Showing 123001 words to 126000 words out of 288773 words
Chapter 42 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
tana son Ayman sosai fiye da zaton kowa,,,,
Tana tsaka da wannan tunanin taji ana neman k'awayen amarya suzo su shigo da ita.
Sai ta koma da kujerar ta saitin shigowa don taga ko zata ga wani abu da zai tabbatar mata da zarginta.
****Daga waje kuwa raihana tana tsaye gefen auntie da take rik'e da hannunta na hagu har k'awayen amarya suka k'araso, suka gaishe da auntie sannan suka kewaye su suka fara takawa sannu a hankali zuwa cikin hall d'in, har lokacin auntie tana rik'e da ita.
Koda suka shigo hall duk d'auke wutaa akayi, hadda masu dawo da abinci daga bakin su saboda tsananin mamaki da fargaba data d'arsu a ran da yawa daga mutanen gurin.
Auntie bata sake hannunta ba har saida ta kaita mazauninta sannan ta samu gefe guda ta zauna ta zuba kunnuwa da ido don sauraron lecture da manyan malaman musulunci zasu gabatar akan zamantakewar aure.
Aikuwa ba b'ata lokaci aka fara gabatar da lecture mai sanya nutsuwa a zuk'ata da kwantar da hankali gami da karya k'ashin bayan y'an hassada na gurin.
Tuni hall ya dawo tsit baka jin komai sai bayanin wad'annan mata masana addinin islama, inda suke bayani akan zamantakewar aure da yadda mace zata sauke hak'k'ok'in mijinta a kanta, da kissoshi iri iri, musamman na tsabtar jiki da tufafi yasa da yawa suka fara d'ago kuskuren da suke tabkawa a gidajen su.
Amarya taja gefen lufaya ta rufe rabin fuskarta tana share hawaye da yatsun hannunta, ana gamawa auntie tayi mata kamu irin na matan larabawa na zallar turaren khumrah dana garwashi, nan da nan kuwa guri ya d'inke da k'amshin mayen turare me kama jiki da muhalli. Aka rarraba kayan gargajiya ga duk wanda ya halarci wannan guri, aikin maman amarya kenan. Amma da d'akin taro da abinda aka ci duk surayyah ce, har masu lecture ita ta gayyatosu, ta kuma raka su da sha tara ta arzik'i rigijib har bakin motar su suka tafi.
Ta gaisa da jama'a sama sama, ta d'auki amarya kamar yadda ta kawo ta da tsirarun k'awaye ta tafi.
Har k'ofar gidan su ta ajiye su, raihana bata futa ba saida duk suka futa sannan ta kalli Auntie da idonta daya tara ruwan hawaye tace, "nagode auntie Allah ya k'ara rufa asiri". Sauke mata hannun k'asa tayi tana murmushi tace, "bar yimun godiya raihana, don a gurina keda Ayman da khaleefa duk d'aya nake kallon ku". Saita share hawayenta da tafin hannunta tayi mata sallama tana d'ingisa k'afa ta shiga gida.
A can ta samu su raheela suna ta shirin d'aura alwalar sallar magrib data k'arato.
Cire lafayar jikinta tayi ta samu kan kujera ta kwanta tana tambayar su Fatima tun yaushe suka zo? Raheela tace, "au duk yadda muka dinga shige da fuce a gabanki baki ganmu bama saboda tsabar shiga busy". Girgiza musu kai tayi tace, "toh y'ar jiran k'iris nidai kar ki had'a ni da Fatima, ba wai ina nufin a gurin taro ba a nan gida tun yaushe kuka zo...".
Kusa da ita raheela ta dawo tace, "au toh na fahimta, kina futa ba jimawa muka zo".
Sai ta tashi zaune sosai itama tana kallon su tace, "Amma dai kwana zakuyi ko?". "Eh insha Allah" sai ta fad'ad'a fara'ar fuskarta, Fatima tace, "Amma fa kinyi kyau Masha Allah raihana, duk da dama ke d'in me kyau ce, sai dai naga kamar kina d'ingishi da kika shigo me ya samu k'afar ki?".
Raheela tace, "Ina shirin tambayarta kika rigani". Yamutsa fuska tayi kad'an tace, "Na had'u da tsautsayi ne". Ta k'arasa fad'a tana janye musu rigar jikinta don suga k'afar tata.
"Ayyah sannu raihana". Duk suka fad'a da damuwa saman fuskar su.
Sunyi shiru zuwa wani lokaci kafun ameena ta shigo itama ta zauna kusa da ita, tana yaba kyaun da tayi har da tambayar me kwalliyar. Ita kuwa raheela taso tambayarta game da sauyin data gani a tare da yanayinta, amma ko data tuna ciwon jikinta da suka gani yanzu sai ta danganta rashin walwalar ta da hakan.
****Haka dai ranar suka hanata bacci akan lokaci har sai zuwa can nisan dare ta samu ta watsa ruwa tasha magungunanta ta kwanta.
Ko data kwanta kasa yin baccin ma tayi sai juyi kurum, daga k'arshe dai dole ta tashi ta zauna dirshan a tsakiyar gadon ta had'a kai da gwiwa, wannan wacce irin rayuwa ce take shirin cusa kanta a ciki? Ita bata tab'a sanin ana aure babu soyayyah bare a kaiga maganar fahimtar juna ba sai data had'u da khaleefa har hakan yake shirin faruwa da ita gobe, toh Amma fa haka shine kad'ai mafutar ta, ta hakane zata tsira daga maganar mutane da sharrance sharrancen su innah da umma salaha, har ta samu nutsuwa ita da mahaifiyar ta itama ta sarara kamar kowanne mutum, Saita kife kanta jikin gwiwar hannunta tana fad'in "Allahumma ajirni fil musibati,,, waklifni khairan minha".
Hakanan ta sake komawa ta kwanta tana sake k'issima abubuwa da yawa a cikin ranta.
★★★★★
Ta b'angaren Ayman kuwa dama tunda abun nan ya faru ya d'auke wutaa gaba d'aya kamar ba Ayman ma'abocin faram faram da barkwanci ba, duk da a haka yana kwararawa kanshi gwiwa ne, tuni ya cire rai da raihana ya hak'ura da ita har abada saboda khaleefa ya fishi cancantar ta, duk da shima har yanzu bai daina mamakin yadda khaleefa ya had'u da raihana har suka fara soyayyar data kaisu ga batun aure ba.
Ya zama hopeless a satin gaba d'aya amma a hakan sai daddannewa yake yi, shi kad'ai yasan ciwon dake cikin kowacce dariyar shi d'aya idan yayi.
Yana kallo aka shiga hidimar biki gadan gadan a gidan, duk da ba wasu mutane auntie ta tara ba, amma kullum bata samun zama.
A ranar da Auntie ta shirya zata futa kamu, yana kwance a parlon su ta shigo ta same shi, sai ya tashi zaune yana kallonta, ba wata kwalliya tayi a fuskarta ba amma tayi kyau sosai.
"Ina son zan kai raihana gurin kamu da walima, ko zaka samu damar yi mun rakiya". Yamutsa fuska yayi wani sabon abu yana taso mishi, laa shakka ba don auntie ce tayi mishi wannan maganar ba,,,, da lallai sai ya ci kwalar mutum yaji dalilin da zaisa yayi mishi irin wannan maganar.
Cikin dakewa da dannar zuciyar shi yace, "Auntie bana jin dad'in jikina gaba d'aya, Ina ganin anjima kad'an ma ganin likita zan tafi".
Cikin kulawa tace, "gaskiya ya kamata,,,, dama a satin nan Ina ankare dakai, kuma nasan ba komai ya haddasa maka haka ba sai wannan damuwar da kake ajiyewa a cikin ranka har yanzu.... Na fad'a maka ka cire komai daga ranka Ayman ka barwa Allah, kana zaune Allah zai kawo maka matarka har gida, ka manta da Nur ka shafe babinta gaba d'aya cikin rayuwarka, sam baka buk'atar mace irinta, wadda zata soka a yadda kake kake nema, ba wadda saika taka wani matsayi a rayuwa ba, ba gashi d'an uwanka da zargin da komai an bashi aure ba....yanzu in banda sharrin mutanen mu ma, mutumin daya mutu aka fad'a musu baya raye...shine zasu dinga bi guri guri suna cewa yaran shi shegu kamar a gaban su akayi cikin shegen aka haife... Mtsss!." Ta k'arasa zancen da jan tsaki.
Ayman daya zuba ido yana sauraronta murmushi kawai yayi bayan gama sauraron kalamanta na son zuciya a gurin shi, duk da maganarta ta sosa ranshi amma ba yadda zaiyi da ita tunda uwa ce. Amma duk da haka yana da kyau ya dinga tunasar da ita wasu abubuwa da tunaninta yake kwacewa a kansu.
"Auntie nifa har kullum bana ganin laifin mammie, iya gaskiyarta ne ta fad'a mun, tace ita bata hanani auren Nur ba amma inje in fara binciko waye mahaifina,,, kuma suwaye dangin shi da bakya son mu sani.... Toh meye laifinta, ba ita kad'ai ba duk inda naje neman aure za'a iya fad'a mun haka,,,,ba kowane irin iyayen raihana ba, da zasu iya bada auren y'ar su ga mutanen da basu san asalin suba, mutane masu dattako da kyakkyawar zuciya, wanda zasu iya sa mayafi su lullub'e duk wani tabo da tambarin da yake tare da wani mutum da basu tab'a doguwar magana ko zama tare dashi ba..... Irin mutanen nan sunfi komai k'aranci a wannan duniyar da muke ciki...".
Duk data fahimci inda maganar Ayman ta dosa amma saita basar ta sake cewa, "mu saka kyakkyawan yak'ini akan kowa Ayman, nayi imanin zaka samu irin wad'annan surukan kaima, ba zasu k'are a iya kan iyayen raihana ba...."
Fahimtar in yaci gaba da zama zai iya ci gaba da ja da duk wata magana da zatayi sai ya mik'e don ya bar mata gurin, "auntie bari naje na kwanta".
"Ya kamata dae". Taku biyu yayi yaci karo da k'afar khaleefa,,,,, kamar kullum yanzu ma sanye yake dogon wando bak'i, sai white shirt mai ratsin bak'i itama. Ya hard'e hannuwan shi duka a k'irji yana kallon su shida auntie, fuskarshi d'auke da wani yanayi mai wuyar fassaruwa farat d'aya.
Kewaye shi Ayman yayi zai huce, don a duk lokacin daya ganshi wani tuk'uk'in bak'in ciki ne ke zuwa ya tokare mishi wuya. A duniya yanzu ba wanda yake ganin bak'in shi kamar Auntie da khaleefa, saboda yana ganin sune ummul'a'ba'isin raba shida masoyiyar shi raihanatu. Har ya huce sai khaleefan ya dafa kafad'ar shi ta baya, aikuwa ya juyo da sauri idon shi cike fal da ruwan hawaye ya janye jikinshi daga rik'on daya mishi.
Zai sake hucewa khaleefa yasha gaban shi yana kallon cikin kwayar idon shi.
Tuni hawayen da suka taru a idonshi sun soma biyo kuncin shi suna sauka a hankali. Jikin khaleefa a matuk'ar sanyaye ya rungume Ayman d'in yana jin idonshi shima yana tara ruwan hawaye. "Ka gafarceni Ayman....." Ya fad'a da kwantaccen sauti k'asa k'asa.
Ita kanta auntie da take tsaye bayan su kallon su take da karyayyiyar zuciya. Tana jin wani luguden bugu a k'irjinta.
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page thirty five3️⃣5️⃣
"Wane laifi kayi mun da zaka nemi yafiyata?". Ayman ya tambaye shi bayan ya janye jikinshi daga nashi bai yarda koda wasa d'an uwan yaga hawayen idonshi ba.
Shima khaleefa daga haka bai sake ce dashi komai ba ya bishi da ido har ya shige d'akin shi ya murza key. K'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya sauke, yasan sana'ar tashi da ya sake maida ita dabi'a cikin y'an kwanakin yake wato kuka.
Auntie ce ta k'araso har inda khaleefa yake ta kira sunan shi a sanyaye, ya amsa bayan ya sunkuyar da kanshi k'asa.
"Wai khaleefa kana nufin babu wanda zaka gayyato gurin d'aurin aurenka na gobe? Na duba cards d'in duka daga kai har Ayman ba wanda ya tab'a shi ma". Kanshi a k'asa har lokacin yace, "ai ni bani da wasu friends da zan gayyata a garin nan". Kama hab'a tayi tana kallon shi da matuk'ar mamaki, "kenan haka zakaje gurin d'aurin auren kai tsuranka?". Bai iya ce mata komai ba, don shi har ga Allah baya son kowa yasan da maganar wannan auren nashi, yafi son ayi shagali na ainahi a lokacin auren shi na gaske da Saleema,
"Toh Ina son magana dakai anjima da dare, yanzu zan futa kamun raihana ne.....".
D'an k'aramin tunani ya tafi akan sunan raihana data ambata yanzu,,,, kafun caan ya tuna kamar yarinyar nan ma sunanta raihana ko? "Kayi shiru ba kace komai ba". Ta sake tambayarshi cikin kafe shi da ido. Sai a lokacin ya d'ago ya kalleta, "Allah ya tsare hanya Auntie".
Yana fad'in haka ya nufi hanyar d'akin shi shima. Ita kuma ta futa zuciyarta fal wasi wasi, shi kam koda ya shiga d'akin shi zama yayi yana nazarin gaba d'aya lamuran Ayman da sauyawar da yayi lokaci d'aya, dama tun cikin y'an kwanakin ya fahimci kamar akwai damuwa tare dashi. Sai dai bai tab'a d'auka rashin walwalar shi nada alak'a da yarinyar da yake so ko mamanta ba, lallai suna cikin matsala shida d'an uwanshi, indai har na jikin auntie ma sun fara zarginta da abinda sauran mutanen gari ke zarginta toh waye zai futo ya kare su a wannan garin.
Sai ya sake girgiza kanshi, ba shakka wannan rik'on alk'awari na auntie yana azabtar dasu.
Wayar shi da take ringing ta zaburar dashi daga nazarce nazarcen da yake yi.
Sai ya d'auko ta daga gefen shi yana duba no me kiran, Ahmad ne,,,, dafe kanshi yayi don shap ya manta ya sanar dashi abinda ake ciki ma. Bai iya d'aga wayar ba har ta katse wani kiran ya sake shigowa. Saida ya kusa tsinkewa shima sannan yayi picking.
Bayan sun gaisa complain Ahmad ya fara mishi kan kwana biyu ya manta dashi gaba d'aya. Hak'uri ya bashi kafun ya fad'a mishi ainahin abinda yake faruwa.
"Man gobe fa zan d'aura aure...". Ahmad a kwance yake amma baisan lokacin daya mik'e zaune ba, "khaleefa are u serious, please let's keep joke aside". Khaleefa yace, "Ni ne fa nake yi maka wannan maganar Ahmad ba kai kake yimun ba....so tun wuri ma ka gane ba zancen Wasa a maganata".
"I can't believe it khaleefa! In na fahimce ka fa kana nufin wata zaka aura ba Saleema ba, toh daina son saleemar kayi ko me? Sannan ni yanzu daka fad'a mun a late, taya zanyi booking tickets har na taho Kano gobe kafun a d'aura aure.....".
Mik'ewa tsaye yayi bayan ya furzar da iska me huci daga bakinshi, ya Isa gaban k'arfen windown d'akin shi ya rik'e da hannunshi d'aya sannan yace, "ka adana tambayoyin ka zuwa ranar da zamu had'u in warware maka komai Ahmad,,,, and sannan kada ka damu kanka ba lallai sai kazo wajen bikin ba, don ba wanda na gayyata ma, duka IC na y'an gidan ku yana hannuna suma ba sai sunzo ba kawai".
Cikin sake jinjina al'amarin Ahmad yace, "Zan iya hak'uri har zuwa sanda zamu had'u kuwa? Toh wai ko auren dole Auntie zata yi maka ne man?, tunda ta rantse ba zaka bar k'asar nan babu aure ba..... Ni dai kam zan fad'awa dad dole sai nazo a gobe ma kuwa....".
"Ahmad ka daina k'ok'arin maida k'aramin abu babba don Allah, nan da 13 days ma dole zamu had'u ai".
Ahmad kanshi har lokacin a d'aure yace, "Wai ka san abinda kake fad'a kuwa? Khaleefa auren mutum fa bana y'ar tsana ba,,,, toh kaidawa zaka gurin d'aurin auren.....". Zuwa yanzu khaleefa ya fara gajiya da magana akan abu d'aya, don haka cikin k'osawa yace, "ba maganar da zamuyi a waya bace,,,,, kuma nima ba zuwa zanyi gurin auren ba khalas na!".
Shi dai Ahmad har yanzu a bai bai yake kallon komai, amma duk da haka sai ya bishi da addu'a "toh sai nace Allah ya sanya alkhairy......" Da sauri khaleefa ya katse mishi hanzari,,,, "ohh kana da matsala Ahmad, wa yace maka kayi addu'a irin wannan kuma?" Zai k'ara yin magana khaleefa ya sake katse shi, "as I said earlier, ka ajiye komai zuwa lokacin da zamu had'u".
"Alright shikenan". Ahmad ya fad'a, Daga haka sukayi sallama khaleefa ya ajiye wayar, yana tunanin ta yadda zai fuskanci rigimar auntie da take son lallai saita tursasa shi yin abinda bai shirya yin shiba, aure nawa akayi ba ango a gurin, ko a Germany yasha ganin ana d'aurawa abokan karatun su aure a turo musu da matan, basu jeba bare wasu abokan su daba su zasu zauna musu da matan ba, kuma har ayi a gama ba'a samun wata matsala, auren be fasu ba....
Da wannan tunanin ya k'arasa duk wani abu da yake shirin yi a ranar.
Ayman kuwa yana shiga d'akin shi yaji kamar ana wujijjiga shi, cikin dauriya da dakiya ya dafa bangon d'akin yana rintsee idanun shi duka biyu, yayinda zafafan hawayen shi suka fara futowa suna sauka sala sala. Sai ya durk'ushe a gurin yana tuna duk lokutan da suka kwashe tare da ita, tun tana k'aramar yarinya a lokacin da yake koya mata assignment, har akazo kan sanda khaleefa ya tafi Germany ya barshi da ita, rashin abokin hira yasa suka sake samun kusanci matuk'a, yasha hira da ita akan abubuwan da suke damun shi, tun bata mallaki hankalin kanta ba, a wasu lokutan ta bashi shawara me kyau data zarce tunanin shi, a wasu lokutan kuma ta kyalkyale mishi da dariya, wani yaji haushinta suyi fad'a ta bashi hak'uri, wani kuma ya