Showing 54001 words to 57000 words out of 288773 words
Chapter 19 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
adalci? Mata ko mijin da Allah ya juyawa al'amarin kansu shin mun kyauta musu kenan, kada ka manta kowanne namiji yana fatan auren mace innocent, haka ma mu mata, idan son samun ku ne zaku ce wadda namiji bai tab'a rik'ewa hannu ba, itama macen wanda bai tab'a rik'e ko tab'a jikin wata d'iya mace ba, shin mun cuce su ko bamu cuce suba? Allah zai yafe mana ranar gobe k'iyama kuwa? Ni dai da haka nake rok'on ka don girman Allah ka cire wancen abun daga cikin zuciyarka, kayi yak'i da zuciyarka aikin sab'o da duk abinda yake haram su daina burge ka, ka dinga niyyar abu mai kyau a zuciyar ka wanda Allah zai baka ladan niyyah in baka samu damar cikawa ba, ba wai Haram da zaka k'are da zunubi ba, Ina fatan zaka yiwa maganganu na kyakkyawar fassara ta hak'ik'a bata son zuciya ba duk da dai tuni ne"
Tunda raihana ta fara magangana Imran ya kafe ta ido yana kallon other side of her, lallai dole yaci gaba da son yarinyar nan, domin abar so ce ga kowa da yasan abinda yake yi a rayuwa. Bai bar kallonta ba har saida takai k'arshen maganar ta, doguwar ajiyar zuciya yaja ya furzar da iska mai huci daga bakin shi kafun ya fara magana da, "alhamdulillah! alhamdulillah!! alhamdulillah!!! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala daya bani ke kyauta a matsayin matar aure raihana, tabbas samun irin ki cikin dubu sai an tona, domin kinfi kowanne kalar mata tsada musamman a wannan zamanin da muke ciki, hak'ik'a nayi nadama dana kasance cikin samari masu bin ra'ayin yahudu ta b'angaren soyayyah, har a minti biyar da Suka gabata kafun yanzun ina d'aukar waccen soyayyar a matsayin soyayyar da tafi kowacce siye zuciyar mace cikin sauri raihana, sannan na d'auke ta hanyar expressing feeling d'ina at sad or happiest moment, shiyasa na yi attempting gwadawa a kanki duk lokacin da nake cikin b'acin rai ko farin ciki, amma insha Allah raihana hakan bazai sake faruwa ba har sai ranar da naji an shafa fatiha". Raihana rufe fuskarta tayi tana k'unshe dariyarta, cikin matuk'a jin dad'i da farin cikin yadda ya fahimceta cikin sauk'i har yayi nufin gyara kuskuren shi.
Sun ci gaba da hirar su rabi duk kan yadda zasu tsara shagalin bikin su, bai tafi ba sai yamma lis don sallar la'asar ma a nan yayi cikin sitting room d'in.
Daga nan Komai yaci gaba da tafiya lafiya, yayinda raihana da Imran Suka ci gaba da tsananta addu'a akan maganar auren su, y'an uwa da abokan arzik'i na taya su.
Ayman kuwa..... Ba zan iya tantance muku halin da yake ciki a yanzu ba, sai dai ya maida kanshi over busy a gida ko office, yak'i yake da zuciyarshi sosai akan raihana da al'amuran aurenta, a kullum dare yakan hana idon shi bacci yayi ta addu'ar da bansan wacce iri bace kuma a kan wa.
Yanzun ya sake nisanta kanshi da raihana gaba d'aya, ya k'ara kusanta kanshi da nuriyyah, ko abinci wani lokacin baya iya ci sai ya taso office ya biya ta gidansu Nur yaci wanda ta dafa da hannunta, yana kallon kyakkyawar fuskarta yana jin dad'ad'an kalamanta, ko Auntie bai fiya yiwa doguwar hira ba, iya kuwa tuni ya yiwa gidan ta yaji baya son ko hanyar gidan ya tuna bare yaje. Iya tayi cigiyar shi har ta gaji, haka malam ma.
@@@@@@@@
_masu iya magana sukace waiwaye.........._
*GERMANY*
zamu iya cewa komai yana tafiya dai dai a rayuwar khaleefa kama daga rayuwar sa a makarantar Humboldt zuwa kan yadda yake iya k'ok'arin shi wajen ganin ya samu nasara akan abinda ya zaunar dashi, haka alak'ar shi da Ahmad suna zaune lafiya duk da sun d'an ja baya kad'an saboda yanzun yafi bada muhimmanci a soyayyar shi da Saleema, ya zamana a yanzun ta d'auke kaso biyu a rayuwar shi wato budurwa kuma k'awa. Soyayyah suke yi tsantsa irinta Nigerians and hausa by tribe da suka rayu cikin masu jan gashi (turawa), duk da kasancewarta y'ar wata k'asa daban, a kowacce rana kusancin su fin na kullum yake yi suna k'ara samun shak'uwa da fahimtar juna, breakfast, lunch and dinner duk zasu yi tare a plate guda, su yini tare suna baiwa juna labarin ban dariya da d'ebe kewa a wasu lokutan hadda na k'uruciyar su daya gabata. Sai dai duk wannan abun da yake faruwa khaleefa bai tab'a yarda sunyi cud'anyar jiki da juna ba, so yake suyi soyayyar su mai tsabta da bazata lalata musu zamantakewar aure ba nan gaba. A yanzun khaleefa yasan wacece Saleema ciki da bai, har yana gaisawa da wasu cikin familyn ta a waya ma.
Saleema Omar asalin ta y'ar k'asar Niger ce garin zinder, mahaifinta shahararren d'an siyasa ne daya keda kud'i da k'arfin iko, su biyu kawai iyayen su suka mallaka a duniya, daga ita sai k'anwarta da take matakin secondary a k'asar su. Iyayen ta suna matuk'ar ji da ita, hakan yasa suka amince da tahowarta Germany karatu ba don ransu na soba. Suna bata goyon baya a karatun ta kuma suna sakar mata kud'i bana wasa ba don taji dad'in yin karatu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Ta b'angaren alak'ar ta da khaleefa bil hak'k'i take son shi da zuciyarta d'aya, hakan yasa ta bada attention d'inta duka kanshi fiye da sauran samarin da tayi a baya.
Duk da kasancewarta sangartacciyar y'ar masu kud'i amma ta samu kulawa da tarbiyyah mai kyau daga iyayenta duka biyu. Hakan ya taka rawar gani wajen sa ta yin takatsantsan da samarin banza da gujewa sharholiyar k'awaye, macece mai matuk'ar aji da k'afulle inba khaleefa ba ba wani namiji data tab'a sakewa har ya shigar mata d'aki kota je mishi da sunan soyayyah ballantana har taji tana son ya bata abinci da hannun shi a baki.
Wannan kenan.
★★★★★
Misalin k'arfe sha d'aya na daren ranar alkhamis, khaleefa ya futo shirye cikin English wears, rigar bak'a ta sanyi mai kauri ya zame hular ta sauka k'eyar shi, sai zaren mad'aurin rigar guda biyu da suka futo ta y'ar k'aramar hudar gaban rigar. Dogon crazy trouser daya d'ame k'afar shi ta k'asa shima bak'i sai socks ta hannu da k'afa. Daga yanayin yadda yake tafiya yana d'age k'afad'u zaka gane sanyin da ake a garin yana matuk'ar ratsa jikin shi.
Direct motar haya ya tare, yayi locating inda zashi. Bayan tafiyar adadin wasu mintuna aka sauke shi gaban wani k'aton mall an rubuta sunan shi daro daro a jikin sunan haske na blinking a cikin duhu *BAYSHORE MALL* a nutse cikin tafiyar shi ta nutsuwa da nuna cikar kamala ya shiga ciki, bai jima sosai ba ya sake futowa rik'e da kwalin siyayya guda biyu, ya k'ara hawa motar da zata mai dashi gida.
Dai dai k'ofar shiga apartment d'insu ya sauka ya shiga ciki da sauri.
K'ofar d'akin shi ya bud'e da hanzari ya shiga, ya cire takalmin shi da socks na hannu, agogo ya duba, he still have 15 mint left, murmushin gefen baki yayi ya d'auko wayarshi da wasu sink'in flowers White and red masu shegen kyau da k'amshi, wani tsadadden zobe ya ciro mai kyau da d'aukar hankali ya had'a kusa da flowern, da wani round kwali na wata Choco. Bathroom ya shiga a gurguje ya sake shiri cikin wasu kayan daban da suka fi wad'an can kyau da d'aukar hankali. Ko'ina na d'akin azababben k'amshin shi ke tashi mai bala'in dad'in shak'a.
Wayar shi ya duba 5 mint left to 12. Text ya yima Saleema kamar haka, "hope ba kiyi bacci ba, I'm on mie way, coming to express my love to you on dis very day of your birthday Saleema".
Seconds kad'an da tura sak'on reply ya dawo kamar haka, "bazan tab'a iya bacci ba tare dana bari ka cika alk'awarin ka na tayani murnar k'arin shekara ba, Ina jiranka hope kana duba lokaci dai". Murmushi ne yayi escaping kan lips d'in shi a lokacin da ya gama karanta sak'on Saleema. "I promise I will be at your door at exactly 12:00 am".
Ta k'ara mishi reply da, "I will definitely open my door room at exactly dat time u mention". Girgiza kai yayi ya duba lokaci again, 3 mint left.
Rufe k'ofar shi yayi hannun shi rik'e da tulin abubuwan daya shirya kai mata as birthday gift, sai dai ya b'oye hannun a baya, sai wanda yake rik'e da wayar shi ne kad'ai a gaba yana typer wani abu. Opposite to d'akin Saleema ya jingina yana duba lokaci, at 12 am as he promise ya tura mata da sak'on "barka da zagayowar ranar haihuwar ki Mrs Abdallah (khaleefa)".
Bud'e k'ofar akayi a lokacin da sak'on ya tafi, Saleema ce tsaye daga ta ciki sanye da wata had'ad'd'iyar gown fara sol, yadin ta mai sulb'i yabi jikinta ya lafe. Rigar tun daga wuyanta har zuwa hannayenta shara sharan farin net ne daya bayyana farar fatarta mai d'aukar ido, yayin data bayyana saman k'irjinta kad'an a waje. Gashin kanta kuwa anyi mishi wani irin gyara da farin bit masu kyalli, fuskarta kuma powder ne kad'ai sai lip balm da idonta da tayi lining da bak'i. Ta matuk'ar yi kyau kamar wata amarya.
Ja baya tayi kad'an, hakan ya bama khaleefa damar shigowa ciki tare da tura k'ofar da k'afar shi ya rufe.
Kusan a tare suka k'arasa cikin d'akin har zuwa tsakiya inda suka shirya candle light da cake an rubuta sunanta a tsakiya in passion.
Da wayar shi yayi amfani ya soma haska ta a hotuna a duk wani k'aramin motsinta, yayi mata pic kala da yawa shi kanshi baisan adadi ba kafun itama ta fara yi mishi da wayarta, a k'arshe kuma suka had'u don su d'auki kansu selphie, Saleema jikin khaleefa kad'an ta shiga tana d'aukar su, saida khaleefa yaji shock yaja jikin shi baya kad'an. Had'e face tayi tace, "common". Ta k'ara zagayowa ta gefen shi ta sak'ala hannunta ata wuyan shi d'aya kuma ta d'auki hoton dashi, da saleema zata lura a lokacin khaleefa is totally in some where saboda yadda ta shiga jikin shi make him feel some how. Sai da ta gama yin hotunanta in different style sannan taja hannun shi suka koma gurin cake in.
Ta hure wutar cake d'in yana mata video, a hankali cikin nutsuwa ta yanko madaidaicin cake ta nufi bakin shi dashi gently, kauda kai khaleefa yayi ya tura wayarshi aljihu ya matso kusa da ita gab, ya sak'ala hannun shi a gadon bayanta yana kallon cikin kwayar idonta, itama shi take kallo cike da so har lokacin hannunta rik'e da gutsiren cake d'in data yanko, bud'e mata bakin shi yayi kad'an ta zura mishi cake d'in a ciki ya gutsira ya saka mata ragowar a bakinta. Bakin shi ya kai saitin kunnenta ya soma yi Mata magana cikin whisper, "May this birthday just be the beginning of a year filled with happie memories, wonderful moments and shining dreams, also wish you long life and prosperity, happie birthday once again Saleema Omar, Mrs Abdallah khaleefa in future".
Saleema tsabar farin cikin data shiga data rasa yadda zatayi sai kawai ta soma yi mishi dariya.
Yayinda ya tsaya kamar wani gaula yana kallon jerarrun hak'oran bakinta da suke haske shi kamar camera flash.
Kafun ya kamo hannunta ya mayar da ita inda ya ajiye kayan hannun shi. Kamo yatsar hannunta yayi ya murza sannan ya zira mata zoben gold mai d'an karan kyau a yatsarta ta tsakiya, ya kai hannun bakin shi ya bata peck da ya sata lumshe ido ba tare data shiryawa hakan ba. Flower ya d'auko itama yasa mata cikin hannunta. Ta kai flower saitin hancinta ta shak'i wani daddad'an k'amshi da suke yi, cikin matuk'ar jin dad'i da yabawa da kyautar masoyinta tare da tunanin abinda zata bashi tukuici ta tafi da gudu ta rungume shi kam kam cikin sanyin muryarta tace, "I love you Abdallah, I love you... Moreeee".
Shima rik'e ta yayi sosai tare da d'ora kanshi cikin gashin kanta ya saki mata wani kiss d'in.
Sun jima a haka kamar kar su rabu da juna kafun a hankali su janye jikin su. Murmushi da ajiyar zuciya khaleefa ya sauke a tare, yadda jikin shi yayi weak ya assasa mishi zama kan sofa bayan ya d'auki kyauta ta uku. Duka abubuwa ukun nan abu ne da yasan Saleema tana matuk'ar so.
Adana flowers d'in tayi bayan tayi pic rungume dasu, tayi switch up d'in wayarta duka sannan ta dawo inda yake zaune yana duba lokaci a wayar shi. Kwalin hannun shi ya mik'a mata, "oya take your Choco".
Da sauri ta amshi kwalin ta soma kiciniyar bud'e shi har Allah ya bata sa'a ta ciro wani guda d'aya takai bakinta, saida ta lumshe ido zak'i da dad'in sweet d'in na kaiwa har cikin brain d'inta. Ajiye kwalin tayi gefe ta zari wata ta nufi bakin khaleefa da yake zaune yana kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa farat d'aya.
Kan jikin shi ta hau ta tura shi baya har saida kanshi ya jingina da jikin bango sannan ta zura mishi a baki, har hannunta ya had'a yana tsotsa, yayinda suke kallon juna ido cikin ido. Saleema ce ta fara bin yatsunta biyu da suke cikin bakin shi da kallo har lokacin kafun ta zame a hankali tana sake kallon su kamar me nazarin wani abu, saukar electric shock da taji a wuyanta yasa ta maida duban ta gare shi cikin son sanin abinda ya aikata tana kallon kwayar idon shi, wani kiss d'in ya sake mata wanda yasa ta jin viberate oll over her body. Kafun ta farga ta fahimci takamaiman abinda yake yi sai jin lips d'inshi tayi cikin nata yana bata wani irin passionate kiss mai tafiya da gangar jiki da ruhi, at the first time da suka tab'a tsintar kansu cikin yanayin su duka daga ita har shi.
Saleema Cikin tafiya duniyar emotions ta soma shafa gadon bayan shi zuwa k'eyar shi tana k'ara shigewa jikin shi sosai.
Shikam Cikin zaucewa ya fara yin k'asa da hannun shi yana shafa ilahirin jikinta da salo na musamman. Wani irin light romance ya dinga binta dashi cikin lura da kiyaye inda hannun shi ke zuwa🙈
At that moment they have gone somewhere, Saida suka d'auki a k'alla tsayin wasu mintuna kafun su tsagaita da abinda suke yi ba don bin umarnin zuciyoyin suba sai don su kiyaye kada su zurma jiki da yawa. A hankali Saleema ta sauka daga jikin shi ta zauna k'asan k'afar shi tare da kwantar da kanta jikin k'afar.
K'asa yayi da kanshi ya kira sunanta cikin sanyin murya, "Saleema". "uhm?". Ta fad'a can k'asan mak'oshi, "Ina sonki Saleema, Ina sonki da yawa fa". Tana murmushi itama tace, "nima Ina sonka khaleefa so mai tsanani da yake bani tsoro a duk ranar da akace watanni biyun da suka rage maka sun cika zaka koma k'asar ku ka barni anan cikin kad'ai ci da tunanin ka".
Saukowa k'asa yayi ya zauna a gaban ta ya tankwashe k'afafun shi, "kada ki k'ara irin wannan tunanin Saleema, ko na koma Nigeria gangar jikina ce kawai zata kasance a can amma ruhina da zuciyata zasu kasance a nan tare dake, sannan na fad'a miki bada jimawa ba zan gabatar da soyayyar mu aje har zinder a nema mun auren ki, zan dawo aiki tare da Doctor raazee d'an asalin k'asar ku, k'ark'ashin andal. Kinga sai muci gaba da zaman mu kina ci gaba da karatun ki bayan auren mu". Shafo fuskar shi tayi da hannunta na dama tana kallon shi still tace, "toh amma futurehus kana sane da har yanzu baka gabatar mun da kanka ba kuwa? Bayan ni na gabatar maka da kaina tuntuni".
Fuskarta ya rik'e cikin tafin hannun shi yace, "Ina sane Saleema insha Allah soon zaki san waye ni wata d'aya kafun na bar Berlin". Ya k'arasa fad'a yana murza hannunta mai taushi da laushi.
Light kiss ya Kuma sake mata kafun ya mik'e, "Cherie please ka kwana kawai a nan" Saleema ta fad'a cikin shagwob'a. Shiru yayi yana nazari kafun yace mata, "zai je yayi Shirin kwanciya saiya dawo". Har k'ofa ta raka shi ya tafi kamar kar ya rabu da ita, itama haka take ji sai dai babu laifi tunda yanzu zai dawo su kwana tare. Wani irin tsalle ta daka tana tuna romantic scene d'insu na yau, bayan duk wasu abubuwan data gama gani tare dashi at the end ya iya soyayyah k'arshe haka ashe.
Shikam khaleefa bayan mintuna k'alilan shiryawa yayi cikin fararen kayan bacci masu taushi. Sai da yayi nafila raka'a biyu ya rok'i Allah akan soyayyar shi da Saleema sannan ya d'auki wayar shi da key ya futo.
Lokacin daya koma itama ta shirya cikin nightgown iya gwiwa mai kauri hawa biyu, hakan yasa ba'a iya gani jikinta sosai, ta d'ora k'aramin bak'in hijab