Showing 246001 words to 249000 words out of 288773 words

Chapter 83 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1047

shiga ta durk'usa har k'asa daga gefe d'aya ta fara gaishe shi da tambayar jikin shi.
Ya amsa ta da kulawa yana kallon kayan abincin hannunta, tunda ta fara zuwa yake son tambayarta daga ina amma kamar an hane shi sai yaji ya kasa, tun baya cin abincin har ya dawo yana ci. Yadda ta iya girki in yaci abincinta sai ta dinga tuna mishi tsohon tarihi.
Ta d'an zauna cikin d'akin na wani lokaci kafun tayi mishi sallama zata tafi.
Ya ajiye magazine d'in gefe yace, "kullum kina kawo mun abinci amma bansan komai a kanki ba, kamar sunan ki, da dangantarki dani".
Kanta a k'asa don bata iya kallon cikin idon mutumin tace, "sunana raihanatu....".
Shiru yayi yana maimaita sunan a zuciyarshi harta gama juye abincin ta fuce, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya ya sauko daga inda yake zaune.
Wannan karon da kanshi yayi saving kanshi ya fara ci, wani b'arin na zuciyarshi na kwab'ar shi da kiyaye lafiyarshi wani kuma na zak'uwa da son irin d'and'anon girkin, shida ko na jikin shi ya kawo mishi abu sai anyi checking d'inshi in and out ake yarda yaje gare shi saboda tsaro, amma yau gashi k'arewarta ma abincin daya futo daga fuskar da bai tab'a sani ba yake ci.... Yaja k'ak'k'arfar ajiyar zuciya yana tuna ranar data fara kawo mishi abincin ya fad'awa andal ta tafi dashi kuma a fad'a mata baya buk'ata, murmushi tayi a lokacin tace mishi, "Kaine kuwa kake buk'atar wannan abincin sooraj don bai futo daga inda zaka ce a'a ba.....".
Sake nisawa yayi cikin duniyar tunanin da yake ciki, tunda yazo ya fahimci akwai magana a bakin likitar, sai shagwub'e take mishi irin abinda ada sam babu a tsakanin su, yakan zo ta ganshi kamar kowanne marar lafiya bata nuna alamun ma ta sanshi, abu d'aya yake tambayarta an samu ganin surayyah kuwa? Zata bashi amsa da a'a daga nan bata sake ce mishi komai har ya tafi,,,,, lallai yana ji a jikin shi wannan karon akwai k'amshin gaskiya duk da gashi yayi rabin zaman shi a k'asar baiji k'amshin gaskiyar ba,,,,, sai dai bazai karaya da wuri ba, zai ci gaba da bin takunta har komai ya futo sarari.

Raihana kuwa tana futa sauri sauri ta dingayi don yamma tayi mata yau, in tayi sake khaleefa zai rigata komawa gidan nan.
Tana cikin tafiya kamar a majigi idanunta suka hasko mata shi da Muhammad suna tahowa, da sauri ta sake gyara rufar fuskarta taci gaba da tafiya. Shi kanshi khaleefan tunda idon shi ya sauka a kanta ya kasa d'auke kanshi, ko shakka ba yayi wannan raihana ce..... Muhammad yana ta mishi hira amma sam hankalin shi baya kai har suka zo gab da ita zasu gifta juna, sassanyan k'amshin turaren ta ya daki hancin khaleefa har ya sashi lumshe idanun shi da tsayawa cak.....
"Yea! Let's go on mana". Inji Muhammad
"Wait!". Ya fad'a da nufin tsaida ita yana bin bayanta da kallo bayan ya juyo.
Ita kuwa k'ara sauri tayi, ganin haka sai ya kira sunanta yadda zata iya jiyowa, "Raihanaaa!". Cak ta dakata kamar zata juyo saita tuna gargad'in andal da tace kar ta kuskura koda wasa khaleefa yasan maganar marar lafiyar nan..... Taci gaba da tafiya hadda k'ara sauri akan nada.
Bin bayanta yayi da sassarfa, Muhammad ya bishi ya rik'o shi, "Muhammad akwai abinda nake son dubawa?".
Dariya Muhammad yayi mai yawa kafun yace, "Man wai tsabar soyayyar ce tasa a ko'ina ma ganinta kake yi?".
Khaleefa ya janye hannun Muhammad lokacin tuni ta fuce daga inda suke. Koda ya lek'a ta harabar gurin bai ganta ba.
Daga nan office d'inshi ya tafi da gudu gudu Muhammad na bin bayan shi, ya had'a duk abinda yazo dashi office d'in ya rufe ko sauraron tambayoyin da Muhammad yake jera mishi baya yi, har zai tafi Muhammad ya rik'e shi yace, "ka manta aikin da yake gaban mu zaka tafi gida? Kada fa ka jawa kanka matsala".
Warce rigar shi daya rik'e yayi bai ce mishi komai ba ya tafi da gudu...
Ahmad daya shawo kwanar ba zato sukayi karo har wayar hannun khaleefa ta sub'uce k'asa ta fad'i. Gara mishi wayar yayi da k'afa yace, "taho mun da ita". Gani yake in ya tsaya d'aukan wayar kamar zata tsere mishi.
Ahmad ya durk'usa ya d'auki wayar Allah yasa ba abinda ya same ta, Muhammad ya k'araso ya dafa kafad'ar shi suka bishi da kallo har ya futa daga asibitin gaba d'aya sannan Ahmad ya tambayi, "me ya same shi?" Muhammad yace,
"Muna cikin tafiya......". Nan ya bashi labarin yadda komai ya faru.
Ahmad ya girgiza kanshi cikin tausayin shi a wannan karon yace, "he's totally lost".

Raihana kuwa tana futa a lucky ta samu motar haya ta tafi gida. Kamar tasan tunanin khaleefa tana shiga gidan ta tura kayan fulasan cikin drower, ta fara cire kayan jikinta ko tsayawa ninkewa bata yiba ta tura su k'asan bed, ta fara neman kayan da zata saka da sauri bata samu ba sai d'aya cikin rigunan data gwada kafun ta futa, rigar iya gwiwar k'afarta ce amma fitet data fudda ilahirin shape d'in jikinta gaba d'aya... Tana jin lokacin da aka tab'a k'ofar shigowa gidan tayi sauri ta zura k'aton hijab saman kayan ta tafi zata futa don kore mishi duk wani zargi.
Shi kuwa yana shigowa parlon jakar shi ya ajiye gefe ya fara duba inda zai ganta ko wani abu cikin wanda ya gani a asibiti bai samu ba, tunanin shine ya kai kan d'akin gadonta ya tafi da sauri...
Tana shirin futa shi kuma yana shirin shigowa, k'arfin namiji da mace ba d'aya ba tuni ya ture ta baya da jikin shi ta tafi zata fad'i yayi saurin taryota amma ina saida suka kai k'asa gaba d'aya shida ita. Ta rintse idanunta don ma Allah yasa akan hannun shi ta fad'a bata daku sosai ba, shi kuwa wani rad'ad'i da zugi ne suka ratsa hannun shi mai ciwo suka bi jijiya suka kai har kwanyarshi.
Cikin dakiya ya tsurawa fuskarta idanu yana mata kallon kusa da kusa.... Sosai ya shagala da kallonta har ya fara manta abinda ya kawo shi d'akin.
Sai ya mik'e da sauri ya juya fuskarshi yace, "sorry". Itama mik'ewar tayi. Tana kallon shi ya dinga laluba cikin d'akin hadda bud'e wardrobe da lek'a bathroom kamar wanda ya ajiye wani abu muhimmi, kafun yayi shiru kamar me nazarin wani abu yana kallon hijabin jikinta, kamar wanda ake umarta haka ya tako gently har gabanta yana sake kallon k'asan hijabin daya rufe har k'afarta. Daga yanayin kallon da take mishi ya gane bata da gaskiya.
Ba tare da saninta, zaton ta bare tsammanin taba ya d'age hijjabin jikinta gaba d'aya ya wurga shi kan gadon d'akin.
Taja jikinta baya da sauri ta jingina da bango tare da rintse idanunta.
Baisan yadda zai fasalta abinda yaji ba, gaba d'aya tunanin shi ya tafi a kallonta da tsarin halittar jikinta, sam in bacin daya kalleta yanzu bai tab'a tunanin akwai mata masu irin shape d'inta cikin jinsin hausa fulani ba, yafi yadda da wanda bature ya k'era don tallata kayan siyarwarsu wato roba roba.
"Wowww". Ya samu bakin shi da furtawa yana sake kallon yadda rigarta ta zana ta, ita kuwa durk'ushewa k'asa tayi ta had'e jikinta waje d'aya, shima hannun shi ya cusa cikin sumar kanshi yaja gwauron numfashi ya juya ya futa da sauri har yana tuntub'e.
Yana futa ta murza key a d'akin tana sauke ajiyar zuciya (kuji yarinyar nan fa🤔). Bata jima jikin k'ofar ba ta nufi gaban mirrow tana kallon yadda rigar ta zauna a jikinta, sai kuma ta tuna abinda khaleefa ya fad'a itama ta maimaita kalmar a bakinta ta juya idanunta had'e da tab'e baki ta bar gurin.
Sai a lokacin ta samu nutsuwar b'oye kayan data tura k'asan gado, ta sauya rigar jikinta da wata mai fad'i kamar bubu, ta yane kanta da gyalenta.
Koda ta futo parlon ba kowa, direct tayi kitchen don samar musu abinda zasu ci tun kafun ya fara tambayarta.
Tana aikin ta dinga jiyo tashin maganarshi cikin taushi, sunan Ayman da yake yawaita kira ya tabbatar mata dashi yake magana a waya, koda taci gaba da sauraron shi sai taji kamar akan auntien su suke magana maybe tak'i d'aga wayar ne.
Zuwa can taji yana murza key zai futa a gidan gaba d'aya.

Tun wannan futar kuwa da yayi bai dawo gidan ba har dare ya fara nisa, sai ta fara tunanin toh ina ya tafi kuma?
Tun tana duba agogo har tunaninta ya tafi akan ta kira wayarshi, sai dai tana d'aukar wayarta da nufin kiran shi tashi wayar ta fara fudda slow music a kusa da ita.
Kamar kada ta d'auka sai kuma dai ta duba don taga me kiran, Ayman ne ashe tun d'azu yake jera mishi missed call bata jiba. A kunnenta ta kara wayar bayan tayi karambanin d'agawa. "Da alama mun b'ata ma auntie rai sosai har yanzu tak'i saurarona, gashi kai kuma sai kiran ka nake baka d'auka".
"Bashi bane Yaya Ayman raihana ce".
"Ohh! Raihana ya kike ya gida? Ina khaleefan?". Ya jera mata duka tambayoyin.
"Lafiya lou, ya futa sai dai in ya dawo".
"Okay" ya fad'a sai kuma kit ya katse wayar. Tabi wayar da kallo a hannunta, ta yink'ura hannunta rik'e da wayarshi ta bud'e k'ofar parlon. Abun mamaki yana tsaye ya dafa k'arfen gaban gidan yana fuskantar gaban gidan. Tayi turus tana kallon shi da k'ok'arin rufe k'ofar daga ta bayan shi.
"Ban futo da key bafa". Ya fad'a ba tare daya motsa daga yadda yake ba, Saita fasa rufewa ta k'araso gab dashi ta mik'a mishi wayar, "Yaya Ayman yana ta kiran ka".
Baice mata komai ba sai juyowa da yayi yana kallon ta. Ta maida kanta wani gefen daban don kaucewa kallon kwayar idanun shi. Ya karb'i wayar ta juya zata koma yayi saurin rik'o hannunta, cak ta tsaya da tafiyar data fara har ya tako suka daidaice ya d'auki hanyar komawa cikin gidan rik'e da ita.
Cikin kujerun parlon ya zauna ya bata umarnin zama kusa dashi, ta zauna a d'arare tana wasa da yatsun hannunta da suka sha adon han lalle yayi maroon.
Yabi yatsun da kallo kamar zaice wani abu sai kuma dai ya fasa.
Yana shirin kiran Ayman wayarshi ta fara shigowa, sai ya d'aga ya kara a kunnen shi, sunyi magana ta adadin wasu mintuna kafun yasa Ayman ya shiga d'akin auntien ya maida wayar handsfree, shima tashi handsfreen ya maida ita don bashi da wani abu da zai iya b'oyewa raihana a yanzun.
Tana zaune tana operating system d'inta fuskarta sam ba walwala Ayman ya shigo da sallama ya ajiye wayar kusa da ita ya koma gefe ya zauna kamar marar gaskiya yana satar kallonta.
Daga ta cikin wayar muryar khaleefa ta fara futowa inda yake magana da fad'in.......

_kuyi hak'uri dani.... ba editing_

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*

_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy 7️⃣0️⃣


"Tabbas mun b'ata miki rai, mun kuma kasa fahimtarki duk da mu a gurin mu muna ganin abinda muke k'ok'arin yi shine dai dai.... Auntie kin kasance d'aya tamkar da million a rayuwarmu, kin raine mu da soyayyah da tarin sadaukarwa irin wadda ba kowacce uwa ba, ko iya nan aka tsaya kin mana abinda ba zamu tab'a iya biyan kiba har k'arshen numfashin mu, Amma in aka zo in terms of maganar lafiya, kema kinsan zamuyi iya yin mu wajen ganin mun tsira da lafiyarki saboda in muka rasa ki bamu da wanda zamu rab'a ya zame mana kwatankwacin ki..... Shiyasa a karon farko muka zo gare ki da neman alfarmar ki taimake mu ki ajiye aikin nan, saboda likita ya tabbatar kina buk'atar hutu garkuwar jikin ki yayi rauni duk da kina ta fafutukar yak'i da hakan..... Koda ba'a fad'a mun akan kari ba kinsa an b'oye mun ruhina bai samu salama ba a lokacin da kika kwanta jinya saida sauk'i ya samu gare ki....".
Rufe system d'in gabanta tayi ta kira sunan shi, "Khaleefa"
Ya amsa da, "na'am". "Yanzu wannan umarnine ko shawara?". Ta tambaye shi.
"Babu ko d'aya, neman alfarma ne idan har zai yiwu".
Shiru tayi kafun can ta nisa tace, "shekara biyu ya rage nayi retire, yanzu kuna son na hak'ura da aikina duk shekarun dana d'auka su tashi a banza?". Ba wanda ya amsa ta cikin su. "magana nake daku ku bani amsa mana kunyi shiru bayan duk kunsan tsarin aikin Nigeria".
Khaleefa ne yanzun yace, "kiyi hak'uri auntie amma da kinyi mana bayani tun farko".
"Saboda kune kuke jagorancin rayuwata ko?".
Kusan a tare suka fara bata hak'uri, bata ja doguwar magana daga kowannen su ba ta kashe wayar khaleefa shima Ayman ta sallame shi.

Khaleefa ya maida duban shi kacokan ga raihana da take zaune gefen shi ko kwakkwaran motsi ba tayi.
"Kin tambayeni zaki futa wani uzuri daga makaranta kullum, sai dai ban tambayeki me zaki yi ko inda zaki je ba ke kuma baki fad'a mun ba".
Tsilli tsilli tayi da ido ta kasa ce mishi komai har saida ya sake maimaita tambayarshi, "Ina kike zuwa?".
Kin ce mishi komai tayi still, hakan ya matuk'ar d'aure mishi kai ya kuma d'an fusata shi kad'an, "abu na k'arshe dana tsana in yiwa mutum magana gani gashi ya share ni.... Wallahi zaki ja na hana ki futa a gidan nan gaba d'aya".
Sai a yanzun ta d'ago ta kalle shi jikinta a sanyaye sosai, bata san me zata ce mishi ba shiyasa ta zab'i yin shiru.
Mik'ewa yayi tsaye ya d'auke wayarshi ya sake kallonta yace, "daga yau ban amince ki d'ara ko'ina daga makaranta ba in kuma kika karya abinda na fad'a......". Sai yayi hucewarshi nashi guri ya barta nan zaune.
Itama bata da zab'in daya huce mik'ewa tayi nata gurin.

***Kwana biyu a tsakani sooraj baya ganin yarinyar, tun yana saran ganinta har ya gaji da ajiye maganar a ranshi ya fad'awa andal a wani yammaci daya futa motsa jiki. Already raihana ta fad'awa likitar yadda sukayi da khaleefa dama, ta kuma goyi bayan tayi biyayyah wa mijinta tunda dai aljannarta tana k'ark'ashin k'afar shi, kuma a k'ark'ashin shi take, shiyasa sooraj yana mata maganar kai tsaye ta bashi amsar mijintane ya hana ta.
Sooraj ya tambayeta, "me yasa ko dama baisan tana zuwa ba?".
"Eh".
"Me yasa zatayi haka ita?".
"Saboda in yaji ba zai tab'a barin tazo gare kaba".
Da wani mamakin ya sake cewa, "meyasa?".
Barin abinda takeyi tayi ta d'ago tana kallon shi kafun ta bashi amsa da cewa, "saboda a duniya bana jin yana da mak'iyin daya huce ka, sooraj kana sane da kuskuren daka aikata a rayuwarka kuwa koka manta? Kasan duk wani makusancin surayyah yaji labarin irin butulcin da kayi mata a rayuwa ya k'ulla gabar har abada da kai mara k'arshe kenan kuma ba zai tab'a bar wani nashi ya rab'e kaba?".
"Idan na fahimce ki kina nufin yarinyar nan tana da alak'a da wani cikin dangin matata surayyah?".
"Matar daka kasa yiwa adalci dai ka saketa sakin daba kome bayan ka huda zuciyarta da soyayyar ka".
"Wayyoh Allah! Har sai zuwa yaushe ne zaki fahimci duk abinda ya faru ba laifina bane? Ko d'aya bani da masaniya akan duk abinda ya faru shekarun da suka gabata, nima an bani komai a juye ne sai daga k'urarren lokaci na gane gaskiya, Amma insha Allahu na had'u da surayyah zan nuna mata nadamata a aikace, zan aureta irin auren da babu saki har abada.....".
Mik'ewa tayi tsaye jikinta har tsuma yake cikin tsananin b'acin rai take duban shi tana cewa, "a wanne hadisin akace namiji zai iya sake auren matar daya yiwa saki uku, sannan kai kana tsammanin surayyah zata ci gaba da zama babu aure?....".
Wani irin fad'uwa gaban shi yayi, kanshi ya sara tashin hankali ya sake bayyana k'arara kan fuskarshi, abubuwan nan biyu shap mantawa yake dasu in bacin yanzu da andal ta mishi tuni. Sai ya had'a hannun shi biyu alamar rok'o yace, "don Allah ki gafarceni, ba don niba ba don na Isa ba, sai don daraja da albarkacin na tab'a rayuwa da k'awar ki, rayuwa irin wadda ba zata tab'a gogewa a cikin kwakwalwa da zuciyata ba, andal ki fad'a mun meye alak'a ta da wannan yarinyar da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login