Showing 72001 words to 75000 words out of 288773 words
Chapter 25 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
sauk'i Auntie yanzu haka kaina ciwo yake".
D'an zaro ido tayi kad'an tace, "ba kyau cewa ba sauk'i a ciwo fa! Yanzun ka tashi kasha magani zaka ji relief insha Allah".
"Bar maganin nan auntie kawai, wai kina samun khaleefa a waya kuwa?". "Ya za'a bar maganar magani zai yiwu kuwa? Toh ni bazan saurare kaba har sai ka sha koda paracetamol ne, dama zuwa gobe ka shirya muje kaga likita".
Shagwob'e fuska yayi ya mik'e, "zansha maganin amma don Allah ki fad'a mun kina samun khaleefa a waya?". Itama mik'ewar tayi tace, "eh Ina samun shi amma ba koda yaushe yake d'agawa ba". Ayman shiru yayi ya k'urawa guri d'aya idanu kafun can ya nisa yace, "Auntie can't you see khaleefa is changing gradually?". Auntie tace, "Anya kuwa? He's busy dai gaskiya these days saboda k'aratowar bikin kammala 2 years course d'in su, baya ga haka ni banga wani sauyi daga gare shiba". Jiki a sanyaye Ayman yace, "toh Allah yasa". Tare suka k'arasa har ma'ajiyar first aid box ta bashi magani yasha, ya kishingid'a na mintuna k'alilan kafun kiran sallar magrib ya tashe shi. Sai daya sauya kayan jikin shi sannan ya futa masallaci, a k'ofar gidan su yau yayi zaman shi yana kallon mutane masu hucewa har akayi isha'i ya koma masjid ya sauke farali sannan ya koma cikin gida.
Haka kurum yake jin kanshi cikin damuwa ba tare dashi kanshi yasan kota meye ba, yadda khaleefa ya watsar dashi baya neman shi haka shima yayi mishi, raihana kuwa ko kira tayi baya d'aga wayarta tuni ya haramtawa kanshi, Nur ma da yake jinta maganin unknown damuwar shi kwana biyu ya saurara da kiranta a waya akai akai, ko wayar sukayi ma baya doguwar hira suke yin sallama.
★★★★★
B'angaren su raihana suna ta shirye shiryen su na biki, kowa ya fara sakin jikin shi ana al'amuran biki saboda har invitation card ma sunsa a buga tunda bikin yanzu ten days ya rage.
Amarya raihana kam an fara shan gyara gurin wata kwararriyar mai gyaran jikin matan gida dana amare, shagon ta yana opposite orthopedic hospital dake gwammaja, (domin son turaren wuta na amare da kuma naku matan gida, gyaran jiki lungu da sak'o maza ku hanzarta baitul aroos ku futo kuna zunbud'a k'amshi na d'aukar hankalin me gida, ga duk wanda yake so sai tayi contacting d'ina ta no wayata kamar haka 08134288477)
Babu inda take zuwa daga gida sai shagon gyaran jiki, dama kuma ita d'in ba ma'abociyar gantali bace, Imran ma ta dakatar dashi da zuwa saboda bata son ya dinga ganinta don bazai ga kyawun gyaran jikin ba kamar in aka kammala gaba d'aya. Alak'ar ta da Ayman kuwa tuni ta ajiyeta a gefe tunda ta tabbatar k'ararriya ce da zarar an d'aura auren ta da Imran, shiyasa take ta yak'i da zuciyarta, in aka kwana biyu dai takan kira shi a waya saboda kar yaga don zata yi aure ta watsar dashi, kuma tunda ta kira biyu uku taji be picking ba bai biyo kiran daga baya ba, bata sake kiran shiba ta kyale shi.
Ranar wata asabar tana kwance da safe tana bacci saboda ta tashi bata jin dad'in jikinta gaba d'aya, shiyasa tana gama aikinta na safe ta koma ta sake kwanciya, tana tsaka da baccin wayarta ta tashe ta da ringing, tana dubawa taga Imran ne, da hanzarinta ta mik'e ta d'auki wayar ta kara a kunnenta, cikin murya k'asa k'asa yake mata magana, "babyy bani da lafiya fa Ina kwance hospital an bamu gado". Saida gabanta ya fad'i ta mik'e zaune dirshan tace, "da gaske baka da lafiyaa ko dai zolayana kake dear". D'an tari yayi cikin sark'ewar murya yace da gaske Ina kwance wallahi, matsanancin ciwon ciki da zazzab'i". Sai taji hankalinta ya tashi, ta gigice tana tambayar shi ya jikin naka fatan dai akwai sauk'i ko?
"Kwantar da hankalin ki raihanata shiyasa tun jiya nace kar a fad'a miki saboda kada ki tashi hankalin ki da yawa, amma yanzu jikin da sauk'i doctor yace zan d'an zauna tsawon kwana biyar ne kawai, kinga still dai za'a d'aura auren mu kwana hud'u bayan futowa ta hospital".
Cikin tausayin shi raihana ta mishi addu'ar samun sauk'i suka yi sallama, daga nan bata sake kwanciya wani bacci ba ta mik'e ta futo parlon su, ummie ce kad'ai a gidan tana waya da ummaaa mahaifiyar ta su muhibba duk sun tafi makaranta, Zama tayi gefenta tayi shiru tana tunanin ta inda zata soma tambayarta abinda Imran ya fad'a mata, ummie kuwa bayan ta ajiye wayar tab'a gefen wuyanta tayi tace, "jikin ki har yanzu da zafi kad'an raihana, ki karya yanzu sai kisha magani" tace "toh ummie" sun sake yin shiru kafun ummie tace, "kinsan Imran yana asibiti kuwa?". "eh yanzu yake fad'a mun amma yace jikin nashi ma da sauk'i". Ummie tace, "toh Allah ya k'ara sauk'i wai poisoning d'inshi akayi jiya, yanzu haka bincike suke yi, an tabbatar a abinci aka sa mishi gubar, amma an kasa fahimtar wanda ya aikata hakan, jiya ai mahaifin shi yazo gurin abban ku ya nemi alfarmar a d'an k'ara bikin zuwa nan da wasu sati biyun masu zuwa, kafun nan sunyi settling komai ta daga b'angaren su".
Ita dai raihana bata ce komai ba, abun ya matuk'ar bata tsoro wai anyi poisoning d'inshi a abinci, Allah sarki watak'ila kada hankalinta ya tashi shiyasa yace mata ciwon ciki da zazzab'i.
Washe garin ranar ummie tasa suka shirya ita da hapser da zainab (y'ay'an yayarta) aka tanadi kayan dubiya suka je suka ga jikin nashi, yana kwance baya iya ko tashi zaune amma bakin shi rad'au duk da ba wai doguwar magana yake iyawa ba har yanzu. Mahaifiyar shi hajiya tafeeda ko kallon su bata yiba bare amsa gaisuwar su, sai y'an uwan tane suka amsa da kuma Imran d'in da yake ta kallonta kamar yaga bak'uwar halitta.
A d'arare dai ita kam raihana take, har suka gama d'an zaman su sukayi musu sallama suka koma gida.
************
Auntie ta d'auki hutun sati biyu saboda tafiyarta Germany, Ayman ma hutun k'arshen shekarar shi yazo dai dai da tafiyar da auntien zatayi, hutun wata guda ya samu.
Tuni auntie tayi musu booking ticket ta shirya musu yadda tafiyar zata kasance, kwana biyu kawai zasuyi su taho har khaleefan. Mishkila guda da aka samu washe garin taron zasu sauka k'asar.
*Germany*
Saleema ce zaune a k'asan d'akinta ta zubawa Amna da take aikin pressing kayanta ido, Amna ganin Saleema sai kallonta take kamar taga wata bak'uwar halitta sai ta dawo gabanta ta zauna dirshan tace, "nasan dai akwai magana a bakin nan naki". Doguwar ajiyar zuciya Saleema taja, "Ina nan Ina tunanin yadda kullum kike yaudara ta ba tare da kin nemo mun mafutar da kika ce zaki nemo mun ba har gashi khaleefa yana gab da barin Berlin.........". Murmushi Amna ta k'ak'alo tace, "ki kwantar da hankalin ki Saleema nifa nayi miki alk'awari, toh kuma me kike ci na baka na zuba? Akwai abinda na shirya wuyarta na had'u da khaleefa ne kici gaba da addu'a kurum, insha Allah khaleefa mallakin kine k'awata". Saleema sai taji d'an sanyi sanyi a ranta tace, "toh Allah ya yarda".
Khaleefa kuwa sun gama hattama komai, a ranar litinin k'arfe 3:00pm dai dai aka basu kwalin su da cikakkiyar shaidar kammala course na musamman akan physiotherapy, Alhamdulillah shine abinda su khaleefa suke ta maimaitawa don nuna godiyar su ga Allah bisa nasarar da suka samu a wannan karon ma. Dukkan su suna sanye da black trouser da white shirt sai LC a sama, basu wani yi dogon taro na kuzo mu gani ba suka gama duk abinda zasuyi isu isu suka kama gaban su, Khaleefa suna tare da zab'ab'b'u bakwai da zasuyi aiki tare da Doctor raazi bisa jagorancin matashiyar balarabiyar k'asar Sudan doctor Fatima. Basu futo meeting ba ranar har sai kusan yamma. Aikuwa suka futo a gajiye lis, LC d'in ma sai a hannu yake rik'e da ita. Suna tafe suna tattaunawa su uku har suka k'arasa wani gurin shan coffee na kusa da inda suka futo, hot coffee kawai suka sha suka futo a nan Muhammad course mate d'insu yayi musu sallama ya huce.
Su kuma suka nufi masaukin da uncle d'in Ahmad yake, sun same shi lafiya sun gaisa shima ya taya su murna matuk'a, ya yaba musu kuma musamman wajen jajircewar da suka nuna da bada himma akan karatun har suka futa da wannan sakamakon.
A gurin shi sukayi sallar magrib da isha'i, sannan khaleefa ya musu sallama ya tafi don ya basu guri ko suna da sirrin da zasu tattauna tsakanin su.
Tafiya yake gently bayan ya futo daga mota har ya k'arasa ginin da apartment d'insu yake ciki.
Kamar a mafarki haka ya tsinci Saleema jingine da k'ofa kwayar idonta na kallon sararin samaniya, ga dukkan alamu ta jima tana jiran shi a gurin.
Tsayawa yayi daga gefenta ya fuskanci gaban d'akin ya hard'e hannuwan shi a k'irji yana jiran yaji da wadda tazo, ganinta kawai da yayi yanzu saida gaban shi ya fad'i. Ita kanta Saleema gabanta faduwar yayi musamman da taga fuskarshi a d'aure kamar khaleefan data sani watanni da yawa baya, tana tsoron kada ya zam da gaske khaleefa ya yanke hukuncin barinta har abada kamar yadda ta buk'ata da farko, da batasan ya zatayi da rayuwarta ba. Khaleefa kuwa da d'aurarriyar fuskarshi yace, "ya akayi Saleema? Ko akwai wani abu da kika manta baki goranta mun ba kika zo first to first ki k'arasa gorantawa ki tafi?". Shiru tayi jikinta ya d'au b'ari, murmushi yayi yaci gaba da maganar shi, "Saleema a yadda na d'auke ki da irin matsayin dana baki a rayuwata sam ban d'auka zaki iya juya mun baya irin yadda kika yiba, na d'auka soyayyah tana nufin yarda da karb'ar masoyi a duk yadda yazo mai kyau ko akasin haka, tunda ba koman shi kike so ba shi d'in kad'ai kike kallo abokin rayuwa a tare dake, ke dai fatan ki ya kasance kin gyara komai kun rayu cikin so da k'auna....... Koda yake kin fahimtar dani abubuwa da yawa da tunani na ya kauce daga kansu, zanje nayi bincike akan asalina Saleema, sannan zan dawo don na baki mamaki". Zoben azurfar dake hannunshi irin nata ya zare ya dank'a mata a hannunta yana kallonta da idonunshi da suke cike da sonta da k'aunar ta yace, "Zan dawo miki da soyayyar ki kamar yadda na karb'a, amma fa ki sani bada jimawa ba zan dawo irin dawowar da zata banbance tsakanin Aya da tsakuwa, bada sunan khaleefa ba, da sunan Abdallah Suraj Abdallah Tofa, a lokacin nake son ki amsa sunan Mrs Abdallah, good bye". Khaleefa yana gama maganar shi ya kewayeta ya shige d'akin shi bai bata dama ko kad'an da zata iya furta wani abu ba.
Haka Saleema taja k'afafun ta da suke rawa ta bar gurin tana kuka, ta kasa fassara kalaman khaleefa a yau, Inta fassara kalmomin shi na k'arshe yana nufin zai aure ta kenan? Toh amma idan har haka yake nufi me yasa zai ce ya dawo mata da soyayyar ta kamar yadda ya karb'a?
Wannan kalmomin dunk'ulallu guda biyu sun d'aure mata kai kwarai har ta kasa zama data koma apartment d'inta, ganin zata cazawa kanta lissafi ba tare data fahimci komai ba, sai ta d'auko gyalenta tayi gurin Amna.
Amnan ma bata nan amma ba nisa tayi ba tana kiran wayarta ta hallara a gurin, ko data bud'e k'ofa suka shiga kasa zama tayi sai safa da marwa kurum da take tana share ruwan hawaye, da kyar Amna ta shawo kanta ta bata labarin komai da khaleefa ya fad'a, ita kanta Amna kanta ya kulle, a iya y'ar hausar data iya bata ga gurbin da zata ajiye wad'an nan maganganu ba. Daga k'arshe sai suka ajiye khaleefa da maganganun shi masu d'aurin goro gefe suka fuskanci abinda yake gabansu Amna na dad'a kwantar mata da hankali.
Khaleefa kanshi ganinta ba k'aramin Miki ya sake tado mishi ba, sai ya zauna kawai yana tunanin maganar da doctor raazi ya fad'a mishi a lokacin daya tashi ciwon nan, kasancewar doctor raazi mutum mai saurin fahimtar halin da mutum yake ciki, bugu d'aya ya fassara damuwar shi da matsalar soyayyah, hakan yasa ya bashi shawarwari a lokacin "a kowacce soyayyah akwai gwagwarmaya a cikinta, duk soyayyar da babu k'alubale bata cika soyayyah ba, ka karb'i rayuwa a yadda tazo maka Abdallah sai kaga ka zauna lafiya da zuciyarka, ka cire ta daga zuciyarka ba don ka rabu da ita ba ko ka daina sonta, a'a sai don kaji dad'in gano bakin zaren da zaka d'ago, ka fuskanci duk abinda ya tunkaro ka da iya k'arfin ka, sai kaga kaci galaba akan komai cikin sauk'i kuma ka samu masoyiyarka a k'arshe". Wani irin murmushi ne ya wanzu saman fuskarshi ya tsaya kurum yana hasaso fuskar Saleema a lokacin daya bata zobenta, ya tabbatar har gobe tana sonshi itama, wannan zaisa ba zata tab'a karb'ar soyayyar wani ba har zuwa lokacin da komai zai tafi mishi yadda yake so ya nemi aurenta su rayu tare.
@@@@@@
Auntie ce zaune kan carpet kusa da iya, malam na zaune daga can gefe yana sauraron surayyah har ta gama bayanin ta kafun yace, "kwana biyu zaku yi kenan sai ku taho tare dashi?". Surayyah tace, "eh insha Allah". Malam yace, "toh madallah! Allah ya tsare ya kare ya kiyaye hanya, ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya". Cikin jin dad'i auntie ta amsa musu da "ameen". Sun sake tattauna muhimman batutuwa dasu ciki harda tsayar da ranar auren Ayman da Nur da zarar khaleefa ya dawo da kwanaki, so take auren kada ya d'au lokaci da tsayi, don a tafiyar da tayi kwanaki tuni ta fara had'a kayan lefe a b'oye, gida kuma bata da matsala zasu zauna tare da ita zuwa wani lokaci, (da yake a gidanta akwai babban part da yake rufe ba'a tab'a bud'e shi bama, sama da k'asan duk iri d'aya ne anyi mishi gini irin na zamani me kyau, a ra'ayinta, kowa zai zauna a part guda ne cikin su, don bata son suyi nesa da ita) malam baice mata komai ba sai iya ce take tambayar ta, "surayyah kuma kina ganin ba matsala sameera zata baki duka yaranta biyu ki aurawa yaranki?".
Ko kad'an surayyah bata kawo komai a kanta a duk lokacin da akayi maganar sameera k'awar ta, tana ganin don basu san sameera bane shiyasa take kawo irin wannan tunanin a kanta. "da amincewarta muka shirya komai iya, insha Allah ba za'a samu wata matsala ba, in ma an samu toh daga khaleefa ne, don shine yake da baud'ad'd'en ra'ayi, amma Ina fata shi d'in ma ya amince don shaheeda bata da makusa tako Ina".
Iya ta rausayar da kai tace, "toh Allah yasa!".
Bata jima ba tayi musu sallama ta kira no Ayman da tunda suka zo bata ga inda ya wulla ba.
Shi kuwa Ayman yana tsaye k'ofar gidan iya yana kallon gidansu raihana tamkar zai ganta ta futo, ji yake kamar ya kirata ta futo ya ganta ko yaji sauk'in bak'on abinda yake ji game da ita, zuciyar shi azalzalar shi kawai take da son ganinta, da ganin a wane hali take. Tunani ya fara tun daga lokacin da suka fara shiri da ita har zuwa yadda ta dinga girma suna tafiyar da alak'ar su cikin mutumci da mutunta juna, har kawo yau da ta zama babbar budurwa ake maganar aurenta, d'aya bayan d'aya haka memories d'innan suka dinga wulgawa ta cikin kwakwalwar kanshi. Sai yaji wani abu mai kama da mashi ya cake shi a k'ahon zuciya, dafe saitin gurin yayi had'i da lumshe idon shi ya bud'e lokaci guda yana karanta duk addu'ar da tazo bakin shi, a haka wayarshi tayi ring, ganin auntie ce sai baiyi picking ba ya nufi cikin gidan direct ya shiga da sallama.
Duk suka amsa mishi suna kallon yadda yake tafiya da jiki a sanyaye, kusa da malam ya zauna. Dafa kanshi malam yayi yace, "ya zaka ware kanka a waje Ayman bayan ka jima rabon mu dakai? Ai ya kamata kazo muyi hirar yaushe gamo ko?". Murmushi kawai yayi baice komai ba sai Auntie ce tace, "ai ganin shi nake kwana biyu ma kamar baya jin dad'i". Iya zatayi magana ya tari numfashinta da sauri da fad'in.........
_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page twenty one2️⃣1️⃣
"Kawai rashin hutu ne iya, amma tunda na samu hutun wata d'ayan nan nasan zan dawo normal insha Allah". Iya tana k'ara nazarin shi tace, "Allah yasa". Daga nan basu kuma doguwar hira ba sukayi sallama dasu malam suka tafi, a motar shi suka zo yanzun a ita suka koma shiya jasu ma. Suna tafe auntie na mishi hirar da sam ba fahimta yake ba har suka k'arasa gida, shi ya futa ya bud'e get