da jin haushinta duk da bata fasa yin iya k'ok'arinta wajen ganin ta faranta mishi ba, ko akan maganar auren raihana sau d'aya ya nuna yana so, amma bata nutsu ba saida taga an d'aura auren raihana ta zama mallakin shi, meyasa tayi haka? Don kawai ya samu cikar burin shi, shi kuma me yayi mata? Akan soyayyar wata can data tsince shi da hak'oran shi talatin rana tsaka yake k'ok'arin mantawa da matsayinta na wadda tafi komai da kowa muhimmanci a rayuwarshi, ya fara neman k'asar da zai cika mata ido da ita. Abun kunya sai gashi yau wata tana magana a kan ita wannan matar data zama silar zuwan shi duniya kamar ita ta kawo bashi ba shiba.
Kallon sashen da take yayi, a kwance take amma ta duk'unkune jikinta sosai, take ranar da matashin nan ya futo yana mata cin mutumci ta dawo mishi, duk zagin daya mata bata kula shiba amma yana tab'a auntien ta nuna fushinta muraran.
_Wannan fa shi ake kira tuntub'e dad'in gushi_
*Littafin JARUMAR UWA gaba d'aya sadaukarwa ne ga ummata, amma a ciki wannan fejin mallakine ga duk wata uwa da ta ke duniya dama wanda suka riga mu gidan gaskiya, dama wanda suke shirin kasancewa iyayen nan gaba kad'an. Fatan Allah ya k'arawa iyayen mu lafiya da nisan kwana*
Hak'ik'a naga ruwan comment d'inku a update da nayi jiya, naji dad'i sosai kuma na jinjina muku bisa yadda kuke nuna mun asalin yadda muke tafiya tare ๐๐๐๐๐๐ na dangwala muku kyauta.
__kada ku jirayu update gobe, naso ace na kokarta mun koma kwana biyar a sati amma hakan bai yiwu ba saboda uzururruka da suka sake sha mun kai, amma insha Allah zaku jini Thursday and Friday. Nagode_
Kada ku manta dai kuna tare da Alk'alamin in-identical twins, merhreeyaert lerwerl da doctor ferhyeezz m Usmern duk abu d'aya ne๐ค
_Comment and share_โ๏ธ
24/03/23, 2:05โฏpm - Merhreeyaertou โ๐ปโ๐ป: *JARUMAR UWA*๐ง
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page fifty seven5๏ธโฃ7๏ธโฃ
Khaleefa ya jima a kwance yana wassafa wasu abubuwa masu nauyi akan mahaifiyarshi da rayuwarsu tare da ita, sai yanzu yake iya rarrabe komai daki daki yana kaishi muhallin daya dace.
Bacci bai samu ba gare shi a wannan dare hakan yasa ya k'arasa raya daren da sallah da addu'o'i, cikin hukuncin Allah zuciyarshi ta k'ara yin sanyi yaji nutsuwarshi tana dawowa.
Bai tashi a dardumar ba har mukhtarin sallar asubah ya shigo. Koda ya sake komawa bathroom ya futo da nufin tashin raihana sai ya ganta a zaune gefen gadon tana jiran futowar shi.
Suka kalli juna a tare lokaci d'aya kuma suka d'auke kai, da bathroom nashi tayi amfani ta kama ruwa da alwala ta futo tana santin d'akin wankan da yasha tsari irin na asalin matasa ma'abota gayu da tsabta.
Shiya jasu jam'i. Suna idarwa raihana a daddafe tayi addu'o'inta suka gaisa ta koma kan gadon ta nad'e cikin tattausan bargon shi da yake fudda k'amshi me dad'i da sanyaya rai. Bata jima da kwanciya ba khaleefa ma yabi bayanta, daga can k'arshen gadon ya kwanta, ba dad'ewa wani daddad'an bacci yayi awon gaba dasu.
*****Ta b'angaren auntie kam baccinta tasha don ta gaji over kuma dama ba wai garkuwar jikinta ta gama dawowa dai dai bane, har yanzu tana shan magani.
Lokacin data tashi bakwai saura y'an mintuna, sallah ta fara gabatarwa kafun ta gyara inda ta kwanta, ta tsabtace d'akin gaba d'aya ta kunna turare ta turare d'akin sannan ta futo parlon, duk da babu datti saida ta sake gyara shi ta d'auke wayar raihana data fashe ta ajiye kan center table ta kawo turare nan ma, a k'arshe kuma ta dire a kitchen, nan kam babu abinda ta tab'a sai abincin karya kumallo data fara had'awa. Koda ta gama tea kawai tasha ta jere abincin a dinning tana sake duba lokaci.
Rana har ta futo amma babu alamun raihana bare khaleefa, da farko tayi tunanin jiran su amma ganin lokaci nata tafiya saita d'auki nata ta rufe musu ragowar.
****Tsaye take a gaban k'ofar shiga d'akin Amna, da kallo d'aya zaka fahimci sam bata cikin nutsuwarta, tun a daren jiya take son had'uwa da amnan abun ya faskara, tsabar takaicin data had'a mata bata iya runtsawa da kyau ba bacci sai b'arawo.
A shirye amnan ta futo cikin shirin futa, turus ta tsaya ganin Saleema tsaye a gabanta. Niyyar hucewa tayi sai dai saleeman ta hana mata damar hakan ta hanyar tunkud'eta ta shige ciki ta maida k'ofar ta rufe.
"Me ya kawo ki?". Amna ta tambayeta cikin k'arfin hali bayan ta ajiye wayarta gefe.
"Har kina da bakin tambayar abinda ya kawo ni bak'ar munafuka! Yau nazo ayita ta k'are koni ko ke don na gaji da irin abubuwan makircin da kike k'ulla mun, dama akace sai ka d'auki tsawon shekaru da mak'iyinka ba tare daka sani ba, yanzu nake fahimtar haka daga sharrance sharrancen da kike k'ulla mun.....". Ta k'are zancen tana zare k'aramin siririn gyalen jikinta ta ajiye gefe d'aya.
Murmushi Amna tayi ta k'ara matsowa har gabanta tace, "kina wasa da rayuwarki Saleema, abinda na miki jiya kin manta na tab'a fad'a miki zan aikata? Koda yake ni yanzu sunan maฦiyiya nake amsawa a gurin ki saboda ina son ganin na ceto rayuwarki daga fad'awa halaka.... Well muje a hakan watarana ai gaskiya zatayi halinta, sai abu na gaba khaleefa naki yaji jiya amma shima akwai nashi laifin da baki sani ba, don yayi aure zuwan shi gida Nigeria".
A zabure Saleema taji zancen don ya shiga ne da gudu ta kafofin jinta, "what? Aure? how comes?" Tayi tambayar a rarrabe tana juya hannunta.
"Aure dai irin wanda kika sani, koda yake ai bai kamata na fad'a miki bama tunda ke dashi kunyi equal babu wanda ya huce ya zalinci wani, sannan labarin nan tunda zafin shi na kawo miki shi kika gwasale ni baki karb'a ba sai yanzu daya huce....".
Durk'ushewa Saleema tayi a gurin ta rabka uban tagumi, "shikenan tasan ba ita ba khaleefa kuma har abada, don khaleefa bai shirya rayuwar shi da auren mace sama da d'aya ba bare tace maybe yana nufin aurota daga baya, kuma koba haka ba sunyi alk'awarin ba kishiya, toh taya ma zai lalata musu duk wani shiri da suka yima rayuwarsu.
Tsam ta sake yi da ranta tana tuna yadda suka rabu, daman khaleefa ya shirya haka gareta shiyasa daya tashi tafiya ya dawo mata da zobenta a nufin shi ya dawo mata da soyayyarta kenan?, Tab in hakane kuwa yayi kuskure don ba zata iya rayuwa da wanin shiba, lallai saita tabbatar ta raba shi da koma wacece koda ba zata same shi ba.
Mik'ewa tayi