Showing 117001 words to 120000 words out of 288773 words
Chapter 40 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
yake son malam ya shige gaba yayi mishi,,,,, amma fa idan har kunji zuciyarku ta nutsu daku bashi auren a yadda yake,,,, ba dangin uban shi, bare uban daya jima da mutuwa a idon shi,,,, nayi alk'awarin indai sai dangin Suraj sun saka hannu a rayuwar yarana zasu zama wani abu,,,, toh wallahi gwara mu dawwama nida su baci gaba a yadda muke, koda ace hakan zai zama silar mutuwa ta kuwa......" Yadda takai k'arshen maganar da wani irin fushi mai futa daga can k'asar muryarta kad'ai ya bayyana tsantsar b'acin ran da take ciki, sai babu wanda yace mata komai, amma zuciyar ummie fal tausayinta, a zuciyarta har tana tunanin irin girman laifin da wad'annan mutanen sukayi mata da take irin wannan ik'irarin. Tana cikin tunanin taji taci gaba da magana, sai ta sake bata hankalinta kacokan.
"Idan har kun amince muna son a d'ora daga inda aka tsaya a maganarta da Imrana, wato bi ma'ana nan da kwanaki biyar a d'aura auren da khaleefa instead of Imran daya janye".
Daga ummie har Abba shiru sukayi bayan gama sauraron ta, hatta raihana da take gefe saida taji kanta gingirin, duk da dama tasan da maganar tunda sun shirya hakan da khaleefa already.
Malam dama tuni ta kashe mishi baki ya zuba mata ido yaga yadda zata kaya da mutanen nan bayan gama fallashe musu duk wani b'oyayyen sirrinta, da suke jin wai a gari.
Abba ne ya kalli raihana da kanta yake a k'asa ya kira sunanta da nutsuwa, "raihana". Bata iya amsawa ba saboda bakinta daya mata nauyi sai d'ago kai da tayi ta kalle shi.
"Shin kin amince da auren khaleefa kamar yadda mahaifiyar shi ta buk'aci a bata?".
Sake mayar da kanta k'asa tayi hawaye na biyo kuncinta marassa tushe bare cikakken makama. Ganin haka sai surayyah ta mik'e ta koma kusa da ita ta d'ago kanta, da kyar ta iya kallon auntien kafun ta kawar da kanta gefe da sauri, "kada kiji komai raihanatu ni d'innan matsayin uwa nake a gurin ki koba maganar aure, Ina fatan kunyi magana da khaleefa kafun zuwana....?". Gyad'a mata kai tayi alamar eh. Ummie ta bita da kallon mamaki, auntie ce ta sake cewa, "Shin khaleefa tursasa miki yayi ki aure shi dole?". Girgiza mata kai tayi,,,, "toh me yasa kike kuka ko baki amince da auren shiba? In bakya so kada ki b'oye mun komai ki fad'a mun don bazan yi miki dole ba, Cox bani zan zauna miki dashi zaman aure ba". Shiru ta sake yi kanta a k'asa, auntie ta sake cewa, "iyayenki suna son suji amincewar ki daga bakin ki".
Sai a lokacin ta d'ago ta saci kallon ummienta don ganin reaction d'in kan fuskarta, kadaran kadahan yanayinta,,,, sai ta maida kanta k'asa idonta yana tara ruwan hawaye, so take ta fahimci yadda ummienta ta karb'i zancen, idan har taga amincewar ta da maganar saita yarda da auren, idan Kuma har batayi na'am ba toh shikenan sai tace Allah ya had'a kowa da rabon shi.
Ganin bata da niyyar cewa wani abu sai abbanta yace, "Wai ba tambayarki muke ba raihanatu?".
Auntie tana murmushi tace, "ayyah ka bita a hankali tana shawara da kanta a zuciyarta ne".
Ummie data gama nazarinta tsaf sai a lokacin tayi magana, "wannan shirun nata fa yana nuna amincewar tane a fili ba sai ta furta ba".
Shi kanshi malam murmushi yayi don ya lura da haka, sai yace, "tabbas! Raihana kuwa akwai kunya". Cikin jin dad'i auntie ta kamo hannunta tace, "na fad'a miki kada kiji kunya ta, ki d'auke ni kamar ummienki don kema y'ata ce kamar su Ayman".
Wannan karon da gefen hijab d'inta ta rufe fuskarta tana k'ok'arin tsaida hawayenta, ambaton Ayman yasa taji wani iri a zuciyarta harda fad'uwar gaba.
Abba ne yace, "Toh Masha Allah raihana shiga ciki zamu k'arasa magana".
Ta mik'e tsam ta shige d'akinta da sauri.
Auntie ta bita da kallo cike da so har ta shige, Allah yasan tun da jimawa take son yarinyar nan, shiyasa ko lokacin da take tare da Ayman bata tab'a jin haushin alak'ar suba, hasalima ta fahimci kamar akwai wani abu tsakanin su ita da Ayman a lokacin. Kuma tasha tambayar shi a farko farko sai yace shi babu wata alak'a a tsakanin su, hakan yasa ta watsar da zancen itama, saboda a lokacin y'ay'an sameera take son had'a zumunci dasu, tana ganin kamar sunfi kowanne yaran wannan zamanin tarbiyyah da hankali, baya ga haka ma tana ganin uwarsu cikakkiyar masoyiyar ta da zatafi kowa fahimtar ta in aka d'auke su malam,,,, ashe su abun a gurin su Sam ba haka bane.
Sai ta sauke b'oyayyen ajiyar zuciya. Abba kuma yayi gyaran murya don karkato da tunaninta ya dawo dai dai kafun ya fara magana da fad'in, "duk naji bayanan ki doctor surayyah, sai dai ni banga wani abun aibu a cikin maganarki ba gaba d'aya, ko suna da cikakken asali ko basu dashi ni abu d'aya zan duba, nagartarku keda su malam da kuma tarbiyyar yaran da nagartarsu su kansu ma, duk da bansan shi wanda za'a nemawa auren raihana a cikin su ba, amma nasan duk d'an da ya taso k'ark'ashin kulawarku keda su malam bazai tab'a kasancewa fitinanne ba, kuma naga zahirin hakan a gurin Ayman, saboda tsawon shekaru tsakanin shi da kowa a anguwar nan gaisuwar mutumcine, da wannan yak'inin na baku amanar auren y'ata raihana, da kyakkyawan zaton cewa zaku kula da ita cikin aminci,,,,". Ko daya dire aya malam ne ya karb'i zancen inda yake cewa, "hak'ik'a naji dad'in wannan maganar da kayi Abubakar matuk'a, wannan abun da kukayi ya tabbatar mana da ku d'in mutane ne na gari da suke kallon kowanne yaro d'aya da nasu yaran ba wani banbanci,,,, sai dai wani hanzari ba gudu ba, da kud'in auren da sadakin da lefe zamu kawo su duka ranar juma'ar da za'a d'aura aure, sannan abu na gaba shin ka tab'a yin tunani akan fashe fashen auren yarinyar nan kusan karo shida ko biyar da akeyi?" Girgiza kai Abba yayi yace, "ko da wasa ban tab'a kawo tunanin komai a raina ba, kawai abu d'aya na sani komai na Allah ne".
Jinjina kai malam yayi yace, "wannan haka yake, shiyasa a wannan karon nake son kayi hak'uri kada ka fad'awa kowa abinda yake faruwa, kamar yadda aka raba invitation card da sunan Imran a bar mutane a hakan in sunzo wajen d'aurin auren saga sauyin da aka samu,,,, kuma har d'an uwanka Abubakar ina so kada ka sanar mishi zancen fasa auren a wannan karon, Ni nan zan nemo shaidu su kasance a tsakiya a lokacin da zamu mayarwa alhaji abubukar kayan auren su,,,, Ina fatan babu illa a cikin shawarata".
Shiru yayi yana d'an tak'aitaccen nazari, sam baiga fa'idar b'oyewa d'an uwan nashi ba, amma tunda har malam d'in ya bashi shawara ba zai k'i biba tunda baisan abinda ya hango ba. Da haka ya amince da shawarar mallam.
Suka rabu girma girma cikin mutumci, Abba ya raka su har k'ofar gida.
Ko da suka tafi ummie zama tayi tare da zabga uban tagumi tana tunanin rayuwar d'iyar tata, raihana tana ganin k'addara kala kala a rayuwa masu kyau da akasin haka, toh ita dai tana fatan alkhairin Allah ya kasance tare da wannan auren nasu da har yanzu bata daina mishi kallon hargitsatstse ba, tana y'an tunane tunanenta Abba ya shigo d'akin, kusa da ita ya zauna yace, "kina tunanin inda rayuwar raihana zata fad'a ko?". Girgiza mishi kai tayi, sai yaci gaba da maganar shi, "nasan zaki ce nayi hakane saboda na gaji da ita so nake kawai naga na aurar da ita ga koma waye...". Shiru ta mishi yanzun ma, "Abu biyu nake so ki fahimta a tare da kalaman wannan baiwar Allahn, na farko, lallai akwai wani b'oyeyyen al'amari da yake bibiye da ita da bata son kowa ya sani, kai tsaye bazan kira yaranta da shegu ba, saboda ni a har kullum Ina kyautatawa d'an Adam zato, sannan ko a gabana tayi cikin shege ta haife yaranta, ni bazan fasa wanke y'ata na basu aurenta ba muddin suna da nagartar da za'a iya basu auren, balle ma surayyah ba tayi kama da marassa kintsi da nutsuwar da za'a ce ta aikata irin wancen al'amari ba,,, da haka nake rok'on ki kan kisa ranki a inuwa, ki sawa zuciyarki salama, insha Allah babu wani abu da zai biyo bayan auren nan sai alkhairy".
Ummie gyara zaman ta tayi tare da girgiza kai kafun ta fara cewa, "a wasu lokutan in kayi magana sai naga kamar baka sanni ba salees, shin kana tunanin akwai wani hukunci da zaka yanke akan raihana har naja da kai? Sannan yadda ka kalli surayyah nima haka na kalleta, Cox a iya sanina da surayyah macece mai matuk'ar kirki da take zaune da kowa lafiya da zuciyarta d'aya,,,, haka d'anta dasu malam ma, kaga ko iya wannan mutum ya tsaya akai hujja ce data isa tasa a k'ulla kyakkyawar mu'amula da ita".
Murmushi Abba yayi yace, "zancen ki gaskiya ne, bari mu gani yanzu ko shima za'a ce an fasa?".
Girgiza kai ummie kawai tayi, tana tuno yadda maganar Imran ta rushe ya zam babu ita cikin d'an k'aramin lokaci har ta khaleefa ta shigo, ko y'an uwanta ta kasa fad'a musu fasa auren daga jiya zuwa yau, gashi sun raba catin biki guri guri,,, Allah yasa ma ita raihana ba mai son bidi'a bace ba abinda ta shirya sai kamu mai had'e da waleema, duk da sunan mother's event,,, angon ne dai yake maganar zaiyi dinner da reception. Saita sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ta mik'e don ganin kwamacalar dasu muhibba sukayi mata a gidan yau.
Raihana kuwa kwanciya kawai tayi ta zubawa rufin d'akin ido tana tariyar kalaman auntie na d'azu cikin kunnenta, da gaske dama haka mutanen gari suke cewa su Yaya Ayman basu da uba? Toh ai ita bata tab'a jiba koda wasa, ko da yake suna tare ai ba lallai ayi maganar a gabanta ba, sannan ita da ba shiga wani shirgin mutanen anguwar takeyi sosai ba, taya zata san abinda yake faruwa?
Sai ta mik'e zaune sosai tana kallon k'afarta da take nad'e da bandage, sai a lokacin ta tuno ko magungunanta bata sha bama, yamutsa fuskarta tayi kad'an tuno da irin zugi da rad'ad'in da k'afar take a duk lokacin data taka ta a k'asa.
******A gidan iya. Malam da surayyah ne zaune sai iyan a k'asan carpet dake malale tsakiyar parlon, bayan sun gama bawa iya labarin komai daya faru a gidan salees basu b'oye mata ba, ita kanta ta jinjinawa wad'annan bayin Allah da basu kawo zargin komai a ransu ba, lallai ta dad'a yarda mutum baya gane masoyin shi sai abu irin haka ya taso. Sai a lokacin iya take warwarewa surayyah yadda sukayi da sameera kwanaki can farkon samun matsalar su, "sameera fa tazo har gidan nan bayan mun gaisa take fad'a mun tazo ne saboda kun samu wani d'an sab'ani da ita akan auren nuriyyah da Ayman, ta bani labarin duk yadda kukayi sannan ta d'ora da cewa, ita ba wai ta hana Nur auren Ayman bane amma tafi son komai ayi shi da k'a'ida da tsari, aga dangin ubansu Ayman kamar yadda aka ga na nuriyyah, shine kawai sannan a k'arshe tana k'ara baki hak'uri saboda ita har abada ba zata tab'a butulcewa alkhairan kiba, sannan har gobe tana jin nadamar juyawa juna baya da kukayi, tace a fad'a miki kiyi hak'uri ki yafe mata". Ajiyar zuciya surayyah ta sauke kafun can ta nisa tace, "Allah ya yafe mana gaba d'aya".
Malam ne yayi gyaran murya ya fara magana da fad'in, "Masha Allah anzo inda nake son bada shawarata nima, saboda lokaci yayi daya kamata ki watsar da komai ki bayyanawa yaran nan abinda kike b'oyewa akansu tsawon shekaru, ya kamata ko basu ga uban suba suga dangin shi don Allah ki taimaki yaranki surayyah, ai ba don kanki zakiyi ba".
Tunda aka fara maganar nan surayyah bata ce komai ba kanta a k'asa tana yak'i da hawayenta da suke barazanar bayyana kansu ga su iya don su nuna rauninta, Wanda ita kuma tayi alk'awarin an daina gani a tare da ita tun shekaru ashirin da doriya da suka gabata. Cikin dakiya da kwarin gwiwa tace, "kayi hak'uri malam, ba wai nak'i bin ta taka bane amma Ina son don Allah wannan maganar mu barta zuwa wani lokaci".
Gyad'a kai malam yayi yace, "insha Allah an barta kamar yadda kike so".
Sun k'ara shirya yadda komai zai gabata kafun tayi musu sallama bayan ta gaisa da harira, don ragowar sun tafi tuni sai ita kad'ai ta rage zata kwana musu biyu, ita d'in ma ance cikin satin zata tafi don komai ya daidaita tsakanin su, tuni sun fahimci gaskiya sunyi nadama ta gaske,,, itama iya ta sauko ta hak'ura tuni.
A ranar da yamma malam da mahaifin raihana da wani limamin babban masallacin juma'ah na anguwar suka mayar da kayan lefe da kud'in auren da aka kawo na Imran har gida.
Farin ciki a zuciyar hajiya tafeeda bakinta ma ya kasa rufuwa, shi kuwa Imran koda yaji labari a bakin k'annen shi kasa cewa komai yayi, a k'arshe ma ya shige d'akin shi ya rufe kanshi da key gaba d'aya. Ko a jikinta Ita kam har ta gama tsara yadda zata tafi da al'amuranta ma da an kwana biyu, ya gama farfad'owa daga rashin raihanatu ta tursasa shi ya nemi auren shaheeda, don itace dai dai dashi, yarinya mai kyau me aji suruka ta futa kunya, don tayi alk'awarin sai Imran ya riga raihanatu aure yadda zasu fi jin ciwo.
***********
Toh cikin satin gidajen biyu shirye shirye suke ba kama hannun yaro a b'oye ba tare da kowa yasan me ake ciki ba.
Umma salaha takai labarin fasa auren raihana da Imran tuni gidan su innah, a cewarta su zuba ido zasu gani koba yanzu ba, don haka suma sai suka zuba ido zuwa lokacin da zata fasu kowa yaji, yayinda zeeyada ta d'ora alamar tambaya ga salahar karo na farko cikin maganar rayuwar gidan yayanta salees, sai dai bata furta komai ba kamar yadda take akan katanga tun dacan.
Wasa Wasa tun su Inna na saka ran jin labarin fasa biki har ya rage kwana uku d'aurin aure amma ba zance bare dalilin shi, hakan yasa ta kira salees a waya ta tambayeshi ko ya maganar auren raihana gashi duk an rarraba cati, murmushi kawai yayi yana tunanin ko suma sun d'auka ba za'ayi auren ba yanzun ma, sai ya fad'a mata biki yana nan anjima zai kawo musu get pass na hall d'in da mamanta zatayi mother's day da kamu, abun sai ya taru ya d'aurewa innah kai, tana gama waya dashi ta k'ara kiran umma salaha ta fad'a mata ko dai k'arya ne abinda taji saboda ga yadda sukayi da salees a waya yanzu. Umma salaha tace, "ba k'arya bane iya daga dangin mahaifin yaron naji daga bakin uwar d'an ma, wallahi har kayan lefen da aka mayar ma na gani da idona, ta yuwu akwai dai abinda suke b'oyewa, nima sun bani get pass d'in d'azu".
Ajiyar zuciya innah ta sauke tace, "toh ta yiwu hakan ne zamu gani ai tunda ba'a tab'a d'aura aure ba miji ba".
Kamar yadda salees ya alk'awarta, bayan ya tashi aiki da kanshi ya kawo mata cards masu yawa yace ta rabawa duk wanda taga ya kamata ya halarci taron, ko anan saida ta sake tambayarshi auren dai Yana nan ko? Wannan karon dariya yayi yace, "Wai innah akwai wanda ya baki wani labari daban ne a gefe". Tace, "a'a kawai dai naga yadda abubuwa suke tafiya ne sai anzo kamar za'ayi sai abu ya rushe".
Shiru yayi kafun ya sake cewa, "ehh toh muna fatan komai zai tafi dai dai wannan karon insha Allah". Kamar gaske Innah tace, "toh Allah yasa".
Kamar yadda Abba yakai musu get pass haka ma ummie ta rabawa y'an gidan su da makusantan ta, ta ajiyewa raihana na tsirarun k'awayenta, duk da ita har yanzu tana kwance tana jinyar k'afarta don ta kanta take sosai, har zazzab'i ya sakar mata,,,, sai ya zamana ita kad'ai take kid'inta sai su khausar da Salma, da suka saki jiki saboda ganin alamun lallai da gaske wannan karon za'ayi auren kenan da alama? Ita dai bata iya basu amsa cikakkiya a duk lokacin da sukayi mata wannan tambayar take fad'awa harkokin gabanta.
Ita kamun ma don auntie ta takura ne ta k'awata shi ta d'abbak'a shi, ta kuma mayar dashi compulsory shiyasa ta amince, amma da kamar yadda raihana bata da wani interest akai itama haka.
Ana gobe kamu y'an biki suka fara cika gida na nesa dana kusa, Salma dama ta riga kowa zuwa sai neman amarya take lungu da sak'o, kamar kowanne biki yanzun ma babu dangin abbansu ko d'aya da suka zo musu har kawo yanzu.
Raihana tana cikin d'aki ta k'ule tana bacci saboda kwanakin gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, komai na gidan ta daina yi sai dai