Showing 99001 words to 102000 words out of 288773 words
Chapter 34 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
mama haleema kasa matsawa daga jikin k'ofar d'akinta tayi tana ta dakon futowarta cike da zullumi da fargabar abinda ka iya zuwa yazo, ta tsorata da yanayin auntien a yau, har lokacin tafiyarta gida yayi ya huce tana nan tsaye tana sak'awa da kwancewa, daga k'arshe kawai saita nufi b'angaren y'an biyun, da Ayman ta fara cin karo zai futo, sai ya matsa baya don ya bata damar shiga parlon, itama tunga taja ta tsaya tace, "anguwa zaka ne?". Sai ya futo wajen shima yace, "a'a gurin auntie zani cikina ya fara kiran...." Sai ya k'arashe da murmushi, mama haleema ta gane abinda yake nufi, sai ta fasa fad'in abinda tayi niyyah don idan suka ji ba zasu iya cin abincin bama, madadin haka sai tace, "dama kuwa abincin tace a fad'a muku an gama tuntuni a kawo muku shi nan"
"Toh tana ina auntien....". Har ta fara inda inda zata had'a wani abun sai ya k'ara cewa, "koda yake bari na biki na amso mana abincin kawai". Tare suka je har kitchen ta had'a musu abincin a tray kamar yadda taga auntie tana yi musu duk dare, Ayman ya karb'a ya tafi ita kuma ta nemi guri a parlon ta zauna.
Khaleefa yana zaune da three quarter wando da riga armless, k'afar shi tankwashe akan gado yana karanta wani littafin addu'o'i dad'ad'd'e da auntie ta basu. A nutse Ayman ya shigo da trayn hannun shi, kallon shi kawai khaleefa yayi har ya k'araso ya ajiye abincin saman table k'arami da yake gefe, "dinner is ready" ya fad'a yana zama don ya saving nasu, khaleefa ajiye littafin yayi a gefe ya sauko yazo ya zauna kusa da Ayman, abincin yake kallo har Ayman ya gama misu saving ya tura mishi, lomar farko da yakai bakin shi ya gane wannan girkin sam bana Auntie bane, duk da tarin yunwar da yake ji sai yaji abincin ya futa a ranshi, haka dai ya tuttura ya kora shi da tea me zafi, yana kallon Ayman yana cin abincin shi a tsanake.
Saida ya gama ya kwashe komai ya mayar kitchen sannan mama haleema tace suzo shida khaleefa, yana fad'awa khaleefa ya mara mishi baya suka taho tare suka sameta, nan ta basu labarin iya abinda idonta ya gani da yadda auntie ta shige d'aki ta rufe sama da hour uku tana ciko. Duk hankalin su tashi yayi, sai suka rasa abinda zasuyi ma, khaleefa ya tambayeta, "kin buga bata bud'e miki ba kuma?".
"A'a tace bata son kowa ya dameta". Sai ya tafi jikin k'ofar ya soma buga mata da k'arfi. A lokacin ta idar da sallah kenan sai dai idonta har kumbura yayi saboda kuka, kamar ta share sai taji muryoyin su Khaleefa da haleema ne, a sanyaye ta tashi sanye da hijab d'in sallar ta ta bud'e k'ofar, kallonta khaleefa yayi sai ya sauke ajiyar zuciya a b'oye ganin tana lafiyarta lou, guri ta basu duk da batace komai ba amma sun gane tana nufin su shigo, aikuwa suka shiga gaba d'aya suna binta ita da parlon da kallo, "mama haleema baki tafi gida ba? Kada fa kisa Inna ta fara kira tana tambayar zaman me kikayi". Tana kallon yadda fuskar surayyan ta dawo luhu luhu tace, "Ai na fad'a mata yau anan zan kwana". Murmushin yak'e tayi tace, "toh yayi".
Ayman da yake kallon yanayinta kasa hak'uri yayi saida yace, "auntie meya same ki haka?". Sai data k'ara danne hawayenta kafun tace, "lafiya lou nake meka gani". Sai yayi k'asa da kanshi kurum. Haka suka zauna jigum sai kallonta suke suna son su tabbatar da lafiyarta, khaleefa ne ya fara musu sallama ya tafi makwancin shi, sannan Ayman, ya rage daga ita sai haleema, gyara zama tayi ta kalli haleeman ta tambayeta, "kin fad'a musu wani abu ne?". Shiru tayi kafun can tace, "tsorata nayi da ganin yanayin ki d'azu da yadda kika kulle kanki shine na fad'a musu saboda ina tsoron ko ba lafiya kike ba".
Sai taja ajiyar zuciya ba tare da tace komai ba ta mik'e don taje ta kwanta, itama haleeman makwancinta da take kwana a duk lokacin da tazo gidan ta nufa.
@@@@@
Raihanatu kuwa tana komawa gida ta shige d'akinta ko ummie bata nunawa rubutun da malam ya bata ba, ita ta manta ma sai bayan da tazo zata kwanta ta tuna ta d'auka ta shanye ta nemi guri tayi kwanciyarta, sunyi waya da Imran sama sama saboda baccin da take ji k'arshe suna wayar bacci ya sadaddafo yayi gaba da ita, sai ya kashe wayar kawai yana murmushi.
Kwana uku a tsakani tana karb'ar rubutun malam tana sha ko ummie bata fad'awa ba har ta cika adadin kwanakin cif.
A rana ta hud'u ta tambayi abbanta tunda sassafe kafun ya futa kan tana son taje ta gaishe da ummaa (kakarta ta wajen uwa). Ta gama abinda take yi tunda wuri ta yiwa ummie sallama ta tafi, a can ta tarar da su Amina sunje suma kamar sun san tana tafe, aikuwa suna ganinta suka d'au murna da sowaa ga amarya ga amarya. Ita dai tayi murmushi kawai ta zauna kusa da ummaa, bayan sun gaisa itama zolayarta ta dinga yi har saida tace zata tashi ta tafi sannan ta kyale ta. Ranar suka yini suna hirar su da budurin su har yamma, nan ta yiwa ummaa sallama ta taho gida.
Auntie kuwa a washe garin ranar da abin nan ya faru tana zaune da safe wayarta ta soma k'ara, ganin bak'uwar no tana kiran private sim d'inta saita d'aga tare dayin sallama, bata gane me muryar ba duk da a haka tana ji kamar tasan muryar, har suka gama gaisawa ya gabatar da kanshi, mahaifin Nur ne, sai tace, "oohh Allah sarki ya kake ya mutanen gidan". Daga can b'angaren yace, "suna lafiya Lou alhamdulillah, dama kira nayi inji k'arfe nawa masu kawo kud'in zasu zo?". D'an Damm tayi kafun ta nisa tace, "ai mun soke wannan maganar bata fad'a maka ba?". Yace, "Ni ba ruwana da abinda ya had'a ki da ita, ni nine nan mahaifin Nur kuma a shirye nake dana ba Adam idan kun shirya ko anjima zasu iya zuwa a tsaida magana". Shiru surayyah ta sake yi kafun ta kuma cewa, "toh aini bansan yadda zan ce maka ba, maganar gaskiya ni tun jiya na kawo k'arshen maganar auren yaran nan, don Allah mu ajiye komai a gefe, ban rik'e sameera da komai ba, tabbas batayi laifi ba ya kamata ace na nuna yarda gareta ko yaya ne, sai dai abinda bata sani ba shine na jima da yiwa raina alk'awarin har abada bazan tab'a iya bada labarina ga wani ruhi ba saboda baki bazai iya hak'uri ba in kunne yaji saiya furta shi,,, na fad'a mata ba ita kad'ai ba kowa ma ban yarda dashi ba har jinina da muka futo ta tsatso d'aya,,, shine kawai...... Da haka nake maka godiya kaima.... Nagode nagode da kulawa Allah ya bar zumunci" Tana gama maganar ta bata tsaya jin ta bakin shiba ta katse kiran, har ta ajiye wayar sai ta sake d'aukowa tayi dialing no malam, bayan sun gaisa shima tambayar daya fara yi mata shine, "kince da safe za'a kai kud'in auren ne gashi muna ta jiran ki tun d'azu shiru har malam mukhtari ya kirani a waya..". Ajiyar zuciya taja tace, "malam maganar auren nan mu barta zuwa wani lokaci.....". Cike da mamaki shima ya tambayeta, "a'a me yasa? Fasawa kukayi?". Tace "ko kad'an malam akwai abinda nake son ya kammala nan da wani lokacine.." ta k'arasa fad'a tana toshe bakinta da hannunta gudun kada sautin kukan ta ya futa, shima saida ya jinjina sannan yace, "toh Allah ya taimaka". Da kyar ta iya cewa "ameen" ta katse wayar. Switch up d'inta tayi gaba d'aya ma ta ajiyeta gefe.
Ta kife kanta jikin gefen gadonta ta fashe da sabon kuka, shikenan yaran ta basu ba aure har k'arshen rayuwar su, indai saida wani cikin dangin ubansu ko shi uban za'a basu auren ta gwammace su rayu ba aure har k'arshen numfashin su.... don ta yiwa ranta alk'awarin har abada ita da neman Suraj ko dangin shi indai akan rayuwar yaranta ne, itace uwarsu, itace ubansu, itace koman su basa buk'atar ubansu da yake matsayin matacce a gurin su......
Knocking k'ofarta da akayi yasa tayi saurin share hawayenta da tafukan hannunta ta mik'e daga sallayar sannan ta bada izinin shiga, haleema ce ta shigo da k'aramin tea plask da cups akan tire ta ajiye gabanta, suka gaisa da surayyah sannan ta futa, da kyar ta iya shan ruwan tea d'in don bakinta har wani d'aci yake mata, haka dai ta daure ta shanye k'aramin cupi d'aya ta shiga bathroom tayi wanka ta shirya cikin yaloluwar doguwar riga marar nauyi ta rufe kanta da k'aramin gyale ta futo parlon.
Ba jimawa Ayman ya sameta, khaleefa ma yazo, duka sun damune akan yanayinta na jiya, ba laifi sun ganta ba kamar jiya ba amma fa Sam bata da walwala. Khaleefa bai zauna da yawa ba ya futa ya barta ita da Ayman.
Toh sai muce kusan kwana biyu a tsakani doctor surayyah bata da walwala sam, duk k'arfin halinta a wannan karon ta gaza, saboda an tab'a wani abu da yake rauninta a rayuwa wato Suraj.
Mama haleema kwananta biyu a gidan ta kasa barinta saboda tsoron kada tana tafiya wani abu mara dad'i ya faru, haka y'an biyunta suna zuwa dubata akai akai barin ma Ayman da yafi nuna damuwarshi a fili.
A tarihin doctor surayyah bata tab'a yin kwana biyu ba tare data futa ko k'ofar gida ba, amma a wannan datsin ta tashi cimma kwana hud'u ko parlon k'asa bata sauka ba,, harkokin business d'inta da komai ya tsaya.
Ayman kuwa yana can cikin kwanakin sai trying no Nur yake baya tafiya, bai kawo komai a ranshi ba sai tunanin k'ila lalacewa wayar tata tayi, har ya fara tunanin irin wayar dazai siya mata sabuwar yayi da zai burge ta. A ranar da yamma ya siya mata sabuwa dal a kwali ko gidan bai shigo da ita ba ya barshi a mota. Abu biyu ne suka zame mishi tsaiko da tuni ya kai mata, yanayin da suka tsinci kansu a gidan na rashin walwala yasa bai samu kwarin gwiwar zuwa gidan su Nur d'in ba tuni.
A yammacin ranar lahadi khaleefa yana zaune kan gadon d'akin shi, bayan tattara duk wani binciken shi guri d'aya adanasu yayi yana tunanin yadda zai had'u da Ahmad ya nuna mishi don Susan yadda zasu b'ullowa komai, bayan ya ajiye komai dake gaban shi gefe kwanciya yayi rigingine kanshi jingine da fuskar gadon, k'afarshi d'aya a tokare jikin gadon d'aya kuma a k'asa.
Tunanin Saleema yake yana tuna duk moments d'insu da ita na k'asar Germany, sai yaji kamar ya tariyo baya ya goge labarin rayuwarshi daya bata har sai bayan ya aureta.
Yana Wannan tunane tunanen Ayman ya shigo da sallama, daga kwance ya kalleshi ba tare daya motsa ba, "it seems like kana da babban bak'o yau....". Fuskarshi kadaran kadahan yace, "who is he". Matsawa Ayman yayi sai ga Ahmad ya bayyana cikin d'akin, ai khaleefa baisan lokacin daya dire k'afafun shi k'asa ya mik'e tsaye yana kallon shiba, shima Ahmad Kallon shi yake kafun yaci gaba da takowa zuwa inda khaleefa yake suka rungume juna. Ajiye jakar hannunshi yayi a nan d'akin khaleefa suka zauna suna gaisawa, khaleefa da kanshi ya kawo mishi ruwa me sanyi. Sun tab'a hira su uku kafun Ayman ya tashi ya basu guri, da sauri khaleefa ya d'auko system d'inshi ya nuna mishi sakamon binciken shi, koda Ahmad ya gama dubawa shiru ne ya biyo baya yana nazari kafun can ya nisa yace, "kasan duk abinda nakeyi kana raina kuwa khaleefa? Shiyasa ina dawowa jiya na biyo hanya yau nazo na ganka, amma fa kayi k'ok'ari matuk'a, sai dai ka manta wani abu wanda ka samo mai suna Suraj Abdallah tofa babban d'an kasuwa ne daya mallaki manyan kamfununuwa a kasashen duniya dama gida Nigeria, har yafi Abdallah tofa kud'i da shahara a b'angaren kasuwanci tunda shi dama d'an siyasa ne, toh sai dai wani hanzari ba gudu ba ba don kud'in da wannan mutumin ya mallaka ba, Ina ganin kamar ba akanshi ya kamata kayi binciken kaba, tunda ku mahaifin ku ya mutu baya raye ko ka manta ne?". Dafe kai khaleefa yayi don shi har ga Allah mantawa yake da mahaifin su baya raye tun lokacin daya fahimci auntie tana b'oye musu wani abu mai muhimmanci na daga rayuwar su, "kasan me Ahmad ni mantawa nakeyi da wannan shap, sannan a yaran Abdallah tofa wannan kad'ai nayi nasarar samu duk da sunkai su kusan shida, sannan shi zan bibiya tunda shine naji tsarin rayuwarshi, asibitin da zamuyi aiki a Germany yana zuwa check-up duk bayan watanni biyar gurin doctor andal itace amintacciyar likitar shi, Ina ganin zamu same shi ta hannun ta, idan muka tabbatar bamu had'a komai ba shikenan sai na hak'ura Ahmad".
Shiru Ahmad yayi kafun caan yace, "toh hakane maganarka, komai ma auntie zata iya b'oyewa ta silar b'acin rai ciki hadda tura rayayye rami a baki, sai maganar aiki ko kayi mata magana?". Nan ya warwarewa Ahmad duk yadda sukayi da ita akan aikin shima da sharad'in data gindaya mishi. "Toh fa wannan shi ake kira ana wata ga wata". Ahmad ya fad'a, khaleefa yace, "Humm ka bari kawai". Ahmad yayi dariya kad'an yace, "kasan me! Nifa har na fara tuno Duk wannan turka turkar watarana sai labari da sannu komai zai huce faaa". "Anya kuwa Ahmad?". Khaleefa ya fad'a cikin sarewa, "haba man babu abinda yake dawwama a duniya sai ikon Allah". Khaleefa yace, "hakane kuma, amma kanajin sharad'in da auntie ta gindaya, bayan ga k'udurin da nake dashi akan neman auren Saleema, ni sai yanzu ma nake jin kwarin gwiwar yin aiki a Germany.....".
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa a tsakanin su, Ahmad yaba khaleefa labarin yadda suka daidaita kansu da Yasmin har an tsaida lokacin biki nan da wata hud'u masu zuwa, khaleefa ya taya shi murna sosai daga k'arshe yayi mishi addu'ar fatan alkhairy, tsawon lokaci suna hirarrakin su kafun su tashi don suje ya gaishe da Auntie.
Suna futowa Ayman ma yana futowa kamar had'in baki, "yaah! Anguwa za'a futa ne". Ahmad ya tambayi Ayman, murmushi yayi yana kad'a mukullin motar da yake hannun shi yace, "ehh zan lek'a gurin gimbiyata ne". "kaji manya da kyau ace manyan yayye suna gaisheta". Ahmad d'in ya fad'a yana d'an dariya, shima Ayman dariyar yayi yace, "sai dai na fad'a mata manyan gwagware daya kamata su huce gaba k'anin su yabi bayansu, amma suka coge a baya suka tura k'anin nasu gaba sunce suna mik'o gaisuwa". Dariya suka sakeyi su biyu khaleefa kam murmushi yayi yace, "sai ka gyara zancen ka Cox Ahmad is engaged". "Ah haba really" Ayman ya tambaya da mamaki, shikam baice komai ba sai murmushi daya sake yi, ahh lallai abu yayi kyau Ahmad Allah ya sanya alkhairy ya nuna mana lokaci, ya kawo namu muma". Ahmad yace, "ameen thumma ameen". Shi kuwa khaleefa kallon Ayman d'in yayi a lokacin daya k'arasa musu sallama ya tafi, abun tausayi baisan watak'ila mu bamu da rabon aure ma a duniya ba. Khaleefa ya fad'a a ranshi.
Sun shiga parlon auntie da sallama su duka biyu, a lokacin tana magana da mama haleema ne kan taje gida su ganta ita lafiyarta lou ta daina damuwa da yanayin da take ganinta ciki y'an kwanakin, gobe goben nan ma zata koma aiki,,,,, shigowar su Khaleefa ya katsewa haleema hanzari akan abinda tayi niyyar fad'a, sai ta d'auki ledar da surayyah ta ajiye mata a gabanta kawai ta mata sallama zata huce, Ahmad gaisheta yayi sannan ya durk'usa har k'asa ya fara gaishe da auntien, cikin farin cikin ganin shi auntien ta amsa tana tambayar shi mutanen gidan su. Ya fad'a mata duk suna lafiyar su lou
Sunyi shiru kowa da tunanin da yakeyi a tsakanin su kafun khaleefa ya fad'a mata an tsayar da ranar auren Ahmad nan da 4 months, sake fad'ad'a fara'ar fuskarta tayi tace, "Masha Allah son Allah ya sanya alkhairy ya nuna mana lokaci da rai da lafiya,,, ahh Masha Allah....". Shikam sadda kai k'asa yayi yana murmushi, bayan sun sake yin shiru auntien ta yiwa Ahmad magana, "kazo a dai dai Ahmad dama Ina son magana dakai" saita kalli khaleefa da shima yake kallonta tace, "ko zaka bamu guri". Ba musu ya mik'e ya fuce daga d'akin, ita kuma ta dawo da dubanta ga Ahmad tace, "magana nake son yi dakai ta sirri akan abokin ka,,, kayi mun alk'awari ba zaka fad'a mishi ba ko da sub'utar baki, saboda bana so yasan nasan abinda yake ciki"
A madadina da d'aukacin members na JARUMAR UWA fans club. Muna mik'a sak'on ta'aziyya ta ga y'ar uwata, mahadin Alk'alamina Dr Ferhyeez m usmern akan rashin da mukayi na y'ar uwa k'anwa gare mu nida ita hasseena. Fatan Allah ya jikanta ya gafarta mata ya haskaka kabarin ta, mu kuma ya kyauta namu zuwan.
Happie juma'at Mubarak.
A yau nayi k'arin shekara guda a duniya,,,, Ina son duk wani fans d'ina ya tayani da addu'ah da fatan alkhairy😊.
_ina godiya da comment na nuna goyon baya,,,,, Ina yinku fiye da yanda kuke yina😍😍😍 much k'auna_
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of